Ku Daraja Aure A Matsayin Baiwa Daga Wurin Allah
“Domin wannan mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne wa matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.”—FAR. 2:24.
1. Me ya sa Jehobah yake bukatar mu daraja shi?
BABU shakka, Jehobah Allah, Wanda shi ne ya kafa aure ya cancanci mu daraja shi. A matsayin Mahalicci, Mai Ikon Mallaka, da Ubanmu na samaniya, ya dace da aka kwatanta shi kamar Mai Bayar da “kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta.” (Yaƙ. 1:17; R. Yoh. 4:11) Wannan alamar ƙaunarsa ce. (1 Yoh. 4:8) Dukan abin da ya koya mana da dukan abin da yake bukata a gare mu da dukan abin da ya ba mu don lafiyarmu ne da kuma amfaninmu.—Isha. 48:17.
2. Waɗanne umurnin ne Jehobah ya ba ma’aurata na fari?
2 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta aure a matsayin ɗaya daga cikin wannan “kyakkyawar” baiwa daga wurin Allah. (Ruth 1:9; 2:12) Sa’ad da Jehobah ya shirya aure na farko, ya ba ma’auratan, Adamu da Hauwa’u, umurnin da zai taimake su su yi nasara. (Karanta Matta 19:4-6.) Da a ce sun bi ja-gorancin Allah, da sun more farin ciki na dindindin. Amma, sun yi banza da umurnin Allah kuma sun samu mummunar sakamako.—Far. 3:6-13, 16-19, 23.
3, 4. (a) Ta yaya mutane da yawa a yau suke nuna rashin daraja ga aure da kuma Jehobah Allah? (b) Waɗanne misalai ne za mu tattauna a talifin nan?
3 Kamar waɗannan ma’aurata na farko, mutane da yawa a yau ba sa bin umurnin Jehobah sa’ad da suke tsai da shawara game da batun aure. Wasu suna zama tare ba su yi aure ba, wasu kuma suna nema su yi gyara ga tsarin aure don ya dace da muradinsu. (Rom. 1:24-32; 2 Tim. 3:1-5) Sun yi banza da gaskiyar nan cewa aure baiwa ce daga wurin Allah, kuma ta ƙin daraja wannan baiwar, sun raina Mai Baiwar, Jehobah Allah.
4 A wasu lokatai, wasu bayin Allah ba sa fahimtar ra’ayin Jehobah game da aure. Wasu ma’aurata Kirista suna tsai da shawara su rabu ko kuma su kashe aurensu ba tare da goyon bayan Nassosi ba. Ta yaya za a guji yin hakan? Ta yaya umurnin Allah da ke Farawa 2:24 ya taimaki Kiristoci ma’aurata su ƙarfafa aurensu? Ta yaya waɗanda suke son yin aure za su shirya yin hakan? Bari mu bincika aure uku da suka yi nasara a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da suka kwatanta yadda daraja Jehobah yake da muhimmanci don sa aure ya jimre.
Ku Kasance da Aminci
5, 6. Wane yanayi ne wataƙila ya gwada Zakariya da Alisabatu, kuma yaya aka yi wa amincinsu albarka?
5 Zakariya da Alisabatu sun yanki shawara mai kyau. Kowannensu ya auri mai aminci ga Jehobah sosai. Zakariya ya yi hidimarsa na firist da kyau, kuma su biyu sun yi biyayya ga Dokar Allah iya ƙarfinsu. Suna da abubuwa da yawa da za su sa su godiya. Duk da haka, idan ka ziyarce gidansu a Yahudiya, za ka fahimci cewa akwai abin da suka rasa. Ba su da yara. Alisabatu bakarariya ce, kuma su biyu sun tsufa.—Luk 1:5-7.
6 Ana daraja haihuwa sosai a Isra’ila ta dā, kuma sau da yawa suna haifan yara da yawa. (1 Sam. 1:2, 6, 10; Zab. 128:3, 4) A lokacin, Ba’isra’ila zai iya sakin matarsa idan ba ta iya haihuwa ba. Amma Zakariya ya kasance tare da matarsa Alisabatu cikin aminci. Da shi da matarsa ba su nemi hujja don su kashe aurensu ba. Ko da yake rashin ’ya’ya ya sa su baƙin ciki, amma sun ci gaba da kasancewa da aminci da juna da kuma Jehobah. Da sannu sannu ta mu’ujiza, Jehobah ya albarkace su da ɗa sa’ad da suka yi tsufa.—Luk 1:8-14.
7. A wacce hanya ce kuma Alisabatu ta kasance da aminci ga mijinta?
7 Alisabatu ta nuna aminci a wata hanya. Sa’ad da ta haifi ɗanta, Yohanna, Zakariya bai iya magana ba domin sa’ad da ya tuhumi Mala’ikan Allah an harbe shi da baibaici. Duk da haka, babu shakka Zakariya ya gaya wa matarsa cewa mala’ikan Jehobah ya ce masa ya sa wa yaron suna “Yohanna.” Maƙwabta da iyalinsa sun so su sa wa yaron sunan mahaifinsa. Amma Alisabatu cikin aminci ta ɗaukaka umurnin da mijinta ya ba ta. Ta ce: “Ba haka ba; za a ce da shi Yohanna.”—Luk 1:59-63.
8, 9. (a) Ta yaya aminci yake ƙarfafa aure? (b) A waɗanne takamammun hanyoyi ne mata da miji za su iya kasance da aminci ga juna?
8 Kamar Zakariya da Alisabatu, ma’aurata a yau suna fuskantar fid da zuciya da wasu ƙalubale. Auren da babu aminci ba zai yi nasara ba. Kwarkwasa da hotunan batsa da zina da kuma wasu halaye suna iya ɓata dangantakar aure. Kuma idan babu aminci a aure, soyayyar za ta soma sanyi. A wasu hanyoyi, aminci tana kamar ganuwa da ta kewaye gidan iyali da take hana baƙi da ba a amince da su ba da kuma masu barazana daga shigowa gidan. Da hakan, idan mata da miji suna kasancewa da aminci ga juna, za su iya kasancewa tare cikin kāriya kuma suna gaya wa juna yadda suke ji, hakan kuma yana sa soyayyarsu ta ƙaru. Hakika, aminci yana da muhimmanci.
9 Jehobah ya ce wa Adamu: ‘Mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne wa matatasa.’ (Far. 2:24) Mene ne hakan yake nufi? Dangantaka na dā da abokai da kuma iyali zai ragu. Wajibi ne kowanne ma’auratan su ba juna lokaci da kula. Abokai da dangogi ba za su kasance da muhimminci fiye da sababbin ma’auratan ba, kuma ma’auratan ba za su ƙyale iyayensu su sa baki a shawarwarin iyalinsu ko kuma saɓaninsu ba. Wajibi ne ma’auratan su manne wa juna. Umurnin Allah ne.
10. Mene ne zai taimaki ma’aurata su gina aminci ga juna?
10 Ko ma a iyalin da ma’aurata ɗaya ba Mashaidi ba ne, aminci yana kawo albarka. Wata ’yar’uwa da mijinta ba mai bi ba ne ta ce: “Ina godiya sosai ga Jehobah don koyar da ni game da yadda zan riƙa ba da kai ga mijina da yi masa biyayya sosai. Kasancewa da aminci da juna ya sa su ci gaba da soyayya da kuma daraja juna na tsawon shekara arba’in da bakwai.” (1 Kor. 7:10, 11; 1 Bit. 3:1, 2) Saboda haka ku yi ƙoƙari sosai don ku sa aboki ko abokiyar aurenku ya ji cewa gaminku yana da kāriya. Ta kalamanku da ayyukanku, ku nemi hanyoyin tabbatar wa aboki ko abokiyar aurenku cewa shi ko ita ce mutum mafi muhimmanci a dukan duniya. Iyakar yadda za ku iya, kada ku ƙyale kowa ko komi ya zo tsakanin ku da abokiyar aurenku. (Karanta Misalai 5:15-20.) Ron da Jeannette, waɗanda suke jin daɗin aurensu fiye da shekara talatin da biyar, sun ce, “Domin mun yi abin da Allah yake bukata a garemu cikin aminci, aurenmu ya yi nasara kuma muna farin ciki.”
Haɗin Kai Yana Ƙarfafa Aure
11, 12. Ta yaya Akila da Biriskilla suka kasance da haɗin kai (a) a gida, (b) a aikinsu, da (c) a hidimar Kirista?
11 Sa’ad da Manzo Bulus ya yi magana game da aminansa Akila da Biriskilla, bai ambata ɗaya kuma ya ƙyale ɗaya ba. Wannan ma’auratan masu haɗin kai misali ne mai kyau game da abin da Allah yake nufi sa’ad da ya ce mata da miji su zama “nama ɗaya.” (Far. 2:24) Suna aiki tare koyaushe a gidansu, a wurin aikinsu, da kuma a hidimar Kirista. Alal misali, sa’ad da Bulus ya fara isa Korinti, Akila da Biriskilla sun gayyace shi ya zauna a gidansu, kuma wataƙila ya zauna a gidan na ɗan lokaci don hidimarsa. Daga baya, a Afisa, sun yi amfani da gidansu don yin tarurrukan ikilisiya kuma sun yi aiki tare don taimaka wa sababbi, kamar Afolos, don ya manyanta a ruhaniya. (A. M. 18:2, 18-26) Waɗannan ma’aurata masu ƙwazo sun je ƙasar Roma, inda suka sake buɗe gidansu don a riƙa yin tarurrukan ikilisiya. Daga baya, suka koma Afisa suna ƙarfafa ’yan’uwan.—Rom. 16:3-5.
12 Akila da Biriskilla sun yi aikin ɗinkin tanti na ɗan lokaci tare da Bulus. A nan wurin kuma mun ga an ambata wannan ma’auratan tare, suna haɗin kai ba tare da yin gasa ko jayayya ba. (A. M. 18:3) Hakika, hidimar Kirista ta taimaka musu su sa hidimar Jehobah farko a aurensu, kuma hakan ya sa aurensu ya kasance mai ƙarfi sosai. Ko da suna Korinti, Afisa ko kuma Roma, an san su a ko’ina kamar ‘abokan aiki cikin Kristi Yesu.’ (Rom. 16:3) Sun yi aiki tare don yaɗa wa’azin Mulkin a duk inda suka yi hidima.
13, 14. (a) Waɗanne yanayoyi ne za su iya sa aure ya kasance marar haɗin kai? (b) Mene ne wasu abubuwa da ma’aurata za su iya yi don su ƙarfafa gaminsu a matsayin “nama ɗaya”?
13 Hakika, haɗin kai don cim ma makasudi da ayyuka yana ƙarfafa gamin aure. (M. Wa. 4:9, 10) Abin baƙin ciki, ma’aurata da yawa a yau ba sa yawan kasancewa tare da juna. Kowannensu yana yin sa’o’i da yawa a wurin aiki. Wasu suna yawan tafiya don aikinsu ko kuma su tafi wata ƙasa su kaɗai sai su riƙa aika kuɗi zuwa gida. Ko da a gida, wasu ma’aurata ba sa cuɗanya da juna don suna yawan kallon talabijin, nishaɗi, yin wasanni, buga wasan bidiyo, ko yin bincike a intane. Hakan yana faruwa a iyalinku sosai? Idan haka ne, za ku iya yin gyara a yanayinku don ku riƙa kasancewa tare da juna sosai? Za ku iya yin wasu ayyuka tare, kamar yin girki, wanke kwanuka, ko kuma yin aiki a lambun ku? Shin za ku iya yin aiki tare don kula da yaranku ko kuma taimaka wa iyayenku tsofaffi?
14 Mafi muhimmanci, ku riƙa yin aiki tare a ayyuka da suka shafi bauta wa Jehobah. Tattauna nassosin yini tare da kuma yin bauta ta iyali tana ba da zarafi mai kyau na sa tunani da makasudan iyalinku su jitu. Ku riƙa fita hidima tare. Idan yanayinku ya ƙyale ku ku yi hidimar majagaba na wata ɗaya ko shekara ɗaya. (Karanta 1 Korintiyawa 15:58.) Wata ’yar’uwa da ta yi hidimar majagaba tare da mijinta ta ce: “Hidima hanya ɗaya ce da muke kasancewa tare da juna kuma mu tattauna sosai. Domin muna da makasudi iri ɗaya na taimaka wa waɗanda muka sami a hidima, na ji cewa mu abokan juna ne sosai. Na kusance shi ba kamar miji na ba kaɗai amma kamar abokina na ƙwarai.” Yayin da kuke aiki tare don biɗan abubuwa masu muhimmanci, muradinku, makasudinku, da kuma halayenku za su jitu da na aboki ko abokiyar aurenku har, kamar Akila da Biriskilla, za ku riƙa tunani, ji, da kuma aikata kamar “nama ɗaya.”
Bari Ruhaniya ta Yi Muku Ja-gora
15. Mene ne zai taimaki aure ya yi nasara? Ka bayyana.
15 Yesu ya san muhimmancin sa Allah farko a aure. Ya ga sa’ad da Jehobah ya yi ja-gora a aure na farko. Ya lura yadda Adamu da Hauwa’u suke farin ciki muddin suna bin ja-gorar Allah, kuma ya ga matsalolin da suka taso sa’ad da suka yi watsi da dokokin Allah. Saboda haka sa’ad da Yesu ya koyar da mutane, ya ambata umurnin Ubansa da ke cikin Farawa 2:24. Ya kuma daɗa wannan kalaman: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:6) Don haka, har ila, biyayya sosai ga Jehobah ne abu mafi muhimmanci don samun farin ciki da kuma yin nasara a aure. Iyayen Yesu na duniya, Yusufu da Maryamu, sun kafa kyakkyawan misali a wannan batun.
16. Ta yaya Yusufu da Maryamu suka nuna suna da ruhaniya a rayuwar iyalinsu?
16 Yusufu ya kasance da Maryamu cikin kirki da kuma daraja. A lokaci na farkon da ya ji cewa ta yi juna biyu, ya so ya nuna mata jin ƙai, kafin ma mala’ikan Allah ya bayyana masa abin da ya faru da Maryamu. (Mat. 1:18-20) A matsayin ma’aurata, sun yi biyayya ga dokokin Kaisar kuma sun bi Dokar Musa sosai. (Luk 2:1-5, 21, 22) Kuma ko da yake maza ne kaɗai ake bukata su halarci manyan idodin addini a Urushalima, Yusufu da Maryamu, tare da iyalinsu sukan halarci idodi duk shekara. (K. Sha 16:16; Luk 2:41) Ta hakan da kuma wasu hanyoyi, waɗannan ma’auratan masu jin tsoron Allah sun ƙoƙarta su faranta wa Jehobah rai kuma sun daraja abubuwa na ruhaniya sosai. Ba abin mamaki ba ne cewa Jehobah ya zaɓe su su kula da Ɗansa kafin ya soma hidimarsa a duniya.
17, 18. (a) A waɗanne hanyoyi ne ma’aurata za su iya sa ruhaniya ta kasance farko a aurensu? (b) Ta yaya hakan zai amfane su?
17 Shin ruhaniya tana yi wa iyalinku ja-gora? Alal misali, kafin ku yanki shawarwari masu muhimmanci, kuna fara bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, ku yi addu’a game da batun, kuma ku nemi shawara daga Kirista da ya manyanta? Ko kuwa kuna neman magance matsaloli ta bin ra’ayoyinku ko na iyalanku da abokanku? Shin kuna ƙoƙari ku yi amfani da shawarwari masu yawa da bawa mai-aminci ya wallafa game da aure da rayuwar iyali a littattafai? Ko kuwa kuna bin al’adunku ko shawarwari na yankinku? Kuna yin addu’a da nazari a kai a kai tare, kuna kafa makasudai na ruhaniya, da kuma tattauna batutuwa mafi muhimmanci a iyalinku?
18 Game da shekara hamsin da suka yi, suna farin ciki a aurensu, Ray ya ce, “Ba mu taɓa samun matsalar da ba mu iya magance ta ba, domin mun sa Jehobah ya zama ɗaya cikin ‘igiya riɓi uku’ a aurenmu.” (Karanta Mai-Wa’azi 4:12.) Danny da Trina sun amince da wannan. Sun ce: “Yayin da mun bauta wa Allah tare, gamin aurenmu ya daɗa ƙarfi sosai.” Sun kasance da farin ciki tare fiye da shekara talatin da huɗu a matsayin ma’aurata. Idan kuna sa Jehobah farko a aurenku, zai taimaka muku ku yi nasara kuma zai albarkace ku sosai.—Zab. 127:1.
Ku Ci Gaba da Daraja Baiwar Allah
19. Me ya sa Allah ya tanadar da baiwar aure?
19 Abin da ya fi muhimmanci ga mutane da yawa a yau shi ne su kasance masu farin ciki. Amma bawan Jehobah yana da ra’ayi dabam. Ya san cewa Allah ya yi tanadin aure a matsayin kyauta don faɗaɗa nufinsa. (Far. 1:26-28) Da a ce Adamu da Hauwa’u sun daraja baiwar, da dukan duniya ta zama aljanna mai cike da bayin Allah masu farin ciki da adalci.
20, 21. (a) Me ya sa ya kamata mu daraja aure? (b) Wace baiwa ce za mu tattauna a mako na gaba?
20 Fiye da komi, bayin Allah suna ɗaukan aure a matsayin zarafi na daraja Jehobah. (Karanta 1 Korintiyawa 10:31.) Kamar yadda muka tattauna, aminci, haɗin kai, da ruhaniya halaye ne masu kyau da suke ƙarfafa aure. Saboda haka ko muna shirin yin aure, muna ƙarfafa aurenmu, ko kuma muna neman sa aurenmu ya yi nasara, wajibi ne mu kasance da ra’ayi mai kyau game da aure, wato, shiri ne mai tsarki kuma daga wurin Allah. Kasancewa da wannan ra’ayin zai motsa mu mu yi iya ƙoƙarinmu don yanke shawarwari na aure bisa Kalmar Allah. A wannan hanyar za mu nuna daraja ba kawai ga baiwa ta aure ba amma ga Wanda ya ba da baiwar, wato, Jehobah Allah.
21 Hakika, ba aure kaɗai ba ne baiwar da Jehobah ya yi mana; kuma ba shi kaɗai ba ne hanyar yin farin ciki a rayuwa. A talifinmu na gaba, za mu tattauna wata kyauta mai daraja daga wurin Allah, wato, gwauronci.
Yaya Za Ka Amsa?
• Yaya ya kamata aminci ya shafi Kiristoci ma’aurata?
• Me ya sa yin aiki da haɗin kai yake ƙarfafa aure?
• A waɗanne hanyoyi ne ma’aurata za su iya sa ruhaniya ta ja-goranci aurensu?
• Ta yaya za mu iya nuna daraja ga Jehobah, Wanda ya shirya aure?
[Hotuna da ke shari na 15]
Yin aiki tare yana taimaka wa ma’aurata su kasance da haɗin kai