Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/1 pp. 16-17
  • Wane Ne Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wane Ne Allah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Wane Ne Allah na Gaskiya?
    Albishiri Daga Allah!
  • Wane ne Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Mece ce Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Amfani da Sunan Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/1 pp. 16-17

Ka Koya Daga Kalmar Allah

Wane Ne Allah?

Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.

1. Wane ne Allah?

Allah na gaskiya shi ne Mahaliccin dukan abubuwa. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “Sarkin zamanai,” ma’ana, ba shi da mafari kuma ba zai taɓa kasancewa da ƙarshe ba. (Ru’ya ta Yohanna 15:3) Tun da yake Allah ne Tushen rai, shi kaɗai ne ya kamata mu bauta wa.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 4:11.

2. Mene ne kamannin Allah?

Babu wanda ya taɓa ganin Allah domin shi Ruhu ne, hakan na nufin cewa shi wani irin rai ne mai girma fiye da halittu na zahiri da suke zaune a duniya. (Yohanna 1:18; 4:24) Yadda Allah yake tunani da kuma ji sun bayyana a abubuwan da ya halitta. Alal misali, idan muka yi tunani a kan tsari da kuma irin ’ya’yan itace dabam-dabam da furanni da ke akwai, za mu ga ƙauna da hikimar Allah. Girman sararin samaniya yana bayyana mana ikon Allah.—Karanta Romawa 1:20.

Za mu iya ƙara koyon halayen Allah daga Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ya gaya mana abin da Allah yake so da abin da ba ya so, yadda yake bi da mutane, da kuma yadda yake bi da batutuwa a yanayi dabam-dabam.—Karanta Zabura 103:7-10.

3. Allah yana da suna?

Yesu ya ce: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Ko da yake Allah yana da laƙabi da yawa, yana da suna guda tak. Kowane harshe yana da yadda yake kiransa. A Hausa muna kiransa “Jehobah” ko kuma “Yahweh.”—Karanta Zabura 83:18.

An cire sunan Allah daga fassarori da dama na Littafi Mai Tsarki kuma an sauya sunan da laƙabin nan Ubangiji ko Allah. Amma sa’ad da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, sunan Allah ya bayyana wajen sau 7,000. Yesu ya bayyana sunan Allah ta wajen yin amfani da shi yayin da yake bayyana Kalmar Allah ga mutane. Ya taimaka wa mutane su san Allah.—Karanta Yohanna 17:26.

4. Jehobah ya damu da mu kuwa?

Jehobah yana nuna cewa ya damu da mu ta wajen sauraron addu’o’inmu da kansa. (Zabura 65:2) Shin, yawan wahala yana nufin cewa Allah bai damu da mu ba ne? Waɗansu mutane suna da’awar cewa Allah yana ƙyale mu mu shan wahala ne don ya jarraba mu, amma hakan ba gaskiya ba ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne.”—Ayuba 34:10, Littafi Mai Tsarki; karanta Yaƙub 1:13.

Allah ya ba mutane damar yin zaɓi. Muna godiya sosai domin ’yancin da muke da shi na bauta wa Allah, ko ba haka ba? (Joshua 24:15) Ana shan wahala sosai ne domin mutane da yawa sun zaɓi su yi mugunta ga wasu. Jehobah yana baƙin ciki sosai yayin da yake ganin irin wannan rashin adalcin.—Karanta Farawa 6:5, 6.

Ba da daɗewa ba, Jehobah zai yi amfani da Yesu don ya kawar da wahala da waɗanda suke haddasa ta. A yanzu, Jehobah yana da kyakkyawan dalilin da ya sa ya ƙyale wahala na ɗan lokaci. Wani darasi da zai bayyana a talifofi na nan gaba zai bayyana dalilin da ya sa Allah ya ƙyale shan wahala.—Karanta Ishaya 11:4.

5. Mene ne Allah yake son mu yi?

Jehobah ya halicce mu a hanyar da za mu iya saninsa kuma mu ƙaunace shi. Yana son mu koyi gaskiya game da shi. (1 Timotawus 2:4) Idan muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki, za mu iya sanin Allah a matsayin Aboki.—Karanta Misalai 2:4, 5.

Tun da yake Jehobah ya ba mu rai, ya kamata mu ƙaunace shi fiye da kowane mutum. Za mu iya nuna wa Allah cewa muna ƙaunarsa ta wurin tattaunawa da shi cikin addu’a da kuma yin abin da ya ce mu yi. (Misalai 15:8) Jehobah ya gaya mana mu bi da mutane cikin ƙauna.—Karanta Markus 12:29, 30; 1 Yohanna 5:3.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 1 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Hoton da ke shafi na 17]

Akwai kyakkyawan dalilin da ya sa aka ƙyale shan wahala na ɗan lokaci?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba