Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 8/15 pp. 17-19
  • Gayyata ga Kowa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gayyata ga Kowa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Bethel?
  • Ka Sadu da Wasu da Suke Bethel
  • Ziyara Tana Iya Ƙarfafawa
  • Ka Zo Ka Ziyarci Bethel!
  • Ayyukan Kirki da Jehobah Ba Zai Manta da Su Ba
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Wane Irin Wuri Ne Bethel?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 8/15 pp. 17-19

Gayyata ga Kowa!

GAYYATAR menene? Gayyata na ziyartan ɗaya daga cikin ofisoshin reshe na Shaidun Jehobah da ake kira Bethel. Da akwai rassa guda 118 a ƙasashe dabam-dabam. Sau da yawa baƙi suna nuna godiyarsu ga abin da suka gani da ake yi a Bethel.

Bayan da ya ga ma’aikata da yawa masu aiki tuƙuru da farin ciki suna hidima ga Jehobah a ofishin reshe da ke Mexico, hakan ya burge wani matashi ɗalibin Littafi Mai Tsarki sosai har ya yi tambaya: “Menene zan yi don in zauna a nan in yi aiki?” Sai aka gaya masa: “Da farko, za ka yi baftisma. Bayan haka yana da kyau ka yi hidimar majagaba, wato, mai shelar Mulki na cikakken lokaci.” Matashin ya yi abubuwan da aka gaya masa ya yi, kuma shekara biyu bayan hakan aka gayyace shi ya yi hidima a Bethel da ke Mexico, inda yake hidima shekaru 20 yanzu.

Menene Bethel?

A yaren Ibrananci, “Bethel” yana nufin “Gidan Allah.” (Far. 28:17, 19) Ana amfani da gine-ginen da ke ofisoshin reshe dabam-dabam don a buga da kuma rarraba Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki kuma a ba da taimako na ruhaniya ga ikilisiyoyi fiye da 100,000 na Shaidun Jehobah a dukan duniya. Masu aiki a Bethel kusan 20,000, maza da mata daga wurare da al’adu dabam-dabam sun saɗaukar da kansu don su yi hidima ta cikakken lokaci ga Jehobah da kuma ’yan’uwansu na ruhaniya. Waɗanda suka yi shekaru da yawa a wannan aiki na Kirista suna hidima tare da matasa masu ƙarfi. Da yamma da kuma ƙarshen mako, waɗanda suke cikin iyalin Bethel suna more tarayya a taro da kuma hidimar Kirista a ikilisiyoyi na Shaidun Jehobah da suke kusa. Suna kuma yin amfani da lokacin da ba sa aiki don nazarin Littafi Mai Tsarki, nishaɗi, da kuma kula da batutuwa na kansu.

Waɗanda suke cikin iyalin Bethel suna karɓan ɗan guzuri na kuɗi a kowane wata. Suna cin abinci mai ɗanɗano mai gina jiki kuma suna da masauki masu kyau da tsabta. Gidajen Bethel ba masu tsada ba ne. Amma, suna da kyau. Abubuwan da ke burge baƙin da suka ziyarci wurin su ne yadda ake kula sosai da gine-ginen da mahallin, yadda tsarin aikin yake tafiya sumul da kuma halin alheri da haɗin kai da ke Bethel. Kowa yana aiki tuƙuru, duk da haka ba wanda ya taƙure ainun da bai zai kasance da fara’a ba. A Bethel, babu nuna bambanci ko fin matsayi saboda irin aikin da mutum yake yi. Kowane aiki yana da muhimmanci, ko shara ne, kula da lambu, dafa abinci, ko kuma yin aiki a inda ake buga littattafai ko ofis. Masu hidima a Bethel suna aiki tare don su tallafa wa hidimar Shaidun Jehobah.—Kol. 3:23.

Ka Sadu da Wasu da Suke Bethel

Bari mu ɗan fahimci waɗanda suke cikin wannan iyali ta dukan duniya. Menene ya motsa su su yi hidima a Bethel? Ka yi la’akari da batun Mario. A lokacin da ya zama Mashaidin Jehobah, Mario yana aiki da ke ba shi kuɗi sosai a wani babban kamfanin mota na Jamus kuma yana da zarafin samun ci gaba. Ba da daɗewa ba bayan baftismarsa, ya ba da kansa ya yi aiki na mako guda a Bethel da ke ƙasarsu. Aka ba shi aikin taimakawa wajen buga littattafai. Mario ya ga bambancin da ke tsakanin abokan aikinsa a Bethel da waɗanda yake aiki tare da su a waje. Sai ya cika takardar shiga hidima na cikakken lokaci a Bethel. Ko da yake danginsa da yawa da abokan aikinsa sun kasa fahimtar dalilin da ya sa ya yi hakan, a yanzu Mario yana farin cikin yin hidima a Bethel a ƙasar Jamus.

Mutane da yawa sun shiga hidima a Bethel ba tare da zuwa makaranta na musamman ko koyan wasu ayyuka na musamman ba. Hakan yake da Abel, wanda a yanzu ya yi shekaru 15 yana hidima a Bethel da ke ƙasar Mexico. “Bethel ya zama makaranta na gaske a gare ni,” in ji shi. “Na koyi yin amfani da na’urori na zamani na buga littattafai. Na san cewa da wannan ilimin, ina iya samun kuɗi sosai a waje, amma ba zan samu abin da nake morewa a nan ba, wato, rayuwa mai gamsarwa da kwanciyar hankali ba tare da damuwa da gasa na wuraren aiki masu yawa ba. Na samu koyarwa da ta fi kyau, wadda ta taimaka mini in samu ci gaba a ruhaniya kuma na samu ilimi. Ba zan iya samun irin wannan amfani na ruhaniya ba har a jami’a mafi kyau.”

Ziyara Tana Iya Ƙarfafawa

Ziyarar Bethel kawai tana kasancewa da tasiri mai kyau ga ruhaniyar mutum. Abin da ya sami Omar ke nan, a ƙasar Mexico. Mamarsa ta koya masa gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Amma sa’ad da ya kai ɗan shekara 17, Omar ya daina halartan taron Kirista da kuma fita hidimar fage. Daga baya ya soma munanan halaye da biɗan abubuwan duniya. Sa’ad da yake aiki da wani kamfanin sadarwa, Omar yana cikin tawagar kamfanin da suka ziyarci Bethel a Mexico. Omar ya ce: “Bayan da muka gama, wanda ya gayyace mu ya kai mu zagaya. Abin da na gani da yadda aka bi da ni cikin alheri ya sa na yi tunani game da irin rayuwar da nake yi, wadda take bare daga Jehobah. Nan da nan na soma halartan taro kuma na soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Watanni shida bayan na ziyarci Bethel, na yi baftisma. Na gode wa Jehobah da ƙarfafawar da na samu ta wurin wannan ziyartan Bethel.”

Masahiko a Japan ya yi girma a iyalin Shaidu. Amma, ya soma tunanin cewa hanyar rayuwa ta Kirista tana matsa wa mutum lamba. Ya shaƙu ainun a ayyukan makaranta kuma ya daina halartan taro da saka hannu a aikin wa’azi. Masahiko ya tuna: “Wata rana iyalinmu da wasu abokai Kirista suka tsai da shawarar zuwa zagaya a Bethel. Domin iyalina sun nace, sai na bi su. Da na zagaya Bethel, sai na samu wartsakewa da ban taɓa samu ba. Farin cikin da na samu ta wurin cuɗanya da sauran Kiristoci a lokacin tafiyar wani abu ne da ban taɓa samu ba a wajen abokaina da ba Shaidu ba. Sai na soma sha’awar bin hanyar rayuwa ta Kirista, kuma na tsai da shawarar soma nazarin Littafi Mai Tsarki.” Masahiko yanzu yana hidima na cikakken lokaci a ikilisiyarsu.

Wata Mashaidiya daga Faransa ta ƙaura zuwa Moscow don ta yi aiki. A wajen ta daina cuɗanya da mutanen Jehobah kuma ruhaniyarta ta yi sanyi. Sai ta soma yin lalata kuma daga baya ta auri wani da ba Mashaidi ba. Sai wata Mashaidiya daga Faransa ta ziyarce ta, kuma suka yi tafiya tare zuwa St. Petersburg, a Rasha don su ziyarci Bethel da ke wajen. Ta rubuta: “An marabce mu sosai a Bethel, kuma hakan ya taɓa ni. Akwai salama sosai a wajen. Na ga cewa akwai ruhun Jehobah. Yaya na yi irin wannan kuskure na janyewa daga ƙungiyar Jehobah? Bayan ziyara ta zuwa Bethel, na yi addu’a don taimakon Jehobah kuma na soma koya wa yarana Littafi Mai Tsarki da sabon ƙudiri.” Ƙari ga taimako na ruhaniya da wannan Mashaidiya da ta raunana a dā a ruhaniya ta samu, ziyararta zuwa Bethel ya ƙarfafa ta sosai kuma bayan haka ta samu ci gaba mai kyau.

Yaya waɗanda ba su san Shaidun Jehobah ba da suke ziyartan Bethel suka ji? A shekara ta 1988, Alberto, wanda ya shaƙu da siyasa sosai, ya ziyarci Bethel da ke ƙasar Brazil. Tsabta, tsarin abubuwa, da kuma musamman rashin ɓoye-ɓoye a aikin da ake yi ya burge shi sosai. Ba da daɗewa ba kafin ya je zagayar Bethel, Alberto ya ziyarci makarantar tauhidi inda ƙanin matarsa yake hidima a matsayin firist. Alberto ya lura da bambancin. “Dukan abubuwan da ake yi a makarantar ana yin sa ne a ɓoye,” in ji Alberto. Ba da daɗewa ba bayan ya ziyarci Bethel, ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki, ya daina siyasa, kuma yanzu yana hidima a matsayin dattijo a ikilisiya.

Ka Zo Ka Ziyarci Bethel!

Mutane da yawa sun ƙoƙarta sosai don su ziyarci ofishin reshe da ke ƙasarsu. Alal misali, a Brazil, Paulo da Eugenia sun tara kuɗi har shekaru huɗu domin su yi tafiyar kwana biyu, wato kilomita 3,000 a bas don su ga Bethel da ke wannan ƙasar. Sun ce: “Kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu. Yanzu muna da cikakken ra’ayi game da ƙungiyar Jehobah. Sa’ad da muka bayyana aikin da ake yi a Bethel ga ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki, a wani lokaci suna tambayarmu, ‘Kun taɓa zuwan wajen ne?’ Yanzu muna iya cewa e.”

Akwai ofishin reshe da kuma gidan Bethel a ƙasarku ko kuma ƙasar da ke kusa da ku? Muna gayyatarku ku ziyarci wajen. Babu shakka za a marabce ku sosai kuma ku samu amfani na ruhaniya mai girma daga ziyartan Bethel.

[Hoton da ke shafi na 18]

Mario

[Hoton da ke shafi na 18]

Abel

[Hoton da ke shafi na 18]

Jamus

[Hoton da ke shafi na 18]

Japan

[Hoton da ke shafi na 18]

Brazil

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba