Ka “Nemi Mafaka A Sunan Jehobah”
“Zan bar mutane . . . masu-tawali’u, za su kuwa nemi mafaka ga sunan Jehobah.”—ZAF. 3:12, NW.
1, 2. Wace guguwa ta alama ce za ta auko wa ’yan Adam ba da daɗewa ba?
A WANI lokaci sa’ad da kake tafiya, ka taɓa neman mafaka daga ruwan sama a ƙarƙashin bukka? Amma idan ana son a yi hadari ko kuma bala’in guguwa, wannan bukkar ba za ta ba ka isashen kāriya ba, kana bukatar ka nemi mafaka a cikin gida mai ƙarfi.
2 Amma wani irin hadari dabam yana nan tafe, wanda ke wa wanzuwar ’yan Adam barazana. ‘Ranar kaɗaici’ ce ta alama. Wannan “ranar Ubangiji” za ta shafi dukan ’yan Adam. Duk da haka, za mu iya samun mafaka da muke bukata. (Karanta Zafaniya 1:14-18.) Ta yaya za mu iya yin hakan a “ranar fushin Ubangiji” da za ta soma ba da daɗewa ba?
Kwanakin Lalatarwa a Lokacin da Aka Rubuta Littafi Mai Tsarki
3. Wanne “hadarin ƙanƙara” ne ya auko wa masarautar ƙabila goma na Isra’ila?
3 Ranar Jehobah za ta soma da halaka dukan addinan ƙarya da suke duniya. Game da yadda za mu iya samun mafaka, za mu iya neman amsa a tarihin mutanen Allah na dā. Ishaya da ya yi rayuwa a ƙarni na takwas K.Z., ya kamanta shari’ar Jehobah a kan mulki na Isra’ila na ƙabila goma mai ridda da “hadarin ƙanƙara” da mutane ba za su iya hana ta ba. (Karanta Ishaya 28:1, 2.) Wannan annabcin ya samu cikawa a shekara ta 740 K.Z., sa’ad da Assuriya ta kai wa waɗannan ƙabilun hari a ƙasarsu, kuma Ifraimu ta fi shahara a cikin ƙabilu goma ɗin.
4. Ta yaya “ranar Ubangiji” ta auko wa Urushalima a shekara ta 607 K.Z.?
4 An yi wa Isra’ilawa marasa aminci hukunci a shekara ta 607 K.Z., ta wurin “ranar Ubangiji” a kan Urushalima da kuma mulkin Yahuda. Wannan aukuwan ta faru ne domin mutanen Yahuda ma sun zama ’yan ridda. Mutanen Babila da ke ƙarƙashin sarautar Nebuchadnezzar sun yi wa Yahuda da kuma babban birninta Urushalima, barazana. Mutanen Yahuda sun koma ga neman taimako na “mafakan ƙarya,” wato, yin haɗin gwiwa da ƙasar Masar. Duk da haka, kamar hadari mai ɓarna, mutanen Babila sun share wannan “mafakar.”—Isha. 28:14, 17.
5. Mene ne zai faru da mutanen Allah a matsayin rukuni sa’ad da aka halaka addinin ƙarya?
5 Babbar ranar Jehobah da ta auko wa Urushalima alama ce ta hukunci da za a wa ridaddun Kiristendom a zamaninmu. Bugu da ƙari, za a halaka sauran “Babila babba,” wato, daular duniya ta addinin ƙarya. Bayan haka, za a halaka sauran mugun tsari na Shaiɗan. Duk da haka, mutanen Allah a matsayin rukuni za su rayu domin suna neman mafaka a Jehobah.—R. Yoh. 7:14; 18:2, 8; 19:19-21.
Mafaka ta Zahiri da ta Ruhaniya
6. Ta yaya mutanen Jehobah za su iya samun mafaka?
6 Ta yaya mutanen Allah za su iya samun mafaka har yanzu a kwanaki na ƙarshe? Muna samun mafaka ta ruhaniya ta wurin “tunawa da sunan [Allah]” cikin addu’a da kuma bauta masa da ƙwazo. (Karanta Malakai 3:16-18.) Amma mun ga cewa ba ma bukatar kawai mu yi tunani game da sunansa ba. Mun karanta: “Dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.” (Rom. 10:13) Akwai nasaba tsakanin kiran sunan Jehobah da kuma ceton rai da yin hakan zai kawo. Kuma mutane masu zukatan kirki da yawa suna ganin bambancin da ke tsakanin Kiristoci na gaske, waɗanda suke “tunawa da sunansa” cikin addu’a da kuma yin hidima a matsayin Shaidunsa, da kuma ’yan Adam da ba sa bauta masa.
7, 8. A wacce hanya ce Kiristoci na ƙarni na farko suka tsira a zahiri, kuma yaya hakan ke faruwa a yau?
7 Duk da haka, ceton da muke da shi ba na ruhaniya kaɗai ba ne. An yi wa mutanen Allah alkawarin mafaka ta zahiri. Mun fahimci hakan don abin da ya faru a shekara ta 66 A.Z. bayan sojojin Roma da suke ƙarƙashin ja-gorar Cestius Gallus suka kai wa Urushalima hari. Yesu ya riga ya annabta cewa za a “gajertadda” waɗannan kwanaki na ƙunci. (Mat. 24:15, 16, 21, 22) Hakan ya faru sa’ad da sojojin Roma ba zato suka ƙyale birnin, wanda hakan ya sa wasu ‘masu rai,’ wato Kiristoci na gaske su “tsira.” Sun samu zarafin fita daga birnin da kuma kewayensa. Wasu sun ƙetare kogin Urdun kuma sun samu mafaka a tudu a gabashin kogin.
8 Za mu iya gwada Kiristoci na wannan zamanin da mutanen Allah a yau. A dā, Kiristoci na ƙarni na farko sun nemi mafaka, mutanen Allah ma a yau za su yi hakan. Amma dai, hakan ba ya nufin yin gudu na zahiri, domin Kiristoci na gaske suna ko’ina a duniya. Duk da haka, a matsayin mutane, “zaɓaɓu” da abokansu amintattu za su tsira daga ƙarshen Kiristendam masu ridda ta yin dogara ga Jehobah da ƙungiyarsa da ke kama da babbar tudu.
9. Waɗanne mutane ne suke ƙoƙari su sa a mance da sunan Jehobah? Ka ba da misali.
9 A wata ɓangare kuma, ya dace a halaka Kiristendam don ba sa koya wa mabiyansu gaskiya game da Allah da kuma ƙa’idodinsa, kuma sun ƙi yin amfani da sunan Allah. A Zamanin Sarakuna, an san sunan Allah sosai a ƙasar Turai. Sunan da aka rubuta da baƙaƙe huɗu na Ibrananci da ake fassara YHWH (ko JHVH), ta bayyana a kan tsabar kuɗi, a gaban gidaje, a littattafai da yawa da Littafi Mai Tsarki, da kuma wasu coci na Katolika da Farostatan. Amma dai, abin da ake yi kwana kwanan nan shi ne kawar da sunan Allah daga fassarar Littafi Mai Tsarki da kuma daina yin amfani da shi gabaki ɗaya. Wani abu da ya nuna hakan shi ne wata Wasiƙa da Congregation for Divine Worship and the Discipline of the Sacrament [Ikilisiya don Bauta ta Allah da Horon Bukukuwa ta Addini] ta rubuta zuwa ga Tarurrukan Bishop game da ‘Sunan Allah,’ a ranar 29 ga Yuni, 2008. A cikin wasiƙar, Cocin Roman Katolika ta shawarci cewa a musanya Baƙaƙe Huɗun da “Ubangiji.” Birnin Vatican sun ba da umurni cewa kada a furta sunan Allah a waƙoƙi da addu’o’i sa’ad da ake hidimomin Addinin Katolika. Kuma shugabannin wasu addinan Kiristendam da waɗanda ba Kiristendam ba sun kuma ɓoye sunan Allah na gaskiya ga miliyoyi masu bautarsa.
Kāriya ga Waɗanda Suke Tsarkake Sunan Allah
10. Ta yaya ake daraja sunan Allah a yau?
10 Akasin abin da wasu addinai suke yi, Shaidun Jehobah suna daraja da kuma ɗaukaka sunan Allah. Suna tsarkake shi ta yin amfani da shi a hanya da ta dace. Jehobah yana daraja waɗanda suke dogara gare shi kuma yana zama kowanne abu da ya dace don ya albarkaci da kuma kāre mutanensa. “Ya kuwa san waɗanda ke sa danganarsu gareshi.”—Nah. 1:7; A. M. 15:14.
11, 12. Wane ne ya ɗaukaka sunan Jehobah a Yahuda ta dā, kuma su wane ne suke yin hakan a yau?
11 Ko da yake yawancin mutane a Yahuda na dā sun zama ’yan ridda, amma akwai wasu da suka “dogara ga sunan Ubangiji.” (Karanta Zafaniya 3:12, 13.) Sa’ad da Allah ya hukunta Yahuduwa marasa imani ta wurin ƙyale Babila ta halaka ƙasar kuma ta kai mutanen ƙasar bauta, an ƙyale wasu kamar Irmiya, Baruch, da Ebed-melek. Sun yi rayuwa ‘cikin tsakiyar’ al’umma mai ridda. Wasu sun kasance da aminci a wurin da aka kai su bauta. A shekara ta 539 K.Z., ƙasar Midiya da Persia a ƙarƙashin ja-gorancin Sairus ta halaka ƙasar Babila. Nan da nan Sairus ya ba da umurni cewa Yahudawa da suka rage su koma ƙasarsu.
12 Game da waɗanda za su more maido da bauta ta gaskiya, Zafaniya ya annabta cewa Jehobah zai cece su kuma zai yi farin ciki. (Karanta Zafaniya 3:14-17.) Hakan ma ya faru a zamaninmu. Bayan an kafa Mulkin Allah a sama, Jehobah ya ceci shafaffu masu aminci da suka rage daga ƙunci na ruhaniya na Babila Babba. Kuma yana farin ciki da su har yau.
13. Wanne ’yanci ne mutane na dukan al’ummai suke morewa?
13 Waɗanda suke da begen yin rayuwa har abada a cikin duniya sun riga sun fita daga cikin Babila Babba kuma suna more ceto daga koyarwa ta addinin ƙarya. (R. Yoh. 18:4) Saboda haka, Zafaniya 2:3 ya samu cikawa sosai a zamaninmu: “Ku biɗi Ubangiji, ku dukan masu-tawali’u na duniya.” Masu tawali’u na dukan al’ummai, ko suna son yin rayuwa a sama ko a duniya, suna dogara ga sunan Jehobah yanzu.
Sunan Allah Ba Laya Ba Ne
14, 15. (a) Mene ne wasu suke amfani da shi a matsayin laya? (b) Mene ne bai kamata a yi amfani da shi a matsayin tsafi ba?
14 Wasu Isra’ilawa sun ɗauki haikali a matsayin laya da zai kāre su daga maƙiyansu. (Irm. 7:1-4) Da farko, Isra’ilawa sun ɗauki akwatin alkawari a matsayin tsafi da zai kāre su a lokacin yaƙi. (1 Sam. 4:3, 10, 11) Constantine Mai Girma ya zana baƙaƙen Helenanci khi da rho, kalmomi biyu na farko na laƙabin nan “Kristi” a Helas a garkuwar sojojinsa yana begen cewa hakan zai kāre sojojinsa a yaƙi. Kuma ana gani cewa Sarki Gustav Adolph na biyu na ƙasar Sweden, wanda ya yi Yaƙi na Shekara Talatin ne ya saka sulken da aka nuna a shafi na 7. Ka lura cewa sunan nan “Iehova” yana a bayyane a wannan maɗaurin wuya.
15 Wasu mutanen Allah waɗanda aljanu suka kai musu hari sun nemi mafaka wurin Jehobah ta kiran sunansa da ƙarfi. Duk da haka, bai kamata a ɗauki wani abu da ke ɗauke da sunan Allah kamar laya a rayuwar yau da kullum ba, kamar yana da tsafi na kāre mutum. Ba abin da ake nufi a nemi mafaka a sunan Jehobah kenan ba.
Yadda Muke Neman Mafaka a Yau
16. Ta yaya za mu iya samun kāriya ta ruhaniya a yau?
16 Muna neman mafaka ga kāriya ta ruhaniya da dukan mutanen Allah suke morewa a yau. (Zab. 91:1) Ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da kuma dattawa a ikilisiya, muna sane da abubuwa na duniya da za su iya yi wa kāriyar barazana. (Mat. 24:45-47; Isha. 32:1, 2) Ka yi tunanin gargaɗin da ake mana a kai a kai game da son abubuwan mallaka, ka kuma yi la’akari da yadda waɗannan gargaɗin ya kāre mu daga matsaloli na ruhaniya. Kuma akwai haɗarin halin babu ruwanmu, wanda zai iya sa mutum ya daina saka hannu a hidimar Jehobah. Kalmar Allah ta ce: “Wadatar wawaye kuma za ta halaka su. Amma dukan wanda ya saurara gareni za ya zauna lafiya, za ya zauna da rai a kwance, ba tsoron masifa.” (Mis. 1:32, 33) Yin ƙoƙari a kasance da tsabtar ɗabi’a tana kuma taimakawa wajen samun kāriya ta ruhaniya.
17, 18. Mene ne yake taimakon miliyoyin mutane su nemi mafaka a sunan Jehobah a yau?
17 Ka kuma yi tunani a kan ƙarfafa da bawa mai aminci ya ba da game da bin shawarar Yesu na yin wa’azin bisharar Mulki a dukan duniya. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Zafaniya ya ambata canjin da zai taimaki mutane su nemi mafaka a sunan Allah. Mun karanta: “Sa’annan zan juya ma al’ummai da harshe mai-tsarki, domin dukansu su kira sunan Ubangiji, su bauta masa da zuciya ɗaya.”—Zaf. 3:9.
18 Mene ne wannan harshe mai-tsarki? Harshe mai tsarki shi ne gaskiya game da Jehobah Allah da kuma nufinsa da ke cikin Kalmarsa. Kana yin amfani da harshen sa’ad da ka gaya wa mutane game da ma’anar Mulkin Allah da kuma yadda zai tsarkake sunansa, yayin da ka nanata kunita ikon mallaka na Allah, kuma sa’ad da ka yi magana da farin ciki game da wannan albarka ta har abada da ’yan Adam za su more. A sakamakon mutane da yawa da suke furta wannan harshe ta alama, mutane da yawa suna ‘kira bisa sunan Jehobah’ kuma suna “bauta masa da zuciya ɗaya.” Hakika, miliyoyin mutane a dukan duniya suna samun mafaka a Jehobah.—Zab. 1:1, 3.
19, 20. Ta yaya yin dogara ga “mafakan ƙarya” ta kasa a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki?
19 Mutane a duniya ma sun jimre da irin waɗannan matsaloli da yawa masu tsanani. Mutane da yawa suna dogara ga ’yan Adam don sun magance matsalolinsu. Ko kuma suna yin bege ga ƙungiyoyin siyasa, kamar yadda ƙasar Isra’ila ta dā ta nemi taimako daga al’ummai da ke kewaye da su, suna zama abokansu. Duk da haka, kun san cewa yin hakan bai taimaki Isra’ilawa ba. Kuma babu wata ƙungiyar siyasa, ko kuwa ƙungiyar Majalisar Ɗinkin Duniya a yau da za ta iya magance matsalolin ’yan Adam. Kuma bai kamata mu dogara ga waɗannan ƙungiyoyin ba. A alamance, Littafi Mai Tsarki ya kira ta “mafakan ƙarya.” Za ku iya ɗaukansu hakan domin za a saɓa wa dukan waɗanda suke neman mafaka a waɗannan ƙungiyoyinsu.—Karanta Ishaya 28:15, 17.
20 Ba da daɗewa ƙanƙara ta alama na ranar Jehobah za ta faɗo a duniya. Ƙulle-ƙulle na ’yan Adam, nukiliya da kuma dukiya ba za su iya kāre su ba. Ishaya 28:17 ya nuna: “Ƙanƙara za ta share mafakan ƙarya, ruwaye kuma za su sha kan maɓoya.”
21. Wane amfani ne za mu iya morewa ta bin shawarar jigon shekara ta 2011?
21 A yanzu da nan gaba, mutanen Jehobah za su samu kāriya ta gaske da maɓuya a Allahnsu, Jehobah. Sunan Zafaniya wanda yake nufin “Jehobah Ya Kāre,” ya nuna wannan wurin mafaka na gaske. Shi ya sa jigon shekara ta 2011 ya dace: “Ka ‘Nemi Mafaka a Sunan Jehobah.’” (Zaf. 3:12) Har yanzu, za mu iya kuma ya kamata mu nemi mafaka a sunan Jehobah, muna dogara gare shi sosai. (Zab. 9:10) Bari mu ci gaba da yin tunani a kan wannan hurarren tabbaci kullum: “Sunan Ubangiji kagara ne mai-ƙarfi: Mai-adalci ya kan gudu ya shiga ciki, shi sami lafiya.”—Mis. 18:10.
Ka Tuna?
• Ta yaya za mu iya neman mafaka a sunan Jehobah yanzu?
• Me ya sa bai kamata mu dogara ga “mafakan ƙarya” ba?
• Wanne alkawari ne aka yi mana a nan gaba?
[Bayanin da ke shafi na 6]
Jigon shekara ta 2011 shi ne: “Ka ‘Nemi Mafaka a Sunan Jehobah.’”—Zafaniya 3:12.
[Inda Aka Ɗauko Hoto shafi na 7]
Thüringer Landesmuseum Heidecksburg Rudolstadt, Waffensammlung “Schwarzburger Zeughaus”