Hanyoyi Bakwai da Za a Amfana Daga Karatun Littafi Mai Tsarki
“Littafi Mai Tsarki ba littafin da aka fi sayarwa ba ne kawai a dukan tarihi, amma an ci gaba da sayar da kofofi da yawa kowace shekara fiye da kowane littafi.”—MUJALLAR TIME.
“Ina karanta Littafi Mai Tsarki a wasu lokatai, amma yana ci mani rai sosai.”—KEITH, SANANNEN MAWAƘI DAGA ƘASAR INGILA.
ABIN mamaki ne cewa mutane da yawa suna da Littafi Mai Tsarki, amma duk da haka ba sa amfana sosai daga karanta shi. Wasu kuma suna daraja abin da suka karanta daga cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, wata mata mai suna Nancy ta ce: “Tun da yake ina soma karanta Littafi Mai Tsarki kuma in yi bimbini a kansa kullum da safiya, ina kasancewa a shirye in bi da kowane irin ƙalubale da zan fuskanta a ranar. Hakan ya kuma rage baƙin cikin da nake fama da shi fiye da duk wani abin da na yi amfani da shi a cikin shekara 35 da suka shige.”
Ko da ba ka taɓa karanta Littafi Mai Tsarki ba, sanin cewa ya taimaka wa wasu yana ba ka mamaki ne? Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki, za ka so ka ƙara amfana daga abin da kake karantawa? Idan haka ne, ka gwada waɗannan matakai bakwai da aka bayyana a talifin nan.
Mataki na 1—Ka karanta da manufa mai kyau
◼ Za ka iya karanta Littafi Mai Tsarki kamar littafi mai daɗi ko don tilas ne ka karanta ko kuma da manufar samun ja-gora a wannan duniyar da ke cike da wahala. Za ka fi amfana idan makasudinka shi ne koyon gaskiya game da Allah. Ƙari ga hakan, za ka samu albarka sosai idan manufarka ita ce ganin yadda saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai iya shafar rayuwarka.
Nassosi sun nanata muhimmancin yin karatu da manufa mai kyau ta wajen kwatanta Littafi Mai Tsarki da madubi: “Idan kowa mai-jin magana ne, ba mai-aikawa ba, yana kama da mutum wanda yana duban halittaciyar fuskarsa a cikin madubi: gama ya duba kansa, kāna ya tafi, nan da nan kuwa ya manta irin mutum da ya ke. Amma wanda ya duba cikin cikakkiyar shari’a, shari’a ta ’yanci, ya lizima, shi kuwa ba mai-ji wanda ke mantawa ba ne, amma mai-yi ne wanda ke aikatawa, wannan za ya zama mai-albarka a cikin aikinsa.”—Yaƙub 1:23-25.
Mutumin da aka ambata a wannan misalin ya duba fuskarsa a cikin madubi amma ya ƙi yin gyaran da yake bukatar yi. Wataƙila ya ɗan kalli kansa ne kawai, ko kuma mai yiwuwa ba shi da niyyar yin gyara. Hakazalika, ba za mu amfana ba idan muka karanta Littafi Mai Tsarki da garaje ko kuma mun ƙi yin amfani da abin da muka karanta. Akasin haka, za mu iya samun farin ciki na gaske idan muka bincika Littafi Mai Tsarki sosai da niyyar zama “mai-yi,” kuma mu ƙyale tunanin Allah ya mulmula tunaninmu da ayyukanmu.
Mataki na 2—Ka zaɓi fassara mai kyau
◼ Wataƙila akwai fassarorin Littafi Mai Tsarki da yawa a yarenka da za ka so ka zaɓa. Ko da yake kowace fassara ta Kalmar Allah za ta iya taimaka maka, wasu suna amfani da fassara mai wuyar fahimta. (Ayyukan Manzanni 4:13) Wasu fassarori sun ma canja saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki saboda al’adunsu. Alal misali, wasu sun sauya sunan Allah, Jehobah, da laƙabi kamar su “Allah” ko “Ubangiji.” Saboda haka, sa’ad da kake neman Littafi Mai Tsarki wanda za ka karanta, ka nemi wanda fassararsa yake da sauƙin karantawa da kuma fahimta.
Miliyoyi masu karatu a dukan duniya sun ga cewa fassarar nan New World Translation yana da sauƙin karantawa da kuma fahimta.a Ka yi la’akari da misalin wani tsoho a ƙasar Bulgeriya. Ya halarci taron Shaidun Jehobah sai aka ba shi fassarar New World Translation na Littafi Mai Tsarki. Bayan hakan, sai ya ce, “Na yi shekaru ina karanta Littafi Mai Tsarki, amma ban taɓa karanta fassara mai sauƙin fahimta kuma mai taɓa zuciya kamar wannan ba.”
Mataki na 3—Ka yi addu’a
◼ Za ka iya ƙara fahimtar Littafi Mai Tsarki ta wajen neman taimako daga Mawallafin, kamar yadda marubucin wannan zabura ya ce: “Ka buɗe mini idanuna, domin in duba al’ajibai daga cikin shari’arka.” (Zabura 119:18) Ka yi addu’a ga Allah a duk lokacin da ka karanta Nassosi, kana roƙonsa ya taimaka maka ka fahimci Kalmarsa. Ya kamata mu yi godiya don Littafi Mai Tsarki, domin in ba shi ba za mu san Allah ba.—Zabura 119:62.
Allah yana sauraron irin addu’o’in nan na neman taimako kuwa? Ka yi la’akari da abin da ya faru ga wasu ’yan mata biyu waɗanda iyayensu ɗaya ne a ƙasar Uruguay. Sun yi mamaki sa’ad da suka ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a littafin Daniyel 2:44, sai suka yi addu’a cewa Allah ya aiko wani ya taimaka musu su fahimci ayar. Kafin ’yan matan su rufe Littafi Mai Tsarkinsu, sai Shaidun Jehobah biyu suka zo bakin ƙofarsu, suka karanta ainihin ayar da ’yan matan suka yi addu’a a kai, kuma suka bayyana musu cewa tana nufin cewa Mulkin Allah zai sauya mulkin ’yan Adam.b ’Yan matan suka amince cewa Allah ya amsa addu’ar da suka yi ta neman taimako.
Mataki na 4—Ka karanta kullum
◼ Wani mawallafin littafi ya bayyana cewa “an sayar da Littafi Mai Tsarki sosai” bayan harin da ’yan ta’adda suka kai wa Amirka a ranar 11 ga Satumba, 2001. Mutane da yawa suna karanta Kalmar Allah ne kawai a lokacin wahala. Amma Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu karanta shi kullum, domin ya ce: “Wannan littafin shari’a ba za ya rabu da bakinka ba, amma za ka riƙa bincikensa dare da rana, domin ka kiyaye ka aika bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki: gama da hakanan za ka sa hanyarka ta yi albarka, da hakanan kuma za ka yi nasara.”—Joshua 1:8.
Za a iya kwatanta amfanin karanta Littafi Mai Tsarki kullum da mutumin da ke da ciwon zuciya kuma ya zaɓi cin abinci mai gina jiki. Shin matakin da ya ɗauka zai taimaka masa idan yana cin wannan abincin ne kawai sa’ad da kirjinsa ya soma yi masa ciwo? A’a. Wajibi ne ya riƙa bin tsarin cin abinci da zai gina jikinsa. Hakazalika, karanta Littafi Mai Tsarki kullum zai taimaka maka ka “yi nasara.”
Mataki na 5—Ka yi amfani da hanyoyi dabam-dabam sa’ad da kake karatu
◼ Karanta Littafi Mai Tsarki daga Farawa zuwa Ru’ya ta Yohanna zai iya kasancewa da amfani sosai, amma za ka iya samun wasu hanyoyin da za ka ji daɗin karatun sosai. Ga wasu shawarwari.
Ka karanta labarin wani a cikin Littafi Mai Tsarki. Ka karanta dukan surori ko kuma littattafai da suka ba da labarin wani mai bauta wa Allah, kamar su:
• Yusufu: Farawa 37–50.
• Ruth: Ruth 1–3.
• Yesu: Matta 1-28; Markus 1-16; Luka 1-24; Yohanna 1-21.c
Ka mai da hankali ga batun. Ka karanta nassosin da ke magana a kan batun. Alal misali, ka yi bincike a kan batun addu’a, sai ka karanta shawarar Littafi Mai Tsarki game da addu’a da kuma addu’o’i da yawa da ke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki.d
Ka karanta da babbar murya. Za ka iya amfana sosai idan ka karanta Littafi Mai Tsarki da babbar murya. (Ru’ya ta Yohanna 1:3) Kuna ma iya karanta shi da babbar murya a matsayin iyali, kuna karatun bi da bi ko kuma a sa kowa cikin iyalin ya ɗauki matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suke cikin labarin. Wasu suna more saurarar karatun Littafi Mai Tsarki da aka ɗauka a faifai. “Soma karanta Littafi Mai Tsarki ya yi mini wuya sosai, saboda haka, sai na soma sauraron karatun Littafi Mai Tsarki da aka ɗauka a faifai. A yanzu na fahimci cewa Littafi Mai Tsarki ya fi kowane littafi muhimmanci,” in ji wata mata.
Mataki na 6—Ka yi bimbini
◼ Yadda rayuwa take da kuma abubuwa da ke janye hankali a wannan zamanin suna sa yin bimbini ya yi wuya. Amma dai, kamar yadda abinci yake bukatan ya narke a cikinmu don ya amfane mu, wajibi ne mu yi bimbini a kan abin da muka karanta daga Littafi Mai Tsarki don mu amfana. Muna yin hakan ta wajen yin bitar abin da muka karanta a cikin zuciyarmu da kuma yi wa kanmu tambayoyi kamar su: ‘Mene ne na koya game da Jehobah Allah? Yaya hakan ya shafe ni? Yaya zan iya yin amfani da shi don taimaka wa wasu?’
Irin waɗannan tunani suna sa saƙon Littafi Mai Tsarki ya taɓa zuciyarmu kuma ya daɗa farin cikin da muke samu wajen karanta Kalmar Allah. Zabura 119:97 ta ce: “Ina ƙaunar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.” Ta wajen yin bimbini, marubucin wannan zabura ya sa Nassosi ya zama abin tunawa a gare shi dukan yini. Yin hakan ya taimaka masa ya gina ƙauna mai zurfi ga abin da ya koya.
Mataki na 7—Ka nemi taimako don ka fahimci Littafi Mai Tsarki
◼ Allah ya san cewa ba za mu iya fahimtar Kalmarsa da kanmu ba. Littafi Mai Tsarki ma ya faɗi cewa yana ɗauke da “waɗansu abu masu-wuyan ganewa.” (2 Bitrus 3:16) Littafin Ayyukan Manzanni ya ambata wani Ba-habashi wanda ya kasa fahimtar ayar da ya karanta cikin Littafi Mai Tsarki sosai. Allah ya aiko da wani bawansa ya taimake shi, a sakamakon hakan, Ba-habashin “ya kama tafiyarsa yana murna.”—Ayyukan Manzanni 8:26-39.
Kai ma za ka iya amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki ta wajen neman taimako don ka fahimci abin da ka karanta. Ka tuntuɓi Shaidun Jehobah a yankinku, ko kuma ka rubuta wasiƙa zuwa ga adireshin da ke shafi na 4 na mujallar nan don a yi maka nazarin Littafi Mai Tsarki kyauta.
[Hasiya]
a An buga New World Translation wanda Shaidun Jehobah suka wallafa gabaki ɗayansa ko kuma rabinta a cikin harsuna 83, kuma za a iya samunsa a duniyar gizon www.watchtower.org a harsuna 17.
b Don ƙarin bayani game da Mulkin Allah da kuma abin da zai yi, ka duba babi na 8 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
c Idan ba ka saba karanta Littafi Mai Tsarki ba, ka soma karanta labarin hidimar Yesu da aka taƙaita a littafin Markus.
d Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ya taimaka wa mutane da yawa wajen nazarin batutuwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, babi na 17, ya tattauna abin da Nassosi suka ce game da addu’a.