Ku Koyar Da Yaranku
Ka Taɓa Jin Kaɗaici da Tsoro Kuwa?
MUTANE da yawa a yau suna jin kaɗaici; suna jin cewa babu wanda ya damu da su. Sau da yawa, tsofaffi sukan yi irin wannan tunanin. Amma yara da yawa a yau, har da waɗanda suke bauta wa Allah, suna jin kaɗaici da tsoro. Ka san abin da ya sa?—a
Da akwai dalilai da yawa. Bari mu ɗauki misalin wani mutumin da ya rayu a dā can, kusan shekaru dubu kafin a haifi Yesu. Sunansa Iliya. Ya rayu ne a lokacin da al’ummar Isra’ila ta daina bauta wa Allah na gaskiya, Jehobah. Yawancin Isra’ilawa sun riga sun soma bauta wa allan ƙarya, Baal. Iliya ya ce: “Ga ni kaɗai na rage.” Amma kana tunanin cewa Iliya ne kaɗai ya rage a cikin waɗanda suke bauta wa Jehobah?—
Ko da yake bai san da hakan ba, akwai mutane a Isra’ila da suke bauta wa Allah na gaskiya. Amma, suna ɓoye. Suna jin tsoro. Ka san abin da ya sa?—
Ahab, sarkin Isra’ila, ba ya bauta wa Jehobah; yana bauta wa Baal, allan ƙarya da muguwar matarsa, Jezebel, take bauta ma wa. Saboda haka, ita da Ahab suna neman waɗanda suke bauta wa Jehobah don su kashe su, musamman Iliya. Abin da ya sa Iliya ya gudu ke nan. Ya yi tafiyar kusan mil 300 (kilomita 483), zuwa cikin hamada a Horeb, wurin da aka kira Sinai a cikin Littafi Mai Tsarki. A wurin, ɗarurruwan shekaru kafin lokacin Iliya, Jehobah ya ba mutanensa Dokoki Goma da kuma sauran Dokarsa. Iliya ya ɓoye kansa a cikin wani kogo a Horeb. Kana ganin ya kamata Iliya ya tsorata ne?—
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kafin lokacin, Jehobah ya yi amfani da Iliya wajen yin mu’ujizai masu girma. Akwai lokacin da Jehobah ya amsa addu’ar da Iliya ya yi na aiko wuta daga sama don ta cinye hadaya. A wannan hanyar, Jehobah ya nuna cewa Shi ne Allah na gaskiya, ba Baal ba. Sa’ad da Iliya yake cikin kogon, Jehobah ya yi magana da shi.
“Mi ka ke yi daga nan?” In ji Jehobah. A lokacin ne Iliya ya ce, ‘Na ga cewa ni kaɗai na rage a cikin waɗanda suke bauta maka.’ A cikin haƙuri, Jehobah ya yi wa Iliya gyara, yana cewa, ‘duk da hakanan na rage mutum dubu bakwai a cikin Isra’ila waɗanda suke bauta mini.’ Jehobah ya gaya wa Iliya ya koma, ya bayyana masa cewa Yana da ƙarin aikin da zai yi masa.
Mene ne kake ganin za mu iya koya daga misalin Iliya?— Waɗanda suke bauta wa Jehobah ma sukan ji tsoro a wasu lokatai. Saboda haka dukanmu, matasa da tsofaffi, muna bukatar mu nemi taimakon Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi.”
Akwai wani darasi kuma: Muna da ’yan’uwa maza da mata a ko’ina waɗanda suke ƙaunarmu da kuma Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “’Yan’uwan[mu] da ke cikin duniya suna shan waɗannan azabai da ku ke sha.” Ba ka farin ciki sanin cewa muna da ’yan’uwa a ko’ina?—
Ka karanta wuraren nan a cikin naka Littafi Mai Tsarki
1 Sarakuna 19:3-18
Kubawar Shari’a 5:1-22
Zabura 145:18
1 Bitrus 5:9
[Hasiya]
a Idan kana karanta wa yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.