Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 6/15 pp. 25-29
  • Ka Sami Wartsakewa Ta Wurin Yin Abubuwa Na Ruhaniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sami Wartsakewa Ta Wurin Yin Abubuwa Na Ruhaniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Sami Wartsakewa ta Wurin Cuɗanya na Kirista
  • Hidimar Fage na Kawo Wartsakewa
  • Bauta ta Iyali Tana Wartsakarwa
  • Ka Guji Abin da Zai Gajiyar da Kai
  • “Ku Zo Gare Ni, . . . Zan Ba Ku Hutawa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Sauƙi Daga Wahala—Hanya Mafi Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Taimako ga Iyalai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ka Yi Nazari da Niyyar Gaya wa Wasu Abin da Ka Koya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 6/15 pp. 25-29

Ka Sami Wartsakewa Ta Wurin Yin Abubuwa Na Ruhaniya

“Ku ɗaukar wa kanku karkiyata . . . , za ku sami hutawa ga rayukanku.”—MAT. 11:29.

1. Menene Jehobah ya yi tanadinsa a Dutsen Sinai, kuma me ya sa?

SA’AD da aka kafa doka ta alkawari a Dutsen Sinai, ta ƙunshi kiyaye ranar Assabaci na mako-mako. Ta bakin kakakinsa Musa, Jehobah ya umurci al’ummar Isra’ila: “Kwana shidda za ka yi aikinka, rana ta bakwai za ka huta: domin bajiminka da jakinka kuma su sami hutawa, ɗan baiwarka kuma, da baƙo, su sami numfasa.” (Fit. 23:12) Hakika, domin nuna sanin ya kamata ga waɗanda suke ƙarƙashin Dokar, Jehobah ya yi tanadin ranar hutu cikin ƙauna saboda mutanensa “su sami numfasa.”

2. Ta yaya Isra’ilawa suka amfana ta wajen kiyaye ranar Assabaci?

2 Ranar Assabaci ranar hutu ne kawai? A’a, sashe ne mai muhimmanci na bautar Isra’ilawa ga Jehobah. Kiyaye ranar Assabaci yana ba shugabannin iyalai lokaci su koyar da iyalansu su “kiyaye tafarkin Ubangiji, domin su yi adalci.” (Far. 18:19) Yana kuma ba iyalai da abokai zarafi su zauna tare don su yi bimbini a kan ayyukan Jehobah kuma su yi cuɗanya na farin ciki. (Isha. 58:13, 14) Mafi muhimmanci, a annabce ranar Assabaci tana nuni ga lokaci da za a samu wartsakewa na gaske ta wurin Sarautar Kristi na Shekara Dubu. (Rom. 8:21) A zamaninmu kuma fa? A ina kuma ta yaya Kiristoci na gaskiya waɗanda suke son su bi hanyoyin Jehobah za su iya samun irin wannan wartsakewa?

Ka Sami Wartsakewa ta Wurin Cuɗanya na Kirista

3. A wace hanya ce Kiristoci na ƙarni na farko suka ƙarfafa juna, menene sakamakon?

3 Manzo Bulus ya kwatanta ikilisiyar Kirista a matsayin “jigon gaskiya da ƙarfinta.” (1 Tim. 3:15) Kiristoci na farko sun sami goyon baya sosai ta wurin ƙarfafa da kuma gina juna cikin ƙauna. (Afis. 4:11, 12, 16) Yayin da yake Afisa, waɗanda suke cikin ikilisiya a Koranti sun kai wa Bulus ziyara mai ƙarfafawa. Ka lura da sakamakon hakan: “Ina murna kuma da zuwan Istifanas da Furtunatus da Akaikus,” in ji Bulus, “gama suka farfaɗo da ruhuna.” (1 Kor. 16:17, 18) Hakazalika, lokacin da Titus ya tafi Koranti don ya yi hidima ga ’yan’uwa da ke wajen, Bulus ya rubuta zuwa ga ikilisiyar, yana cewa: “Ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka.” (2 Kor. 7:13) Hakanan ma a yau, Shaidun Jehobah suna samun wartsakewa na ainihi ta wajen zumunci mai ƙarfafawa na ’yan’uwa Kirista.

4. Yaya taron ikilisiya yake wartsake mu?

4 Kai da kanka ka shaida cewa taron ikilisiya tushen farin ciki ne sosai. A nan ne muke samun “ƙarfafawa . . . kowannenmu ta wurin bangaskiyar junanmu.” (Rom. 1:12) ’Yan’uwanmu Kiristoci maza da mata ba waɗanda muke yi wa sanin shanu ba ne. Abokai ne na ƙwarai, mutanen da muke ƙauna da kuma mutuntawa. Muna samun farin ciki da kuma ƙarfafawa yayin da muka haɗu da su a taronmu.—Fil. 7.

5. Ta yaya za mu wartsake juna a taron gunduma da manyan taro?

5 Wani tushen wartsakewa shi ne taron gunduma da manyan taro na shekara-shekara. Ƙari ga yin tanadin ruwa mai ba da rai daga Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, waɗannan manyan taron suna ba mu zarafin “buɗe zuciya” a tarayyarmu. (2 Kor. 6:12, 13) Amma idan muna jin kunya kuma tattaunawa da mutane yana yi mana wuya fa? Hanya guda da za mu iya sanin ’yan’uwanmu maza da mata ita ce ba da kanmu a taron gunduma. Wata ’yar’uwa ta taimaka a taro na ƙasashe kuma ta taimaka wajen aikin tsabtace wurare. Bayan hakan, ta ce: “Ban san mutane da yawa ba a wurin, sai iyalina da kuma abokai kaɗan kawai. Amma da na taimaka wajen tsabtace wurin, na haɗu da ’yan’uwa maza da mata masu yawa! Na yi farin ciki sosai!”

6. Wace hanya guda za mu iya samun wartsakewa a lokacin hutu?

6 Isra’ilawa suna zuwa Urushalima don yin bauta sau uku a shekara. (Fit. 34:23) Sau da yawa, hakan ya bukaci barin gonaki da shaguna don yin tafiya na kwanaki da kafa a hanyoyi masu ƙura. Duk da haka, sa’ad da suka isa haikalin kuma suka ga waɗanda suka halarci taron “suna yabon Ubangiji,” suna yin “murna ƙwarai.” (2 Laba. 30:21) Yawancin bayin Jehobah a yau ma sun gano cewa yin tafiya tare da iyalansu don ziyartar Bethel, rassan Shaidun Jehobah na kusa, yana kawo farin ciki mai girma. Za ka iya haɗa wannan ziyartan a hutun iyalinka na gaba?

7. (a) Ta yaya taron shaƙatawa zai kasance mai amfani? (b) Me zai sa liyafa ta kasance abin tunawa kuma mai ban ƙarfafa?

7 Kasancewa tare da iyali da abokai don taron liyafa zai iya ƙarfafawa. Sarki Sulemanu mai hikima ya ce: “Babu abin da ya fi ga mutum ya ci ya sha, ya ji wa ransa daɗi cikin aikinsa.” (M. Wa. 2:24) Taron liyafa yana wartsake rai kuma yana ƙarfafa gaminmu na ƙauna da ’yan’uwa Kiristoci yayin da muka san su sosai. Don ya kasance abin tunawa da kuma ban ƙarfafa, ya fi kyau mutane kaɗan su halarci taron shakatawar kuma a tabbata cewa ana duba kowa sosai, musamman idan za a ba da giya.

Hidimar Fage na Kawo Wartsakewa

8, 9. (a) Ka bambanta saƙon Yesu da na marubuta da kuma Farisawa. (b) Yaya muke amfana ta wajen yaɗa gaskiyar Littafi Mai Tsarki?

8 Yesu ya yi ƙwazo a hidimar fage, kuma ya ƙarfafa almajiransa su yi hakan. Wannan ya bayyana a kalmominsa: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aiko ma’aikata cikin girbinsa.” (Mat. 9:37, 38) Saƙon da Yesu ya koyar mai wartsakewa ne; “bishara” ce. (Mat. 4:23; 24:14) Wannan ya bambanta da dokoki masu nauyi da Farisawa suka ɗora wa mutane.—Karanta Matta 23:4, 23, 24.

9 Sa’ad da muke gaya wa mutane saƙon Mulki, muna wartsakar da su ne a ruhaniya, kuma muna cusa gaskiyar Littafi Mai Tsarki a cikin zuciyarmu. Shi ya sa ya dace da mai zabura ya ce: “Halleluyah! Gama ya yi kyau a raira yabbai ga Allahnmu; gama abu mai-daɗi ne.” (Zab. 147:1) Za ka ƙara farin cikin da kake samu wajen yabon Jehobah ga maƙwabtanka?

10. Nasararmu a hidima ta dangana ne a kan yadda ake karɓan saƙonmu da kyau? Ka bayyana.

10 Hakika, a wasu ’yankuna mutane suna saurarar bishara sosai fiye da wasu wurare. (Karanta Ayyukan Manzanni 18:1, 5-8.) Idan kana zama ne a yankin da ba a karɓan saƙon Mulkin sosai, ka ƙoƙarta ka mai da hankali ga abin da kake cim ma wa a hidimar fage. Ka tuna cewa ƙoƙarinka na ci gaba da yin shelar sunan Jehobah ba a banza ba ne. (1 Kor. 15:58) Ƙari ga haka, nasarar mu a hidimar fage ba ta dangana a kan yadda mutane ke karɓan bisharar ba. Muna da tabbacin cewa Jehobah ne yake jawo masu zuciyar kirki ga kansa kuma za su samu zarafin karɓan saƙon Mulki.—Yoh. 6:44.

Bauta ta Iyali Tana Wartsakarwa

11. Wane hakki ne Jehobah ya ba iyaye, kuma ta yaya za su iya cika shi?

11 Iyayen da suke bauta wa Allah suna da hakkin koyar da yaransu game da Jehobah da kuma hanyoyinsa. (K. Sha 11:18, 19) Idan kana da yara, kana keɓe lokacin koyar da yaranka game da Ubanmu na samaniya mai ƙauna? Domin ka cika wannan hakki mai muhimmanci kuma ka kula da bukatun iyalinka, Jehobah ya yi tanadin abinci na ruhaniya mai yawa ta wurin littattafai, mujallu, bidiyo, da kuma faifan da aka ɗauka.

12, 13. (a) Yaya iyalai za su iya amfana daga Bauta ta Iyali da yamma? (b) Ta yaya iyaye za su tabbata cewa bautarsu ta iyali tushen wartsakewa ne?

12 Ƙari ga haka, rukunin bawa mai aminci mai hikima ya yi shirye-shirye don yin Bauta ta Iyali da yamma. Wannan yamma ce da aka keɓe a kowanne mako don iyali su yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Mutane da yawa sun gano cewa wannan shirin ya jawo su kusa ga juna cikin ƙauna kuma ya ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Amma ta yaya iyaye za su tabbata cewa bautarsu ta iyali tana wartsakarwa a ruhaniya?

13 Bai kamata lokacin Bauta ta Iyali da yamma ya zama lokacin cin rai ko na baƙin ciki ba. Balle ma, muna bauta wa “Allah mai” farin ciki, kuma yana son mu yi farin ciki a bautarmu. (1 Tim. 1:11; Filib. 4:4) Samun ƙarin yamma don tattauna gaskiya mai tamani daga Littafi Mai Tsarki albarka ce sosai. Iyaye suna iya yin amfani da hanyoyin koyarwa masu kyau, yin amfani da kwatanci da kuma ƙirƙiro sababbin abubuwa. Alal misali, wata iyali ta sa ɗansu Brandon, mai shekara goma, ya ba da rahoto mai jigo “Me ya sa Aka Kira Shaiɗan Maciji a Cikin Littafi Mai Tsarki?” Wannan batun ya dami Brandon domin yana ƙaunar macizai, kuma ya yi baƙin ciki da jin cewa an kwatanta su da Shaiɗan. Wasu iyalai suna yin wasan kwaikwayo jifa-jifa, kowannensu ya ɗauki matsayin wani daga Littafi Mai Tsarki, ya karanta sashensa daga cikin Littafi Mai Tsarki, ko kuma ya yi kwaikwayon wata aukuwa. Waɗannan hanyoyin koyarwa suna da daɗi kuma za su iya shafan yaranka, kuma hakan zai sa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki su taɓa zuciyarsu.a

Ka Guji Abin da Zai Gajiyar da Kai

14, 15. (a) Yaya matsi da rashin kwanciyar hankali suka ƙaru a waɗannan kwanaki na ƙarshe? (b) Waɗanne ƙarin matsi za mu iya fuskanta?

14 Matsi da rashin kwanciyar hankali sun ƙaru a waɗannan kwanaki na ƙarshe na wannan mugun zamani. Rashin aiki da talauci sun shafi mutane da yawa. Waɗanda suke da aiki sau da yawa suna jin cewa suna kai kuɗin da suke samu gida cikin aljihun da ke cike da huji, kuma hakan ba ya amfanar iyalansu sosai. (Gwada Haggai 1:4-6.) ’Yan siyasa da shugabannai sun rasa abin yi yayin da suke fama su kawar da ta’addanci da sauran hanyoyin mugunta. Mutane da yawa suna baƙin ciki domin kasawarsu.—Zab. 38:4.

15 Kiristoci na gaskiya suna fuskantar matsaloli da matsi na zamanin Shaiɗan. (1 Yoh. 5:19) A wasu lokatai, almajiran Kristi suna iya fuskantar ƙarin matsi yayin da suke ƙoƙarin su kasance da aminci ga Jehobah. “Idan suka tsananta mini, zasu tsananta muku kuma,” in ji Yesu. (Yoh. 15:20) Amma, ko sa’ad da ake “binmu da tsanani,” ba a “bar mu yasassu ba.” (2 Kor. 4:9) Me ya sa hakan?

16. Menene zai taimaka mana mu ci gaba da farin ciki?

16 Yesu ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa.” (Mat. 11:28) Ta wurin kasancewa da cikakkiyar bangaskiya ga tanadin fansa na Kristi, a alamance muna saka kanmu a hannun Jehobah. Ta hakan, muna samun “mafificin girman iko.” (2 Kor. 4:7) “Mai-taimako,” ruhu mai tsarki na Allah yana ƙarfafa bangaskiyarmu domin mu jimre da gwaje-gwaje da ƙunci da muke fuskanta kuma mu ci gaba da farin ciki.—Yoh. 14:26; Yaƙ. 1:2-4.

17, 18. (a) Wane hali ne muke bukata mu guje wa? (b) Menene zai faru idan muna mai da hankali ga nishaɗi na yau da kullum?

17 Kiristoci na gaskiya a yau suna bukatan su mai da hankali kada halin wannan duniya da ke sa mutane su biɗi nishaɗi ko ta yaya ya rinjaye su. (Karanta Afisawa 2:2-5.) Idan ba haka ba, za mu faɗa tarkon “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi.” (1 Yoh. 2:16) Ko kuma cikin kuskure muna iya gaskata cewa bin sha’awoyi na jiki zai kawo wartsakewa. (Rom. 8:6) Alal misali, wasu mutane sun soma shan ƙwaya da mugun shan giya, batsa, mugun wasanni, ko kuma ayyukan lalata dabam dabam don su cika sha’awarsu. Shaiɗan ya tsara ‘dabarunsa’ ne don ya yaudari mutum ya kasance da ra’ayin da bai dace ba game da wartsakewa.—Afis. 6:11.

18 Hakika, yana da kyau mutum ya ci, ya sha kuma ya yi wasu ayyukan nishaɗi idan aka yi hakan daidai yadda ya kamata. Duk da haka, ba za mu ƙyale irin waɗannan abubuwa su zama ainihin abin da muka fi so a rayuwa ba. Kasancewa da daidaituwa da kame kai suna da muhimmanci, musamman domin zamanin da muke zama ciki. Biɗan abubuwa na kanmu suna iya gajiyar da mu har mu zama “raggaye ko kuwa marasa-amfani zuwa ga sanin Ubangijinmu Yesu Kristi.”—2 Bit. 1:8.

19, 20. Ta yaya za a samu wartsakewa ta gaske?

19 Sa’ad da muka sa tunaninmu ya jitu da ƙa’idodin Jehobah, za mu fahimci cewa jin daɗi na wannan duniya na ɗan lokaci ne. Musa ya fahimci hakan, mu ma hakan. (Ibran. 11:25) Gaskiyar ita ce, muna samun wartsakewa ta gaske, irin wadda ke kawo farin ciki da gamsuwa na dindindin ta wurin yin nufin Ubanmu na samaniya.—Mat. 5:6.

20 Bari mu ci gaba da samun wartsakewa ta wurin yin abubuwa na ruhaniya. Ta yin hakan, muna “ƙin rashin ibada da sha’awoyi na duniya; muna sauraron begen nan mai-albarka da bayanuwar darajar Allahnmu mai-girma Mai-cetonmu kuma Yesu Kristi.” (Tit. 2:12, 13) Saboda haka bari mu ƙuduri aniya mu kasance a ƙarƙashin karkiyar Yesu ta wajen miƙa kai ga ikonsa da ja-gorarsa. Ta yin haka, za mu sami farin ciki da wartsakewa ta gaske!

[Hasiya]

a Don ƙarin bayanin a kan yadda za a sa nazari na iyali ya yi daɗi ya kuma kasance mai amfani, ka duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga Oktoba, 2009, shafuffuka na 29-31.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya mutanen Jehobah suke samun wartsakewa a yau?

• A wace hanya ce hidima take wartsakar da mu da waɗanda muke yi wa magana?

• Menene magidanta za su yi don su tabbata cewa bautarsu ta iyali tana kawo wartsakewa?

• Waɗanne abubuwa ne suke gajiyar da mu a ruhaniya?

[Hotuna da ke shafi na 26]

Ta wajen ɗaukan karkiyar Yesu a kanmu, muna samun tushen wartsakewa masu yawa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba