Ƙage Na 2: Miyagu Suna Shan Azaba Cikin Wutar Jahannama
Menene tushen wannan ƙagen? “A cikin dukan ’yan ussan ilimi na Hellenanci, wanda ya fi tasiri a kan koyarwar wutar jahannama na Plato.”—Histoire des enfers (The History of Hell), na Georges Minois shafi na 50.
“Tun tsakiyar ƙarni na biyu A.Z. Kiristoci da suke da wasu koyarwa daga ussan ilimi na Hellenanci suka soma ganin amfanin bayyana imaninsu cikin jituwa da abin da aka koya musu . . . Ussan ilimi da ya fi dacewa da su shi ne Platonism [wato, koyarwar Plato].”—The New Encyclopædia Britannica (1988), Volume 25, shafi na 890.
“Koyarwar Cocin ta tabbatar da wanzuwar wutar jahannama da dauwammarsa. Ba da daɗewa ba bayan mutuwa, kurwar waɗanda suka mutu saboda zunubi za su shiga cikin wutar jahannama, wurin da za su sha azabar wutar jahannama, ‘wutar har abada.’ Ainihin azabar wutar jahannama ita ce rabuwa da Allah har abada.”—Catechism of the Catholic Church, bugun 1994, shafi na 270.
Menene Littafi Mai Tsarki ya ce? “Gama masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san komi ba, . . . gama babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.”—Mai-Wa’azi 9:5, 10.
Menene wannan ya nuna game da halin da matattu suke ciki? Suna shan azaba ne a wani wuri don su nemi gafarar zunubansu? A’a, domin “ba su san komi ba.” Shi ya sa sa’ad da uban iyali Ayuba, yake shan wahala saboda ciwo mai tsanani, ya roƙi Allah: ‘Ka ɓoye ni cikin kabari.’ (Ayuba 14:13) Kalamansa sun nuna cewa “kabari” ba wurin azaba ba ne amma yana nufin kabarin dukan ’yan Adam, wurin da dukan ayyuka suke ƙarewa.
Amma, wane irin laifi ne, ko da menene tsananinsa ne zai sa Allahn ƙauna ya ƙona mutum har abada? (1 Yohanna 4:8) Amma idan wutar jahannama ƙage ne, yin rayuwa a sama ita ma ƙage ne kuwa?
Ka gwada waɗannan ayoyin Littafi Mai Tsarki: Zabura 146:3, 4; Ayyukan Manzanni 2:25-27; Romawa 6:7, 23
GASKIYA:
Allah ba ya ƙona mutane a cikin wutar jahannama
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 11]
Barrators—Giampolo/The Doré Illustrations For Dante’s Divine Comedy/Dover Publications Inc.