Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 8/15 pp. 6-7
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Allah Zai Gafarta Mini Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Allah “Mai Yin Gafara”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Allah Ya Kyale Zunuban da Aka Yi a Dā
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Jehovah Yana Biyan Bukatunmu Na Kullum
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 8/15 pp. 6-7

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Me ya sa Yesu ya gaya wa matar da aka san cewa mai zunubi ce an gafarta mata zunubanta?—Luka 7:37, 48

Sa’ad da Yesu yake cin abinci a gidan wani Bafarisi mai suna Siman, wata mata ta ‘tsaya a bayan Yesu wajen ƙafafunsa.’ Ta jiƙa ƙafafunsa da hawayenta kuma ta goge su da gashin kanta. Sai ta riƙa sumbatar ƙafafunsa kuma ta shafa musu māi mai ƙanshi. Matar ‘mai-zunubi ce wadda take cikin birni,’ in ji labarin Linjila. Hakika, kowane ɗan Adam ajizi mai zunubi ne, amma Nassosi suna yin amfani da wannan kalmar don kwatanta mutumin da zunubansa sanannu ne ko wanda aka san shi da yin zunubi. Wataƙila, matar karuwa ce. Irin wannan mutumiyar ce Yesu ya gaya wa cewa: “An gafarta miki zunubanki.” (Luk 7:36-38, 48) Menene Yesu yake nufi da wannan? Tun da yake ba a miƙa hadayar fansa ba tukuna, yaya wannan gafara za ta yiwu?

Bayan da matar ta wanke ƙafafun Yesu kuma ta shafa musu mai amma kafin ya gafarta mata, Yesu ya yi amfani da wani kwatanci don ya bayyana wani darassi mai muhimmanci ga wanda ya gayyace shi, Siman. Da yake kamanta zunubi da bashi mai yawa da ba za a iya biya ba, Yesu ya gaya wa Siman: “Wani mai-bada bashi yana da mabarta biyu: ɗayan sule ɗari biyar ke kansa, ɗayan kuma sule hamsin. Sa’anda ba su da abin biya, ya yafe masu duka biyu. A cikinsu fa wanene za ya fi sonsa? Siman ya amsa, ya ce, ina tsammani, shi wanda aka yafe masa mai-yawa.” Yesu ya amsa: “Kā yanka daidai.” (Luk 7:41-43) Allah yana bin dukanmu bashin biyayya, saboda haka, sa’ad da muka yi masa rashin biyayya kuma muka yi zunubi, mun kasa biyan Allah abin da ya cancance shi. Ta hakan muna tara bashi. Amma, Jehobah yana kama ne da mai ba da bashi wanda yake a shirye ya yafe basussuka. Yesu yana nuni ne ga basussukanmu, sa’ad da ya ƙarfafa mabiyansa su yi addu’a ga Allah kuma su roƙe shi: “Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda mu kuma muke gafarta wa waɗanda ke yi mana laifi.” (Mat. 6:12) Luka 11:4 ta nuna cewa waɗannan basussuka zunubai ne.

A kan waɗanne yanayi ne Allah ya gafarta zunubai a dā? Cikakken adalcinsa ya bukaci mutuwa don zunubi. Saboda haka, Adamu ya mutu saboda zunubinsa. Amma, a ƙarƙashin Dokar da Allah ya ba al’ummar Isra’ila, za a iya gafarta wa mai laifi zunubansa idan ya yi hadayar dabba ga Jehobah. Manzo Bulus ya ce: “Saura kaɗan sai in ce dukan abu, bisa ga shari’a, da jini a kan tsarkake shi, kuma in ba zubawar jini babu gafara.” (Ibran. 9:22) Yahudawa ba su san wata hanyar da ta fi wannan da za a samu gafara daga wurin Allah ba. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa mutane a zamanin Yesu sun ƙi amincewa da abin da ya gaya wa matar. Waɗanda suke cin abinci tare da Yesu suka fara cewa a cikin ransu: “Wanene wannan har da ya ke gafarta zunubai?” (Luk 7:49) Saboda haka, bisa menene za a gafarta laifofin wannan matar mai zunubi?

Annabci na farko da aka furta bayan da ma’aurata na farko suka yi tawaye ya yi maganar nufin Jehobah na ta da ‘zuriya’ wanda Shaiɗan da ‘zuriyarsa’ za su ƙuje duddugensa. (Far. 3:15) An yi wannan ƙujewar sa’ad da maƙiyan Allah suka kashe Yesu. (Gal. 3:13, 16) Jinin da Kristi ya zubar ya kasance a matsayin fansa da ya ’yantar da ’yan Adam daga zunubi da mutuwa. Tun da yake ba abin da zai iya hana Jehobah cika nufinsa, da ya furta kalaman da ke rubuce a Farawa 3:15, a ra’ayin Allah kamar an riga an biya fansar ne. Da haka, zai iya gafarta zunuban waɗanda suka ba da gaskiya ga alkawuransa.

Kafin zamanin Kiristoci, Jehobah ya ambata wasu mutane masu aminci. A cikinsu akwai Anuhu, Nuhu, Ibrahim, Rahab, da Ayuba. Da bangaskiya, sun saurari cikar alkawuran Allah. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Ibrahim ya gaskanta Allah, aka lissafta wannan kuwa adalci a gare shi.” Game da Rahab, Yaƙub ya ce: “Haka nan kuma Rahab karuwan nan, . . . ba ta wurin ayyuka ta barata ba?”—Yaƙ. 2:21-25.

Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya yi zunubai da yawa masu tsanani, amma yana da bangaskiya mai ƙarfi ga Allah na gaskiya kuma ya nuna ya tuba ta gaske a kowane lokaci. Ƙari ga haka, Nassosi sun ce: “Allah ya ayana [Yesu] abin fansa ne, ta wurin bangaskiya, bisa ga jininsa, domin a bayyana adalcinsa, inda ya bar lura da zunubai marigaya cikin jimrewar Allah; domin bayyanuwar adalcinsa a cikin zamani na yanzu: domin shi da kansa shi barata, ya kuma baratar da wanda yake da bangaskiya cikin Yesu.” (Rom. 3:25, 26) Bisa ga hadayar fansa ta Yesu da za a yi tanadinsa nan gaba, Jehobah ya gafarta laifofin Dauda ba tare da taka nasa bukatu na adalci ba.

Babu shakka, irin wannan yanayin ne matar da ta shafa ƙafafun Yesu da māi ta samu kanta. Ta yi rayuwa ta lalata, amma ta tuba. Ta fahimci cewa tana bukatan fansa daga zunubi kuma ta wurin abin da ta yi ta nuna cewa tana godiya sosai ga mutumin da ta wurinsa Jehobah zai yi tanadin wannan fansa. Ko da yake ba a yi hadayar ba a lokacin, hadayar ta zama tabbas har ake amfani da fa’idodinta ga mutane kamar ta. Shi ya sa Yesu ya gaya mata: “An gafarta maki zunubanki.”

Kamar yadda wannan labarin ya nuna sarai, Yesu bai guji masu zunubi ba. Ya yi musu alheri. Bugu da ƙari, Jehobah yana a shirye ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba. Wannan tabbaci ne mai ban al’ajabi kuma mai ƙarfafawa ga mu ’yan Adam ajizai!

[Hoton da ke shafi na 7]

An lissafa wannan adalci a gare su

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba