Ka Koya Daga Kalmar Allah
Mene Ne Nufin Allah ga Duniya?
Wannan talifin ya tattauna tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin tunani a kansu kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Mene ne nufin Allah ga duniya?
Duniya wurin zaman ’yan Adam ne. Bayan ya halicce mala’iku don su zauna a sama, Allah ya halicci mutum domin ya ji daɗin duniya. (Ayuba 38:4, 7) Shi ya sa Jehobah ya saka mutumi na farko a cikin aljanna mai kyau mai suna Adnin, kuma ya ba Adamu da zuriyar da zai samu a nan gaba begen more rayuwa har abada a duniya.—Farawa 2:15-17; karanta Zabura 115:16.
Lambun Adnin wani ɗan ƙaramin yanki ne a duniya. Ma’aurata na farko, Adamu da Hauwa’u, za su haifi ’ya’ya. Yayin da iyalin take ƙaruwa, za su gyara duniya kuma su mai da ita aljanna. (Farawa 1:28) Ba za a taɓa halaka duniya ba.—Karanta Zabura 104:5.
2. Me ya sa duniya ba aljanna ba ce yanzu?
Adamu da Hauwa’u sun yi rashin biyayya ga Allah, shi ya sa aka kore su daga Adnin. Daga nan ne aljanna ta ɓace, kuma babu wani ɗan Adam ɗin da ya yi nasarar sake kafa ta. Littafi Mai Tsarki ya ce: “An miƙa duniya ga hannun miyagu.”—Ayuba 9:24; karanta Farawa 3:23, 24.
Amma Jehobah bai mance ainihin nufinsa ga ’yan Adam ba, kuma Allah ba zai taɓa kasawa ba. (Ishaya 45:18) Zai mai da ’yan Adam ga ainihin yadda yake son su kasance.—Karanta Zabura 37:11.
3. Ta yaya Allah zai sake kawo salama a duniya?
Domin ’yan Adam su more salama, dole ne Allah ya fara kawar da mugayen mutane. A yaƙin Armageddon, mala’ikun Allah za su halaka dukan waɗanda suke hamayya da Allah. Za a ɗaure Shaiɗan har tsawon shekara 1,000, amma mutanen da suke ƙaunar Allah za su tsira domin su more sabon tsari a duniya.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 20:1-3; 21:3, 4.
4. A yaushe ne wahala za ta ƙare?
A cikin shekara 1,000, Yesu zai yi sarauta daga sama bisa duniya kuma zai mai da ta aljanna. Zai kuma kawar da zunuban waɗanda suke ƙaunar Allah. Da haka, Yesu zai kawar da ciwo, tsufa da kuma mutuwa.—Karanta Ishaya 11:9; 25:8; 33:24; 35:1.
A yaushe ne Allah zai kawar da mugunta a duniya? Yesu ya ba da “alamar” da za ta nuna cewa ƙarshe ya yi kusa. Yanayin da duniya take a ciki a yau yana yin barazana ga rayuwar ’yan Adam kuma hakan ya nuna cewa muna rayuwa ne a “karewar zamani.”—Karanta Matta 24:3, 7-14, 21, 22, Littafi Mai Tsarki; 2 Timotawus 3:1-5.
5. Su wane ne za su shiga Aljanna?
Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi almajirai kuma su koya musu hanyoyin Allah ta ƙauna. (Matta 28:19, 20) A dukan duniya, Jehobah yana shirya miliyoyin mutane don su yi rayuwa a cikin sabon yanayi a duniya. (Zafaniya 2:3) A Majami’un Mulki na Shaidun Jehobah, mutane suna koyon yadda za su zama magidanta da matan aure, da kuma iyaye maza da mata masu halin kirki. Yara tare da iyaye suna koyon dalilan da za su sa su gaskata da rayuwa mai daɗi da ke tafe a nan gaba.—Karanta Mikah 4:1-4.
A Majami’ar Mulki, za ka sadu da mutanen da suke ƙaunar Allah waɗanda suke so su koyi yadda za su faranta masa rai.—Ibraniyawa 10:24, 25.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 3 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.