Ku Koyar Da Yaranku
Dalilin da Ya Sa Yesu Bai Hanzarta Ba
YESU ya samu labari cewa Li’azaru abokinsa na kud da kud yana rashin lafiya sosai. ’Yan’uwan Li’azaru, Maryamu da Martha ne suka aika da wannan saƙon ga Yesu. Masinjan ya fito ne daga Bait’anya, inda Li’azaru da ’yar’uwarsa suke da zama. ’Yan’uwansa mata sun gaskata cewa Yesu zai iya warkar da ɗan’uwansu, ko da yake suna da zama a wancan ɓangare na Kogin Urdun. Sun san cewa a dā ya taɓa warkar da mutane da ke nesa da inda yake.—Matta 8:5-13; Yohanna 11:1-3.
Sa’ad da masinjan ya gaya wa Yesu wannan saƙo na baƙin ciki, Yesu bai ɗauki kowane mataki ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya kwana biyu a wurin da yake a loton nan.” (Yohanna 11:6) Ka san dalilin da ya sa Yesu bai hanzarta don ya taimaki Li’azaru ba?—a Bari mu tattauna dalilin.
Sa’ad da Yesu ya san cewa Li’azaru ya mutu sanadiyyar ciwon, ya gaya wa almajiransa: “Bari mu tafi cikin Yahudiya kuma.” Sai suka yi musu: “Bai daɗe ba Yahudawa suna nema su jejjefe ka da duwatsu; za ka fa can kuma?” Yesu ya bayyana: “Abokinmu Li’azaru yana barci; amma zan tafi, domin in tashe shi daga barci.”
Almajiran suka amsa: “Ubangiji, idan barci ya ɗauke shi, zai farka.” Sai Yesu ya bayyana: “Li’azaru ya mutu.” Sai ya faɗi abin da babu shakka ya ba su mamaki: “Ina murna ba ni nan saboda ku, . . . duk da haka bari mu tafi wurinsa.”
Da gaba gaɗi Toma ya ce: ‘Bari mu tafi kuma, domin mu mutu tare da Yesu.’ Toma ya san cewa maƙiya za su sake yin ƙoƙarin kashe Yesu, kuma suna iya kashe almajiran. Duk da haka, sun bi shi. Bayan kwanaki biyu ko fiye da hakan, suka isa Bait’anya, garin su Li’azaru. Kusan mil biyu ne daga Urushalima.—Yohanna 11:7-18.
Ka san dalilin da ya sa Yesu ya yi murna cewa bai yi saurin zuwa wurin ba?— Yesu ya tayar da wasu mutane daga matattu a dā, amma ya yi hakan ne bayan ’yan sa’o’i da mutuwarsu. (Luka 7:11-17, 22; 8:49-56) Amma Li’azaru ya yi kwanaki a cikin kabari. Babu wanda zai iya yin musu cewa bai mutu ba!
Sa’ad da Martha ’yar’uwar Li’azaru ta samu labari cewa Yesu ya kusan kai Bait’anya, sai ta ruga don ta sadu da shi. Sai ta ce: “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.” Yesu ya tabbatar mata cewa: “Ɗan’uwanki zai tashi kuma.” Sai Martha to ruga ta gaya wa ’yar’uwarta, Maryamu a asirce, ta ce: “Malam yana nan, yana kiranki.”
Nan da nan sai Maryamu ta tashi don ta sadu da Yesu. Amma taron jama’a da suke wurin suka bi Maryamu, suna tunanin cewa za ta koma kabarin ne. Sa’ad da Yesu ya ga Maryamu da jama’ar da ke tare da ita suna kuka, sai shi ma ya yi “kuka.” Ba da daɗewa ba sai suka isa kabarin, wanda aka rufe bakin da babban dutse. Yesu ya ba da umurni: “Ku kawar da dutsen.” Amma Martha ta ce: ‘Ubangiji, yanzu ya yi ɗoyi; gama kwanansa huɗu yanzu da mutuwa.’
Mutanen suka yi biyayya ga umurnin Yesu kuma suka cire dutsen. Sai ya yi addu’a, yana yi wa Allah godiya game da ikon da ya tabbata cewa Allah zai ba shi don ya ta da Li’azaru daga matattu. Yesu ya yi kira “da babbar murya, ya ce, Li’azaru, ka fito.” Sai Li’azaru ya fito, da ‘ɗaurarren hannu da ƙafa da likafani; fuskarsa kuma tana ɗaure da adiko.’ Sai Yesu ya ba da umurni: “Ku kwance shi, ku sake shi.”—Yohanna 11:19-44.
Yanzu ka fahimci dalilin da ya sa Yesu bai hanzarta ba?— Ya san cewa idan ya ɗan jira, zai ba da shaida mai kyau game da Ubansa, Jehobah. Kuma domin ya zaɓi lokaci mafi kyau, mutane da yawa sun yi imani ga Allah. (Yohanna 11:45) Ka ga abin da za mu iya koya daga misalin Yesu kuwa?—
Kai ma za ka iya zaɓar lokaci mafi kyau don ba da shaida game da abubuwa masu ban al’ajabi da Allah ya yi da kuma waɗanda zai yi. Wataƙila kana iya tattaunawa da abonkan makarantarka ko kuma malamanka. Ko ma sa’ad da malami yake koyarwa a cikin aji, wasu matasa sun yi amfani da zarafin don su gaya wa wasu game da albarkar da Mulkin Allah zai kawo wa ’yan Adam. Ko da yake, ba za ka iya ta da matattu ba, amma za ka iya taimaka wa wasu su san Allahn da zai iya kuma zai ta da ƙaunatattunmu daga matattu.
[Hasiya]
a Idan kana karanta wa yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.
TAMBAYOYI:
▪ Me ya sa Yesu bai hanzarta zuwa taimaka wa Li’azaru ba?
▪ Me ya sa Toma ya ce: ‘Bari mu tafi kuma, domin mu mutu tare da Yesu’?
▪ Ta yaya Yesu ya samu ikon ta da Li’azaru daga matattu?
▪ Mene ne za ka iya yi don ka nuna cewa ka yi koyi da misalin Yesu?