Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 10/1 pp. 10-13
  • Yadda Za a Yi Nasara a Shekara ta Farko na Aure

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za a Yi Nasara a Shekara ta Farko na Aure
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Kasance da Daidaita Game da Abin da Kuke Bukata
  • Shaidun Jehobah Suna Raba Aure Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Mene ne Zai Sa Ma’aurata Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Yadda Iyalinka Za Ta Zauna Lafiya
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 10/1 pp. 10-13

Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali

Yadda Za a Yi Nasara a Shekara ta Farko na Aure

Ya ce: “Na yi mamakin ganin cewa ni da matata mun sha bamban sosai! Alal misali, ina tashi daga barci tun da sassafe, amma tana tashi a makare. Yadda take saurin canjawa daga yin annashuwa zuwa baƙin ciki yana ba ni mamaki! Wani abu kuma shi ne, idan na yi girki tana yawan kushe ni, musamman yadda nake share hannuna da tsummar share hannu.”

Ta ce: “Maigidana ba ya hira sosai. Amma ni na saba da iyalina sosai. Suna yin hira sosai, musamman a lokacin cin abinci. Kuma sa’ad da maigidana ya yi girki, yana yin amfani da ƙyalle guda ya share kwanuka da kuma hannunsa! Hakan yana bala’in ɓata mini rai! Me ya sa maza suke da wuyan fahimta? Yaya mutane suke nasara a aurensu?”

IDAN ba ka daɗe da yin aure ba, ka taɓa fuskantar irin waɗannan ƙalubalen kuwa? Shin hakan yana nufin cewa abokiyar aurenkaa ta samu wasu halaye marar kyau ne yanzu waɗanda babu su a lokacin da kuke fita zance? Ta yaya za ka iya rage “wahala a cikin jiki” da ma’aurata za su sha.—1 Korintiyawa 7:28.

Na ɗaya, kada ka yi zaton cewa don kun yi wa juna alkawari a ranar aurenku, kai da abokiyar aurenka kun zama ƙwararru a rayuwar aure. Babu shakka ka koya yadda ake sha’ani da mutane sa’ad da ba ka yi aure ba, kuma mai yiwuwa ka kyautata yin hakan sa’ad da ka soma fita zance. Amma, aure zai gwada waɗannan halayen a sababbin hanyoyi kuma wataƙila zai bukaci koyon wasu sababbin halaye. Za ka yi kurakurai kuwa? Hakika. Za ka iya samun gwanintar da kake bukata? Ƙwarai kuwa!

Hanya mafi kyau na kyautata kowane irin gwaninta ita ce zuwa wajen wanda ya ƙware a batun kuma a yi amfani da shawarwarin da zai bayar. Wanda ya fi ƙwarewa a batun aure shi ne Jehobah Allah. Ballantana ma, shi ne ya halicce mu da sha’awar yin aure. (Farawa 2:22-24) Ka lura da yadda Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, za ta iya taimaka maka ka shawo kan matsaloli kuma ka koya halayen da kake bukata don aurenka ya jure fiye da shekara ta farko.

HALI NA 1. KU KOYI TUNTUƁAR JUNA

Mene ne ƙalubalen? Keiji,b wani miji da ke zaune a ƙasar Japan, yana mantawa a wasu lokatai cewa zaɓin da ya yi suna shafar matarsa. Ya ce: “Ina amincewa da gayyata ba tare da tuntuɓar matata ba. Bayan haka, sai in ga cewa ba za ta iya zuwa ba.” Allen, wani miji a ƙasar Ostareliya, ya ce: “Ina ganin cewa bai dace ba in tuntuɓi matata game da komi.” Ya fuskanci ƙalubale saboda yadda aka rene shi. Yadda Dianne ta ji ke nan, wadda take zaune a ƙasar Britaniya. Ta ce: “Na saba neman shawara wurin iyalina. Saboda hakan da fari ina neman shawara daga wurinsu ba wurin maigidana ba.”

Mene ne maganin? Ka tuna cewa Jehobah Allah yana ɗaukan ma’aurata a matsayin “nama ɗaya.” (Matta 19:3-6) A idanunsa, babu wata dangantaka na ’yan Adam da ta fi na mata da miji muhimmanci! Don wannan gami ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi, ana bukatar tattaunawa sosai.

Miji da mata za su iya koyon abubuwa da yawa idan suka lura da yadda Jehobah ya tattauna da Ibrahim. Alal misali, don Allah ka karanta tattaunawar da ke Farawa 18:17-33. Ka lura cewa Allah ya daraja Ibrahim a hanyoyi uku. (1) Jehobah ya bayyana abin da yake da niyyar yi. (2) Ya saurara yayin da Ibrahim yake faɗin ra’ayoyinsa. (3) Har ga yadda ya yiwu, Jehobah yana shirye ya sauya matakin da yake son ya ɗauka don ya yi abin da Ibrahim yake so. Ta yaya za ka iya bin wannan misalin yayin da kake tattaunawa da matarka?

GWADA WANNAN: Sa’ad da kake tattauna abin da zai shafi matarka, (1) ka bayyana yadda kake son ka bi da yanayin, amma ka faɗi ra’ayinka a matsayin shawara, ba kamar ka riga ka yanke shawarar ba, (2) ka sa matarka ta faɗi nata ra’ayin, kuma ka nuna cewa kowannenku yana da damar kasancewa da ra’ayi dabam, kuma (3) “ku bari jimrewarku ta sanu” ta wajen amincewa da shawarar abokiyar aurenku a duk lokacin da hakan ya yiwu.—Filibiyawa 4:5.

HALI NA 2. KA KOYA YIN ABU DA DABARA

Mene ne ƙalubalen? Ya dangana ga iyalinka ko kuma al’adarku, wataƙila kana da halin furta ra’ayinka yadda ka ga dama. Alal misali, Liam, wanda ke zaune a ƙasar Turai, ya ce: “A garinmu, mutane suna yin magana yadda suka ga dama. Yadda nake furta bukatuna ɓaro-ɓaro yana yawan ɓata wa matata rai. Dole na koya yin magana a hankali.”

Mene ne maganin? Kada ka yi tsammani cewa abokiyar aurenka za ta so ka yi mata magana yadda ka saba yi. (Filibiyawa 2:3, 4) Shawarar da manzo Bulus ya ba wani mai wa’azi a ƙasashen waje zai iya taimaka wa waɗanda ba su daɗe da yin aure ba. Ya rubuta: “Bawan Ubangiji kuwa lalle ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa.” Kalmar nan salihi tana nufin sanin ya kamata. (2 Timotawus 2:24, Littafi Mai Tsarki) Sanin ya kamata shi ne fahimtar yanayin abu da kuma bi da batun cikin hikima, ba tare da ɓata wa wasu rai ba.

GWADA WANNAN: Sa’ad da ka yi fushi da abokiyar aurenka, ka yi tsammani cewa kana magana ne da abokinka ko kuma shugaban aikinka ba matarka ba. Za ka iya yin amfani da irin murya ko kalaman da kake amfani da su? Yanzu ka yi tunani a kan dalilan da ya sa ya kamata ka yi magana cikin daraja ga matarka fiye da aboki ko shugaban aikinka.—Kolosiyawa 4:6.

HALI NA 3. KA KOYA YADDA ZA KA SABA DA SABON HAKKINKA

Mene ne ƙalubalen? Da farko miji zai iya yin amfani da ikonsa a hanyar da zai ɓata wa matarsa rai, ko kuma mata ba ta saba furta shawarwarinta yadda ya kamata ba. Alal misali, Antonio, wani miji a ƙasar Italiya, ya ce: “Mahaifina ba ya tuntuɓar mahaifiyata game da shawarwarin da suka shafi iyali. Saboda haka da farko, na shugabanci iyalina kamar sarki mai iko.” Debbie, wata matar aure a ƙasar Kanada, ta ce: “Na gaya wa mijina ya riƙa kasancewa da tsabta sosai. Amma yadda nake faɗin hakan yana daɗa ɓata zancen.”

Mene ne zai taimaki miji? Wasu magidanta ba su fahimci bambancin da ke tsakanin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da biyayyar matar aure da kuma biyayyar da yara za su yi wa iyayensu ba. (Kolosiyawa 3:20; 1 Bitrus 3:1) Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce miji ya “manne wa matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya”, bai ce haka ba game da iyaye da yara. (Matta 19:5) Jehobah ya kira mata mataimakiyar mijinta. (Farawa 2:18) Bai taɓa kiran yara mataimakan iyayensu ba. Idan maigida ya bi da matarsa kamar yarinya, yana daraja tsarin aure kuwa?

Hakika, Kalmar Allah ta aririce ku ku bi da matanku kamar yadda Yesu ya bi da ikilisiyar Kirista. Za ka iya sa matarka ta ɗauke ka a matsayin shugabanta cikin sauƙi idan (1) ba ka sa rai ta yi maka biyayya nan da nan ba tare da wani saɓani ba kuma (2) ka ƙaunace ta yadda kake ƙaunar jikinka, ko da a mawuyacin lokaci.—Afisawa 5:25-29.

Mene ne zai taimaki mata? Ki amince cewa mijinki ne sabon shugabanki wanda Allah ya naɗa. (1 Korintiyawa 11:3) Idan kika girmama mijinki, kina girmama Allah. Amma idan kin ƙi shugabancinsa, kina nuna yadda kike ɗaukan mijinki da kuma Allah da bukatunsa.—Kolosiyawa 3:18.

Sa’ad da kuke tattaunawa game da matsaloli masu wuya, ki koyi magance matsalolin, ba kushe halin mijinki ba. Alal misali, Sarauniya Esther, ta so mijinta, Sarki Ahasuerus, ya daidaita wani rashin adalcin da aka yi. Maimakon ta gaya masa baƙar magana, ta faɗi kalamanta cikin hikima. Maigidanta ya amince da shawararta kuma daga baya ya yi abin da ya dace. (Esther 7:1-4; 8:3-8) Maigidanki zai ƙaunace ki sosai idan (1) kika ba shi isashen lokaci ya saba da sabon hakkinsa na shugaban iyali da kuma (2) idan kika girmama shi, har da lokatan da ya yi kurakurai.—Afisawa 5:33.

GWADA WANNAN: Maimakon ku riƙa yin tunani game da hanyoyin da ya kamata abokin aurenku ya ko ta yi gyara, ku yi tunani a kan gyaran da ku da kanku ya kamata ku yi. Magidanta: Idan ka ɓata wa matarka rai domin yadda ka nuna ko ka kasa nuna shugabancinka, ka tambaye ta gyaran da ya kamata ka yi, sai ka rubuta shawarar. Mata: Idan mijinki yana jin cewa ba ki girmama shi, ki tambaye shi inda kike bukatan gyara, kuma ki mai da hankali ga shawarar.

Ku Kasance da Daidaita Game da Abin da Kuke Bukata

Koyon kasancewa da dangantaka mai farin ciki da kuma mai daidaita a aure yana kama ne da koyon tuka keke. Ka san cewa za ka iya faɗuwa sau da yawa kafin ka saba da tukin. Hakazalika, ya kamata ku sa rai cewa za ku yi wasu kurakurai masu kunyatarwa yayin da kuke daɗa ƙwarewa a aurenku.

Ka kasance mai fara’a. Ka ɗauki bukatun abokiyar aurenka da muhimmanci, amma ka koya yin dariya game da kurakuran da ka yi. Ka nemi zarafin sa abokiyar aurenka ta yi farin ciki a shekarar farko ta aurenku. (Kubawar Shari’a 24:5) Mafi muhimmanci, ku ƙyale Kalmar Allah ta yi wa dangantakarku ja-gora. Idan ku ka yi hakan, aurenku zai ci gaba da kasancewa da ƙarfi a kowace shekara.

[Hasiya]

a Ko da wannan talifin ya mai da hankali ga maza ne, amma ƙa’idodin sun shafi miji da mata.

b An canja wasu sunaye.

KA TAMBAYI KANKA . . .

▪ Shin na sa abokiyar aurena ta zama aminiya ta, ko kuwa ina neman shawara daga wurin wasu?

▪ A cikin awoyi 24 da suka wuce, mene ne ainihin abin da na yi don na nuna cewa ina ƙauna da kuma girmama abokiyar aurena?

[Akwati/Hotuna da ke shafi na 11]

Littafi Mai Tsarki Ya Ceci Aurenmu

Toru da Akiko suna ƙaunar juna sosai sa’ad da suka auri juna. Bayan wata takwas da yin aurensu, waɗannan ma’aurata ’yan Japan suka yanke shawara su kashe aurensu. Sun faɗi abin da ya faru.

Toru: “Na fahimci cewa ni da matata ba mu dace da juna ba kamar yadda na yi zato. Alal misali, sa’ad da muke kallon talabijin, ni ina son wasannin motsa jiki, amma ita tana son wasannin kwaikwayo. Ina son fita yawo, amma ta fi son zaman gida.”

Akiko: “Toru yana yin duk wani abin da iyalinsa suka ce ya yi, amma ba ya tuntuɓa ta. Sai na tambaye shi, ‘Wane ne ya fi muhimmanci a wajen ka, ni ko mahaifiyarka? Wani abu kuma da ya ba ni mamaki shi ne yadda Toru yake yin ƙarya. Na gaya masa cewa ƙarya guda na kai ga yin wata kuma idan bai daina ba, aurenmu zai mutu.”

Toru: “Raina ya ɓace kuma na nemi shawara daga babban shugaba da muke aiki tare game da yadda zan bi da matata. ‘Ka gaya mata ta rufe bakinta,’ in ji shi. ‘Idan ta yi gunaguni, ka buge ta.’ Akwai lokacin da na kwaɗa wa Akiko mari kuma na kifar da teburi. Mun yi faɗa sosai, kuma ta bar gida. Sai da na je na dawo da ita daga wani hotal a birnin Tokyo. Daga ƙarshe, muka yanke shawarar kashe aurenmu. Yayin da nake kan hanyata zuwa ofishi a safiyar ranar, matata ta soma kwashe kayanta.”

Akiko: “Ƙararrawar ƙofa ta yi ƙara yayin da nake kwashe jakunkuna na zuwa bakin ƙofa. Wata mace tana tsaye a bakin ƙofar. Mashaidiyar Jehobah ce. Sai na ce ta shigo.”

Toru: “Sa’ad da na isa ofishina, sai zuciyata ta soma canjawa game da kashe auren, sai na hanzarta zuwa gida. Sa’ad da na isa gida, na tarar da Akiko tana tattaunawa da wannan matar. Sai matar ta gaya mini: ‘Kana bukatan wani abin da ku biyun za ku iya yi tare. Za ka so ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki?’ ‘Ƙwarai kuwa,’ na ce, zan yi duk wani abin da zai ceci aurenmu!’”

Akiko: “Matar ta yi shirye-shirye don mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Abubuwa suka soma canjawa sa’ad da muka karanta tsarin aure da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ya ce: “Domin wannan mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne wa matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.”—Farawa 2:24.

Toru: “Nan da nan na fahimci batun. Sai na gaya wa iyaye na, ‘Daga yanzu, da matata ne zan riƙa tattauna batutuwa kafin in yanke shawara.’ Kuma na daina yawan shan giya. Sa’ad da na ji cewa Allah ya ƙi jinin ƙaryace-ƙaryace, ina ƙoƙarin faɗin gaskiya kawai.”

Akiko: “Ni ma na canja. Alal misali, a dā ina raina Toru. Amma sa’ad da na ga yadda yake amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki, sai na ƙara tallafa masa. (Afisawa 5:22-24) A yanzu mun yi shekaru fiye da 28 da yin aure cike da farin ciki. Mun magance matsalolinmu ta wajen sanin juna sosai da kuma yin amfani shawara mai hikima da ke cikin Littafi Mai Tsarki.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba