Yesu Kristi Yadda Saƙonsa Ya Shafe Ka
“Ni na zo domin su sami rai, su same shi a yalwace.” —YOHANNA 10:10.
YESU KRISTI ya zo duniya musamman domin ya bayar, ba domin ya karɓa ba. Ta wurin hidimarsa, ya ba da kyauta mai tamanin gaske ga ’yan Adam, wato, saƙon da ya bayyana gaskiya game da Allah da kuma nufinsa. Waɗanda suka yi na’am da wannan saƙon za su iya more rayuwa mai kyau a yanzu, kamar yadda miliyoyin Kiristoci na gaskiya za su iya shaida.a Amma ainihin saƙon da Yesu ya yi wa’azi akai ita ce kyauta mafi tamani duka, wato, kamiltaccen rai da ya bayar domin mu. Rayuwarmu ta har abada ta dangana ne akan yin na’am da wannan sashe mafi muhimmanci na saƙonsa.
Abin da Allah da kuma Kristi Suka bayar Yesu ya san cewa zai yi mutuwar azaba a hannun magabtansa. (Matta 20:17-19) Duk da haka, a cikin sanannen kalmominsa da ke Yohanna 3:16, ya ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” Yesu ya kuma ce ya zo ‘shi ba da ransa kuma abin fansar mutane dayawa.’ (Matta 20:28) Me ya sa ya ce zai ba da ransa maimakon a karɓan ransa?
Cike da ƙauna marar iyaka, Allah ya yi tanadi ga ’yan Adam su sami ceto daga zunubin da suka gāda da kuma sakamakonsa, wato, ajizanci da mutuwa. Allah ya yi hakan ne ta wurin aiko da Ɗansa makaɗaici zuwa duniya domin ya yi mutuwar hadaya. Yesu da yardar ransa ya yi biyayya, ya ba da ransa kamiltacce domin mu. Wannan tanadi, da aka kira fansa, ita ce kyauta mafi girma da Allah ya ba wa ’yan Adam.b Kyauta ce da za ta iya kai ga rai na har abada.
Abin da kake bukatan ka yi Fansar kyauta ce a gareka? Wannan ya rage naka. Alal misali: A ce wani ya miƙa maka kyautar da ke cikin akwatin da aka nannaɗe da takarda. Gaskiyar ita ce, ba ta zama kyautar ka ba tukun har sai ka miƙa hannu ka karɓe ta. Hakazalika, Jehobah yana miƙa maka wannan fansar, amma wannan kyautar ba ta zama taka ba tukun har sai ka miƙa hannu ka karɓe ta. Ta yaya?
Yesu ya ce waɗanda suka “bada gaskiya” a gare shi kaɗai ne za su sami rai na har abada. Bangaskiya ta ƙunshi yadda kake yin rayuwarka. (Yaƙub 2:26) Ba da gaskiya ga Yesu yana nufin yin rayuwar da ta jitu da abubuwan da ya ce da waɗanda ya yi. Domin ka yi hakan, dole ka san Yesu da kuma Ubansa sosai. “Rai na har abada ke nan,” in ji Yesu, “su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”—Yohanna 17:3.
Shekaru dubu biyu da suka shige, Yesu Kristi ya yaɗa saƙon da ta canza hanyar rayuwar miliyoyin mutane a dukan duniya. Za ka so ka sami ƙarin bayani game da wannan saƙon da kuma yadda kai da waɗanda kake ƙauna za ku amfana daga gareta, a yanzu, da kuma har abada? Shaidun Jehobah za su yi farincikin taimaka muku.
Talifofi na gaba za su sa ka ƙara sanin Yesu Kristi, mutumin da ya yi wa’azin saƙon da zai iya canza rayuwarka har abada.
[Hasiya]
a Ba dukan mai da’awar cewa shi Kirista ba ne mai bin Kristi da gaske ba. Mabiyan Kristi na gaske su ne waɗanda suke yin rayuwar da ta jitu da gaskiyar da ya koyar game da Allah da kuma nufinsa.—Matta 7:21-23.
b Domin ƙarin bayani a kan koyarwar Nassi game da fansa, duba babi na 5, “Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah,” a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.