Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 9/15 pp. 3-7
  • Yin Hidima A Lokacin Faɗaɗawa Mai Girma

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Hidima A Lokacin Faɗaɗawa Mai Girma
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jimre Tsanantawa
  • Tarurrukan Gunduma Sun Ƙarfafa Mu
  • Saka Hannu Sosai a Aikin Faɗaɗawa
  • Aikin Kula da Da’ira
  • Hidimar Wa’azi a Ƙasar Waje
  • Ganin Faɗaɗawa a Reshen
  • Ƙarin Mutane da ke Tallafa wa Aikin Faɗaɗawar da Son Rai
  • Abin da Na Cim Ma a Hidima ta Cikakken Lokaci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Na Ji Dadin Koya da Kuma Koyar da Wasu Game da Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Jehobah Ya Albarkace Ni Sosai Don Zabin da Na Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 9/15 pp. 3-7

Yin Hidima A Lokacin Faɗaɗawa Mai Girma

Harley Harris ne ya ba da labarin

A ranar 2 ga Satumba, a shekara ta 1950, a birnin Kennett, Missouri, a Amirka. Muna taron da’ira, sa’ad da taron ’yan iska suka kewaye mu. Magajin garin ya kawo Rukunin Tsaro don su kāre mu daga taron jama’a masu taurin kai. Sojoji riƙe da bindigogi da banati sun cika titin. Taron suna ta zage-zage, sa’ad da muka taka zuwa wurin da motocinmu suke kuma muka tafi birnin Cape Girardeau, Missouri, don kammala sauran sashen taron da’irar. A wajen ne aka yi mini baftisma ina ɗan shekara 14. Amma bari in gaya muku yadda na soma bauta wa Jehobah a cikin irin wannan hayaniya.

A FARKON shekarun 1930, iyayen babana da yaransu takwas sun saurari wani tef na jawaban Ɗan’uwa Rutherford kuma suka gaskata cewa sun samu gaskiya. Iyayena, Bay da Mildred Harris sun yi baftisma a shekara ta 1935 a taron gunduma a Washington, D.C. Sun yi farin cikin kasancewa cikin “taro mai-girma,” da aka bayyana a wannan taron!—R. Yoh. 7:9, 14.

An haife ni shekara ɗaya bayan wannan aukuwar. Kuma bayan shekara ɗaya, iyayena suka ƙaura zuwa wani yankin da babu shaidu ko ikilisiya a Missisippi. Sa’ad da muke zaune a wannan yankin, ba mu samu ziyarar mai kula mai ziyara ba. Iyalinmu tana tattaunawa da Bethel ta hanyar wasiƙu kuma mun halarci manyan taro, a wannan lokacin, wannan cuɗanyar ce kaɗai muke yi da ’yan’uwanci.

Jimre Tsanantawa

A lokacin Yaƙin Duniya na biyu, Shaidun Jehobah sun fuskanci tsanantawa don tsaka-tsakinsu. Mun ƙaura zuwa garin Mountain Home, Arkansas. Wata rana, ni da babana muna wa’azi a kan titi. Sai wani mutum ya fizge mujallun daga hannun babana, ya cinna musu wuta, kuma ya ƙona su nan da nan. Ya kira mu matsorata don mun ƙi zuwa yaƙi. Da yake ni ɗan shekara biyar ne kawai, sai na soma kuka. Babana ya kalli mutumin bai ce uffan ba har sai da mutumin ya tafi.

Amma da akwai mutanen kirki da suke son mu. Akwai lokacin da taron ’yan iska suka kewaye mu a cikin motarmu, sai wani lauyan gwamnati a yankin ya ga gungun mutanen. Sai ya tambaye su, “Menene ke faruwa ne?” Sai wani mutum ya amsa, “Waɗannan Shaidun Jehobah ba sa son su yi yaƙi domin ƙasarsu!” Sai lauyan ya yi tsalle ya hau gefen motarmu kuma ya ce da babbar murya: “Na yi faɗa a Yaƙin Duniya na ɗaya, kuma zan yi a wannan ma! Ku ƙyale mutanen nan su tafi, ba sa neman faɗa!” Taron suka watse a hankali. Muna godiya ga irin waɗannan mutanen kirki da suka nuna mana alheri!—A. M. 27:3.

Tarurrukan Gunduma Sun Ƙarfafa Mu

Taron gunduma da aka yi a birnin St. Louis, Missouri, a shekara ta 1941 ne ainihin abin da muke bukata. In ji wani kimantawa da aka yi, fiye da mutane 115,000 ne suka halarta. An yi wa mutane 3,903 baftisma! Na tuna jawabin Ɗan’uwa Rutherford mai jigo “Children of the King.” (“Yaran Sarki”) Ya yi magana kai tsaye ga mu yara ƙanana, kuma dukanmu mun karɓi kyakkyawan littafi mai kala shuɗi mai suna Children. Wannan taron ya ƙarfafa ni in jimre abin da ya faru a shekara ta gaba, shekarar da zan fara makarantar firamare. An kore ni da yaran ɗan’uwan babana daga makaranta don ba mu sara wa tuta ba. Muna zuwa makaranta a kowace rana don mu ga ko shugabannin makarantar za su canja ra’ayinsu. Ranaku da yawa muna keta daji kafin mu kai makaranta, amma sai a kore mu. Amma, na ɗauki hakan a matsayin hanyar nuna amincinmu ga Mulkin Allah.

Amma, ba da daɗewa ba, Babban Kotu na Amirka ya ba da doka cewa sara wa tuta ba dole ba ne. Sai muka koma makaranta. Malamin mutumin kirki ne sosai kuma ya ƙyale mu mu koyi darussan da ba mu koya ba. Abokan makarantarmu sun bi da mu cikin daraja.

Na kuma tuna taron da aka yi a birnin Cleveland, Ohio, a shekara ta 1942, inda Ɗan’uwa Nathan H. Knorr ya ba da jawabin nan “Peace—Can It Last?” (“Salama Za Ta Daɗe Kuwa?”) Wannan tattaunawa ta Ru’ya ta Yohanna sura ta 17 ta nuna cewa salama za ta kasance bayan Yaƙin Duniya na biyu. Saboda haka, ana ganin za a samu ƙaruwa. Don yin shiri saboda wannan ƙaruwa, an buɗe Makarantar Gilead a shekara ta 1943. A lokacin, ban sani ba cewa makarantar za ta shafi rayuwata a nan gaba. Hakika an samu salama bayan yaƙin kuma tsanantawa ta ragu. Amma, sa’ad da Yaƙin Koriya ya soma a shekara ta 1950, tsanantawa ga aikinmu na wa’azi ya sake somawa, kamar yadda na kwatanta a farkon wannan labarin.

Saka Hannu Sosai a Aikin Faɗaɗawa

A shekara ta 1954, na gama makarantar sakandare, kuma bayan wata guda na soma majagaba. Bayan na yi hidima a garin Kenneth, Missouri, inda taron ’yan iska suka kewaye mu shekara ta 1950, an gayyace ni zuwa Bethel a watan Maris a shekara ta 1955. Times Square (Filin Wasa) yana cikin yankin ikilisiyarmu a tsakiyar Birnin New York. Wannan canji ne daga rayuwar ƙauye! Na samu damar jawo hankalin mutanen New York da suke aiki tuƙuru ta wajen buɗe talifi mai sa mutum ya yi tunani a cikin mujallar, kuma in ce, “Ka taɓa yi wa kanka wannan tambayar?” Mutane da yawa sun karɓi mujallun.

Ɗaya daga cikin abubuwan da na fi so a Bethel shi ne ibadar safiya da Ɗan’uwa Knorr yake gudanarwa. Ya iya sa ayoyin Littafi Mai Tsarki su kasance da gaske kuma ya bayyana su yadda za mu yi amfani da su a rayuwarmu! Yana tattaunawa da mu ’yan’uwa maza marar aure kamar yadda uba zai yi wa ɗansa, sau da yawa yana ba mu shawara mai kyau a kan yadda za mu bi da mata. A shekara ta 1960, na tsai da shawarar yin aure.

Kwanaki 30 kafin lokacin ya kai, na sa takarda don na sanar cewa zan bar Bethel amma ban samu amsa ba. Bayan kwanaki 30, ko da yake ina jin kunya, na yi gaba gaɗi don in yi tambaya ko sun samu takarda ta na barin Bethel. Ɗan’uwa Robert Wallen ne ya amsa wayar kuma ya zo inda nake aiki. Ya tambaye ni ko ina son aikin majagaba na musamman ko kuma aikin mai kula da da’ira. Na amsa: “Ɗan’uwa Robert, shekara ta 24 ne kawai, ba ni da ƙwarewa.”

Aikin Kula da Da’ira

A daren nan, na samu katon ambulan a ɗakina. A ciki akwai afilkeshan na majagaba na musamman da kuma na aikin kula da da’ira. Kai! Abin ya ba ni mamaki ƙwarai! Ina da gata mai girma na yi wa ’yan’uwana hidima a aikin kula da da’ira a kudu maso yammacin Missouri da kuma Kansas na gabas. Amma, kafin na bar Bethel, na halarci taro na masu kula masu ziyara. A furcinsa na kammalawa, Ɗan’uwa Knorr ya ce: “Zama masu kula da da’ira da gunduma ba ya nufin kun san abubuwa fiye da ’yan’uwan da ke ikilisiyoyi. Wasu sun fi ku sanin abubuwa a rayuwa. Amma yanayi bai ƙyale su su samu gatar da kuke da shi ba. Kuna iya koyan abubuwa da yawa daga wajensu.”

Hakan ya zama gaskiya! Ɗan’uwa Fred Molohan da matarsa tare da wansa Charley da ke garin Parsons, Kansas, fitattun misalai ne. Sun koyi gaskiya a farkon shekarun 1900. Abin farin ciki ne in ji labaran abubuwan da suka gani a rayuwa kafin ma a haife ni! Wani ɗan’uwa kuma John Wristen ne, ɗan’uwa tsoho mai kirki a garin Joplin, Missouri, wanda ya yi shekaru yana aikin majagaba. Waɗannan ’yan’uwa ƙaunatattu suna daraja yadda ake gudanar da ƙungiyar Jehobah. Sun sa ni farin ciki a matsayin mai kula da da’irarsu, duk da cewa ni matashi ne.

A shekara ta 1962, na auri Cloris Knoche majagaba mai fara’a mai jan gashi. Na ci gaba da aikin kula da da’ira tare da Cloris. Zama a gidajen ’yan’uwa ya taimaka mana mu san su sosai. Mun ƙarfafa matasa su soma hidima ta cikakken lokaci. Matasa biyu a da’irar, Jay Kosinski da JoAnn Kresyman, sun karɓi wannan shawarar da hannu biyu. Yin wa’azi tare da su da kuma ba su labaran farin cikin rayuwa ta sadaukar da kai ya motsa su su kafa makasudai. JoAnn ya zama majagaba na musamman, kuma Jay ya yi hidima a Bethel. Daga baya, su biyun suka yi aure, kuma yanzu sun yi shekaru 30 suna hidimar kula da da’ira.

Hidimar Wa’azi a Ƙasar Waje

A shekara ta 1966, Ɗan’uwa Knorr ya tambaye mu ko muna son yin hidima a wata ƙasa. Muka amsa, “Muna jin daɗin hidimar da muke yi, amma idan da bukata a wani wuri, muna shirye.” Bayan mako guda, aka gayyace mu zuwa Makarantar Gilead. Abin farin ciki ne na koma Bethel sa’ad da muke halartar makarantar kuma mu kasance tare da mutane da yawa da nake ƙauna da kuma girmamawa! Mun kuma ƙulla abuta da ɗalibai da ke cikin ajinmu, kuma suna hidima da aminci har yau.

An tura ni da Cloris zuwa Ecuador a Amirka ta Kudu tare da Dennis da Edwina Crist, Ana Rodríguez, da Delia Sánchez. Dennis da Edwina Crist suka tafi Quito, babban birnin. Kamar mu, Ana da Delia, zuwa Cuenca, birni na uku mafi girma a Ecuador. Yankin ya haɗa da lardi biyu. Ikilisiyar Cuenca ta farko ta soma a falonmu. Mu huɗu ne tare da wasu mutane biyu. Muna tunanin yadda za mu iya yin aikin wa’azi.

Cuenca tana cike da coci, saboda haka, a ranakun bukukuwa, mutanen addini masu tafiya a jere suna cika birnin. Amma, mutanen Cuenca suna da tambayoyi masu yawa. Alal misali, sa’ad da na soma saduwa da Mario Polo, wanda ya ci gasar tuƙa babur a Cuenca, na yi mamakin tambayar da ya yi, “Wacece karuwa da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna?”

Wani lokaci kuma, Mario ya zo gidanmu daddare, ya ɗan damu. Wani fasto ya ba shi wasu littattafai da suke sūkar Shaidun Jehobah. Na gaya masa cewa ya kamata a ƙyale wanda ake zargi ya kāre kansa. Saboda haka, washegari, Mario ya gayyace ni da faston zuwa gidansa don mu amsa zargin. A wannan taron, na ba da shawarar mu yi magana a kan Allah-Uku-Cikin Ɗaya. Sa’ad da faston ya karanta Yohanna 1:1, Mario da kansa ya bayyana ma’anar Yohanna 1:1 da kyau. Haka muka yi da kowace ayar Littafi Mai Tsarki da aka ambata. Saboda haka, faston ya tafi ba tare da ba da ma’anar Allah-Uku-Cikin Ɗaya ba. Hakan ya tabbatar wa Mario da matarsa cewa mu muke da gaskiya, kuma suka zama masu goyon bayan koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai. Abin farin ciki ne ganin ikilisiyoyin da ke cikin birnin Cuenca sun ƙaru zuwa 33 kuma a cikin yanki mai faɗi inda muka soma hidima, ya ƙaru zuwa adadin 63, hakika hakan ƙaruwa ne mai girma!

Ganin Faɗaɗawa a Reshen

A shekara ta 1970, an gaya mini in tafi reshen da ke Guayaquil tare da Al Schullo. Mu biyun mun kula da aikin reshe. Joe Sekerak ya yi aiki na ɗan lokaci na shirya littattafan da ake aika wa ikilisiyoyi 46 da ke dukan ƙasar. A cikin wani ɗan lokaci, Cloris tana aikin wa’azi sa’ad da nake aiki a Bethel. Ta taimaka wa mutane 55 su yi baftisma, sau da yawa tana samun ɗalibai uku zuwa biyar da suke baftisma a manyan taro.

Alal misali, Cloris ta yi nazari da wata mata mai suna Lucresia, wadda mijinta yake hamayya sosai da nazarin. Duk da haka, Lucresia ta yi baftisma kuma ta soma hidimar majagaba na kullum. Ta koya wa yaranta hanyoyin Jehobah. Yanzu yaranta maza biyu dattawa ne, ɗaya yana hidima na majagaba na musamman; ’yarta tana hidimar majagaba. Jikarta ta auri ɗan’uwa mai hankali, su ma suna hidimar majagaba na musamman. Wannan iyalin ta taimaka wa mutane da yawa su koyi gaskiya.

A shekara ta 1980 akwai masu shela 5,000 a Ecuador. Mutane sun soma fin ƙarfin ƙaramin ofishinmu. Wani ɗan’uwa ya ba mu filin da ya kai eka 80 a bayan garin Guayaquil. A shekara ta 1984 muka soma gina sabon ofishin reshe da Majami’ar Babban Taro a wannan filin, kuma an keɓe ginin a shekara ta 1987.

Ƙarin Mutane da ke Tallafa wa Aikin Faɗaɗawar da Son Rai

Cikin shekaru da yawa, abin farin ciki ne mu ga masu shela da yawa da majagaba daga wasu ƙasashe da suka zo Ecuador don su taimaka a inda ake da bukata mai girma na masu shelar Mulki. Wani misali da na tuna sarai shi ne na Andy Kidd, wani malamin makaranta daga Kanada da ya yi murabus. Ya ƙaura zuwa Ecuador a shekara ta 1985 sa’ad da yake ɗan shekara 70 kuma ya yi hidima da aminci har mutuwarsa a shekara ta 2008 sa’ad da yake ɗan shekara 93. Sa’ad da na sadu da shi da farko a inda yake hidima, shi kaɗai ne mai kula da wata ’yar ƙaramar ikilisiya. Ko da yake yana faman koyon harshen Sfanisanci, ya ba da jawabi ga jama’a kuma ya gudanar da Nazarin Hasumiyar Tsaro. Ya kuma gudanar da Makarantar Hidima ta Allah da yawancin sashe ne na Taron Hidima! A wannan yankin yanzu, akwai ikilisiyoyi biyu, da masu shela wajen 200 da kuma dattawa masu yawa.

Wani ɗan’uwa, Ernesto Diaz, wanda ya ƙaura daga Amirka da iyalinsa, ya ce bayan ya yi watanni takwas a Ecuador: “Yaranmu uku sun koyi yaren kuma sun zama masu koyar da Littafi Mai Tsarki sosai a yaren Sfanisanci. A matsayin uba, na cim ma makasudin da kamar ba zai yiwu ba a wannan zamanin, wato, na zama majagaba na kullum, ina yin hidima na cikakken lokaci tare da iyalina. Dukanmu muna gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki guda 25. Dukan waɗannan sun ƙara haɗa kan iyalinmu, kuma fiye da kome, na kusaci Jehobah fiye da yadda ban taɓa yi ba.” Muna ƙaunar waɗannan ƙaunatattun ’yan’uwa maza da mata sosai!

An ƙara faɗaɗa reshen a shekara ta 1994, hakan ya ƙara girman wurin sau biyu. A shekara ta 2005 mun wuce adadin masu shela 50,000 da ake bukata, hakan ya sa ƙara faɗaɗa reshen ya wajaba. Wannan ya ƙunshi ƙara girman Majami’ar Taro, sabon mazauni, da ofisoshin fassara. An keɓe waɗannan sababbin gine-ginen a ranar 31 ga Oktoba, 2009.

Sa’ad da aka kore ni daga makaranta a shekara ta 1942, da akwai wajen Shaidu 60,000 a Amirka. Yanzu sun fi miliyan ɗaya. Sa’ad da muka zo Ecuador a shekara ta 1966, akwai masu shelar Mulki 1,400 a nan. Yanzu akwai masu shela fiye da 68,000. Kuma babu shakka za a samu ƙari daga masu nazarin Littafi Mai Tsarki guda 120,000 da kuma fiye da mutane 232,000 da suka halarci Tuna Mutuwar Kristi a shekara ta 2009. Hakika, Jehobah ya albarkaci mutanensa a hanyar da ba mu taɓa zato ba. Abin farin ciki ne da muke raye a lokaci da kuma wurin da ake samun faɗaɗawa mai girma!a

[Hasiya]

a Sa’ad da ake shirya wannan talifin don bugawa, Harley Harris ya mutu da amincinsa ga Jehobah.

[Hotuna da ke shafi na 5]

Babban taro da aka yi a fili (shekara ta 1981) da Majami’ar Babban Taro a Guayaquil (shekara ta 2009) a wannan filin

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba