Ka Kusaci Allah
Yana ‘Sane da Zukatan ’Ya’yan Mutane’
2 LABARBARU 6:29, 30
WANE ne a cikinmu bai taɓa jin cewa ya gaji da ƙalubale da kuma matsaloli na rayuwa ba? A wasu lokatai, kamar dai babu wanda zai iya fahimtar gwagwarmayar da muke fama da ita ko kuma yadda muke ji a zuciyarmu. Duk da haka, akwai wanda ya fahimci yadda muke ji sosai, Jehobah Allah ne. Za mu iya samun ƙarfafawa a kalaman Sulemanu, waɗanda ke 2 Labarbaru 6:29, 30.
Sulemanu ya yi addu’a a lokacin da yake keɓe haikalin da ke Urushalima a shekara ta 1026 K.Z. A cikin addu’arsa, wadda ake tunanin ta kai minti goma, Sulemanu ya ɗaukaka Jehobah a matsayin Allah mai aminci, wanda Mai cika alkawuransa ne, kuma Mai jin addu’a.—1 Sarakuna 8:23-53; 2 Labarbaru 6:14-42.
Sulemanu ya roƙi Allah ya ji roƙon masu bauta masa. (Aya ta 29) Ko da yake Sulemanu ya ambata bala’o’i masu yawa (Aya ta 28), ya ambata cewa kowane mai bauta wa Allah yana sane da “irin wahalarsa” da kuma “baƙin cikinsa.” Wani yana da matsala dabam da ke sa shi baƙin ciki yayin da wani yake ɗauke da wani nauyi dabam.
Ko da mece ce matsalar, masu tsoron Allah ba za su ɗauki matsalolinsu su kaɗai ba. A cikin addu’arsa, Sulemanu yana nuni ne ga kowane mai bauta da zai “miƙe hannuwansa,” ya yi addu’a ga Jehobah daga zuciyarsa.a Wataƙila Sulemanu ya tuna cewa sa’ad da mahaifinsa, Dauda, yake cikin mugun baƙin ciki, ya ce: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji.”—Zabura 55:4, 22.
Yaya Jehobah zai amsa roƙo na gaske da aka yi na neman taimako? Sulemanu ya roƙi Jehobah: “Sai ka ji daga sama wurin zamanka, ka gafarta, ka sāka wa kowane mutum bisa ga dukan aikinsa.” (Aya ta 30) Sulemanu ya san cewa “Mai-jin addu’a” yana kula da masu bauta masa ba a matsayin rukuni ba kawai, amma a matsayin ɗaɗɗaya. (Zabura 65:2) Jehobah yana yin tanadin taimakon da ake bukata, har da gafarta wa mai zunubin da ya koma ga Allah da dukan zuciyarsa.—2 Labarbaru 6:36-39.
Me ya sa Sulemanu yake da tabbaci cewa Jehobah zai ji roƙon mai zunubin da ke bauta masa da ya tuba? Sa’ad da yake ci gaba da addu’arsa, Sulemanu ya ce: “[Jehobah] kana sane da zuciyarsa; (gama kai, i, kai kaɗai ka san zukatan ’ya’yan mutane).” Jehobah ya san wahala ko baƙin cikin da kowanne mai bauta masa cikin aminci yake ɗauke da shi a cikin zuciyarsa, kuma Ya damu da wahalar.—Zabura 37:4.
Za mu iya samun ƙarfafawa daga addu’ar Sulemanu. Mutane ba za su iya fahimtar abin da muke ji a cikin zuciyarmu sosai ba, wato, ‘wahalarmu’ da ‘baƙin cikinmu.’ (Misalai 14:10) Amma Jehobah ya san zuciyarmu, kuma yana kula da mu sosai. Idan muka gaya masa abin da ke cikin zuciyarmu a addu’a, hakan zai rage yawan alhininmu. “Kuna zuba dukan alhininku a bisansa,” in ji Littafi Mai Tsarki, “domin yana kula da ku.”—1 Bitrus 5:7.
[Hasiya]
a A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, ‘miƙa hannuwa,’ wato, buɗe hannuwa zuwa sama, alama ce ta yin addu’a.—2 Labarbaru 6:13.