Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 7/15 pp. 24-28
  • Mene Ne Hutun Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene Ne Hutun Allah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Shin Jehobah Yana “Hutu” Har Ila?
  • Kada Ka “Faɗi Bisa Wannan Misalin Kangara”
  • “Ba Za Su Shiga Cikin Hutuna Ba”
  • Wasu Sun Kasa Shiga Cikin Hutun Allah
  • Ta Yaya Za Mu Iya Shiga Hutun Allah a Yau
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • ‘Akwai Lokacin’ Yin Aiki da Kuma Hutu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 7/15 pp. 24-28

Mene Ne Hutun Allah?

“Akwai fa hutun assabbat ajiyayye domin jama’ar Allah.”—IBRAN. 4:9.

1, 2. Mene ne muka koya daga Farawa 2:3? Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa?

MUN koya daga sura ta farko ta littafin Farawa cewa Allah ya shirya duniya a ranaku shida don mutane su kasance a cikinta. Waɗannan ba ranaku na sa’o’i ashirin da huɗu ba ne. Littafi Mai Tsarki ya furta wannan game da kowanne cikin waɗannan kwanakin: “Akwai maraice akwai safiya kuma.” (Far. 1:5, 8, 13, 19, 23, 31) Amma dai, game da rana ta bakwai, Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Allah ya albarkaci rana ta bakwai, ya tsarkake ta: domin a cikin ta ya huta daga dukan aikin sa wanda Allah ya halitta.’—Far. 2:3.

2 Sa’ad da littafin Farawa ya ce Allah “ya huta,” yana nufi ne cewa Allah yana kan hutawa a lokacin. Saboda haka, za mu iya ce sa’ad da Musa ya rubuta littafin Farawa, a shekara ta 1513 K.Z., Allah yana kan hutawa. Kuma daga baya, Allah ya faɗa a cikin Littafi Mai Tsarki cewa mutane za su iya shiga cikin hutunsa. Shin har yau Allah yana hutu? Idan haka ne, ta yaya za mu iya shiga hutunsa? Yana da muhimmanci sosai mu san amsoshin waɗannan tambayoyin?

Shin Jehobah Yana “Hutu” Har Ila?

3. Ta yaya kalaman Yesu a Yohanna 5:16, 17 suka nuna cewa sa’ad da Yesu ya yi hidima yana cikin rana ta bakwai?

3 Da akwai dalilai biyu da suka sa mu kammala cewa zamanin Yesu da kuma na Kiristoci na ƙarni na farko sun kasance a rana ta bakwai. Mun san dalili na farko daga abin da Yesu ya gaya wa wasu maƙiyansa waɗanda suka yi fushi da shi domin ya warkar da mutane a ranar Assabbaci. Yesu ya ce: ‘Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.’ (Yoh. 5:16, 17) Mene ne yake nufi? Yana nufin cewa: “Ni da Ubana muna aiki iri ɗaya. Ubana ya yi aiki a Assabbacinsa na shekaru dubbai, kuma har ila yana aiki, domin hakan, ni ma ina da izinin yin aiki a Assabbaci.” Kalaman Yesu sun nuna cewa, Yesu ya yi hidimarsa a cikin rana ta bakwai na hutun Allah.a

4. Yaya abin da Bulus ya faɗa ya nuna cewa Kiristoci na ƙarni na farko sun yi hidimarsu a rana ta bakwai?

4 Manzo Bulus ya ba da dalili na biyu. Manzo Bulus ya rubuta game da hutun Allah a cikin wasiƙarsa ga Ibraniyawa. A sura ta 4 ta wasiƙarsa, kafin ya maimaita kalaman da ke Farawa 2:2, Bulus ya rubuta: ‘Mu da muka ba da gaskiya muna shiga cikin wannan hutu.’ (Ibran. 4:3, 4, 6, 9) Hakan ya nuna cewa Bulus ya yi hidimarsa a rana ta bakwai ɗin. Yaushe ne ƙarshen rana ta bakwai?

5. Mene ne Jehobah ya zaɓi ya cim ma a rana ta bakwai? Yaushe ne Allah zai cika nufinsa?

5 Domin mu amsa wannan tambayar, wajibi ne mu tuna cewa Jehobah ya zaɓi rana ta bakwai don dalili na musamman. Farawa 2:3 ya ce: ‘Allah ya albarkaci rana ta bakwai, ya tsarkake ta.’ Jehobah ya tsarkaka ranar domin ya zaɓe ta ta zama ranar da ya kammala nufinsa ga duniya. Nufinsa shi ne mutane masu aminci su kasance a cikin duniya kuma su kula da ita da kuma komi da ke cikinta. (Far. 1:28) Dalilin da ya sa Allah da Yesu Kristi, wanda shi ne “ubangijin assabbaci,” suke “aiki har yanzu” shi ne su sa nufin Allah ga duniya ya cika. (Mat. 12:8) Saboda haka, ranar hutu na Allah za ta ci gaba har nufinsa ya cika. Hakan zai faru a ƙarshen shekara dubu da Yesu zai yi sarauta.

Kada Ka “Faɗi Bisa Wannan Misalin Kangara”

6. Wane misali ne zai iya zama gargaɗi a gare mu, kuma wane darasi ne za mu iya koya daga waɗannan misalan?

6 Allah ya bayyana wa Adamu da Hauwa’u nufinsa dalla-dalla, amma sun saɓa wa nufin. Miliyoyin mutane ma sun bi misalin rashin biyayya na Adamu da Hauwa’u. Har Isra’ilawa ma da Allah ya zaɓa, sun yi masa rashin biyayya sau da yawa. Kuma Bulus ya yi wa Kiristoci na zamaninsa gargaɗi cewa wasu cikinsu za su iya yin rashin biyayya kamar Isra’ilawa. Ya rubuta: “Mu yi anniya fa mu shiga cikin wannan hutu, kada kowanne mutum ya fāɗi bisa wannan misalin kangara.” (Ibran. 4:11) Abin da Bulus ya ce ya nuna cewa masu rashin biyayya ba za su iya shiga hutun Allah ba. Mene ne hakan yake nufi a gare mu? Shin hakan yana nufi ne cewa idan muka yi abin da ya saɓa wa nufin Allah, ba za mu shiga hutunsa ba? Yana da muhimmanci sosai mu san amsar wannan tambayar, kuma za mu tattauna wannan sosai a cikin wannan talifin. Amma da farko za mu yi magana game da misali marasa kyau na Isra’ilawa da kuma dalilin da ya sa ba su shiga hutun Allah ba.

“Ba Za Su Shiga Cikin Hutuna Ba”

7. Mene ne nufin Allah ga Isra’ilawa sa’ad da ya cece su daga ƙasar Masar? Mene ne Isra’ilawa suke bukatar yi?

7 Jehobah ya gaya wa bawansa Musa nufinsa ga Isra’ilawa a shekara ta 1513 K.Z. Allah ya ce: “Na kuwa sauko domin in cece su daga hannun Masarawa, in fishe su daga wacan ƙasa, in kai su cikin ƙasa mai-kyau mai-faɗi, ƙasa mai-zubar da madara da zuma.” (Fit. 3:8) Jehobah ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar don ya mai da su mutanensa, kamar yadda ya yi wa Ibrahim alkawari. (Far. 22:17) Allah ya ba Isra’ilawa dokokin da za su iya taimaka musu su kasance da salama da Allah kuma su zama abokansa. (Isha. 48:17, 18) Ya gaya wa Isra’ilawa: ‘Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina [kamar yadda aka tsara a cikin Doka da Aka Ba da ta Hannun Musa] kuma, sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gare ni daga cikin dukan al’umman duniya; gama dukan duniya tawa ce.’ (Fit. 19:5, 6) Saboda haka, abin da zai iya sa Isra’ilawa su zama mutanen Allah shi ne yin biyayya ga dokokin Allah kaɗai.

8. Waɗanne zarafi ne Isra’ilawa za su kasance da shi idan sun yi biyayya ga Allah?

8 Ka yi tunanin zarafin da Isra’ilawa suke da shi! Jehobah ya yi musu alkawari cewa idan sun yi masa biyayya, zai albarkaci gonakinsu da garkar anab ɗinsu da kuma dabbobinsu. Ya kuma yi musu alkawari cewa zai kāre su daga maƙiyansu. (Karanta 1 Sarakuna 10:23-27.) Ba su kasance ƙarƙashin sarautar wasu al’ummai ba, har a zamanin Yesu sa’ad da Romawa suke sarautar al’ummai da yawa. Jehobah yana son al’ummar Isra’ila ta kasance misali mai kyau ga sauran al’ummai. Ya so kowa ya fahimci sarai cewa dukan waɗanda suka yi biyayya ga Allah na gaskiya za su samu albarkarsa.

9, 10. (a) Me ya sa bai dace ba da Isra’ilawa suka so su koma ƙasar Masar? (b) Shin Isra’ilawa za su iya bauta wa Jehobah yadda yake so idan suka koma ƙasar Masar?

9 Isra’ilawa suna da zarafi na musamman na ƙyale Jehobah ya yi amfani da su don cika nufinsa. Suna iya samun albarkar Jehobah kuma hakan ya sa dukan iyalan duniya su albarkaci kansu. (Far. 22:18) Amma yawancin Isra’ilawa ba su ɗauki zarafi na zama al’ummar Allah da kuma zama misali ga wasu al’ummai da muhimmanci ba. Sun ma ce suna son su koma ƙasar Masar! (Karanta Littafin Lissafi 14:2-4.) Amma idan sun koma ƙasar Masar, ba za su iya bauta wa Jehobah yadda yake son su yi ba kuma su zama misali ga wasu al’ummai. Idan sun sake zama bayi a ƙasar Masar, ba za su samu zarafin yin biyayya ga Dokar Allah a sake ba kuma ba za a gafarta zunubansu ba. Sun nuna son kai sa’ad da suka ce suna son su koma ƙasar Masar. Ba su yi tunanin Allah da kuma nufinsa ba. Shi ya sa Jehobah ya ce game da su: “Raina ya ɓaci da wannan tsara, na ce, Tuttur suna kuskure a zuciyarsu: Amma ba su san tafarkuna ba; kamar yadda na yi rantsuwa cikin fushina, Ba za su shiga cikin hutuna ba.”—Ibran. 3:10, 11; Zab. 95:10, 11.

10 Muradinsu na son su koma ƙasar Masar ya nuna cewa ba su daraja albarkar da suka samu daga wurin Jehobah ba. Maimakon haka, waɗannan Isra’ilawa marasa biyayya sun yi marmarin abinci mai kyau da ke ƙasar Masar. (Lit. Lis. 11:5) Suna kamar Isuwa da bai daraja gatarsa a matsayin ɗa na fari ba amma ya sayar da gatar a kan abinci.—Far. 25:30-32; Ibran. 12:16.

11. Isra’ilawa da suka fita daga ƙasar Masar ba su yi imani ba. Shin hakan ya canja nufin Jehobah?

11 Ko da yake waɗannan Isra’ilawa da suka bar ƙasar Masar ba su yi imani ga Jehobah ba, amma bai canja nufinsa ga Isra’ila ba. Yaransu sun fi iyayensu biyayya. Sun yi biyayya ga umurnin Jehobah na su shiga cikin Ƙasar Alkawari kuma su ci nasara bisa ƙasar. Joshua 24:31 ya ce: “Isra’ila kuwa suka bauta ma Ubangiji dukan kwanakin Joshua, da kwanakin dattiɓan da suka wanzu bayan Joshua, waɗanda suka san ayyuka duka na Ubangiji da ya aika domin Isra’ila.”

12. Ta yaya muka sani cewa Kiristoci a yau za su iya shiga hutun Allah?

12 Amma waɗannan Isra’ilawa marasa biyayya sun tsufa kuma sun mutu. Isra’ilawa da suka kasance bayan zamanin su “ba su san Ubangiji ba, ko aikin da ya aika domin Isra’ila” ba. Sai suka soma yin “mugunta a idanun Ubangiji” kuma suka bauta wa allolin ƙarya. (Alƙa. 2:10, 11) Rashin biyayyarsu ya sa ba su sake kasance da salama da Allah kuma ba. Saboda haka, Ƙasar Alkawari ba ta kasance musu wurin “hutu” ba. Bulus ya rubuta game da waɗannan Isra’ilawa: “Da Yashu’a ya ba su hutu, da [Allah] ba ya anbata wata rana daga baya ba.” Sai ya ce: “Akwai fa hutun assabbat ajiyayye domin jama’ar Allah.” (Ibran. 4:8, 9) “Jama’ar Allah” da Bulus ya yi maganarsu Kiristoci ne. Sun haɗa da waɗanda suka yi biyayya ga Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa kafin su zama Kiristoci da kuma waɗanda ba su taɓa yin biyayya ga Dokar ba. Abin da Bulus ya ce yana nufin cewa Kiristoci a yau za su iya shiga cikin hutun Allah.

Wasu Sun Kasa Shiga Cikin Hutun Allah

13, 14. (a) Mene ne Isra’ilawa suke bukatar su yi a zamanin Musa don su shiga hutun Allah? (b) Mene ne Kiristoci suke bukatar su yi don su shiga hutun Allah a zamanin Bulus?

13 Bulus ya rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa domin wasu cikinsu ba su aikata daidai da nufin Allah ba. (Karanta Ibraniyawa 4:1.) Mene ne suke kan yi? Suna biyayya ga wasu abubuwa da ke cikin Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa. Gaskiya ne cewa an bukaci jama’ar Allah su yi biyayya ga Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa don su faranta wa Allah rai kusan shekara 1,500 da suka shige. Amma bayan Yesu ya mutu ba sa bukatar Dokar da Aka Ba da ta Hannu Musa kuma. Wasu Kiristoci ba su fahimci hakan ba, kuma shi ya sa suke tunani cewa suna bukatar su yi biyayya ga wasu sashen Dokar.b

14 Bulus ya bayyana wa waɗannan Kiristoci Yahudawa cewa Yesu ya fi kowanne babban firist ajizi daraja. Ya nuna cewa sabon alkawari ya fi alkawari da aka yi da Isra’ilawa daraja. Ya kuma nuna cewa babbar haikali na Jehobah ya fi haikalin da aka yi da “hannuwa” ‘girma da kamalta.’ (Ibran. 7:26-28; 8:7-10; 9:11, 12) Bulus ya yi amfani da misalin Assabbaci na Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa don ya bayyana yadda Kiristoci za su iya shiga ranar hutu na Jehobah. Ya ce: “Akwai fa hutun assabbat ajiyayye domin jama’ar Allah. Gama wanda ya shiga cikin hutunsa shi da kansa ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah ya yi daga nasa.” (Ibran. 4:8-10) Waɗannan Yahudawa Kiristoci suna bukatar su daina tunani cewa mutum zai iya samun amincewar Allah domin “ayyukansa,” wato, domin ya yi biyayya ga Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa. Tun ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., Jehobah yana amincewa da waɗanda suke imani ga Yesu Kristi.

15. Ta yaya muka san cewa muna bukatar mu yi biyayya ga Jehobah domin mu shiga hutunsa?

15 Me ya sa Isra’ilawa na zamanin Musa ba su shiga Ƙasar Alkawari ba? Domin ba su yi biyayya ga Jehobah ba. Me ya sa wasu Kiristoci a zamanin Bulus ba su shiga hutun Allah ba? Domin su ma ba su yi bayayya ba. Ba su amince cewa Jehobah ba ya son a bauta masa kuma ta yin biyayya ga Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ba.

Ta Yaya Za Mu Iya Shiga Hutun Allah a Yau

16, 17. (a) Ta yaya Kiristoci za su iya shiga hutun Allah a yau? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

16 Babu kowannenmu a yau da ya amince cewa Kirista yana bukatar ya yi biyayya ga Dokar da Aka Ba da Ta Hannun Musa domin ya samu ceto. Kalaman Bulus ga Afisawa suna a bayane sosai: “Bisa ga alheri an cece ku ta wurin bangaskiya; wannan kuwa ba daga gareku ba ne; kyauta ce ta Allah: ba daga ayyuka ba ne.” (Afis. 2:8, 9) Ta yaya Kirista zai iya shigan hutun Allah a yau? Ka tuna cewa Jehobah ya zaɓi ranar hutunsa ya kasance ranar da ya cika nufinsa domin duniya da kuma ’yan Adam masu biyayya. Jehobah ya gaya mana nufinsa da kuma abin da yake bukata a gare mu ta ƙungiyarsa. Za mu iya shiga hutun Allah idan muna masa biyayya da kuma ƙungiyarsa.

17 Amma idan ba mu yi biyayya ga bawan nan mai aminci mai hikima ba ko kuma muka zaɓa mu bi abin da muke ji ya fi muhimmanci, ba za mu aikata bisa nufin Jehobah ba. Kuma ba za mu iya zaman abokinsa ba, idan ayyukanmu sun saɓa wa nufin Jehobah. A talifi na gaba, za mu tattauna wasu zarafi da muke da su na nuna cewa muna biyayya. Zaɓin da muka yi a wannan batun zai nuna ko mun shiga hutun Allah.

[Hasiya]

a Firistoci da Lawiyawa sun yi aiki a cikin haikali a Assabbaci, kuma hakan bai saɓa wa Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ba. Allah ya zaɓi Yesu ya zama mana Babbar Firist. Saboda haka, ba laifi ba ne Yesu ya yi aikin da Allah ya ba shi a ranar Assabbaci ba.—Mat. 12:5, 6.

b Ba mu sani ba ko akwai kowane Kirista Bayahude wanda ya ci gaba da miƙa hadaya a Ranar Kafara, bayan ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z. ba. Amma in sun yi hakan, ba su nuna daraja ga hadayar Yesu ba. Mun san cewa wasu Kiristoci Yahudawa sun ci gaba da bin al’adun da suke cikin Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa.—Gal. 4:9-11.

Tambayoyi don Bimbini

• Mene ne Jehobah ya so ya yi a rana ta bakwai?

• Yaya muka sani cewa har yau muna cikin rana ta bakwai ɗin?

• Me ya sa wasu Isra’ilawa a zamanin Musa da kuma wasu Kiristoci a zamanin Bulus ba su shiga hutun Allah ba?

• Mene ne yake nufi mu shiga hutun Allah a yau?

[Bayanin da ke shafi na 27]

Za mu iya shiga hutun Jehobah a yau idan muka yi biyayya a gare shi da kuma ƙungiyarsa

[Hotona a shafi na 26]

Mene ne mutanen Allah suke bukata su yi don su shiga hutunsa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba