Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 1/15 pp. 17-21
  • Ku Yi Amfani Da Yanayinku Na Marasa Aure Da Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Amfani Da Yanayinku Na Marasa Aure Da Kyau
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Baiwa Mai Tamani
  • Marasa Aure Sa’ad da Suke Matasa
  • Kasance Marasa Aure a Lokacin Tsufa
  • Kasance Marasa Aure Har Ƙarshen Rayuwa
  • Ku Yi Amfani da Yanayinku da Kyau
  • Yadda Za ka Iya More Yanayinka na Marar Aure
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Shawara Mai Kyau Game Da Kasancewa Marar Aure Da Kuma Mai Aure
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aure da Rashin Aure.
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Albarkar Kasancewa Marasa Aure
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 1/15 pp. 17-21

Ku Yi Amfani Da Yanayinku Na Marasa Aure Da Kyau

“Wanda ya ke da iko shi karɓi wannan shi karɓa.”—MAT. 19:12.

1, 2. (a) Ta yaya Yesu, Bulus da wasu suka ɗauki kasancewa marasa aure? (b) Me ya sa wasu ba za su ɗauki kasancewa marasa aure a matsayin baiwa ba?

BABU shakka, aure ɗaya daga cikin baiwar Allah mafi tamani ne ga ’yan Adam. (Mis. 19:14) Duk da haka, Kiristoci da yawa da ba su yi aure ba suna more rayuwa mai gamsarwa sosai. Wani ɗan’uwa Harold mai shekara 95 wanda bai taɓa aure ba ya ce: “Ko da yake ina more kasancewa tare da wasu da kuma karɓan su a sake, amma ba na kaɗaitawa sa’ad da nake ni kaɗai. Ina ji da gaske cewa ina da baiwar kasancewa marar aure.”

2 Hakika, Yesu Kristi da Manzo Bulus sun ambata kasancewa marasa aure da kuma yin aure kamar baiwa daga wurin Allah. (Karanta Matta 19:11, 12; 1 Korintiyawa 7:7.) Babu shakka, ba dukan waɗanda ba su yi aure ba ne suka zaɓa kasancewa hakan. A wasu lokatai yanayi yana sa ya kasance da wuya a samo abokiyar aure da ta dace. Ko kuma bayan shekaru da yawa na aure, wasu suna kaɗaitawa domin aurensu ya mutu ko kuma abokiyar aurensu ta rasu. Amma a wacce hanya ce kasancewa marasa aure zai iya zama baiwa? Kuma ta yaya Kiristoci da ba su yi aure ba za su iya yin amfani da yanayinsu na marasa aure da kyau?

Baiwa Mai Tamani

3. Waɗanne abubuwa ne Kiristoci da ba su yi aure ba suke morewa?

3 Wanda bai yi aure ba yakan samu lokaci da kuma ’yanci sosai fiye da wanda ya yi aure. (1 Kor. 7:32-35) Waɗannan zarafi ne masu kyau da za su sa ya faɗaɗa hidimarsa, faɗaɗa ƙaunarsa ga mutane, da kuma kusantar Jehobah. Kiristoci da yawa sun ga amfanin kasancewa marasa aure kuma sun yanki shawara su ‘karɓi wannan baiwar,’ ko da na ɗan lokaci ne. Wasu kuma da farko ba su yi shirin kasancewa marasa aure ba, amma sa’ad da yanayinsu ya canja, suka yi tunani game da yanayinsu cikin addu’a kuma suka fahimci cewa da taimakon Jehobah za su iya samun kwanciyar hankali. Saboda haka, suka karɓi sabon yanayinsu kuma suka karɓi baiwar kasancewa marasa aure.—1 Kor. 7:37, 38.

4. Me ya sa Kiristoci da ba su yi aure ba za su iya ɗaukan kansu da daraja a hidimar Allah?

4 Kiristoci da ba su yi aure ba sun san cewa ba lallai sai sun yi aure ba ne tukuna kafin Jehobah da kuma ƙungiyarsa su amince da su. Ƙaunar Allah ta wanzu ga ɗaɗɗayanmu. (Mat. 10:29-31) Babu kowa da kuma komi da zai iya raba mu da ƙaunar Allah. (Rom. 8:38, 39) Ko da mu ma’aurata ne ko kuma marasa aure, akwai dalilai da suka sa ya kamata mu ɗauki kanmu da daraja a hidimar Allah.

5. Mene ne ake bukata don a amfana daga kasancewa marasa aure?

5 Kamar yadda yake da baiwar mawaƙa da kuma wasanni, ana bukatar a koya kasancewa marasa aure kafin a amfana sosai. Saboda haka, ta yaya Kiristoci a yau, ko da ’yan’uwa maza ne ko mata, matasa ko kuma tsofaffi, suka zaɓa su kasance marasa aure ko kuma yanayinsu ne ya sa hakan, za su iya yin amfani da yanayinsu yadda ya dace? Bari mu yi la’akari da wasu misalai na ikilisiyar Kirista ta dā masu ban ƙarfafa kuma mu ga abin da za mu iya koya.

Marasa Aure Sa’ad da Suke Matasa

6, 7. (a) Wane gata ne ’ya’yan Filibus budurwoyi suka samu a hidimar Allah? (b) A waɗanne hanyoyi ne Timotawus ya yi amfani da shekarunsa na marar aure da kyau, kuma yaya aka yi masa albarka don yin hidima da yardar rai sa’ad da yake matashi?

6 Filibus mai wa’azin bishara yana da ’ya’ya budurwoyi huɗu waɗanda suka bi sawun mahaifinsu na kasancewa da ƙwazo a hidima. (A. M. 21:8, 9) Yin annabci yana cikin baiwa ta al’ajabi na ruhu mai tsarki, kuma waɗannan matan sun yi amfani da wannan baiwar don cika abin da ke littafin Joel 2:28, 29.

7 Timotawus matashi ne da ya yi amfani da yanayinsa na marar aure da kyau. Daga jariri, mahaifiyarsa Afniki, da kakarsa Lois sun koya masa “littattafai masu tsarki.” (2 Tim. 1:5; 3:14, 15) Amma wataƙila sun zama Kiristoci sa’ad da Bulus ya ziyarci garinsu Listra da farko, a kusan shekara ta 47 A.Z. Shekara biyu bayan hakan, sa’ad da Bulus ya yi ziyara ta biyu, wataƙila Timotawus ya kusan shekara 20 ko kuma yana farkon shekararsa ta 20. Duk da cewa shi matashi ne kuma bai manyanta ba sosai a gaskiya, dattawan Kiristoci na birnin Listra da Ikoniya sun ‘yaba masa sosai.’ (A. M. 16:1, 2) Saboda haka Bulus ya gayyaci Timotawus ya zama amininsa na yin ziyara da kuma wa’azi. (1 Tim. 1:18; 4:14) Ba za mu iya cewa Timotawus bai taɓa yin aure ba. Amma mun san cewa a matsayinsa na matashi, ya amince da gayyatar Bulus da yardar rai, kuma a shekaru da yawa bayan hakan, ya more yin hidima a matsayin mai wa’azi a ƙasashen waje da kuma dattijo wanda bai yi aure ba.—Filib. 2:20-22.

8. Mene ne ya taimaki Yohanna Markus ya biɗi maƙasudai na ruhaniya, kuma waɗanne albarka ne ya samu don yin hakan?

8 Sa’ad da yake matashi, Yohanna Markus ya yi amfani da shekarun da bai yi aure ba da kyau. Da shi da mahaifiyarsa, Maryamu, da kuma ɗan kawunsa Barnaba, ne suke cikin ikilisiya na farko da ke Urushalima. Wataƙila iyalin Markus suna da wadata, tun da yake suna da nasu gida a cikin birnin da kuma baiwa. (A. M. 12:12, 13) Amma, duk da waɗannan jin daɗi, har a matsayin matashi, Markus bai yi rayuwa ta son kai ba. Wataƙila cuɗanyarsa da manzannin ya sa ya samu marmarin yin hidima a matsayin mai wa’azi a ƙasashen waje. Saboda haka ya yi hidima tare da Bulus da Barnaba a tafiyar hidimarsu ta farko a ƙasashen waje kuma yana yi musu hidima. (A. M. 13:5) Daga baya, ya yi tafiya tare da Barnaba, bayan hakan kuma, ya yi hidima tare da Bitrus a ƙasar Babila. (A. M. 15:39; 1 Bit. 5:13) Ba mu san yawan shekarun da Markus ya yi bai yi aure ba. Amma an yaba masa sosai a matsayin wanda yake wa wasu hidima da kuma yin ayyuka da yawa a hidimar Allah.

9, 10. Waɗanne zarafi na faɗaɗa hidimarsu ne matasa Kiristoci da ba su yi aure ba suke da shi a yau? Ka ba da misali.

9 Matasa da yawa a cikin ikilisiya a yau suna yin amfani da shekarunsu na marasa aure da son rai don saka hannu sosai a hidimar Allah. Kamar Yohanna Markus da Timotawus, sun amince cewa kasancewa marasa aure yana sa su “yi hidimar Ubangiji ba da raba hankali ba.” (1 Kor. 7:35) Wannan gata ne mai girma. Waɗanda ba su yi aure ba suna da hanyoyi da yawa na bauta wa Jehobah, kamar yin hidimar majagaba, yin wa’azi a inda ake da bukatar masu wa’azi sosai, koyon sabon yare, taimakawa don gina Majami’ar Mulki ko kuma ofishin reshe, halartar Makarantar Koyar da Masu Hidima, da yin hidima a Bethel. Idan kai matashi ne kuma ba ka yi aure ba tukuna, kana yin amfani da yanayinka da kyau?

10 Wani ɗan’uwa mai suna Mark ya soma hidimar majagaba sa’ad da ya kusan shekara ashirin, ya halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima, kuma ya yi hidimomi dabam dabam a wurare da yawa a duniya. Da ya yi tunani a kan shekaru ashirin da biyar da ya yi yana hidima ta cikakken lokaci, ya ce: “Na yi ƙoƙari na ƙarfafa kowa a cikin ikilisiya, ina yin aiki tare da su a hidima, muna kai musu ziyarar ƙarfafawa, gayyatarsu zuwa gidana don mu ci abinci tare, da kuma shirya liyafa. Dukan waɗannan abubuwa sun sa ni farin ciki sosai.” Kamar yadda kalaman Mark suka nuna, ana samun farin ciki mafi girma a rayuwa ta wurin bayarwa, kuma saka hannu a tsarkakkiyar hidima sosai tana ba da zarafi da yawa na yi wa wasu baiwa. (A. M. 20:35) Ko mene ne muradinka, ingancinka, ko kuma yanayinka a rayuwa, matasa a yau suna da ayyuka da yawa a hidimar Ubangiji.—1 Kor. 15:58.

11. Mene ne wasu amfanin jira kafin a yi aure?

11 Ko da yake a ƙarshe yawancin matasa za su so su yi aure, akwai dalilai masu kyau da ya sa bai kamata a yi hanzarin yin aure ba. Bulus ya ƙarfafa matasa su jira har sai sun wuce “lokaci” da sha’awar jima’i take da ƙarfi sosai. (1 Kor. 7:36) Yana ɗaukan lokaci mutum ya fahimci kansa sosai kuma ya samu basira da ake bukata don a zaɓi abokiyar aure da ta dace. Furta wa’adin aure muhimmiyar zaɓi ce, wanda ya kamata ya kasance dindindin.—M. Wa. 5:2-5.

Kasance Marasa Aure a Lokacin Tsufa

12. (a) Ta yaya Hannatu gwauruwa ta jimre da yanayinta da ya canja? (b) Wanne gata ne ta samu?

12 Wataƙila Hannatu wadda aka ambata a Linjilar Luka, ta yi baƙin ciki sosai sa’ad da maigidanta ya rasu babu zato bayan sun yi aure na shekara bakwai. Ba mu san ko suna da ’ya’ya ba ko kuwa ta sake yin aure. Amma Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa Hannatu gwauruwa ce sa’ad da take da shekara 84. Bisa ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, za mu iya kammala cewa Hannatu ta yi amfani da yanayinta da ya canja wajen kusantar Jehobah. Ba ta taɓa “rabuwa da haikali, tana sujada tare da azumi da addu’o’i dare da rana.” (Luk 2:36, 37) Saboda haka, bauta wa Jehobah ne abin farko a rayuwarta. Hakan yana bukatar ƙuduri ainun da kuma ƙoƙari, amma an yi mata albarka sosai. Ta samu gatar ganin Yesu sa’ad da yake jariri, kuma ta shaida wa mutane game da ’yancin da za a samu ta wurin Almasihu.—Luk 2:38.

13. (a) Mene ne ya nuna cewa Dokas tana saka hannu sosai a ayyukan ikilisiya? (b) Ta yaya aka yi wa Dokas albarka saboda nagarta da kirkinta?

13 Wata mata mai suna Dokas, ko Tabita, tana zama a birnin Yafa, da ke kusa da teku a arewa matso yamma na Urushalima. Tun da Littafi Mai Tsarki bai ambata mijinta ba, wataƙila ba ta da aure a lokacin. Dokas “cike ta ke da ayyukan nagarta da bayebayen.” Babu shakka ta ɗinka wa gwauraye da yawa tufafi, kuma hakan ya sa sun ƙaunace ta sosai. Saboda haka sa’ad da ta yi rashin lafiya kuma ta rasu, ikilisiyar gabaki ɗaya sun aika wa Bitrus saƙo cewa ya ta da ’yar’uwarsu daga matattu. Yayin da labarin tashinta daga matattu ya yaɗu a Yafa baki ɗaya, mutane da yawa suka zama masu bi. (A. M. 9:36-42) Babu shakka Dokas ma ta taimaka wa wasu cikinsu ta ayyukanta na nagarta.

14. Mene ne yake motsa Kiristoci marasa aure su kusaci Jehobah?

14 Kamar Hannatu da Dokas, mutane da yawa a ikilisiyoyi a yau suna kasancewa marasa aure ko kuma gwauraye. Wasu ba su samu abokiyar aure da ta dace ba. Wasu kuma aurensu ya mutu ko kuma sun zama gwauraye. Rashin abokiyar aure da za a riƙa tattauna damuwa da ita, ya sa Kiristoci da ba su yi aure ba sukan dogara ga Jehobah sosai. (Mis. 16:3) Silvia, wata ’yar’uwa marar aure da take hidima a Bethel fiye da shekara 38 ta ɗauki wannan kamar albarka. Wani lokaci ina gajiyar kasancewa mai ƙarfi,” ta ce. “Ina mamaki, ‘Wane ne zai ƙarfafa ni?’” Amma sai ta daɗa: “Sanin cewa Jehobah ya san abin da muke bukata fiye da yadda na sani ya taimaka mini na kusance shi. Kuma a wani lokaci, ina samun ƙarfafa daga wurin da ban yi tsammani ba.” A duk lokacin da muka matso kusa da Jehobah, yana aikatawa cikin tausayi da kuma tabbaci.

15. Ta yaya Kiristoci marasa aure za su iya ‘sakin zuciyarsu’ wajen nuna ƙauna?

15 Rashin aure yana ba da zarafin ‘sakin zuciya’ wajen nuna ƙauna. (Karanta 2 Korintiyawa 6:11-13.) Jolene, wata ’yar’uwa gwauruwa wadda ta yi shekara 34 tana hidima ta cikakken lokaci, ta ce: “Na yi ƙoƙari don gina dangantaka mai kusa da mutane, ba da tsara na kaɗai ba, amma da dukan mutane. Rashin aure zarafi ne na yin baiwa ga Jehobah, iyalinku, da ’yan’uwanku maza da mata, da kuma maƙwabtanku. Yayin da na daɗa yin tsufa, ina daɗa yin farin ciki game da yanayina na marar aure.” Babu shakka, tsofaffi, naƙasassu, iyaye gwauraye, matasa, da kuma wasu a cikin ikilisiya suna amfana daga tallafawa da waɗanda ba su yi aure ba suke musu. Hakika, a duk lokacin da muka nuna ƙauna ga mutane, muna yin farin ciki. Kai ma za ka iya ‘saki zuciya’ wajen nuna ƙauna ga mutane?

Kasance Marasa Aure Har Ƙarshen Rayuwa

16. (a) Me ya sa Yesu bai taɓa aure ba? (b) Ta yaya Bulus ya yi amfani da matsayinsa na marar aure da kyau?

16 Yesu bai yi aure ba, ya shirya kuma ya yi hidimar da aka ɗanka masa. Ya yi tafiya sosai, kuma ya yi aiki daga asuba zuwa da daddare, kuma daga ƙarshe ya ba da ransa don fansa. Yanayinsa na marasa aure ya taimaka masa ya cim ma hidimarsa sosai. Manzo Bulus ya yi tafiya na mil dubbai kuma ya fuskanci mawuyacin yanayi a hidima. (2 Kor. 11:23-27) Ko da yake wataƙila ya taɓa aure, amma Bulus ya zaɓa ya kasance marar aure bayan da aka zaɓe shi a matsayin manzo. (1 Kor. 7:7; 9:5) Domin hidima, Yesu da Bulus sun ƙarfafa wasu su yi koyi da misalinsu idan ya yiwu. Duk da haka, babu kowannensu da ya ce sai marar auren ne kaɗai zai iya bauta wa Allah.—1 Tim. 4:1-3.

17. Ta yaya wasu a yau suke bin misalin Yesu da Bulus, kuma me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana amincewa da waɗanda suke yin irin wannan sadaukarwa?

17 Wasu kuma a yau sun zaɓa su kasance marasa aure domin su saka hannu a hidima sosai. Harold, da aka ambata ɗazun ya more hidimar Bethel fiye da shekara 56. “Sa’ad da na cika shekara goma a Bethel,” ya ce, “Na ga ma’aurata da yawa suna barin Bethel saboda rashin lafiya ko kuma suna son su kula da iyayensu tsofaffi. Iyayena sun riga sun rasu. Amma ina son Bethel sosai saboda haka ba na son na yi wasa da wannan gatar ta wajen yin aure.” Hakazalika, a shekaru da suka wuce, wata mai suna Margaret da ta daɗe tana hidimar majagaba ta lura: “Na samu zarafi da yawa na yin aure a rayuwata, amma ban taɓa yin hakan ba. Maimakon hakan, na samu zarafin yin amfani da ’yanci da nake da shi na yanayina na marar aure don kasancewa da ƙwazo a hidima, kuma hakan ya sa ni farin ciki matuƙa.” Hakika, Jehobah ba zai taɓa manta da kowanne mutum da ya yi irin wannan sadaukarwa don bauta ta gaskiya ba.—Karanta Ishaya 56:4, 5.

Ku Yi Amfani da Yanayinku da Kyau

18. Ta yaya wasu za su iya tallafa wa Kiristoci da ba su yi aure ba?

18 Dukan Kiristoci da ba su yi aure ba da suke iya ƙoƙarinsu don su bauta wa Jehobah sun cancanci mu yaba musu da kuma ƙarfafa su. Muna ƙaunarsu don ƙoƙarce-ƙoƙarcensu da kuma sadaukarwa da suke yi a ikilisiya. Ba za su taɓa kaɗaitawa ba idan muka zama musu “’yan’uwa maza, ko ’yan’uwa mata, ko uwa, ko ’ya’ya.”—Karanta Markus 10:28-30.

19. Mene ne za mu iya yi don mu yi amfani da yanayinmu na marasa aure da kyau?

19 Ko kun zaɓa ku zauna ba ku yi aure ba ko kuma yanayi ne ya jawo hakan, bari waɗannan misalai na Nassosi da na zamani su tabbatar muku cewa za ku iya yin rayuwa mai farin ciki da mai amfani. Kasancewa marasa aure yana kamar kyauta da ake jira ko kuma wanda ba a sa rai ba. Wasu suna samun wanda yake son su da sauri, wasu kuma suna daɗewa kafin su samu wanda yake son su. Amma dukansu sun dangana ga halinmu. Mene ne za ku iya yi don ku yi amfani da yanayinku na marasa aure da kyau? Ku kusanci Jehobah, ku yi aiki da yawa a hidimar Allah, kuma ku saki zuciyarku wajen ƙaunarku ga mutane. Kamar aure, za a iya samun amfani don kasancewa ba a yi aure ba idan mun samu ra’ayin Allah kuma mun yi amfani da kyautarmu da kyau.

Ka Tuna?

• A waɗanne hanyoyi ne kasancewa marasa aure zai iya zama baiwa?

• Ta yaya kasancewa marasa aure zai iya zama albarka sa’ad da ake matasa?

• Waɗanne zarafi ne Kiristoci da ba su yi aure ba suke da shi na kusantar Jehobah da kuma saki zuciya wajen ƙauna?

[Hotuna da ke shari na 18]

Kana yin amfani da yanayinka da kyau a hidimar Allah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba