Menene Addu’o’inka Suke Nunawa Game Da Kai?
“Ya mai-jin addu’a, a gareka dukan masu-rai za su zo.”—ZAB. 65:2.
1, 2. Me ya sa bayin Jehobah za su yi addu’a a gare shi da tabbaci?
JEHOBAH yana jin roƙe-roƙen bayinsa masu aminci a koyaushe. Ya kamata mu kasance da gaba gaɗi cewa yana sauraronmu. Ko da miliyoyin Shaidun Jehobah sun yi addu’a ga Allah a lokaci ɗaya, babu wanda Allah ba zai ji addu’arsa ba.
2 Da yake yana da gaba gaɗi cewa Allah ya ji roƙe-roƙensa, mai zabura Dauda ya rera: “Ya mai-jin addu’a, a gareka dukan masu-rai za su zo.” (Zab. 65:2) An amsa addu’o’in Dauda domin ya bauta wa Jehobah da aminci. Ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Addu’o’ina suna nuna cewa na dogara ga Jehobah kuma bauta ta gaskiya ita ce damuwata ta musamman? Menene addu’o’ina suke nunawa game da ni?’
Ka Yi Addu’a ga Jehobah Cikin Tawali’u
3, 4. (a) Sa’ad da muke addu’a ga Allah, wane hali ne ya kamata mu kasance da shi? (b) Menene ya kamata mu yi idan ‘tunani’ game da zunubi mai tsanani da muka yi yana damunmu?
3 Idan muna son a amsa addu’o’inmu, dole ne mu yi addu’a ga Allah cikin tawali’u. (Zab. 138:6) Ya kamata mu roƙi Jehobah ya bincika mu, yadda Dauda ya yi sa’ad da ya ce: “Ka yi bincikena, ya Ubangiji, ka san zuciyata: Ka auna ni, ka san tunanina: Ka duba ko da wata hanyar mugunta daga cikina, ka bishe ni cikin tafarki na har abada.” (Zab. 139:23, 24) Bari mu ci gaba da yin addu’a kuma mu miƙa kanmu ga binciken Allah da kuma shawarar da ke cikin Kalmarsa. Jehobah yana iya yi mana ja-gora a “cikin tafarki na har abada,” kuma ya taimaka mana mu biɗi tafarkin da zai sa mu samu rai madawwami.
4 Idan ‘tunani’ game da zunubi mai tsanani da muka yi yana damunmu kuma fa? (Karanta Zabura 32:1-5.) Yin ƙoƙarin danne lamirin da ke damunmu yana iya raunana mu kamar yadda itace ke bushewa a lokacin rani. Domin zunubinsa, Dauda ya yi rashin farin cikinsa kuma mai yiwuwa ya yi rashin lafiya. Amma ya samu sauƙi sa’ad da ya faɗi zunubansa ga Allah! Ka yi tunanin irin farin cikin da Dauda ya yi sa’ad da ya ji cewa Jehobah ya “gafarta masa laifinsa.” Faɗin zunubi ga Allah yana iya kawo sauƙi, kuma taimakon da za a samu daga dattawa Kiristoci zai sa mutumin da ya yi zunubin ya sake soma dangantaka da Jehobah.—Mis. 28:13; Yaƙ. 5:13-16.
Ka Yi Roƙo ga Allah Kuma Ka Gode Masa
5. Menene ya kamata mu yi sa’ad da muke alhini sosai?
5 Idan muna alhini sosai domin wani dalili, ya kamata mu bi shawarar Bulus: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.” (Filib. 4:6) Ya kamata mu roƙi Jehobah ya taimake mu kuma ya yi mana ja-gora musamman sa’ad da muke fuskantar haɗari ko kuma tsanantawa.
6, 7. Waɗanne dalilai suka sa ya kamata mu haɗa godiya a cikin addu’o’inmu?
6 Idan sa’ad da muke bukatar wani abu ne kawai muke yin addu’a, menene hakan zai nuna game da muradinmu? Bulus ya ce ya kamata mu yi roƙe-roƙenmu ga Allah “tare da godiya.” Muna da dalilin furta godiya kamar Dauda, wanda ya ce: “Girma, da iko, da ɗaukaka, da nasara, da sarauta, naka ne, ya Ubangiji: gama abin da ke cikin sama da ƙasa duk naka ne; mulki naka ne, ya Ubangiji, ka ɗaukaka kuma bisa kan kome. . . . Ya Allahnmu, muna gode maka, muna yabon sunanka mai-daraja.”—1 Laba. 29:11-13.
7 Yesu ya gode wa Allah domin abinci da gurasa da kuma ruwan inabi da suka yi amfani da shi a Jibin Maraice na Ubangiji. (Mat. 15:36; Mar. 14:22, 23) Ban da furta irin wannan godiyar, ya kamata mu ‘yi godiya ga Jehobah’ don “al’ajibansa da ya ke yi wa yan adam,” don ‘hukuncinsa masu-adalci,’ da kuma don kalmarsa, ko saƙo, da ke cikin Littafi Mai Tsarki.—Zab. 107:15; 119:62, 105.
Ka Yi wa Wasu Addu’a
8, 9. Me ya sa za mu yi addu’a domin Kiristoci masu bi?
8 Babu shakka, muna yin addu’a don kanmu, amma ya kamata mu haɗa wasu a cikin addu’o’inmu, har da Kiristoci da ba mu san sunansu ba. Ko da yake manzo Bulus wataƙila bai san dukan masu bi da ke Kolosi ba, ya rubuta: “Muna godiya ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, kullayaumi muna yi maku addu’a, domin mun ji labarin bangaskiyarku cikin Kristi Yesu, da ƙaunarku zuwa ga tsarkaka duka.” (Kol. 1:3, 4) Bulus ya kuma yi addu’a domin Kiristocin da ke Tassaluniki. (2 Tas. 1:11, 12) Irin waɗannan addu’o’in suna nuna ko waɗanne irin mutane ne mu da kuma yadda muka ɗauki ’yan’uwanmu maza da mata masu imani.
9 Addu’o’inmu domin shafaffun Kiristoci da kuma abokansu “waɗansu tumaki” yana tabbatar da cewa muna damuwa game da ƙungiyar Allah. (Yoh. 10:16) Bulus ya gaya wa ’yan’uwa masu bi su yi addu’a ‘domin a ba shi ikon faɗi, don ya sanar da asirin bishara.’ (Afis. 6:17-20) Muna addu’a domin wasu Kiristoci kamar hakan?
10. Yaya yin addu’a a madadin wasu zai shafe mu?
10 Yin addu’a domin wasu yana iya canja halinmu game da su. Idan muka yi addu’a a madadin mutumin da ba ma so, wataƙila hakan zai sa mu canja halin da muke nuna masa. (1 Yoh. 4:20, 21) Irin waɗannan addu’o’in suna da ban ƙarfafa kuma suna ɗaukaka haɗin kai tsakaninmu da ’yan’uwanmu. Ƙari ga haka, irin waɗannan addu’o’in suna nuna cewa muna da ƙauna irin ta Kristi. (Yoh. 13:34, 35) Irin wannan halin sashe ne na ’yar ruhu na Allah. Kowannenmu yana addu’a don samun ruhu mai tsarki ne, muna gaya wa Jehobah ya taimaka mana mu nuna ’yar ruhu kamar ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, da kamewa kuwa? (Luk 11:13; Gal. 5:22, 23) Idan haka ne, furcinmu da ayyukanmu za su nuna cewa muna tafiya da kuma rayuwa da ruhu.—Karanta Galatiyawa 5:16, 25.
11. Me ya sa za ka iya cewa ya dace mu gaya wa wasu su yi addu’a dominmu?
11 Idan muka ji cewa ana jarraba yaranmu su saci amsa a jarrabawa a makaranta, ya kamata mu yi musu addu’a kuma mu yi amfani da Nassosi mu taimaka musu su yi abin da ya yi daidai kuma su guji yin duk wani abin da bai da kyau. Bulus ya gaya wa Kiristocin da ke Koranti: “Muna fa addu’a ga Allah kada ku yi kowace mugunta.” (2 Kor. 13:7) Yin irin waɗannan addu’o’in cikin tawali’u na faranta wa Jehobah rai kuma suna nuna cewa mu mutanen kirki ne. (Karanta Misalai 15:8.) Muna iya gaya wa wasu su yi addu’a domin mu, kamar yadda manzo Bulus ya yi. Ya rubuta: “Ku yi addu’a dominmu: gama mun kawar da shakka muna da kyakkyawan lamiri, muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.”—Ibran. 13:18.
Wasu Abubuwan da Addu’o’inmu Suke Nunawa Game da Mu
12. Waɗanne abubuwa ne ya kamata su zama batutuwa na musamman a addu’o’inmu?
12 Addu’o’inmu suna nuna cewa mu Shaidun Jehobah ne masu farin ciki da kuma ƙwazo? A roƙe-roƙenmu, muna mai da hankali ne musamman ga yin nufin Allah, wa’azin saƙon Mulki, kunita ikon mallakar Jehobah, da kuma tsarkake sunansa? Ya kamata waɗannan su zama batutuwa na musamman a addu’o’inmu, kamar yadda Yesu ya nuna a addu’arsa ta misali, wadda ta soma da waɗannan kalaman: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—Mat. 6:9, 10.
13, 14. Addu’o’inmu suna nuna menene game da mu?
13 Addu’o’inmu ga Allah suna nuna muradinmu, abubuwan da muke so, da kuma sha’awoyinmu. Jehobah ya san ko waɗanne irin mutane ne mu. Misalai 17:3 ta ce: “Tukunya ta tuya domin azurfa, tanderu kuma domin zinariya: amma Ubangiji yana auna zukata.” Allah yana ganin abin da ke zuciyarmu. (1 Sam. 16:7) Ya san yadda muke ji game da taronmu, hidimarmu, da kuma ’yan’uwanmu na ruhaniya maza da mata. Jehobah ya san tunanin da muke yi game da ‘’yan’uwan’ Kristi. (Mat. 25:40) Ya sani ko ainihi muna son abin da muke addu’arsa ko kuma muna maimaita kalmomi ne kawai. Domin mutanen zamaninsa suna da ra’ayin da bai dace ba game da addu’a, Yesu ya ce: “Garin yin addu’a kuma kada ku yi ta maimaitawa ta banza, kamar yadda arna su ke yi: gama suna tsammani bisa ga yawan maganarsu za a amsa masu.”—Mat. 6:7.
14 Abubuwan da muke faɗa a addu’armu suna nuna ko da gaske mun dogara ga Allah. Dauda ya ce: “[Jehobah] mafaka ka ke gareni, hasumiya mai-tsawo kuma inda zan ɓuya wa maƙiyi. Zan zauna cikin tenti naka kullum: zan nemi kāriya cikin inuwar fukafukanka.” (Zab. 61:3, 4) Sa’ad da Allah a alamance ya ‘inuwantar da mu da alfarwarsa,’ za mu more kāriyarsa da kulawarsa. (R. Yoh. 7:15) Abin ƙarfafa ne mu kusaci Jehobah cikin addu’a da tabbaci cewa yana ‘wajenmu’ a duk wani lokacin da muka fuskanci gwajin bangaskiyarmu!—Karanta Zabura 118:5-9.
15, 16. Menene addu’a za ta iya taimaka mana mu fahimta game da muradinmu na samun gatar hidima a cikin ikilisiya?
15 Yin addu’a ta gaske ga Jehobah game da muradinmu tana iya taimaka mana mu fahimci ainihin muradinmu. Alal misali, ɗokin yin hidima a matsayin mai kula tsakanin mutanen Allah, yana nuna da gaske cewa muna son mu taimaka kuma mu yi iyakacin ƙoƙarinmu wajen ɗaukaka al’amura na Mulki ne? Ko kuwa muna son “shugabanci” ne ko kuma mu ‘nuna wa wasu iko’? Ba hakan ba ne ya kamata abubuwa su kasance tsakanin mutanen Jehobah ba. (Karanta 3 Yoh. 9, 10; Luk 22:24-27.) Idan muna da sha’awoyin da ba su da kyau, faɗin gaskiya sa’ad da muke yin addu’a ga Jehobah zai fallasa su kuma ya taimaka mana mu canja kafin su kahu sosai a cikinmu.
16 Mai yiwuwa, mata Kirista suna son mazansu su zama bayi masu hidima kuma wataƙila daga baya su zama masu kula, ko kuma dattawa. Waɗannan ’yan’uwa mata suna iya aikata daidai da addu’o’insu da suke yi na kansu ta wajen yin ƙoƙari su nuna halin kirki. Hakan yana da muhimmanci, domin furci da halin iyalin mutum suna shafan yadda ikilisiya za ta ɗauke shi.
Wakiltar Jama’a a Addu’a
17. Me ya sa kaɗaitawa take da kyau sa’ad da muke addu’a ta kanmu?
17 Sau da yawa Yesu ya janye kansa daga cikin jama’a domin ya yi addu’a ga Ubansa. (Mat. 14:13; Luk 5:16; 6:12) Mu ma muna bukatar mu kaɗaita kanmu. Idan muka yi addu’a a yanayi na lumana, za mu iya tsai da shawarwarin da za su faranta wa Jehobah rai kuma za su taimaka mana a ruhaniya. Amma, Yesu ya kuma yi addu’a cikin jama’a, kuma yana da kyau mu bincika yadda za a yi hakan da kyau.
18. Waɗanne batutuwa ne ya kamata ’yan’uwa maza su tuna sa’ad da suke addu’a a madadin ikilisiya?
18 A taronmu, maza masu aminci suna yin addu’a a madadin ikilisiya. (1 Tim. 2:8) Ya kamata ’yan’uwa masu bi su faɗi “amin” wanda yake nufin “ya kasance hakan,” a ƙarshen irin wannan addu’ar. Amma, don su yi hakan, dole ne su yarda da abin da aka faɗa. A cikin addu’arsa ta misali, Yesu bai faɗi abin ban mamaki ba ko kuma abin da ya ba mutane fushi. (Luk 11:2-4) Bugu da ƙari, bai ambata dukan bukatu ko kuma matsalolin masu sauraronsa ba. Ya dace mutum ya ambata damuwarsa a cikin addu’a na kansa, ba na jama’a ba. Kuma sa’ad da muka wakilci jama’a a addu’a, ya kamata mu guji ambata al’amura na asiri.
19. Yaya ya kamata mu aikata a lokacin da ake addu’a ga jama’a?
19 Sa’ad da ake wakiltarmu a addu’a ga jama’a, muna bukatar mu nuna muna jin “tsoron Allah.” (1 Bit. 2:17) Da akwai lokaci da wurin da ya dace don wasu ayyuka da ba za su dace ba a taron Kirista. (M. Wa. 3:1) Alal misali, a ce wani yana so dukan waɗanda suke cikin rukuni su riƙe hannayensu a lokacin da ake addu’a. Hakan yana iya ɓata wa wasu rai ko kuma ya janye hankalinsu, har da baƙi da ba sa bin imaninmu. Wasu ma’aurata suna iya riƙe hannu cikin dabara, amma idan suka rungumi juna a lokacin addu’a ga jama’a, waɗanda suka ga irin wannan halin suna iya yin tuntuɓe. Suna iya yin tunanin cewa ma’aurata suna mai da hankali ga dangantakarsu ce ta soyayya maimakon bauta wa Jehobah. Domin muna daraja shi, bari mu ‘yi duka abu domin muna girmama Allah’ kuma mu guji halin da zai janye hankalin wasu, ya sa mutane mamaki ko kuma ya sa su yi tuntuɓe.—1 Kor. 10:31, 32; 2 Kor. 6:3.
A Kan Menene Za a Yi Addu’a?
20. Yaya za ka bayyana Romawa 8:26, 27?
20 A wani lokaci, ba za mu san abin da za mu faɗa ba a cikin addu’o’inmu. Bulus ya rubuta: “Ba mu san yadda za mu yi addu’a kamar da ya kamata ba; amma Ruhu [mai tsarki] da kansa yana roƙo dominmu da nishenishe waɗanda ba su furtuwa; shi [Allah] kuma wanda yake binciken zukata ya san ko menene nufin Ruhu.” (Rom. 8:26, 27) Jehobah ya sa an rubuta addu’o’i da yawa a cikin Nassosi. Ya amince da waɗannan hurarrun roƙe-roƙe a matsayin roƙo da za mu so mu yi kuma zai amsa su. Allah ya san mu, da kuma ma’anar abubuwan da ya sa ruhunsa ya faɗa ta wurin marubutan Littafi Mai Tsarki. Jehobah yana amsa addu’o’inmu sa’ad da ruhu ya yi “roƙo” dominmu. Amma sa’ad da muka san Kalmar Allah sosai, za mu tuna abin da ya kamata mu yi addu’a a kansa.
21. Menene za mu bincika a talifi na gaba?
21 Kamar yadda muka koya, addu’o’inmu suna nuna ko waɗanne irin mutane ne mu. Alal misali, suna iya nuna yadda muka kusaci Jehobah da kuma yadda muka san Kalmarsa sosai. (Yaƙ. 4:8) A talifi na gaba, za mu bincika wasu addu’o’i da kuma furci na addu’o’i da aka rubuta cikin Littafi Mai Tsarki. Yaya irin wannan bincike na Nassosi zai shafi yadda muke kusantar Allah cikin addu’a?
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane irin hali ne ya kamata mu nuna sa’ad da muke addu’a ga Jehobah?
• Me ya sa za mu yi addu’a don ’yan’uwanmu masu bi?
• Menene addu’o’inmu za su nuna game da mu da kuma muradinmu?
• Yaya ya kamata mu aikata sa’ad da ake addu’a a cikin jama’a?
[Hotunan da ke shafi na 4]
Kana yabon Jehobah da kuma yi masa godiya a kai a kai?
[Hotunan da ke shafi na 6]
A koyaushe ya kamata halinmu a lokacin da ake addu’a ga jama’a ya ɗaukaka Jehobah