Ka Dogara Ga Jehobah Yayin Da Ƙarshe Ya Yi Kusa
“Ku dogara ga Ubangiji har abada.”—ISHA. 26:4.
1. Wane bambanci ne ke tsakanin bayin Allah da mutane a duniya?
MUNA zama a duniyar da miliyoyin mutane ba su san wanda ko abin da za su dogara ga ba, wataƙila domin an ɓata musu rai sau da yawa. Amma ba haka yake da bayin Jehobah ba! Da yake hikimar Allah ce ke musu ja-gora, sun san cewa bai kamata su dogara ga duniya ko kuma “sarakuna” ba. (Zab. 146:3) Maimakon haka, suna dogara ga Jehobah a yanzu da kuma a nan gaba, sun san cewa yana ƙaunarsu kuma yana cika Kalmarsa a ko da yaushe.—Rom. 3:4; 8:38, 39.
2. Ta yaya Joshua ya tabbatar cewa za a iya dogara ga Allah?
2 Joshua na zamanin dā ya tabbatar cewa za a iya dogara ga Allah. Dab da ƙarshen rayuwarsa, ya ce wa ’yan’uwansa Isra’ilawa: “Ku kuma kun sani cikin zukatanku duka da cikin rayukanku duka, babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku.”—Josh. 23:14.
3. Mene ne sunan Allah ya nuna game da shi?
3 Jehobah yana cika alkawuransa, ba don yana ƙaunar bayinsa kawai ba amma musamman don sunansa. (Fit. 3:14; 1 Sam. 12:22) Game da sunan Allah, littafin nan The Emphasized Bible, wanda J. B. Rotherham, ya wallafa ya ce: “[Ya] zama alkawari mafi kyau, ingancin cim ma kowanne yanayi da kowacce matsala da kuma bukata da ake da su . . . Wannan sunan alkawari ne, ya gaya mana game da Allah, kuma ya taimaka mana mu tuna da shi. Allah zai kasance da aminci har abada game da sunansa, kuma ba zai taɓa jin kunya ba.”
4. (a) Mene ne Ishaya 26:4 ya aririce mu mu yi? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
4 Ka tambayi kanka: ‘Shin na san Jehobah sosai har na dogara gare shi? Ina sauraron abin da zai faru a nan gaba da gaba gaɗi kuwa, da sanin cewa Allah yana ja-goranci?’ Ishaya 26:4 ya ce: “Ku dogara ga Ubangiji har abada: gama cikin Ubangiji Yahweh akwai madawwamin dutse.” Hakika, Allah ba ya sa hannu a cikin harkokin mutane ta mu’ujiza kamar yadda ya yi a wasu lokatai a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, a matsayin “madawwamin dutse” za a iya dogara gare shi “har abada.” Ta yaya Allahnmu da za mu iya dogara gare shi yake taimakon bayinsa amintattu a yau? Bari mu tattauna hanyoyi uku: Yana ƙarfafa mu idan mun nemi taimakonsa don mu jimre wa gwaji, yana taimakonmu idan muna fuskantar wariya ko kuma tsanantawa, kuma yana ƙarfafa mu sa’ad da muke alhini sosai. Yayin da muke bincika waɗannan hanyoyi, ku yi ƙoƙarin yin tunani a kan yadda za ku iya ƙarfafa dogararku ga Jehobah.
Ka Dogara ga Allah Sa’ad da Aka Gwada Ka Ka Yi Abu Marar Kyau
5. Kamar yadda yake da dogararmu ga Allah, a wacce hanya ce za mu iya fuskantar gwaji sosai?
5 Zai iya kasance mana da sauƙi mu dogara ga Jehobah idan ya zo ga alkawarinsa na Aljanna ko kuma tashin matattu, tun da abubuwan da muke ɗokin gani ne. Amma zai iya kasancewa da wuya mu dogara gare shi idan ya zo ga batun ɗabi’a, muna amince cewa yin biyayya ga dokokinsa da ƙa’idodinsa ya dace kuma zai sa mu farin ciki matuƙa. Sarki Sulemanu ya rubuta wannan faɗakarwa: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” (Mis. 3:5, 6) Ka lura da kalmomin nan “al’amuranka” da “hanyoyinka.” Hakika, ya kamata hanyoyin rayuwarmu gabaki ɗaya su nuna begenmu na Kirista da kuma dogararmu ga Allah. Sa’ad da muke fuskantar gwaje-gwaje, ta yaya za mu iya nuna cewa muna dogara ga Allah?
6. Ta yaya za mu iya ƙarfafa dogararmu na ƙin mugun tunani?
6 Daina yin mugunta yana somawa daga tunaninmu. (Karanta Romawa 8:5; Afisawa 2:3.) Ta yaya za ka iya ƙarfafa ƙudurinka na ƙin tunanin banza? Ka yi la’akari da waɗannan hanyoyi biyar: 1. Ka nemi taimakon Allah ta wurin addu’a. (Mat. 6:9, 13) 2. Ka yi bimbini a kan misalan Littafi Mai Tsarki na waɗanda ba su yi biyayya ga Jehobah ba da kuma waɗanda suka yi biyayya. Sai ku lura da yadda abubuwa suka kasance musu.a (1 Kor. 10:8-11) 3. Ka yi tunani a kan lahani na tunani da na motsin rai da zunubi zai iya jawo muku da kuma ƙaunatattunku. 4. Ka yi tunani a kan yadda Allah yake ji sa’ad da ɗaya cikin bayinsa ya yi zunubi mai tsanani. (Karanta Zabura 78:40, 41.) 5. Ka yi tunanin farin cikin da Jehobah yake yi sa’ad da ya ga bawansa amintacce ya ƙi mugunta kuma ya yi abu mai kyau ko a fili ko kuma a asirce. (Zab. 15:1, 2; Mis. 27:11) Kai ma za ka iya dogara ga Jehobah ta yin abin da ya dace.
Ka Dogara ga Allah Sa’ad da Kake Fuskantar Wariya da Hamayya
7. Waɗanne gwaje-gwaje ne Irmiya ya fuskanta, kuma yaya ya ji a wasu lokatai?
7 ’Yan’uwanmu da yawa suna zama a yankuna masu wuya sosai. Annabi Irmiya ya yi hidima a irin wannan wurin, wato, a kwanaki na ƙarshe na al’ummar Yahuda. Ana gwada imaninsa ga Jehobah kullum domin yana shelar saƙon Allah na hukunci. A wani lokaci, har ma Baruch, sakatarensa amintacce, ya yi kukan kasala. (Irm. 45:2, 3) Shin Irmiya ya yi sanyin gwiwa ne? Ya yi baƙin ciki a wasu lokatai. Ya ce: “La’antaciya ce ranan nan da aka haife ni. Don menene na fito daga cikin ciki domin in ga wahala da baƙinciki, kwanakina su lalace da kunya?”—Irm. 20:14, 15, 18.
8, 9. Bisa ga Irmiya 17:7, 8 da Zabura 1:1-3, mene ne ya kamata mu yi don mu ci gaba da ba da ’ya’ya?
8 Duk da haka, Irmiya bai yi sanyin gwiwa ba. Ya ci gaba da dogara ga Jehobah. A sakamakon haka, wannan annabi mai aminci ya shaida cikawar kalaman Jehobah da ke rubuce a Irmiya 17:7, 8: “Mai-albarka ne mutum wanda ya ke dogara ga Ubangiji, wanda Ubangiji ne begensa. Gama za ya zama kamar itacen da aka dasa a bakin ruwaye, wanda yana miƙa sawayensa a wajen kogi, ba za ya ji tsoro sa’anda zafin rana ke zuwa ba, amma ganyayensa za su yi kore; babu abin da za ya dame shi a shekaran fari, ba kuwa za ya dena bada ’ya’ya ba.”
9 Kamar itace mai ’ya’ya wanda aka “dasa a bakin ruwaye” Irmiya bai taɓa “dena bada ’ya’ya ba.” Bai ƙyale mugaye masu hamayya da suka kewaye shi su rinjaye shi ba. Maimakon haka, ya manne wa Mai Ba Da “ruwaye” da ke kiyaye rai kuma ya saurari dukan abin da Jehobah ya gaya masa. (Karanta Zabura 1:1-3; Irm. 20:9) Irmiya misali ne mai kyau a gare mu, musamman ga wasu cikinmu da suke bauta wa Allah a yankuna masu cike da matsaloli! Idan kana cikin wannan yanayin, ka ci gaba da dogara ga Jehobah, wanda zai ba ka jimiri yayin da kake “miƙa hadaya ta yabo ga . . . sunansa.”—Ibran. 13:15.
10. Waɗanne albarka ne muke da su, kuma me ya kamata mu tambayi kanmu?
10 Jehobah ya ba mu abubuwa masu yawa don su taimaka mana mu jimre wa matsaloli na rayuwa a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ita ce, cikakkiyar Kalmar Allah, wadda aka fassara ta daidai cikin harsuna da yawa. Ya yi mana tanadin abinci na ruhaniya a kan kari ta wajen rukunin bawan nan mai-aminci, mai-hikima. Ya kuma yi mana tanadin ’yan’uwa masu bi a tarurruka da kuma manyan taro da za su tallafa mana. Shin kana yin amfani da waɗannan tanadodin sosai kuwa? Dukan waɗanda suke yin hakan za su “yi rairawa domin murna a zuci.” Amma dai waɗanda suka ƙi sauraron Allah za su ‘yi kuka domin ɓacin zuciya, za su yi ihu domin karyawar ruhu.’—Isha. 65:13, 14.
Ka Dogara ga Allah Sa’ad da Kake Bi da Alhini
11, 12. Game da matsaloli na duniya, wanne abu mai kyau ne ya kamata mu yi?
11 Kamar yadda aka annabta, annoba da yawa suna shafan ’yan Adam. (Mat. 24:6-8; R. Yoh. 12:12) Idan ambaliyar ruwa ta faru, abin da mutane sukan yawan yi shi ne su gudu zuwa kan tsauni ko kuma su hau kan rufin gini mai tsayi. Hakazalika, yayin da matsalolin duniya suke daɗa ƙaruwa, mutane da yawa suna dogara ga arziki da siyasa, ko ƙungiyoyin addinai, da kuma kimiyya da fasaha. Amma babu ɗaya daga cikin waɗannan da ke kawo kāriya ta ainihi. (Irm. 17:5, 6) A wani ɓangaren kuma, bayin Jehobah suna samun kāriya ta ainihi daga “madawwamin dutse.” (Isha. 26:4) Marubucin wannan zaburar ya ce: “[Jehobah] ne mai kiyaye ni, Mai Cetona, Shi ne kariyata.” (Karanta Zabura 62:6-9, Littafi Mai Tsarki.) Ta yaya za mu sa wannan Mai Kiyaye mu ya zama mafakarmu?
12 Muna manne wa Jehobah sa’ad da muka yi biyayya ga Kalmarsa, wadda ta saɓa wa hikimar ’yan Adam. (Zab. 73:23, 24) Alal misali, mutanen da hikimar ’yan Adam ta rinjaye su suna iya cewa: ‘Rai guda kaɗai kake da shi, saboda haka, ka yi amfani da shi sosai.’ ‘Ka biɗi aiki mai kyau.’ ‘Ka nemi kuɗi sosai.’ ‘Ka sayi wannan, ka sayi wancan.’ ‘Ka yi tafiye-tafiye, ka more duniya.’ Amma hikima daga wurin Allah ta jitu da wannan shawara ta gaba: ‘[Bari] waɗanda suke moran duniya, [su zama] kamar ba su cika moriyatata ba: gama ƙa’idar duniyan nan tana shuɗewa.’ (1 Kor. 7:31) Hakazalika, Yesu ya aririce mu mu saka ayyukan Mulki farko a rayuwarmu da hakan mu tara “dukiya cikin sama,” inda za su samu tsaro na ainihi.—Mat. 6:19, 20.
13. Ta yin tunani a kan kalaman da ke 1 Yohanna 2:15-17, me ya kamata mu tambayi kanmu?
13 Shin ra’ayinka game da “duniya” da “abin da ke cikin duniya” yana nuna cewa kana dogara gabaki ɗaya ga Allah? (1 Yoh. 2:15-17) Shin wadata ta ruhaniya da kuma gatar yin hidimar Mulki suna da muhimminci sosai a gare ka fiye da abin da duniyar nan take tanadarwa? (Filib. 3:8) Kana ƙoƙari ka sa ‘idonka ya kasance sarai’? (Mat. 6:22) Hakika, Allah ba ya son ka kasance marar kan gado musamman idan kana da iyali da kake kula da su. (1 Tim. 5:8) Amma yana bukatar bayinsa su dogara gare shi gabaki ɗaya, ba ga duniyar Shaiɗan da take taɓarɓarewa ba.—Ibran. 13:5.
14-16. Ta yaya wasu suka amfana ta wajen sa ‘idanunsu ya kasance sarai’ da kuma sa abubuwan Mulki farko a rayuwarsu?
14 Ka yi la’akari da misalin Richard da Ruth, masu ƙananan ’ya’ya uku. “Ina ji a cikin zuciyata cewa akwai abubuwa da yawa da zan iya yi wa Jehobah,” in ji Richard. “Ina yin rayuwa mai gamsarwa amma ina ji cewa ba na ba Allah dukan abin da nake da shi. Bayan na yi addu’a a kan batun kuma na yi shawara sosai, Ni da Ruth muka tsai da shawara cewa zan nemi izini daga shugaban aikina don na riƙa yin aiki kwanaki huɗu a mako, ko da yake tattalin arzikin ƙasar tana ƙan taɓarɓarewa. Shugaban ya amince da roƙona, kuma na soma yin amfani da sabon tsarin kafin wata ɗaya.” Yaya Richard yake ji yanzu?
15 “Albashin da ake biya na ya ragu da kashi ashirin,” in ji shi, “amma yanzu ina da ƙarin kwanaki hamsin a shekara don na kasance tare da iyalina kuma na kula da yara na. Na ninka sa’o’in da nake yi a hidimar fage sau biyu, na ninka nazarin Littafi Mai Tsarki da nake gudanarwa sau uku, kuma ina yin ja-gora a cikin ikilisiya sosai. Kuma don lokacin da nake kasancewa tare da yara na ya ƙaru, hakan ya ba Ruth zarafin yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a kai a kai. Kuma na ƙuduri aniya na ci gaba da wannan tsarin yadda zai yiwu.”
16 Roy da Petina, waɗanda har yanzu suna da ’ya da take tare da su a gida, sun rage sa’o’in da suke kasancewa a wurin aikinsu don su saka hannu sosai a hidima ta cikakken lokaci. “Ina aiki kwanaki uku a mako,” in ji Roy, “kuma Petina tana yi na tsawon kwanaki biyu. Kuma, mun ƙaura daga wani babban gida da muke zama ciki zuwa ƙaramin gida, wanda ya fi sauƙi a kula da shi. Kafin mu haifi ɗanmu da ’yarmu, mun yi hidimar majagaba, kuma ba mu taɓa rashin marmarin yin hidimar majagaba ba. Saboda haka, sa’ad da yaranmu suka yi girma, muka soma hidima ta cikakken lokaci kuma. Babu yawan kuɗi da za a iya kwatanta da albarka da muke morewa.”
Bari ‘Salama ta Allah’ ta Yi wa Zuciyarka Ja-gora
17. Tun da ba mu san abin da zai faru gobe ba, ta yaya Nassosi suka ƙarfafa ka?
17 Babu kowannenmu da ya san abin da zai faru gobe, domin “sa’a, da tsautsayi” sukan sami kowannenmu. (M. Wa. 9:11, LMT) Amma bai kamata yin tunani game da abin da zai iya faruwa a nan gaba ya sa mu rasa kwanciyar hankali ba, kamar yadda yake faruwa da waɗanda ba su da dangantaka na kud da kud da Allah. (Mat. 6:34) Manzo Bulus ya rubuta: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku.”—Filib. 4:6, 7.
18, 19. A waɗanne hanyoyi ne Allah yake ƙarfafa mu? Ka ba da misali.
18 ’Yan’uwa da yawa da suke fuskantar matsaloli suna shaida kwanciyar rai da lumana daga Jehobah. Wata ’yar’uwa ta ce: “Wani likita ya yi ƙoƙari sau da yawa ya tilasta mini na amince a ƙara mini jini. Abin da yake fara furtawa kowacce safiya shi ne, ‘Wanne irin shashanci ne wannan na ƙin ƙarin jini.’ Na yi addu’a ga Jehobah cikin zuciyata a lokacin da kuma wasu lokatai, kuma na shaida salamarsa. Na kasance da ƙarfi sosai kamar dutse. Duk da cewa na gaji sosai don ƙanƙantar jini da ke jiki na, na samu ƙarfin bayyana imani na dalla-dalla daga Nassosi.”
19 A wasu lokatai, Allah zai iya ƙarfafa mu ta ɗan’uwanmu mai bi ko kuma ta abinci na ruhaniya a lokacinsa. Wataƙila ka taɓa ji ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ce: “Lallai wannan talifin ne nake bukata. Don ni aka rubuta shi!” Hakika, ko mene ne yanayinmu ko kuma bukatarmu, Jehobah zai ƙaunace mu idan mun dogara gare shi. Ballantana ma, mu “tumakin[sa]” ne, kuma yana kiranmu da sunansa.—Zab. 100:3; Yoh. 10:16; A. M. 15:14, 17.
20. Me ya sa bayin Jehobah za su samu kāriya sa’ad da aka halaka duniyar Shaiɗan?
20 Za a halaka dukan abubuwa da mutane da ke duniyar Shaiɗan suke dogara a kai a “ranar fushin Ubangiji” da ke kusatowa. Zinariya da azurfa, da kuma ko waɗanne irin dukiyoyi ba za su iya kāre su ba. (Zaf. 1:18; Mis. 11:4) “Madawwamin dutse” ne kaɗai zai iya zama mafakarmu. (Isha. 26:4) Saboda haka bari mu dogara gabaki ɗaya ga Jehobah yanzu ta yin biyayya ga hanyoyinsa na adalci, ta wurin yaɗa saƙon Mulki duk da cewa muna fuskantar wariya ko hamayya, da kuma ta miƙa masa dukan alhininmu. Yayin da muke yin dukan waɗannan abubuwan, za mu ‘zauna lafiya, mu zauna da rai a kwance, ba tsoron masifa.’—Mis. 1:33.
[Hasiya]
Za Ka Iya Bayyanawa?
Ta yaya za mu iya dogara ga Allah
• sa’ad da muke fuskantar jarrabar yin zunubi?
• sa’ad da muke fuskantar wariya ko hamayya?
• sa’ad da muke fuskantar alhini?
[Hoton da ke shafi na 13]
Yin biyayya ga mizanan Allah suna kai ga samun farin ciki
[Hoton da ke shafi na 15]
‘Jehobah madawwamin dutse ne’