Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 7/1 pp. 24-25
  • Me ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta da Wahala?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta da Wahala?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta da Wahala?
    Albishiri Daga Allah!
  • Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Me Ya Sa Akwai Mugunta da Wahala a Ko’ina?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Me Ya Sa Allah Ya Halicci Mutane?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 7/1 pp. 24-25

Ka Koya Daga Kalmar Allah

Me ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta da Wahala?

Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.

1. Ta yaya aka soma mugunta?

An soma mugunta ne a duniya sa’ad da Shaiɗan ya tabka ƙarya ta farko. Shaiɗan ba mugu ba ne sa’ad da aka halicce shi. Shi kamiltaccen mala’ika ne, amma ‘bai tsaya a kan gaskiya ba.’ (Yohanna 8:44) Ya yi sha’awar ainihin bautar da ake yi wa Allah. Shaiɗan ya tabka ƙarya ga mace ta farko, Hauwa’u, kuma ya shawo kanta ta yi masa biyayya a maimakon Allah. Adamu da Hauwa’u sun yi rashin biyayya ga Allah. Matakin da Adamu ya ɗauka ne ya jawo wahala da mutuwa.—Karanta Farawa 3:1-6, 17-19.

Sa’ad da Shaiɗan ya gaya wa Hauwa’u ta yi rashin biyayya ga Allah, yana tawaye ne ga ikon mallakar Allah. Kamar Shaiɗan, yawancin mutane sun ƙi Allah a matsayin Sarki. Shi ya sa, Shaiɗan ya zama “sarkin duniya.”—Karanta Yohanna 14:30; Ru’ya ta Yohanna 12:9.

2. Shin halittun Allah suna da aibi ne?

Mutane da kuma mala’ikun da Allah ya halitta suna da kamiltacciyar damar cika umurnin Allah. (Kubawar Shari’a 32:5) Allah ya halicce mu da ’yancin zaɓen yin nagarta ko mugunta. Wannan ’yancin ya ba mu zarafin nuna ƙaunarmu ga Allah.—Karanta Yaƙub 1:13-15; 1 Yohanna 5:3.

3. Me ya sa Allah ya ƙyale wahala?

Jehobah ya ɗan ba da lokaci ga waɗanda suke tawaye da ikon mallakarsa. Me ya sa? Domin ya nuna cewa mutane ba za su taɓa amfana ba idan suka yi sarauta ba tare da ja-gorarsa ba. (Irmiya 10:23) An riga an warware wannan batun bayan shekaru 6,000 da halittar ’yan Adam. ’Yan Adam masu sarauta sun kasa kawar da yaƙi da aikata laifi da rashin gaskiya da cuta.—Karanta Mai-Wa’azi 7:29; 8:9; Romawa 9:17.

Akasin haka, waɗanda suka amince da Sarautar Allah suna amfana. (Ishaya 48:17, 18) Ba da daɗewa ba, Jehobah zai halaka dukan gwamnatocin ’yan Adam. Waɗanda suka zaɓi sarautar Allah ne kawai za su zauna a duniya.—Ishaya 2:3, 4; 11:9; karanta Daniyel 2:44.

4. Wane zarafi ne muke da shi saboda haƙurin da Allah yake nunawa?

Shaiɗan ya yi da’awar cewa ’yan Adam ba za su yi biyayya cikin aminci ga Jehobah ba. Haƙurin da Allah ya yi yana ba mu zarafin nuna ko mulkin Allah muke so ko na ’yan Adam. Muna nuna zaɓin da muka yi ta wajen salon rayuwar da muke yi.—Karanta Ayuba 1:8-11; Misalai 27:11.

5. Ta yaya za mu zaɓi Allah a matsayin Sarki?

Muna zaɓan Allah a matsayin Sarki sa’ad da muka biɗi bauta ta gaskiya kuma muka rungume ta kamar yadda Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ya ce. (Yohanna 4:23) Za mu kuma guji saka hannu a siyasa da yaƙi, kamar yadda Yesu ya yi.—Karanta Yohanna 17:14.

Shaiɗan yana amfani da ikonsa ya ɗaukaka yin lalata da kuma ayyuka masu lahani. Idan muka ƙi irin waɗannan ayyukan, wasu daga cikin abokanmu da danginmu suna iya yi mana ba’a ko hamayya. (1 Bitrus 4:3, 4) Saboda haka, muna da zaɓi. Za mu yi tarayya da mutanen da suke ƙaunar Allah? Za mu bi dokokinsa da ke cike da ƙauna da hikima? Idan muka yi hakan, za mu nuna cewa Shaiɗan ya yi ƙarya sa’ad da ya yi da’awar cewa babu wanda zai yi abin da Allah ya ce.—Karanta 1 Korintiyawa 6:9, 10; 15:33.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 11 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Hoto a shafi na 24]

Adamu ya yi mugun zaɓi

[Hoto a shafi na 25]

Zaɓin da muka yi za su nuna ko Allah ne muka zaɓa ya zama Sarkinmu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba