Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 2/15 pp. 21-23
  • Yin “Biyayya ta Fi Hadaya”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin “Biyayya ta Fi Hadaya”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Ya Sanar da Sarkin da Ya Zaɓa
  • A Bakin Daga
  • “Ka Yi Aikin Wauta”
  • Jehobah Ya Ƙi Saul
  • Saul, Sarkin Isra’ila Na Farko
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Sarki Na Farko a Isra’ila
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Yesu Ya Zabi Shawulu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Dauda da Saul
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 2/15 pp. 21-23

Yin “Biyayya ta Fi Hadaya”

SAUL ne sarki na fari na ƙasar Isra’ila ta dā. Daga baya Saul ya yi rashin biyayya, ko da yake Allah na gaskiya ne ya zaɓe shi.

Waɗanne laifuffuka ne Saul ya yi? Da zai iya guje musu ne? Ta yaya za mu amfana daga yin la’akari da misalinsa?

Jehobah Ya Sanar da Sarkin da Ya Zaɓa

Annabi Sama’ila ne yake yi wa Allah hidima a matsayin wakilinsa a ƙasar Isra’ila kafin Saul ya zama sarki. Yanzu Sama’ila ya yi tsufa, kuma yaransa ba su kasance da aminci ba. Har ila, abokan gaba suna yi wa al’ummar barazana. Sa’ad da dattibai mazaje na Isra’ila suka gaya wa Sama’ila ya naɗa musu sarki da zai zama alƙalinsu kuma ya ja-gorance su a yaƙi, Jehobah ya ja-goranci annabin ya shafe Saul a matsayin shugabansu kuma ya ce: “Za ya ceci jama’ata daga hannun Filistiyawa.”—1 Sam. 8:4-7, 20; 9:16.

Saul “sarmayi ne kyakkyawa.” Ban da cewa yana da kyaun siffa, Saul yana da wasu halaye masu kyau. Shi kuma mai tawali’u ne. Alal misali, Saul ya tambayi Sama’ila: “Ni ba Ba-banyamin ba ne, daga mafi ƙanƙanta cikin ƙabilan Isra’ila? gidana kuma mafi-ƙanƙanta cikin gidajen ƙabilar Banyamin? Don menene fa ka ke yi mani wannan irin zance?” Saul yana da ra’ayin filako game da kansa da kuma iyalinsa, ko da yake Mahaifinsa, Kish, “[attajiri] ne.”—1 Sam. 9:1, 2, 21.

Ka yi la’akari kuma da amsar da Saul ya ba da sa’ad da Sama’ila ya furta zaɓin da Jehobah ya yi game da sarkin Isra’ila. Da farko Sama’ila ya naɗa Saul a ɓoye kuma ya gaya masa: “Sai ka yi abin da hali ya nuna: gama Allah yana tare da kai.” Daga baya kuma, annabin ya ƙira jama’a don ya furta zaɓin Jehobah a fili. Amma aka nemi Saul aka rasa. Saul ya ɓuya domin yana jin kunya. Jehobah ya faɗa inda yake, kuma aka sanar cewa Saul ne sarki.—1 Sam. 10:7, 20-24.

A Bakin Daga

Ba da daɗewa ba Saul ya ƙaryata duk wani da ya yi shakkar ƙwarewarsa. Sa’ad da Ammonawa suka yi wa birnin Isra’ila barazana, “sai ruhun Allah ya afko masa [Saul] da iko.” Da iko ya tattara mayaƙan al’ummar, ya tsara su, kuma ya ja-gorance su zuwa yin nasara. Amma Saul ya yabi Allah don wannan nasarar, yana cewa: “Gama yau Ubangiji ya yiwo ceto cikin Isra’ila.”—1 Sam. 11:1-13.

Saul yana da halaye masu kyau kuma Allah ya albarkace shi. Ya kuma amince da ikon Jehobah. Duk da haka, Isra’ilawa da kuma sarkinsu za su ci gaba da yin nasara idan suka yi wani abu mai muhimmanci. Sama’ila ya gaya wa mutanen Isra’ila: “Idan za ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa, ku saurari muryatasa, ba ku tayas ma umurnin Ubangiji ba, da ku da sarkin da ke sarautanku, kun zama masu-biyayya ga Ubangiji Allahnku.” Mene ne Isra’ilawa za su tabbata da shi idan suka kasance da aminci ga Allah? “Ubangiji ba za ya yarda jama’atasa ba sabili da sunansa mai-girma,” in ji Sama’ila, domin “Ubangiji ya nufa shi maishe ku al’umma ga kansa.”—1 Sam. 12:14, 22.

Biyayya ce ta fi muhimmanci wajen samun amincewar Allah, kuma hakan yake har yanzu. Sa’ad da bayin Jehobah suka yi biyayya ga umurnansa, yakan albarkace su. Amma idan suka ƙi yin biyayya kuma fa?

“Ka Yi Aikin Wauta”

Abin da Saul ya sake yi wa Filistiyawa ya sa suka ƙara kawo masa hari. Rundunar “kamar yashi wanda ke bakin teku don yawa” suka kawo wa Saul hari. “Mazajen Isra’ila suka ga sun matsu, gama jama’a sun damu, sai suka yi ta ɓuya a cikin koganni da sarƙaƙiya, da duwatsu, da ramummuka, da rijiyoyi.” (1 Sam. 13:5, 6) Mene ne Saul zai yi?

Sama’ila ya gaya wa Saul cewa su haɗu a Gilgal, inda annabin zai miƙa hadaya. Saul ya yi ta jira, amma Sama’ila ya makara da zuwa, kuma rundunar Saul suka soma watsewa. Saul ya ɗauki matsayin miƙa hadayun. Da zarar ya yi hakan, sai Sama’ila ya iso. Da ya ji abin da Saul ya yi, sai Sama’ila ya gaya masa: “Ka yi aikin wauta: ba ka kiyaye umurnin Ubangiji Allahnka ba, wanda ya umurce ka: gama yanzu da Ubangiji ya tabbatadda mulkinka bisa Isra’ila har abada. Amma yanzu mulkinka ba za ya dawwama ba: Ubangiji ya rigaya ya biɗa ma kansa mutum gwargwadon zuciyarsa, har Ubangiji ya sanya shi shi zama shugaba bisa jama’arsa da shi ke ba ka kiyaye abin da Ubangiji ya umurce ka ba.”—1 Sam. 10:8; 13:8, 13, 14.

Saul ya nuna rashin bangaskiya sa’ad da girman kai ya sa ya ƙi bin umurnin Jehobah na jiran Sama’ila ya zo ya miƙa hadayar. Tafarkin Saul ya yi dabam da na Gidiyon, wanda shi dā shugaba ne na rundunar Isra’ila! Jehobah ya gaya wa Gidiyon ya rage rundunarsa daga 32,000 zuwa 300, kuma Gidiyon ya yi biyayya. Me ya sa? Domin yana da bangaskiya ga Jehobah. Da taimakon Allah ya ci nasara a kan mutane 135,000 da suka kawo musu hari. (Alƙa. 7:1-7, 17-22; 8:10) Da Jehobah ya taimaka wa Saul ma. Amma, domin rashin biyayyar Saul Filistiyawa suka ci ganimar Isra’ila.—1 Sam. 13:17, 18.

Sa’ad da muke fuskantar matsaloli, yaya muke tsai da shawarwari? Daga ra’ayin waɗanda suke rashin bangaskiya, rashin biyayya ga ƙa’idodin Allah shi ne abin da ya dace a yi. A lokacin da Sama’ila ba ya nan, wataƙila Saul yana ganin abin da ya yi daidai ne. Amma, ga waɗanda suka ƙuduri aniya su samu amincewar Allah, bin ƙa’idodin Nassi da suka shafi shawarwari da suke son su tsai da ne kaɗai tafarkin da ya dace.

Jehobah Ya Ƙi Saul

A lokacin da yake yaƙi da ’yan Amalek, Saul ya yi wani laifi mai tsanani. Allah ya hukunta mutanen Amalek saboda farmaki da suka kai wa Isra’ilawa bayan sun fito daga ƙasar Masar. (Fit. 17:8; K. Sha 25:17, 18) Bugu da ƙari, mutanen Amalek sun haɗa kai da wasu wajen kai wa mutanen da Allah ya zaɓa farmaki a lokacin alƙalawa. (Alƙa. 3:12, 13; 6:1-3, 33) Jehobah ya hukunta mutanen Amalek kuma ya gaya wa Saul ya zartar da hukunci a kan su.—1 Sam. 15:1-3.

Maimakon ya yi biyayya ga dokar Allah na kawar da dukan Amalekawa masu gaba kuma ya halaka dukiyoyinsu, Saul ya kama sarkinsu kuma ya adana dabbobinsu da suka fi kyau. Mene ne ya faru sa’ad da Sama’ila ya tuhumi Saul a wannan batun? Saul ya yi ƙoƙari ya kawar da tuhumar ta wurin cewa: “Jama’a suka keɓe mafiya kyau daga cikin tumaki da shanu, domin a yi hadaya ga Ubangiji Allahnka.” Ko da Saul ya so ya yi hadaya da dabbobin ko a’a, ya yi rashin biyayya. Saul kuma ba ya ‘ganin kansa ƙanƙani.’ Saboda haka, annabin Allah ya gaya wa Saul cewa ya yi rashin biyayya ga Allah. Sama’ila kuma ya ce: “Ko Ubangiji yana murna dayawa da hadayu na ƙonawa da sacrifices kuma, kamar yadda ya ke murna da biyayya ga muryar Ubangiji? Ka lura, biyayya ta fi hadaya . . . Tun da ka ƙi jin maganar Ubangiji, shi kuma ya ƙi ka da zaman sarauta.”—1 Sam. 15:15, 17, 22, 23.

“Mugun ruhu” ya soma yi masa ja-gora, sa’ad da Jehobah ya janye ruhunsa mai tsarki da kuma albarkarsa daga Saul sarki na fari na Isra’ila. Saul ya fara tuhuma da ƙishin Dauda, mutumin da daga baya Jehobah zai ba wa sarauta. Fiye da sau ɗaya, Saul ya yi ƙoƙari ya kashe Dauda. Da ya lura cewa “Ubangiji yana tare da Dauda,” in ji Littafi Mai Tsarki, “Saul yana nan yana riƙe da magabtaka da Dauda kullayaumi.” Saul ya yi ƙoƙari ya kashe shi ya kuma ba da umurni a kashe firistoci tamanin da biyar da kuma wasu mutane. Ba abin mamaki ba ne Jehobah ya yashe Saul!—1 Sam. 16:14; 18:11, 25, 28, 29; 19:10, 11; 20:32, 33; 22:16-19.

Sa’ad da Filistiyawa suka kai wa Isra’ila hari kuma, Saul ya koma yin sihiri don neman taimako. Washegari, aka ji masa rauni sosai sa’ad da suke yaƙi kuma ya kashe kansa. (1 Sam. 28:4-8; 31:3, 4) Game da sarkin Isra’ila na farko da ya yi rashin biyayya, Nassosi sun ce: “Saul ya mutu domin laifin da ya yi wa Ubangiji, domin kuma ba ya kiyaye maganar Ubangiji ba; domin kuma ya biɗi shawara a wurin wata mai-mabiya; a gareta ya biɗa, ba ya biɗa ga Ubangiji ba.”—1 Laba. 10:13, 14.

Mummunan misalin Saul ya nuna sarai cewa yin biyayya ga Jehobah ya fi miƙa kowace hadaya a gare shi. Manzo Yohanna ya rubuta: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yoh. 5:3) Kada mu taɓa manta da wannan gaskiya mai muhimmanci: Za mu ci gaba da abuta da Allah idan muna yi masa biyayya.

[Hoton da ke shafi na 21]

Saul shugaba ne mai tawali’u sa’ad da ya soma

[Hoton da ke shafi na 23]

Me ya sa Sama’ila ya gaya wa Saul cewa “biyayya ta fi hadaya”?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba