Ku “Zauna A Faɗake” A Matsayin Iyalan Kirista
“Mu zauna a faɗake, da natsuwa.”—1 TAS. 5:6, Littafi Mai Tsarki.
1, 2. Mene ne iyali take bukata ta yi don ta yi nasara wajen kasancewa a faɗake a ruhaniya?
DA YAKE magana game da “babbar ranan nan mai bantsoro ta Ubangiji,” manzo Bulus ya rubuta zuwa ga Kiristoci da ke Tasalonika: “Ba a cikin duhu kuke ba, ’yan’uwa, har da ranan nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo. Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne.” Bulus ya daɗa: “Saboda haka kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu zauna a faɗake, da natsuwa.”—Joel 2:31; 1 Tas. 5:4-6, LMT.
2 Gargaɗin da Bulus ya yi wa Tasalonikawa ya dace ga Kiristoci da suke zama a “kwanakin ƙarshe.” (Dan. 12:4) Yayin da ƙarshen mugun zamanin nan ya kusa, Shaiɗan ya ƙuduri aniya ya yi iya ƙoƙarinsa ya sa mutane da yawa da suke bauta ta gaskiya su daina bauta wa Allah. Saboda haka, yana da kyau mu riƙa tunawa da gargaɗin Bulus na mu kasance a faɗake a ruhaniya. Idan iyalai Kiristoci za su yi nasara wajen kasancewa a faɗake, yana da muhimmanci kowannensu ya cika hakkin da Jehobah ya ba shi ko ita, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana. Saboda haka, wane hakki ne magidanta da mata da kuma yara suke da shi wajen taimaka wa iyalansu su “zauna a faɗake”?
Magidanta, Ku Yi Koyi da “Makiyayi Mai-Kyau”
3. Mene ne hakkin namiji a matsayin shugaban iyali ya ƙunsa bisa ga 1 Timotawus 5:8?
3 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kan mace kuma namiji ne.” (1 Kor. 11:3) Mene ne hakkin namiji ya ƙunsa, a matsayin shugaban iyali? Da suke lissafa fanni ɗaya na shugabanci, Nassosi sun ce: “Idan wani bai yi tattalin nasa ba, balle na iyalinsa, ya musunci imani, gwamma marar-bangaskiya da shi.” (1 Tim. 5:8) Hakika, ya kamata namiji ya yi tanadin abin biyan bukatar iyalinsa. Amma, ba zai riƙa neman kuɗi kaɗai ba don ya biya bukatun iyalinsa idan zai taimaka wa iyalinsa su kasance a faɗake a ruhaniya. Yana bukatar ya ƙarfafa iyalinsa a ruhaniya, yana taimaka wa dukan waɗanda suke cikin iyalin su ƙarfafa dangantakarsu da Allah. (Mis. 24:3, 4) Ta yaya zai iya yin hakan?
4. Mene ne zai iya taimaki namiji ya yi nasara wajen ƙarfafa iyalinsa a ruhaniya?
4 Tun da yake “miji shi ne shugaban mata tasa, kamar yadda Almasihu ke shugaban ikilisiya,” ya kamata namiji mai aure ya bincika kuma ya yi koyi da irin shugabanci da Yesu yake yi a ikilisiya. (Afis. 5:23, LMT) Ka yi la’akari da yadda Yesu ya kwatanta dangantakarsa da mabiyansa. (Karanta Yohanna 10:14, 15.) Mene ne zai taimaki namiji da yake son ya ƙarfafa iyalinsa a ruhaniya ya yi nasara? Ga abin da zai taimake shi: Ya yi nazarin abin da Yesu a matsayin “makiyayi mai-kyau,” ya yi kuma ya faɗa kuma ya “bi sawunsa.” (1 Bit. 2:21) Bari mu yi la’akari da abin da shugaban iyali zai iya koya daga misalin Kristi.
5. Mene ne Makiyayi Mai Kyau ya sani game da ikilisiyar?
5 Don makiyayi da tumakinsa su ƙulla dangantaka, ya kamata su san kuma su amince da juna. Makiyayi ya san kome game da tumakinsa kuma tumakin sun san makiyayinsu kuma sun amince da shi. Sun san muryarsa kuma suna yi masa biyayya. Yesu ya ce: ‘Na san tumaki na, tumaki na kuma sun san ni.’ Bai san ikilisiyar sama sama ba kawai. A Helenanci, kalmar nan “san” tana nufin “sanin abu sosai.” Hakika, Makiyayi Mai Kyau ya san kowanne tumakinsa sosai. Ya san bukatunsu da kasawarsu da kuma ƙarfinsu. Wanda muke bin misalinsa yana lura da kome game da tumakinsa. Kuma tumakin sun san makiyayinsu sosai kuma suna amincewa da shugabancinsa.
6. Ta yaya magidanta za su iya yin koyi da Makiyayi Mai Kyau?
6 Don maigida ya yi koyi da Kristi a yin shugabanci, dole ne ya koya ɗaukan kansa a matsayin makiyayi kuma ya ɗauki waɗanda yake kula da su a matsayin tumaki. Ya kamata ya yi ƙoƙari ya san iyalinsa sosai. Shin maigida yana iya sanin iyalinsa sosai? Hakika, yana kafa misali mai kyau idan yana tattaunawa da kyau da dukan waɗanda suke cikin iyalinsa, yana saurarar damuwarsu, yana shugabanci a ayyukan iyali, kuma yana mai da hankali ga tsai da shawarwari masu kyau da suka shafi batutuwa kamar su bauta ta iyali da halartar taro da fitar hidimar fage da kuma nishaɗi. Yayin da maigida Kirista ya mai da hankali wajen koyon abin da Kalmar Allah ta faɗa kuma ya san waɗanda suke cikin iyalinsa sosai don ya kafa misali kuma ya tsai da shawarwari masu kyau, zai fi sauƙi waɗanda suke cikin iyalinsa su amince da shugabancinsa kuma zai samu gamsuwa don ganin cewa sun kasance da haɗin kai a bauta ta gaskiya.
7, 8. Ta yaya maigida zai iya yin koyi da Makiyayi Mai Kyau wajen nuna ƙauna ga waɗanda suke ƙarƙashin kulawarsa?
7 Makiyayi mai kyau yana kuma ƙaunar tumakinsa. Sa’ad da muka yi nazarin labaran rayuwar Yesu da kuma hidimarsa da ke cikin Linjila, muna godiya sosai don ƙaunar da Yesu ya nuna wa almajiransa. Har ma ya ‘bada ransa domin tumakin.’ Ya kamata magidanta su yi koyi da Yesu wajen nuna ƙauna ga waɗanda suke ƙarƙashin kulawarsu. Maigida da yake son Allah ya amince da shi zai ci gaba da ƙaunar matarsa “kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya” maimakon ya mallake ta. (Afis. 5:25) Da yake ta cancanci a ɗaukaka ta, ya kamata kalamansa su zama na alheri da kuma sanin ya kamata.—1 Bit. 3:7.
8 Ya kamata shugaban iyali ya bi ƙa’idodin Allah sa’ad da yake koyar da yara. Amma, dole ne ya nuna ƙauna ga yaransa. Ya kamata a yi horo cikin ƙauna. Yana iya ɗaukan dogon lokaci kafin wasu yara su fahimci abin da ake son su sani. Saboda haka, ya kamata mahaifi ya kasance da haƙuri sosai. Idan maza suka bi misalin Yesu a ko da yaushe, za su sa gidajensu su zama wurin kāriya da kwanciyar hankali. Iyalansu za su more irin kāriya ta ruhaniya da marubucin zabura ya rera waƙa game da ita.—Karanta Zabura 23:1-6.
9. Kamar Nuhu uban iyali, magidanta Kirista suna da wane hakkin kuma mene ne zai taimaka musu su cika shi?
9 Nuhu uban iyali ya rayu ne a lokacin ƙarshe na duniyar zamaninsa. Amma Jehobah ya cece shi “tare da waɗansu bakwai, sa’anda ya kawo rigyawa bisa duniya ta masu-fajirci.” (2 Bit. 2:5) Nuhu yana da hakkin taimaka wa iyalinsa su tsira wa Rigyawa. Shugaban iyalan Kirista suna da irin wannan matsayin a waɗannan kwanaki na ƙarshe. (Mat. 24:37) Kuma za su iya taimaka wa iyalansu idan suka yi nazarin misalin “makiyayi mai-kyau” kuma suka yi ƙoƙari su yi koyi da shi!
Matan Aure, ‘Ku Gina Gidajenku’
10. Mene ne yake nufi matar aure ta miƙa kai ga mijinta?
10 Manzo Bulus ya rubuta: “Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji.” (Afis. 5:22) Wannan furucin ba ya nufin matsayi marar daraja. Kafin ya halicci Hauwa’u mace ta fari, Allah na gaskiya ya ce: “Ba ya yi kyau ba mutum shi kasance shi ɗaya; sai in yi masa mataimaki mai-dacewa da shi.” (Far. 2:18) Matsayin ‘mataimakiya’ da ‘ta dace’ wato, na tallafa wa mijinta yayin da yake cika hakkinsa na iyali mai daraja ne sosai.
11. Ta yaya mata da abin koyi ne take ‘gina gidanta’?
11 Mata da abin koyi ne tana ayyuka da za su sa iyalinta su amfana. (Karanta Misalai 14:1.) Akasin mata mai wauta wadda take rashin biyayya ga tsarin shugabanci, mata mai hikima tana daraja wannan tsarin sosai. Maimakon ta riƙa nuna halin rashin biyayya da ’yancin kai na mutanen duniya, tana miƙa kai ga mijinta. (Afis. 2:2) Mata mai wauta ba ta jinkirin yin baƙar magana game da mijinta, amma mata mai hikima tana ƙoƙari ta sa yaranta da mutane su ƙara daraja shi. Irin wannan matar tana mai da hankali don kada ta rena shugabancin mijinta ta wajen yin gunaguni ko kuma musu da shi. Da akwai batun yin tattali wajen kashe kuɗi kuma. Mata mai wauta tana iya ɓatar da dukiyar da iyalin ta sha wahala ta samu. Mata mai tallafa wa mijinta ba ta yin hakan. Tana ba da haɗin kai ga mijinta a batutuwan kuɗi. Tana abubuwa da hikima da kuma yin tattali. Ba ta matsa wa mijinta ya yi aiki bayan lokacin aiki.
12. Mene ne mata za ta iya yi don ta taimaka wa iyalinta su kasance “a faɗake”?
12 Mata da abin koyi ne tana taimaka wa iyalinta ta kasance “a faɗake” ta wajen taimaka wa mijin ya koyar da yaransu game da Jehobah. (Mis. 1:8) Tana ƙarfafa tsarin Bauta ta Iyali. Bugu da ƙari, tana goyon bayan mijinta sa’ad da yake ba yaransu gargaɗi da kuma yi musu horo. Dabam take da mata da ba ta da haɗin kai, kuma yaran suna shan wahala a zahiri da kuma a ruhaniya!
13. Me ya sa yake da muhimmanci mata ta tallafa wa mijinta a ayyukansa na tsarin Allah?
13 Ta yaya mata mai tallafa wa mijinta take ji game da hakkin da yake cikawa a cikin ikilisiyar Kirista? Tana murna sosai! Tana farin ciki game da gatarsa ko idan mijin bawa mai hidima ne ko dattijo ko kuma wataƙila yana Kwamitin Hulɗa da Asibitoci ko kuma Masu Tallafa wa Sashen Gina Majami’un Mulki. Babu shakka, za ta yi sadaukarwa wajen tallafa wa mijin ta kalamanta da kuma ayyukanta. Da yake mijinta yana sa hannu a ayyuka na tsarin Allah, ta san cewa hakan na taimaka wa dukan iyalin su kasance a faɗake a ruhaniya.
14. (a) Mene ne zai iya kasance da ƙalubale ga mata mai ba da haɗin kai, kuma yaya za ta iya sha kan wannan ƙalubalen? (b) Ta yaya mata za ta sa iyalinta gabaki ɗaya ta yi zaman lafiya?
14 Zama abin koyi wajen tallafa wa mijin yana iya zama da ƙalubale ga mata sa’ad da mijin ya tsai da shawarar da ba ta so. Duk da haka, tana nuna “ruhu mai-ladabi mai-lafiya” kuma tana haɗa kai da shi don ta sa shawararsa ta yi nasara. (1 Bit. 3:4) Mata mai hikima tana ƙoƙari ta bi misalai masu kyau na mata masu ibada na dā, kamar su Saratu da Ruth da Abigail da kuma Maryamu, mahaifiyar Yesu. (1 Bit. 3:5, 6) Tana kuma koyi da mata tsofaffi na zamani masu “ladabi cikin al’amuransu.” (Tit. 2:3, 4) Ta wajen nuna ƙauna da ladabi ga mijinta, mata da abin koyi ne tana sa aurensu ya yi nasara kuma tana sa iyalin gabaki ɗaya su yi zaman lafiya. Gidanta wurin samun ta’aziyya ne da kuma kāriya. Mata mai ba da haɗin kai tana da tamani ga mutum mai ruhaniya!—Mis. 18:22.
Matasa, ‘Kuna Lura da Al’amura Marasa Ganuwa’
15. Ta yaya matasa za su iya sa hannu don iyalin ta kasance “a faɗake”?
15 Matasa, ta yaya za ku iya sa hannu don iyalinku ta kasance “a faɗake” a ruhaniya? Ku yi la’akari da albarkar da Jehobah zai ba ku. Wataƙila tun lokacin da kuke ƙanana, iyayenku sun nuna muku hotuna da ke nuna yadda rayuwa za ta kasance a cikin Aljanna. Mai yiwuwa sa’ad da kuke girma sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki da littattafai na Kirista don su taimaka muku ku zana hoton zuci na yadda rai madawwami zai kasance a sabuwar duniya. Mai da hankali ga bauta wa Jehobah da kuma tsara rayuwarku bisa hakan zai taimaka muku ku kasance “a faɗake.”
16, 17. Mene ne matasa za su iya yi don su yi nasara a tseren rai?
16 Ku tuna da kalaman manzo Bulus da ke 1 Korantiyawa 9:24. (Karanta.) Ku yi tseren rayuwa da niyyar cin nasara. Ku zaɓi tafarkin da zai sa ku samu rawanin rai madawwami. Mutane da yawa sun ƙyale biɗan abubuwan mallaka su janye hankalinsu daga samun rawanin. Hakan aikin wauta ne! Tsara rayuwa bisa samun wadata ba ya kawo farin ciki na gaske. Abubuwan da za a iya saya da kuɗi na ɗan lokaci ne. Amma, kana lura ‘da al’amura marasa-ganuwa.’ Me ya sa? Domin “al’amuran da ba su ganuwa madawwama ne.”—2 Kor. 4:18.
17 ‘Al’amura marasa-ganuwa’ sun haɗa da albarka na Mulkin. Ku tsara rayuwarku yadda za ku samu wannan albarka. Za ku samu farin ciki na gaske ta wajen yin amfani da rayuwarku a hidimar Jehobah. Bauta wa Allah na gaskiya yana kawo zarafin cim ma maƙasudai na ɗan lokaci da kuma na dogon lokaci.a Kafa maƙasudai da za su yiwu zai taimaka muku ku mai da hankali ga bauta wa Allah da ra’ayin samun rawanin rai madawwami.—1 Yoh. 2:17.
18, 19. Ta yaya matashi zai san ko ya mai da gaskiya tasa?
18 Matasa, mataki na farko da za ku ɗauka don ku samu rai madawwami shi ne, ku mai da gaskiya ta zama taku. Kun ɗauki wannan matakin kuwa? Ku tambayi kanku: ‘Ni mai ruhaniya ne, ko kuwa iyayena ne suke sa ni na sa hannu a ayyuka na ruhaniya? Shin ina koyon halaye da suke sa na faranta wa Allah rai? Ina yin ƙoƙari na riƙa yin ayyuka da suka shafi bauta ta gaskiya a kai a kai, kamar yin addu’a da yin nazari da halartan taro da kuma fita hidimar fage a kai a kai? Ina kusaci Allah ta wurin ƙulla dangantaka na kud da kud da shi?—Yaƙ. 4:8.
19 Ku yi bimbini a kan misalin Musa. Duk da cewa yana wurin da ake bin wata al’ada, ya zaɓa a san shi a matsayin mai bauta wa Jehobah maimakon ɗan ’yar Fir’auna. (Karanta Ibraniyawa 11:24-27.) Ku ma matasa Kirista, kuna bukatar ku ƙuduri aniyar bauta wa Jehobah da aminci. Ta yin hakan, za ku samu farin ciki na gaske kuma za ku yi rayuwa mafi kyau a yanzu da kuma begen samun “hakikanin rai.”—1 Tim. 6:19.
20. Su waye ne za su samu rawanin, a tsere na rai?
20 Mutum ɗaya ne kaɗai yake cin tsere na zamanin dā. Ba hakan yake da tsere na rai ba. Nufin Allah ne “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:3, 4) Mutane da yawa sun ci tsere kafin kai kuma da yawa suna tseren tare da kai. (Ibran. 12:1, 2) Dukan waɗanda ba su yi kasala ba za su samu rawanin. Saboda haka, ka ƙuduri aniya ka ci rawanin!
21. Mene ne za a tattauna a talifi na gaba?
21 Babu shakka “ranan nan mai-girma mai-ban razana ta Ubangiji” za ta zo. (Mal. 4:5) Bai kamata ranan nan ta kama iyalai Kirista babu shiri ba. Wajibi ne dukan waɗanda suke cikin iyali su cika hakkinsu na Nassi. Mene ne kuma za ku iya yi don ku kasance a faɗake a ruhaniya kuma ku ƙarfafa dangantakarku da Allah? Talifi na gaba zai tattauna fannoni uku da suka shafi ruhaniya na dukan iyali.
[Hasiya]
a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2010 shafuffuka na 12-16.
Me Ka Koya?
• Me ya sa yake da muhimmanci iyalai Kirista su kasance “a faɗake”?
• Ta yaya maigida zai iya yin koyi da Makiyayi Mai Kyau?
• Mene ne mata da abin koyi ne za ta iya yi don ta tallafa wa mijinta?
• Ta yaya matasa za su iya taimaka wajen sa iyalansu su kasance a faɗake a ruhaniya?
[Hoton da ke shafi na 9]
Mata mai ba da haɗin kai ga mijinta tana da tamani ga mutum mai ruhaniya