Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 6/15 pp. 3-6
  • Ya Kamata a Yi wa Matasa Baftisma Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Kamata a Yi wa Matasa Baftisma Ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zama Almajirin Yesu ne Abu Mafi Muhimmanci
  • Tabbaci Cewa Ɗanka Almajirin Kristi Ne
  • Matasa Za Su Iya Yaba wa Jehobah
  • Iyaye, Kuna Taimaka wa Yaranku Su Yi Baftisma?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Baftisma Tana da Muhimmanci ga Kiristoci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Yara da Matasa, Kun Yi Shirin Yin Baftisma Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Za Ka Amfana Sosai Idan Ka Yi Baftisma!
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 6/15 pp. 3-6

Ya Kamata a Yi wa Matasa Baftisma Ne?

“I NA farin ciki matuƙa cewa yanzu ’yata tana bauta wa Jehobah, kuma na san cewa ita ma tana farin ciki,” in ji Carlos,a wani mahaifi Kirista a ƙasar Philippines. Wani mahaifi daga ƙasar Hellas ya rubuta: “Ni da matata mun yi farin ciki cewa yaranmu uku sun yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah sa’ad da suke ƙuruciya. Suna samun ci gaba a ruhaniya kuma suna farin cikin bauta wa Jehobah.”

Iyaye Kiristoci suna da dalilin yin farin ciki sosai sa’ad da yaransu suka yi baftisma, amma a wasu lokatai suna farin ciki da kuma damuwa. Wata mahaifiya ta ce: “Na yi farin ciki sosai amma na damu ƙwarai.” Me ya sa mahaifiyar take jin hakan? “Na fahimci cewa ɗana yanzu zai ba da lissafin kansa ga Jehobah.”

Bauta wa Jehobah a matsayin Mashaidi da ya yi baftisma maƙasudi ne da ya kamata dukan matasa su kafa wa kansu. Duk da haka, iyayen da suke bauta wa Allah suna iya yin mamaki, ‘Na san cewa ɗana ya samu ci gaba, amma shin yana da ƙarfi ya tsayayya wa matsi na yin lalata kuma ya kasance da tsabta a gaban Jehobah?’ Wasu suna iya tambayar kansu, ‘Sa’ad da ɗana ya fuskanci gwajin son abin duniya, shin zai iya ci gaba da bauta wa Allah da farin ciki da kuma himma?’ Saboda haka, wace ja-gora ta Littafi Mai Tsarki ce za ta iya taimaka wa iyaye su san ko yaransu suna shirye su yi baftisma?

Zama Almajirin Yesu ne Abu Mafi Muhimmanci

Maimakon faɗan shekara na yin baftisma, Kalmar Allah ta kwatanta yanayi na ruhaniya na waɗanda suka cancanci ɗaukan wannan matakin. Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Ku almajirtarda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma.” (Mat. 28:19) Saboda haka, waɗanda sun riga sun zama almajiran Kristi ne za su yi baftisma.

Wane ne almajiri? Littafin nan Insight on the Scriptures ya bayyana: “Wannan kalmar tana nuni musamman ga dukan waɗanda suka gaskata da koyarwar Kristi da kuma waɗanda suka bi koyarwarsa sosai.” Shin matasa za su iya zama tabbatattun almajiran Kristi ne? Wata ’yar’uwa wadda ta yi hidima fiye da shekara 40 a matsayin mai wa’azi a ƙasar waje a Amirka ta Tsakiya zuwa Yamma ta rubuta game da kanta da yayanta da kuma ƙanwarta: “Kafin mu yi baftisma, mun yi girma kuma mun kasance da muradin bauta wa Allah da kuma kasancewa a Aljanna. Keɓe kanmu ya taimaka mana mu kasance da ƙarfi sa’ad da muka fuskanci gwaje-gwaje da matasa suke fuskanta. Ba mu yi nadamar keɓe kanmu ga Allah ba tun muna ƙanana.”

Ta yaya za ka san ko ɗanka ya zama almajirin Kristi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ko yaro ya sanu ta wurin ayyukansa, Ko aikinsa mai-tsabta ne, ko daidai ne kuma.” (Mis. 20:11) Ka yi la’akari da wasu ayyuka da suke nuna cewa matashi yana sa ‘ci gabansa ya bayanu’ a matsayin almajiri.—1 Tim. 4:15.

Tabbaci Cewa Ɗanka Almajirin Kristi Ne

Shin ɗanka yana yi maka biyayya? (Kol. 3:20) Yana yin aikace-aikacen gida da aka ba shi? Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu sa’ad da yake shekara goma sha biyu: “Yana biyayya da [iyayensa].” (Luk 2:51) Hakika, babu yaro a yau da zai yi cikkakiyar biyayya ga iyayensa. Amma ya kamata Kiristoci na gaskiya su “bi sawun [Yesu].” Saboda haka, ya kamata a san matasa da suke son su yi baftisma a matsayin masu yin biyayya ga iyayensu.—1 Bit. 2:21.

Ka yi la’akari da tambayoyi na gaba: Shin ɗanka ko ’yarka yana ko tana ‘fara biɗan mulkin’ ta wajen saka hannu sosai a hidimar fage? (Mat. 6:33) Yana a shirye ya gaya wa mutane bishara ko kuwa kana tilasta masa kafin ya fita hidimar fage kuma ya yi magana a ƙofa-ƙofa? Shin yana mai da hankali ga hakkinsa a matsayin mai shela da bai yi baftisma ba? Shin yana son koma ziyara ga waɗanda suke son saƙon? Ya sanar da abokan makaranta da malamansa cewa shi Mashaidin Jehobah ne?

Halartar tarurrukan ikilisiya tana da muhimmanci ne a gare shi? (Zab. 122:1) Yana jin daɗin yin kalami a Nazarin Hasumiyar Tsaro da kuma Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya? Shin ya sa suna a Makarantar Hidima ta Allah kuma yana jin daɗin yin ayyukansa na makaranta?—Ibran. 10:24, 25.

Shin ɗanka yana ƙoƙari ya kasance da tsabta ta ɗabi’a ta wajen guje wa tarayya mai lahani a makaranta da wani wuri? (Mis. 13:20) Waɗanne kaɗe-kaɗe da fina-finai da shirye-shirye na talabijin da wasannin bidiyo da kuma dandalin Intane ne ya fi so? Shin kalamansa da ayyukansa sun nuna cewa yana son ya bi mizanan Littafi Mai Tsarki?

Shin ɗanka ya san Littafi Mai Tsarki sosai? Zai iya faɗan abin da ya koya a lokacin Bauta ta Iyali da yamma a nasa kalmomi? Zai iya bayyana muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki? (Mis. 2:6-9) Shin yana son karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin nazarin littattafan da bawan nan mai-aminci mai-hikima ya wallafa? (Mat. 24:45) Shin yana yin tambayoyi game da koyarwa da ayoyin Littafi Mai Tsarki?

Waɗannan tambayoyin suna iya taimaka maka ka gwada ci gaba da ɗanka yake yi a ruhaniya. Bayan ka yi la’akari da su, kana iya kammala cewa yana bukatar ya yi gyara a wasu wurare kafin ya yi baftisma. Amma, idan tafarkin rayuwarsa ya nuna cewa ya zama almajiri kuma ya keɓe kansa ga Allah, kana iya jin cewa za ka ƙyale shi ya yi baftisma.

Matasa Za Su Iya Yaba wa Jehobah

Bayin Allah da yawa sun nuna amincinsu a lokacin da suke ƙuruciya ko kuma sa’ad da suke ƙanana. Ka yi tunanin Yusufu da Sama’ila da Yosiya da kuma Yesu. (Far. 37:2; 39:1-3; 1 Sam. 1:24-28; 2:18-20; 2 Laba. 34:1-3; Luk 2:42-49) Babu shakka an tarbiyyar da ’ya’yan Filibus mata huɗu sosai da suke annabci sa’ad da suke ƙanana.—A. M. 21:8, 9.

Wani Mashaidi a ƙasar Hellas ya ce: “Na yi baftisma sa’ad da nake ɗan shekara sha biyu. Ban taɓa yin nadama da shawarata ba. Shekaru ashirin da huɗu sun shige, kuma na yi shekaru ashirin da uku ina hidima ta cikakken lokaci. Ƙaunata ga Jehobah ne ta taimake ni na jimre da wahaloli da matasa suke fuskanta. Sa’ad da nake ɗan shekara sha biyu, ban san Nassi a lokacin kamar yanzu ba. Amma na sani cewa ina ƙaunar Jehobah kuma ina son na bauta masa har abada. Ina farin ciki cewa ya taimaka mini na ci gaba a hidimarsa.”

Ya kamata wanda yake nuna cewa shi almajiri ne na gaske ya yi baftisma ko shi matashi ne ko tsoho. Manzo Bulus ya rubuta: “Da zuciya mutum ya ke bada gaskiya zuwa adalci; da baki kuma a ke shaida zuwa ceto.” (Rom. 10:10) Sa’ad da matashi almajiri na Kristi ya ɗauki wannan mataki na yin baftisma, shi da iyayensa sun cim ma wani abu na musamman. Kada ku bar kome ya hana ku ko kuma yaranku daga samun farin ciki da za ku more a nan gaba.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

[Akwati a shafi na 5]

Ra’ayin da Ya Dace na Yin Baftisma

Wasu iyaye suna ɗaukan baftismar yaransu a matsayin mataki mai kyau da ya ƙunshi kasada, wato, yana kamar samun lasisin direba. Shin yin baftisma da tsarkakkar hidima za su iya hana mutum yin nasara a nan gaba ne? A’a, in ji Littafi Mai Tsarki. Misalai 10:22 ya ce: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.” Kuma Bulus ya rubuta wa matashi Timotawus: “Amma ibada tare da wadar zuci riba ce mai-girma.”—1 Tim. 6:6.

Hakika, bauta wa Jehobah ba ta da sauƙi. Irmiya ya fuskanci matsaloli da yawa a aikinsa a matsayinsa na annabin Allah. Duk da haka, ya rubuta game da bautarsa ga Allah na gaskiya: “Zantattukanka sun zama mani murna da farinciki na zuciyata: gama an kira ni da sunanka, ya Ubangiji Allah mai-runduna.” (Irm. 15:16) Irmiya ya sani cewa hidimar Allah ne tushen farin cikinsa. Duniyar Shaiɗan ce tushen wahaloli. Iyaye suna bukatar su taimaka wa yaransu su fahimci wannan bambancin.—Irm. 1:19.

[Akwati/​Hoto a shafi na 6]

Shin Ya Kamata Ɗana Ya Jira Kafin Ya Yi Baftisma?

A wasu lokatai iyaye suna yanka shawara cewa kada yaransu su yi baftisma tukuna, ko da sun cancanci yin hakan. Mene ne wataƙila yake jawo hakan?

Ina tsoron cewa idan ɗana ya yi baftisma, zai iya yin zunubi mai tsanani a nan gaba kuma a yi masa yankan zumunci. Shin ya dace a gaskata cewa matashin da ya ƙi yin baftisma ba shi da alhaki don ayyukansa ga Allah? Sulemanu ya faɗa waɗannan kalaman ga matasa: “Ka sani, a kan dukan waɗannan abu [ayyukanka] Allah za shi kawo ka cikin shari’a.” (M. Wa. 11:9) Bulus bai ambata wata shekara ba sa’ad da ya ba da wannan tunasarwa: “Kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.”—Rom. 14:12.

Waɗanda suka yi baftisma da waɗanda ba su yi ba za su kawo lissafin kansu ga Allah. Kada ka manta, Jehobah yana kāre bayinsa ta ‘ƙin barin a yi musu jaraba wadda ta fi ƙarfinsu.’ (1 Kor. 10:13) Muddin sun yi “hankali shinfiɗe” kuma suna tsayayya wa gwaji, irin waɗannan za su kasance da tabbaci cewa Allah zai iya taimake su. (1 Bit. 5:6-9) Wata mahaifiya Kirista ta rubuta: “Yaran da suka yi baftisma suna da ƙarin dalilai na ƙin saka hannu a munanan abubuwa na duniya. Ɗana da ya yi baftisma sa’ad da yake da shekara sha biyar, yana jin cewa baftisma kāriya ce. Ya ce: ‘Ba za ka ji yin abin da ya saɓa wa dokar Jehobah ba.’ Baftisma tana sa mutum ya kasance mai adalci.”

Idan ka koyar da yaranka ta kalamai da ayyuka su yi biyayya ga Jehobah, za ka iya kasance da tabbaci cewa za su ci gaba da yin biyayya bayan sun yi baftisma. Misalai 20:7 ya ce: “Mutum mai-adalci wanda ya ke tafiya cikin kamalarsa, ’ya’yansa masu-albarka ne.”

Zan so yaro na ya cim ma wasu maƙasudai tukun. Ya kamata matasa su koya yin aiki don su kasance da wadar zuci da sannu-sannu. Amma ƙarfafa su su biɗi ilimi da wadata maimakon bauta ta gaskiya tana da haɗari. Sa’ad da yake magana game da “iri,” ko kalma ta Mulkin, da ba ta yi girma ba, Yesu ya ce: “Wanda aka shuka wurin ƙayayuwa kuma, shi ne wanda ya kan ji magana; amma ɗawainiyar duniya, da ruɗin dukiya, su kan shaƙe magana, ta zama marar-amfani.” (Mat. 13:22) Idan iyaye suka ƙarfafa yaronsu ya biɗi maƙasudai na duniya, hakan zai rage muradinsa na bauta wa Allah.

Wani dattijo da ya manyanta da ke magana game da matasa da suka cancanci yin baftisma amma iyayensu ba su yarda ba ya ce: “Hana matashi yin baftisma zai iya rage ƙwazonsa na ruhaniya kuma ya sa shi sanyin gwiwa.” Kuma wani mai kula mai ziyara ya rubuta: “Matashi zai iya soma ji kamar bai da tamani a ruhaniya. Zai iya dogara ga duniya don ta biya bukatunsa.”

[Hoto]

Shin zuwan jami’a ne ya kamata ya kasance farko?

[Hoto a shafi na 3]

Matashi yana iya nuna cewa ya cancanci ya zama almajiri

[Hoto a shafi na 3]

Shirya tarurruka da kuma yin kalamai

[Hoto a shafi na 4]

Yin biyayya ga iyaye

[Hoto a shafi na 4]

Fita hidimar fage

[Hoto a shafi na 4]

Yin addu’a ta kansa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba