Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 7/15 pp. 4-9
  • An Yi Nasara Bisa Shari’a Da Aka Yi Shekaru Da Yawa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Yi Nasara Bisa Shari’a Da Aka Yi Shekaru Da Yawa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AN SOMA BINCIKE
  • LITTAFI MAI TSARKI A CIKIN KOTU
  • TUHUMAR BA TA YI NASARA BA
  • MUN YI NASARA, AMMA BA SHI KE NAN BA
  • BA MU YI NASARA BA, AMMA BA SHI KE NAN BA
  • TSANANTAWAR TA ƘARU
  • SHARI’AR DA AKA “BA DA SHAIDA”
  • Gwagwarmaya don Samun ’Yancin Yin Ibada
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Masu Wa’azin Mulkin Sun Kai Ƙara Kotu
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 7/15 pp. 4-9

An Yi Nasara Bisa Shari’a Da Aka Yi Shekaru Da Yawa!

A SHEKARA ta 1991, gwamnatin ƙasar Rasha ta dā ta yi wa Shaidun Jehobah rajista a matsayin addinin da aka amince da shi a ƙasar. Sa’ad da tsohuwar gwamnatin ta daina sarauta, sabuwar gwamnatin Rasha ma ta yi wa Shaidun Jehobah rajista. Sabuwar gwamnatin ta amince cewa tsohuwar gwamnatin ta tsananta wa Shaidun Jehobah. A shekara ta 1993, ƙungiyar nan Moscow’s Department of Justice [Sashen Shari’a na Birnin Moscow] ya yi wa Shaidun Jehobah rajista da sunan nan Moscow Community of Jehobah’s Witnesses [Jama’ar Shaidun Jehobah na Birnin Moscow]. Kuma a shekarar, gwamnatin ƙasar Rasha ta yi sabon tsarin mulki da ya ba mutane ’yancin yin wasu abubuwa. Tsarin mulkin ya ce kowa yana da ’yancin bin kowanne addinin da yake so. ’Yan’uwanmu sun daɗe suna jiran wannan ’yancin.

Bayan wannan sanarwar ’yan’uwanmu a ƙasar Rasha sun daɗa ƙwazonsu na yin wa’azi, kuma mutane da yawa sun koyi gaskiya a sakamako. (2 Tim. 4:2) Daga Shekara ta 1990 zuwa 1995, adadin Shaidun Jehobah a ƙasar Rasha ya ƙaru daga ɗari uku zuwa dubu biyar! Maƙiyan Shaidun Jehobah suka damu ƙwarai saboda wannan ƙarin. Sai suka soma tsananta wa mutanen Jehobah a kotuna.

AN SOMA BINCIKE

An kai ƙara ta farko a watan Yuni na 1995. Wasu rukunin mutane a birnin Moscow waɗanda suke goyon bayan Cocin Orthodox na Rasha sun kai ƙarar ’yan’uwanmu cewa suna karya doka. A watan Yuni na shekara ta 1996, masu binciken sun ce ba su ga wani laifin da Shaidun Jehobah suka yi ba. Amma rukunin suka kai ƙarar ’yan’uwanmu a kan batun sau huɗu. Kuma masu binciken sun duba sosai amma ba su ga wani laifi da Shaidun Jehobah suka yi ba. A ƙarshe, aka kammala shari’ar a ranar 13 ga Afrilu, 1998.

Lauyan gwamnatin ta ce babu alama da ta nuna cewa Shaidun Jehobah sun yi wani laifi. Amma sai ta ba da shawara cewa wata hanya da za a iya hana Shaidun Jehobah aikinsu shi ne jama’ar su kai ƙara kotu, ba ’yan sanda ba. Sai lauyan Northern Administrative Circuit of Moscow [Kotun Arewancin Birnin Moscow] ya amince da ƙarar da aka kai game da Shaidun Jehobah. A ranar 29 ga Satumba, 1998, aka soma shari’ar a Golovinsky District Court a Birnin Moscow.

LITTAFI MAI TSARKI A CIKIN KOTU

Tatyana Kondratyeva ce Lauyar gwamnati a wannan shari’ar. Ta tuhumi Shaidun Jehobah da dokar da aka sa hannu a shekara ta 1997. Wannan dokar ta ce Kiristocin Orthodox da Musulunci da Yahudanci da kuma Buddhawa ne kaɗai aka amince da su a ƙasar. Wata jarida ta ce Cocin Orthodox ne ya tilasta wa gwamnati ta kafa wannan dokar don yana son gwamnati ta hana aikin Shaidun Jehobah. (Associated Press, 25 ga Yuni, 1999) Wannan dokar ta ba kotu izini ya hana kowanne addinin da ke sa mutane su tsane wasu. Lauyar gwamnatin ta ce gwamnati ta hana aikin Shaidun Jehobah domin suna sa mutane su tsane juna kuma suna rushe iyalai.

Lauyan da ke kāre Shaidun Jehobah ya yi tambaya: “Su wane ne cikin Addinan Birnin Moscow suke karya doka kuma suke sa mutane su tsane juna?” Lauyar gwamnatin ba ta iya ambata kowa ba. Amma ta ce littattafan Shaidun Jehobah suna sa su tsane mutanen wasu addinai domin littattafan suna koyar cewa Shaidun Jehobah ne kaɗai suke bin addinin gaskiya.

Wani lauya wanda ɗan’uwanmu ne ya miƙa wa alƙalin da kuma lauyar gwamnatin Littafi Mai Tsarki. Sai ya karanta littafin Afisawa 4:5, wanda ya ce: “Ubangiji ɗaya, imani ɗaya, baftisma ɗaya.” Ba da daɗewa ba, alƙalin da lauyar gwamnatin da kuma lauyan da ke kāre ’yan’uwanmu suka soma tattauna Littafi Mai Tsarki, sun tattauna nassosi kamar su Yohanna 17:18 da Yaƙub 1:27. Sai alƙalin ya yi tambaya: “Shin waɗannan ayoyin suna sa mutane su tsane wasu addinai?” Lauyan gwamnatin ta ce yadda take ji ba shi da muhimmanci tun da ba ta da yawan ilimi game da Littafi Mai Tsarki. Sai lauyan da ke kāre ’yan’uwanmu ya nuna littattafan da Cocin Orthodox na Rasha ya wallafa wanda ya faɗa abubuwa da yawa game da Shaidun Jehobah, sai ya yi tambaya: “Shin abubuwan da suka faɗa a cikin waɗannan littattafai sun saɓa wa doka?” Sai lauyar gwamnatin ta sake cewa yadda take ji bai shi da muhimmanci tun da ba ta san addini sosai ba.

TUHUMAR BA TA YI NASARA BA

Lauyar gwamnatin ta ce abin da ya sa ta ce Shaidun Jehobah suna rushe iyalai shi ne don ba sa yin bukukuwa. Ta kuma ce Shaidu ba sa barin yaransu su yi bukukuwa da za su sa su farin ciki kamar yadda kowa ya saba. Daga baya shi ne ta ce dokar ƙasar Rasha ba ta ce mazaunan ƙasar su yi bukukuwa ba. Sai ta kuma ce ba ta taɓa tattauna da wani yaron Shaidu ba kuma ba ta taɓa halartar taron Shaidun Jehobah ba.

Sai lauyar gwamnatin ta gayyaci wani farfesa wanda likitan taɓaɓɓu ne ya faɗa ra’ayinsa a gaban kotun. Ya ce wai karanta littattafanmu yana jawo matsaloli ga ƙwaƙwalwa. Sai ya amince cewa ya kofa abubuwa da yawa da ya faɗa game da wannan shari’ar daga littattafai da shugabannin Cocin Orthodox a Moscow suka rubuta. Ya kuma ce bai taɓa yi wa wani Mashaidin Jehobah jinya ba. Wani likita kuma ya faɗa a gaban kotun cewa ya bincika fiye da Shaidu ɗari a Moscow. Ya ce waɗannan Shaidu ba taɓaɓɓu ba ne kuma suna daɗa daraja addinan wasu bayan sun zama Shaidun Jehobah.

MUN YI NASARA, AMMA BA SHI KE NAN BA

A ranar 12 ga Maris, 1999, alƙalin ta zaɓi mutane biyar masu ilimi su nazarta littattafan Shaidun Jehobah, sai ta dakatar da shari’a na ɗan lokaci. Amma kafin wannan lokacin, Hukumar Shari’a ta Ƙasar Rasha ta ba wasu rukunin mutane izini su nazarta littattafan Shaidu. A ranar 15 ga Afrilu, 1999, wannan rukunin sun ce ba su ga wani laifin da ke littattafanmu ba. Saboda haka, a ranar 29 ga Afrilu, 1999, Hukumar Shari’a ta Ƙasar Rasha ta sanar cewa Shaidun Jehobah su ci gaba da ayyukansu a ƙasar Rasha. Amma a birnin Moscow, alƙalin ta ce mutane biyar da ta zaɓa su ci gaba da nazarin littattafanmu. Wannan abin mamaki ne. Hukumar Shari’a ta Ƙasar Rasha gabaki ɗaya ta ce Shaidun Jehobah suna biyayya ga doka kuma su ci gaba da addininsu. Amma a Moscow, Hukumar Shari’a ta Moscow ta ci gaba da neman laifi da Shaidu domin wasu sun ce suna karya doka!

Shari’ar ta sake somawa a Moscow bayan shekara biyu. A ranar 23 ga Fabrairu, 2001, Alƙali Yelena Prokhorycheva ya yanki shawara cewa babu wani dalili da zai sa a hana Shaidun Jehobah a Moscow yin ayyukansu. A ƙarshe, kotun ya ce dukan laifuffukan da aka ce ’yan’uwanmu sun yi ƙarya ne! Amma lauyar gwamnatin ba ta amince da shawara da aka yanka ba sai ta ce Kotun Birnin Moscow ta sake bincika batun. Watanni uku bayan hakan, a ranar 30 ga Mayu, 2001, kotun ya soke shawarar da Alƙali Prokhorycheva ya yanka. Kotun ya ce a sake wata shari’a kuma a yi amfani da lauyar gwamnatin amma kada a sake amfani da alƙalin da ya yi wancan shari’ar.

BA MU YI NASARA BA, AMMA BA SHI KE NAN BA

A ranar 30 ga Oktoba, 2001, aka sake soma wata shari’a kuma. Sunan alƙalin Vera Dubinskaya ce. Lauyar gwamnatin Kondratyeva ta sake tuhumar Shaidun Jehobah cewa suna sa mutane su tsane juna. Sai ta ce idan gwamnati tana son ta kāre kanta lallai sai ta hana aikin Shaidun Jehobah! Sa’ad da Shaidun Jehobah guda 10,000 da suke Moscow suka ji wannan tuhuma, dukansu suka rubuta wa alƙalin takarda cewa ba su amince da “kāriyar” da lauyan gwamnatin ta ambata ba. Abin farin ciki shi ne cewa a wannan kwanan wata, 30 ga Oktoba, 1999, wato, shekaru goma da suka shige ne gwamnati ta faɗi cewa gwamnatin Rasha ta dā ta tsananta wa Shaidun Jehobah saboda addininsu.

Lauyar gwamnatin ta ce ba ta bukatar ta ba da alamun da suka nuna cewa Shaidun Jehobah suna karya doka. Ta ce ba abin da Shaidun Jehobah suke yi ba ne yake da laifi, amma littattafansu da abin da suka gaskata ne. Ta ce za ta gayyaci wani daga Cocin Orthodox na Ƙasar Rasha ya ba da shaida a kotun. Hakan ya nuna cewa shugabannin Cocin Orthodox na Ƙasar Rasha ne suke son su hana aikin Shaidu. A ranar 22 ga Mayu, 2003, alƙalin ta ba da umurni cewa wasu masana su sake nazarta littattafan Shaidun Jehobah.

A ranar 17 ga Fabrairu, 2004, kotun sun taru don su saurari sakamakon binciken. A binciken da suka yi sun ce littattafanmu na koya wa mutanen yadda za su samu farin ciki a iyalinsu da kuma aurensu. Ba su ga komi a ciki ba da ya nuna cewa muna koya wa mutane su tsane juna. Wasu masana ma suka amince da hakan. Alƙalin ta tambayi wani farfesa na tarihin addinai cewa: “Mene ne ya sa Shaidun Jehobah suke wa’azi?” Farfesa ɗin ya ce wajibi ne Kiristoci su yi wa’azi. Ya ce Littafi Mai Tsarki ya ce musu su riƙa yin wa’azi kuma Kristi ya umurci almajiransa su je su yi wa’azi a dukan ƙasashe. Duk da waɗannan batutuwa, a ranar 26 ga Maris, 2004, alƙalin ta hana aikin Shaidun Jehobah a Moscow. Kotun Birnin Moscow ya amince da wannan hukuncin a ranar 16 ga Yuni, 2004. Wannan yana nufin cewa ikilisiyoyin da ke Moscow ba su da izinin yin ayyukansu. Maƙiyansu sun sa rai cewa za su jawo wa ’yan’uwanmu matsaloli kuma su hana su yin wa’azi.

Amma mene ne ’yan’uwanmu suka yi? ’Yan’uwanmu a Moscow ba su ƙyale maƙiyansu su hana su aikinsu ba. Sun ci gaba da yin wa’azin bishara. (1 Bit. 4:12, 16) Sun tabbata cewa Jehobah zai taimaka musu. Kuma sun kasance a shirye su kāre damar da suke da ita na bauta wa Jehobah.

TSANANTAWAR TA ƘARU

A ranar 25 ga Agusta, 2004, ’yan’uwanmu suka kai ƙara wajen Vladimir Putin, wanda shi ne shugaban ƙasar Rasha a lokacin. Sun bayyana a cikin takardar ƙarar game da yadda suka ji bayan kotun birnin Moscow ya hana aikinsu. Takardar ƙarar tana da kundi 76, kuma mutane 315,000 ne suka sa hannu. A wannan lokacin kuma, shugabannin Cocin Orthodox na Rasha sun ce: “Sam-sam ba mu amince da aikin Shaidun Jehobah ba.”

Wasu mutane a ƙasar Rasha sun amince da wannan ƙaryar game da Shaidun Jehobah kuma suka soma tsananta musu. Sun naushi kuma sun shure Shaidu sa’ad da suke wa’azi a birnin Moscow. Wani mutum cike da fushi ya shure wata ’yar’uwa a kashin bayanta sa’ad da take wa’azi har ta faɗi ta buga kanta a ƙasa. Har aka kai ta asibiti don jinya. Amma ’yan sanda ba su kama wannan mutumin ba. ’Yan sanda suka kama Shaidu da yawa, suka bi da su kamar masu karya doka, kuma suka kulle su a gidan yari. Waɗanda suke kula da gidajen da Shaidun Jehobah suke amfani da su don tarurruka suka kwace gidajen, suna tsoro don kada a kore su daga aiki. Ikilisiyoyi da yawa ba su samu wurin taro ba. Alal misali, ikilisiyoyi arba’in suka soma yin amfani da Majami’un Mulki huɗu da suke wuri ɗaya. Ɗaya cikin ikilisiyar nan tana soma taro na Jawabi ga Jama’a da ƙarfe bakwai da rabi na safiya. Wani mai kula mai ziyara ya ce masu shela sukan tashi ƙarfe biyar na safiya don su halarci taro, kuma sun yi hakan da farin ciki fiye da shekara guda.

SHARI’AR DA AKA “BA DA SHAIDA”

Shaidun Jehobah suna son su nuna cewa hanin da aka yi ga aikinsu na wa’azi a Moscow ya saɓa wa dokar. Saboda haka, a watan Disamba 2004, lauyoyinmu sun kai ƙara a Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam. (Duba akwatin nan “Dalilin da Ya Sa Aka Sake Bincika Shari’ar da Aka Yi a Ƙasar Rasha a Faransa,” a shafi na 6.) Shekara shida bayan hakan, a ranar 10 ga Yuni, 2010, bayan kotun ya bincika dukan tuhumar, ya yanka hukunci cewa Shaidun ba su yi wani laifi ba! Kotun ya ce tuhumar ƙarya ce. Ya kuma ce ya kamata gwamnatin ƙasar Rasha ta daina hanin kuma ta ƙoƙarta don daidaita dukan laifuffukan da ta yi wa Shaidu. Bayan wannan shari’ar, gwamnatin ƙasar Rasha ta kuma ce tana son a sake shari’ar. Sai ta ce Grand Chamber of the European Court of Human Rights [Jam’iyya Mai Girma na Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam] ya sake bincika tuhumar. Amma a ranar 22 ga Nuwamba, 2010, alƙalai biyar daga Kotun suka yanke shawara cewa ba za a sake wata shari’a a kan wannan tuhumar ba. Hakan yana nufin cewa hukuncin da aka yanka ranar 10 ga Yuni, 2010, na ƙarshe ne kuma dole ne a bi hukuncin.—Ka duba akwatin nan “Hukuncin Kotun,” a shafi na 8.

Kotun ya yanka shawara cewa Rukunin Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya kāre ayyukan Shaidun Jehobah. Wannan shawarar ba don ƙasar Rasha kaɗai ba ce. Ta shafi ƙasashe 46 da suke cikin wannan Ƙungiyar Ƙasashen Turai. Alƙalai da lauyoyi da yawa da kuma mutane a duniya baki ɗaya da suka karance ’yancin ’yan Adam za su so su bincika wannan hukuncin. Don me? Domin sa’ad da alƙalan suka yanke hukuncin, sun yi amfani da misalai takwas na hukunce-hukunce da Kotun ya tsai da a dā don ya kāre Shaidun Jehobah. Sun kuma yi amfani da hukunce-hukunce tara da kotuna mafi girma na ƙasar Ajantina da Kanada da Japan da Rasha da Afirka na Kudu da Sifen da Haɗaɗɗen Mulki da kuma Amirka suka yanka don kāre Shaidu. Shaidun Jehobah a dukan duniya za su iya yin amfani da hukuncin da Kotun ya yanke don kāre bautarsu.

Yesu ya gaya wa almajiransa cewa mutane za su kai su “gaban mahukunta da sarakuna” sabili da shi, “domin shaida garesu da Al’ummai kuma.” (Mat. 10:18) Waɗannan shari’o’i da aka yi cikin shekaru sha biyar a ƙasar Rasha ta ba mutanen birnin Moscow da kuma na wasu wurare zarafin ji game da Jehobah sosai fiye da dā. Dukan abubuwan da suka faru a waɗannan shari’o’in sun ba da “shaida” kuma sun taimaka wajen “yaɗuwar bishara.” (Filib. 1:12) Babu komi da kuma kowa da zai iya hana mu yin wa’azin bishara ta Mulkin. Muna addu’a cewa Jehobah ya ci gaba da taimaka wa ’yan’uwanmu masu gaba gaɗi a ƙasar Rasha, waɗanda muke ƙaunarsu matuƙa.

[Akwati/​Hoto a shafi na 6]

Dalilin da Ya Sa Aka Sake Bincika Shari’ar da Aka Yi a Ƙasar Rasha a Faransa

A ranar 28 ga Fabrairu, 1996, ƙasar Rasha ta sa hannu a Takardar Rukunin Turai na ’Yancin ’Yan Adam. (A ranar 5 ga Mayu, 1998, ƙasar Rasha ta amince da Takardar.) Ta wajen sa hannu a takardar hukuncin, gwamnatin ƙasar Rasha ta amince cewa talakawanta suna da

‘’yancin zaɓar addini da kuma ’yancin bin addinin a gida a fili da kuma ’yancin canja addininsu idan bukata ta kama.’—Talifi na 9.

‘’yancin rubuta da kuma faɗin abin da suke ganin ya dace da kuma idar da saƙonni ga mutane.’—Talifi na 10.

‘’yancin yin tarurruka da ba na tawaye ba ne.’—Talifi na 11.

Mutane da kuma ƙungiyoyin da suke da waɗannan matsalolin kuma ba su yi nasara a shari’o’in da aka yi a ƙasarsu ba, su kawo ƙara Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam wanda ke birnin Strasbourg, a Faransa (wanda aka nuna hotonsa a sama). Kotun yana da Alƙalawa 47, wanda ya yi daidai da adadin ƙasashen da suka sa hannu a Takardar Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam. Wajibi ne a aikata bisa ga hukuncin da kotun ya yanka. Wajibi ne ƙasashen da suka sa hannu a takardar kotun su yi biyayya ga hukuncin da ya yanka.

[Akwati a shafi na 8]

Hukuncin Kotun

Ga wasu cikin hukunce-hukuncen da Kotun ya yanka.

Wata tuhumar da aka yi ta ce Shaidun Jehobah suna rushe iyalai. Alƙalan sun yanke hukuncin cewa hakan ba gaskiya ba ce. Sun ce:

“Abin da ke jawo rikicin shi ne wasu da ke cikin iyalin da ba sa bin addini ba sa daraja da kuma amince da ’yancin bin addinin na sauran da suke cikin iyalinsu.”—Sakin layi na 111.

Alƙalan Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ba su samu wani tabbacin da ya goyi bayan zargin da ake yi wa Shaidun Jehobah cewa suna “sa mutane taɓuwa.” Sun ce:

“Kotun ya yi mamaki cewa kotuna na Rasha ba su ambata sunan mutum ɗaya ba da aka yi amfani da wannan hanyar don taka ’yancin lamirinsa ba.”—Sakin layi na 129.

Wani zargin da aka yi wa Shaidun Jehobah shi ne cewa suna sa lafiyar ’yan’uwansu cikin haɗari domin ba sa amince da ƙarin jini. Alƙalan Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ba su amince da tuhumar ba. Sun ce:

“Kowa yana da ’yancin tsai da wa kansa shawarar karɓa ko kuma ƙin wani irin jinya, ko kuma zaɓan wasu hanyoyin magani. Majiyyaci da ya girma yana da ’yancin ya tsai da shawarar ko zai amince a yi masa fiɗa ko kuma ƙarin jini.”—Sakin layi na 136.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba