Ka Koya Daga Kalmar Allah
Wane Ne Yesu Kristi?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yi kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Wane ne Yesu Kristi?
Akasin duk wani ɗan Adam, Yesu yana zaune ne a sama a matsayin ruhu kafin a haife shi a duniya. (Yohanna 8:23) Shi ne halittar Allah na farko, kuma ya taimaka wajen halittar sauran abubuwa. Shi ne kaɗai wanda Allah ya halitta da kansa shi ya sa ake kiransa Ɗan Allah “haifaffe shi ka ɗai.” Yesu ne Kakakin Allah, shi ya sa ake kiransa “Kalma.” Yohanna 1:1-3, 14; karanta Misalai 8:22, 23, 30; Kolosiyawa 1:15, 16.
2. Me ya sa Yesu ya zo duniya?
Allah ya aiko Ɗansa zuwa duniya ta wurin mayar da ransa daga sama zuwa cikin mahaifar wata budurwa Bayahudiya mai suna Maryamu. Saboda haka Yesu ba shi da mahaifi ɗan Adam. (Luka 1:30-35) Yesu ya zo duniya ne (1) don ya koyar da gaskiya game da Allah, (2) don ya kafa misali na yin nufin Allah, kuma (3) don ya ba da kamiltaccen ransa a matsayin “fansa.”—Karanta Matta 20:28; Yohanna 18:37.
3. Me ya sa muke bukatar fansa?
Fansa diyya ce da ake biya don a ’yantar da mutum daga bauta. Mutuwa da tsufa ba sa cikin ainihin nufin Allah ga ’yan Adam. Ta yaya muka san hakan? Allah ya gaya wa mutumi na farko, Adamu, cewa idan ya aikata abin da Littafi Mai Tsarki ya kira zunubi, zai mutu. Da a ce Adamu bai yi zunubi ba, da bai mutu ba. Ko da yake Adamu bai mutu ba nan take sai bayan ƙarnuka da dama, ya soma mutuwa ne tun daga ranar da ya yi rashin biyayya ga Allah. (Farawa 2:16, 17; 5:5) Adamu ya yaɗa zunubi da kuma sakamakonsa, wato, mutuwa, ga dukan zuriyarsa. Da haka, mutuwa ta “shigo” duniya ta wurin Adamu. Shi ya sa muke bukatar fansa.—Karanta Romawa 5:12; 6:23.
4. Me ya sa Yesu ya mutu?
Wane ne zai iya biyan fansa don ya ’yantar da mu daga mutuwa? Mutuwar da muke yi ita ce sakamakon zunubanmu. Tun da yake mu ajizai ne, ba za mu iya fansar wani ba.—Karanta Zabura 49:7-9.
Tun da yake Yesu bai gaji ajizanci daga uba ɗan Adam ba, ya mutu ne domin zunuban wasu, ba domin zunubansa ba. Allah ya aiko da Ɗansa ya mutu dominmu don Ya nuna ƙaunarsa mafi girma ga ’yan Adam. Yesu ya nuna mana ƙauna ta wurin yin biyayya ga Ubansa da kuma ba da ransa domin zunubanmu.—Karanta Yohanna 3:16; Romawa 5:18, 19.
5. Mene ne Yesu yake yi a yanzu?
Ta wurin warkar da marasa lafiya, ta da matattu, da kuma ba da ransa don ya ceci mutane daga zunubi da mutuwa, Yesu ya nuna abin da zai yi a nan gaba ga dukan mutane masu biyayya. (Luka 18:35-42; Yohanna 5:28, 29) Bayan Yesu ya mutu, Allah ya ta da shi daga matattu a matsayin ruhu. (1 Bitrus 3:18) Bayan hakan, Yesu ya yi jira a hannun damar Allah har sa’ad da Jehobah ya ba shi ikon yin sarauta a matsayin Sarki bisa dukan duniya. (Ibraniyawa 10:12, 13) A yanzu Yesu yana mulki a matsayin Sarki a sama, kuma mabiyansa a duniya suna shelar bisharar a dukan duniya.—Karanta Daniyel 7:13, 14; Matta 24:14.
Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai yi amfani da ikonsa a matsayin Sarki don ya kawar da dukan wahala da kuma waɗanda suke haddasa ta. Miliyoyin mutanen da suke ba da gaskiya ga Yesu kuma suna yi masa biyayya za su more rayuwa a cikin aljanna a duniya.—Karanta Zabura 37:9-11.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 4 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Hoton da ke shafi na 23]
Miliyoyin mutanen da suka ba da gaskiya ga Yesu kuma suna yi masa biyayya za su more rayuwa a cikin aljanna a duniya