Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/15 pp. 6-8
  • Yadda Za Mu Kasance Masu Gaskiya a Duniya Marar Gaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Kasance Masu Gaskiya a Duniya Marar Gaskiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jin Tsoron Jehobah Yadda ya Dace
  • Lamiri da Aka Koyar da Littafi Mai Tsarki
  • Yin Wadar Zuci
  • Ka Zama Mai Yin Gaskiya a Wajen Aiki
  • Ka Biya Basussuka
  • Ka Guji Yin Ƙarya
  • Yin Gaskiya Hali ne da Ke Ɗaukaka Jehobah
  • Ku Zama Masu Gaskiya a Kowane Abu
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ku Kasance Masu Gaskiya Cikin Dukan Abu
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Amfanin Zama Mai Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ka Kasance Mai Gaskiya Cikin Dukan Abu
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/15 pp. 6-8

Yadda Za Mu Kasance Masu Gaskiya a Duniya Marar Gaskiya

RASHIN gaskiya yana ko’ina a duniya kamar iskar da muke shaƙa. Mutane suna faɗin ƙarya, suna cutan mutane, suna sata, ba sa biyan bashi kuma suna yin maguɗi a kasuwanci. Sau da yawa, kasancewa a irin wannan wurin yana gwada ƙudurinmu na yin gaskiya. Ta yaya za mu ci gaba da guje wa yin ha’inci? Bari mu yi la’akari da abubuwa uku da za su taimaka mana mu yi hakan. Su ne tsoron Jehobah da lamiri mai kyau da kuma kasancewa da wadar zuci.

Jin Tsoron Jehobah Yadda ya Dace

Annabi Ishaya ya rubuta: “Ubangiji shi ne mai-mulkinmu, Ubangiji shi ne mai-bada shari’a, Ubangiji shi ne sarkinmu.” (Isha. 33:22) Fahimtar ikon Jehobah zai sa mu ji tsoro ta ibada, wanda abin da ke sa mu ƙudurta guje wa halin ha’inci ne. Misalai 16:6 ta ce: “Ta wurin tsoron Ubangiji kuma mutane su kan rabu da mugunta.” Wannan ba irin tsoron da muke yi ba ne cewa Allah zai hukunta mu, amma tsoro ne don kada mu ɓata wa Ubanmu na samaniya rai, wanda yake son zaman lafiyarmu sosai.—1 Bit. 3:12.

Labari na gaba ya kwatanta sakamako mai kyau na irin wannan tsoron da ya dace. Ricardo da matarsa, Fernanda, sun karɓi kuɗin da ya yi daidai da daloli ɗari bakwai daga asusun bankinsu.a Fernanda ta saka kuɗin a cikin jakarta ba tare da ƙirgawa ba. Sa’ad da suka isa gida bayan sun yi amfani da wasu kuɗaɗe daga ciki, sun yi mamaki cewa kuɗin da ya rage da ke cikin jakar Fernanda ya yi daidai da kuɗin da suka karɓo. Suka kammala cewa: “Babu shakka, kuɗin da kashiyar ta ba mu ya ninka wanda muke bukata.” Da farko, sun ji kamar su ajiye kuɗin, tun da yake suna da sauran abubuwa da yawa da za su saya. Ricardo ya bayyana cewa: “Mun yi addu’a ga Jehobah sosai don ya ba mu ƙarfi mu mayar da kuɗin. Muradinmu na faranta masa rai da ya jitu da roƙonsa da ke Misalai 27:11 ya sa mu so mayar da kuɗin.”

Lamiri da Aka Koyar da Littafi Mai Tsarki

Za mu iya koyar da lamirinmu ta wurin yin nazarin Littafi Mai tsarki da kuma yin amfani da abin muke koya. Da hakan, ‘maganar Allah da rayayyiya ce, kuma mai-aikatawa,’ za ta taɓa tunaninmu har da zuciyarmu. Wannan za ta motsa mu mu “yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.”—Ibran. 4:12; 13:18.

Ka yi la’akari da labarin João. Ya ci bashin da ya yi daidai da daloli dubu biyar. Sai ya ƙaura zuwa wani birni, ba tare da biyan bashin ba. Bayan shekaru takwas, João ya koyi gaskiya, kuma lamirinsa da Littafi Mai Tsarki ya koyar ya motsa shi ya koma kamfani inda ya ci bashin don ya biya su! Tun da yake João zai kula da matarsa da kuma yara huɗu da ɗan ƙaramin kuɗin da yake samu, kamfanin ya amince ya biya bashin kaɗan-kaɗan duk wata.

Yin Wadar Zuci

Manzo Bulus ya rubuta: “Ibada tare da wadar zuci riba ce mai-girma. . . . Da ya ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.” (1 Tim. 6:6-8) Yin amfani da wannan gargaɗin zai taimaka mana mu guji hadama, kasuwanci da haram ne, da tsarin yin arziki dare ɗaya. (Mis. 28:20) Bin gargaɗin Bulus zai kuma taimaka mana mu saka Mulkin Allah farko a rayuwarmu muna yin gaba gaɗi cewa zai tanadar mana da bukatunmu.—Mat. 6:25-34.

Amma, saboda “ruɗin dukiya,” bai kamata mu yi tunanin cewa ba za mu iya faɗa wa haɗarin yin haɗama da ƙyashi ba. (Mat. 13:22) Ka yi la’akari da labarin Achan. Ya shaida sa’ad da Isra’ilawa suka ƙetare Kogin Urdun ta mu’ujiza. Duk da haka, haɗamarsa ba ta ƙyale shi ya ƙi jarrabar satar azurfa da zinariya da kuma tufafi masu tsada daga ganimar birnin Yariko ba. Yin hakan ya sa ya rasa ransa. (Josh. 7:1, 20-26) Shi ya sa ƙarnuka da yawa bayan hakan, Yesu ya ba da wannan kashedin: “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi.”—Luk 12:15.

Ka Zama Mai Yin Gaskiya a Wajen Aiki

Yanzu bari mu tattauna wasu yanayi da za su iya gwada ƙudurinmu na kasancewa masu gaskiya a dukan abubuwa. Kasancewa masu gaskiya a wurin aiki ya haɗa da ƙin yin “taɓe taɓe,” ko da yin hakan gama gari ne. (Tit. 2:9, 10) Jurandir, wanda yake aikin gwamnati, yana faɗan gaskiya sa’ad da yake rubuta kuɗaɗen da ya kashe idan ya yi tafiya. Amma abokan aikinsa suna karɓan fiye da kuɗaɗen da suka kashe. Suna yin hakan domin shugaban sashensu yana rufe maguɗin da suke yi. Har shugaban aikin ya tsauta wa Jurandir domin ba ya yin maguɗi, sai ya daina tura shi tafiye-tafiye don sana’a. Da shigewar lokaci, kamfanin ya ƙididdiga kuɗaɗen da aka kashe a tafiye-tafiyen, kuma ya yaba wa Jurandir don gaskiya da ya yi. Aka kuma ƙara mai girma.

Matsayin André a inda yake aiki shi ne sayar da kayayyakin da kamfani ya yi, kuma shugabansa ya gaya masa cewa ya cire kuɗi sau biyu daga asusun waɗanda suka yi sayayya. Amma ɗan’uwanmu ya yi addu’a ga Jehobah don ya ba shi gaba gaɗi ya yi biyayya ga ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Zab. 145:18-20) Ya kuma yi ƙoƙari ya bayyana wa shugabansa dalilin da ya sa bai yi hakan ba, amma hakan ya ci tura. Saboda haka, André ya yi murabus daga wurin aikin da ake biyansa albashi mai tsoka. Amma dai, kusan shekara ɗaya bayan hakan, shugaban wurin aikinsa na dā ya sake kiransa ya soma yi masa aiki, kuma ya tabbatar masa cewa ya daina wannan halin. Sai aka ƙara wa André matsayi zuwa manaja.

Ka Biya Basussuka

Manzo Bulus ya shawarci Kiristoci: “Kada ku ku riƙe bashin kome ga kowa.” (Rom. 13:8) Muna iya yin ƙoƙarin neman hujja don kada mu biya bashi, ta yin tunani cewa wanda yake bin mu bashi ba ya bukatar kuɗin domin yana da isashen kuɗi. Amma Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan gargaɗin: “Mai-mugunta ya kan ci bashi, ba ya kan biya ba.”—Zab. 37:21.

Shin idan “sa’a, da tsautsayi” suka hana mu biyan bashi kuma fa? (M. Wa. 9:11, Littafi Mai Tsarki) Francisco ya ari kuɗi da ya yi daidai da daloli dubu bakwai daga wurin Alfredo don ya biya bashi da shi. Amma domin wasu matsalolin kasuwanci, Francisco bai samu biyan bashin a daidai lokacin da aka tsara ba. Sai ya je wurin Alfredo don su tattauna batun, kuma Alfredo ya amince ya biya shi kuɗin kaɗan-kaɗan.

Ka Guji Yin Ƙarya

Ka tuna mummunar misalin Hananiya da Safiratu, wasu ma’aurata a ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko. Bayan sun sayar da fili, suka kawo wa manzannin rabin riɓar kuma suka yi da’awa cewa shi ke nan kuɗin. Sun so su burge mutane da karimcinsu na ƙarya. Amma manzo Bitrus da taimakon ruhu mai tsarki na Allah ya tona asirinsu, kuma Jehobah ya kashe su.—A. M. 5:1-11.

Akasin Hananiya da Safiratu marasa gaskiya, marubutan Littafi Mai Tsarki sun faɗi gaskiya. Musa cikin gaskiya ya rubuta yadda rashin kame fushinsa ya hana shi shigar Ƙasar Alkawari. (Lit. Lis. 20:7-13) Hakazalika, Yunana bai rufe ƙasawarsa ba kafin da kuma bayan ya yi wa mutanen Nineba wa’azi. Maimakon haka, ya rubuta kome.—Yun. 1:1-3; 4:1-3.

Abin da ya faru da Nathalia ’yar shekara 14 a makaranta ya nuna cewa ana bukatar gaba gaɗi don a faɗi gaskiya, ko da hakan zai kawo sakamako marar kyau. Ta sake duba takardun jarabawa da ta rubuta kuma ta lura cewa ba ta ci ɗaya daga cikin amsoshin da malaminta ya maka cewa ta ci ba. Nathalia ba ta yi jinkirin gaya wa malaminta ba, ko da yake ta san cewa hakan zai rage makin da za ta samu. Ta ce: “Iyaye na sun koya mini cewa idan ina so na faranta wa Jehobah rai, dole ne na riƙa faɗin gaskiya. Da a ce ban gaya wa malamina ba, da lamirina ya dame ni.” Malamin ya yi farin ciki don gaskiyar da Nathalia ta yi.

Yin Gaskiya Hali ne da Ke Ɗaukaka Jehobah

Wata ’yar shekara 17, mai suna Giselle, ta tsinci zabira da ke ɗauke da takardu da kuma daloli 35. Ta yi shirye-shirye ta hanyar malaman makarantar don a mayar da zabirar ga mai shi. Bayan wata ɗaya, mataimakin shugaban makarantar ya karanta wa dukan ’yan ajin Giselle wasiƙa da ke yabonta don gaskiyar da ta yi kuma ya yaba wa iyalinta da addininta domin reno mai kyau da suka yi mata. ‘Ayyukanta masu-kyau’ sun ɗaukaka Jehobah.—Mat. 5:14-16.

Ana bukatar ƙoƙari sosai don a kasance da gaskiya idan ana zama cikin mutane ‘masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, marasa-tsarki.’ (2 Tim. 3:2) Duk da haka, tsoron Jehobah da ya dace da lamirin da aka koyar da Littafi Mai Tsarki da kuma yin wadar zuci za su taimaka mana mu kasance da gaskiya a duniya da ake yin rashin gaskiya. Muna kuma samun dangantaka na kud da kud da Jehobah, wanda ‘mai-adalci ne; kuma yana ƙaunar adalci’.—Zab. 11:7.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

[Hotuna da ke shari na 7]

Jin tsoron Jehobah da ya dace yana ƙarfafa ƙudurinmu na kasancewa masu gaskiya

[Hoton da ke shari na 8]

Halinmu na yin gaskiya yana ɗaukaka Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba