Abin Da Muka Koya Daga Wurin Yesu
Game da Bauta ta Gaskiya
Allah yana amincewa da dukan bauta kuwa?
▪ Yesu ya ji tausayin mutanen da addinin ƙarya ya ruɗa. Ya yi gargaɗi game da “masu-ƙaryan annabci, masu-zuwa . . . da fatar tumaki, amma daga ciki kerketai ne masu-hauka.” (Matta 7:15) Ka lura cewa wasu mutane suna yin amfani da sunan addini don aikata mugunta?
A cikin addu’a ga Allah, Yesu ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Saboda haka, Allah ya ƙi bautar da ta saɓa wa gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Don haka, ga wasu ’yan riya na addini, Yesu ya yi amfani da kalmar Allah da ta ce: “Amma banza su ke yi mani sujada, koyarwa da su ke yi dokokin mutane ne.”—Matta 15:9.
Akwai addinin gaskiya kuwa?
▪ Sa’ad da Yesu ya saɗu da wata mata ’yar Samariya wadda addinin ƙarya ya ruɗa, ya ce mata: ‘Ku kuna yin sujada ga abin da ba ku sani ba . . . Masu-yin sujada da gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin Ruhu da cikin gaskiya kuma; gama irin waɗannan Uban ya ke nema, su zama masu yi masa sujada.’ (Yohanna 4:22, 23) Babu shakka, za a iya samun bauta ta gaskiya.
Yesu ya ce: “Ba na yin komi domin kaina ba, amma ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani.” Yesu ya san cewa addinin da ya koyar ne kaɗai na gaskiya. (Yohanna 8:28) Saboda haka, ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Tun da masu bauta ta gaskiya suna kusantar Uba ta hanya ɗaya, wajibi ne su kasance cikin addini ɗaya na gaskiya.
Ta yaya za ka san masu bauta ta gaskiya?
▪ Kirista shi ne wanda yake bin Yesu Kristi. Ka yi la’akari da hanyoyi huɗu da yin koyi da misalin Yesu ya bayyana almajiransa dalla-dalla.
1. A cikin addu’a ga Jehobah Yesu Kristi ya ce: “Na kuma sanar masu da sunanka.” (Yohanna 17:26) Har ila, Kiristoci na gaskiya suna yin hakan.
2. Yesu ya yi wa’azi game da Mulkin Jehobah kuma ya aika almajiransa su yi hakan daga gida zuwa gida. Ya ce: “Kuma kowane birni ko ƙauye inda kuka shiga, a cikinsa ku nemi wanda ya cancanta.” Daga baya ya gaya wa mabiyansa: “Ku tafi fa, ku almajirtarda dukan al’ummai.” (Matta 10:7, 11; 28:19) Za ka gane Kiristoci na gaskiya a yau da sauƙi domin sun ci gaba da yin irin wannan aikin.
3. Yesu ya ƙi saka hannu a siyasa. Saboda haka, ya ce game da mabiyansa: “Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:14) Ya kamata a san masu bauta ta gaskiya da ƙin saka hannu a siyasa.
4. Yesu ya sadaukar da kansa domin ƙaunarsa ga wasu. Ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Kiristoci na gaskiya suna kula da juna kuma ba sa saka hannu a yaƙe-yaƙe.
Ta yaya bauta ta gaskiya za ta amfane ka?
▪ Don yin addini ta gaskiya, wajibi ne ka soma sanin Jehobah sosai. Sanin Allah zai sa ka biɗi hanya mafi kyau a rayuwa kuma zai cika zuciyarka da ƙauna ga Allah. Jehobah ya yi wa waɗanda suke ƙaunarsa alkawarin rayuwa marar matuƙa. Saboda haka, Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya.”—Yohanna 17:3.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 15 na littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Hoton da ke shafi na 16]
“Ku yi hankali da masu-ƙaryan annabci, masu-zuwa wurinku da fatar tumaki, amma daga ciki kerketai ne masu-hauka.” —Matta 7:15