Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 7/1 pp. 26-27
  • Akwai Bege ga Matattu Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwai Bege ga Matattu Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Wane Bege Ne Matattu Suke da Shi?
    Albishiri Daga Allah!
  • Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Za a Ta da Matattu!
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Menene Zai Faru Idan Muka Mutu?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 7/1 pp. 26-27

Ka Koya Daga Kalmar Allah

Akwai Bege ga Matattu Kuwa?

Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.

1. Wane bege ne matattu suke da shi?

Sa’ad da Yesu ya iso Bait’anya kusa da Urushalima, abokinsa Li’azaru ya riga ya yi kwanaki huɗu da mutuwa. Yesu ya tafi inda kabarin yake tare da Martha da Maryamu, ’yan’uwan mamacin. Ba da daɗewa ba, jama’a ta taru. Ka yi tunanin irin farin cikin da Martha da Maryamu suka yi sa’ad da Yesu ya ta da Li’azaru!—Karanta Yohanna 11:20-24, 38-44.

Martha ta ba da gaskiya cewa matattu za su tashi. Tun da daɗewa bayin Jehobah masu aminci suka san cewa a nan gaba, Allah zai ta da waɗanda suka mutu don su sake rayuwa a duniya.—Karanta Ayuba 14:14, 15.

2. Mene ne yanayin matattu?

Ko da yake lumfashin rai da ake kira “ruhu,” yana taimaka wa ’yan Adam da dabobbi su ci gaba da rayuwa, mu ba ruhohi ba ne da ke zaune a naman jiki. (Mai-Wa’azi 3:19; Farawa 7:21, 22) Mu halittu ne da aka sifanta daga turɓayar ƙasa. (Farawa 2:7; 3:19) Sa’ad da ƙwaƙwalwarmu ta mutu, shawarwarinmu sun ƙare. Shi ya sa, bayan da aka ta da shi daga matattu, Li’azaru bai faɗi kome ba game da wani abin da ya faru da shi sa’ad da ya mutu, domin matattu ba su san kome ba.—Zabura 146:4; Mai-Wa’azi 9:5, 10.

Hakika, matattu ba sa shan wahala. Saboda haka, wannan koyarwar da ta ce wai Allah yana azabtar da mutane bayan sun mutu ƙarya ce. Tana ɓata sunan Allah. Yana ƙyamar ra’ayin azabtar da mutane a cikin wuta.—Karanta Irmiya 7:31.

3. Za mu iya yin magana da matattu?

Matattu ba za su iya yin magana ba. (Zabura 115:17) Amma sa’ad da mugayen mala’iku suka yi magana da mutane, suna iya yin ƙaryar cewa su ruhun mutumin da ya mutu ne. (2 Bitrus 2:4) Jehobah ya haramta ƙoƙarin yin magana da matattu.—Karanta Kubawar Shari’a 18:10, 11.

4. Su waye ne za a ta da daga matattu?

A sabuwar duniya mai zuwa, za a ta da miliyoyin mutane da suke cikin kabari. Za a ta da waɗanda suka aikata mugunta domin ba su san Jehobah ba.—Karanta Luka 23:43; Ayyukan Manzanni 24:15.

Waɗanda aka ta da daga matattu za su iya koyon gaskiya game da Allah kuma su ba da gaskiya ga Yesu ta wajen yi masa biyayya. (Ru’ya ta Yohanna 20:11-13) Waɗanda suka yi abubuwa masu kyau bayan an ta da su daga matattu za su rayu har abada a duniya. Amma, wasu daga cikin waɗanda aka ta da daga matattu za su ci gaba da aikata mugunta. Tun da yake a lokacin ne za a yi musu hukunci bisa ga mugun halinsu, tashinsu zai zama “tashi na shari’a.”—Karanta Yohanna 5:28, 29.

5. Mene ne tashin matattu ya koya mana game da Jehobah?

Tashin matattu ya yiwu ne saboda Jehobah ya aiko Ɗansa ya ba da ransa domin mu. Saboda haka, Jehobah ya nuna mana ƙauna da alheri ne da ba mu cancanci samu ba.—Karanta Yohanna 3:16; Romawa 6:23.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 6 da 7 na wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Hoto a shafi na 26]

An halicci Adamu ne daga turɓayar ƙasa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba