Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 10/1 pp. 26-28
  • Yadda Za Ka Daraja Matarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ka Daraja Matarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sa’ad da Matarka Take Son Ta Tattauna da Kai
  • Sa’ad da Kake da Abin da Za Ka Faɗa
  • Ka Amince da Bambancin da Ke Tsakaninka da Matarka
  • Ku Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Kada Ku Ci Amanar Juna
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Magance Matsaloli
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yadda Za Ku Warware Matsaloli
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 10/1 pp. 26-28

Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali

Yadda Za Ka Daraja Matarka

Willa ya ce: “Idan ran Rachel ya ɓace, sai ta daɗe tana kuka. Idan muka zauna don mu tattauna abin da ya faru, sai ta ƙara fusata ko kuma ta ƙi yin magana. Kamar dai zama tare ba za ta yiwu ba. Sai na ji kamar rabuwa ce ta fi alheri.”

Rachel ta ce: “Sa’ad da Will ya dawo gida, ya tarar da ni ina kuka. Na yi ƙoƙarin bayyana masa abin da ya sa raina ya ɓace, sai ya katse mini hanzari. Ya ce wannan batun bai taka kara ya karya ba, saboda haka, kada in ƙyale hakan ya dame ni. Sai hakan ya ƙara ɓata mini rai.”

A WASU lokatai, ka kan ji kamar yadda Will da Rachel suke ji? Suna son su tattauna da juna, amma sau da yawa sai ƙoƙarinsu ya ci tura. Me ya sa?

Yadda maza da mata suke tattaunawa ya bambanta, bukatunsu kuma sun bambanta. Mace za ta so ta riƙa faɗin yadda take ji a fili kuma tana nanatawa. A wani ɓangare kuma, mazaje da yawa suna son zaman lafiya ta wajen magance matsaloli da wuri da kuma guje wa batutuwa da za su jawo matsaloli. Ta yaya za ku iya magance waɗannan bambancin kuma ku tattauna da mijinku ko kuma matarku? Za ku yi hakan ne ta wurin daraja abokin zaman aurenku.b

Mutumin da ke daraja wasu ya san kima kuma yana ƙoƙarin ya fahimci yadda mutane suke ji. Tun yaranta, mai yiwuwa ka koyi ka daraja mutanen da suka fi ka iko ko waɗanda suka girme ka. Amma, a aure, ƙalubalen shi ne daraja wanda kake ganin daidai kuke, wato, matarka. “Na san cewa Phil zai saurara cikin haƙuri da sanin yakamata idan wani can yana tattaunawa da shi,” in ji Linda, wadda ta yi shekara takwas da yin aure. “Ni ma ina so ya riƙa sauraro na kamar haka.” Mai yiwuwa, kana saurarawa sosai kuma kana nuna daraja sa’ad da abokai da kuma waɗanda ba ka sani ba suke magana. Amma, kana yin hakan ga matarka?

Cin mutunci yana jawo matsala a cikin gida kuma hakan yana haifar da rigima. Wani sarki mai hikima ya ce: “Gwamma loma gāya tare da kwanciyar rai, da gida cike da buki game da husuma.” (Misalai 17:1) Saboda a sami zaman lafiya, Littafi Mai Tsarki ya gaya wa maigida ya daraja ko kuma ya girmama matarsa. (1 Bitrus 3:7) Ita “matar kuwa ta ladabta wa mijinta.”—Afisawa 5:33, Littafi Mai Tsarki.

Ta yaya za ka tattauna da matarka cikin daraja? Ga wasu shawarwari masu amfani da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Sa’ad da Matarka Take Son Ta Tattauna da Kai

Ƙalubale: Mutane da yawa sun fi son su yi magana fiye da yadda suke sauraro. Kana ɗaya daga cikinsu ne? Littafi Mai Tsarki ya kira ‘wanda ya mayar da magana tun bai ji ba’ wawa. (Misalai 18:13) Saboda haka, kafin ka yi magana, ka saurara. Me ya sa? “Na fi so kada maigidana ya yi ƙoƙarin warware matsalolina nan da nan,” in ji Kara, wadda ta yi shekara 26 da yin aure. “Ba ya bukatar ya amince ko kuma ya bincika dalilin da ya jawo matsalar. Abin da kawai nake so shi ne ya saurare ni kuma ya amince cewa haka batun yake.”

A wani ɓangare kuma, wasu maza da mata suna jinkirin faɗin abin da ke zuciyarsu kuma ba sa jin daɗi idan abokin aurensu ya matsa musu su faɗi abin da ke damun su. Lorrie, wadda ba ta daɗe da yin aure ba, ta fahimci cewa maigidanta ba ya saurin faɗin abin da ke damun sa. Ta ce: “Dole ne in yi haƙuri har sai ya faɗi abin da ke zuciyarsa.”

Yadda Za a Warware Matsalar: Idan kai da matarka kuna bukatar ku tattauna wani batu da zai iya jawo rashin jituwa a tsakaninku, ka ta da batun sa’ad da kuke cikin natsuwa. Idan matarka tana nawar faɗi abin da ke zuciyarta fa? Ka tuna cewa “tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi.” (Misalai 20:5, LMT) Idan ka jawo ruwa da guga daga cikin rijiya da gaggawa, ruwan zai zuba sosai. Hakazalika, idan ka tilasta wa matarka ta gaya maka abin da ke zuciyarta, mai yiwuwa ba za ta so ta ba ka haɗin kai ba kuma hakan zai sa ka rasa damar sanin abin da ke zuciyarta. A maimakon haka, ka yi tambayoyi a hankali da daraja, kuma ka kasance da haƙuri idan matarka ba ta bayyana ra’ayinta da wuri kamar yadda kake so ba.

Sa’ad da matarka take magana, ‘ka yi hanzarin ji, ka yi jinkirin yin magana, ka yi jinkirin yin fushi.’ (Yaƙub 1:19) Mai saurarawa sosai yana mai da hankali sosai ga abin da ake cewa da kuma dalilin da ya jawo hakan. Sa’ad da matarka take magana, ka ƙoƙarta sosai ka fahimci yadda take ji. Matarka za ta gane ko tana da kima a gabanka ko a’a, ta yadda kake sauraronta.

Yesu ya koya mana yadda ake sauraro. Alal misali, sa’ad da wani marar lafiya ya zo wurinsa yana neman taimako, Yesu bai warware matsalarsa nan take ba. Da farko, ya saurari roƙon da mutumin ya yi. Sa’an nan ya ƙyale abin da ya ji ya motsa shi sosai. A ƙarshe, ya warkar da mutumin. (Markus 1:40-42) Sa’ad da matarka take magana, ka bi wannan gurbin. Ka tuna cewa tana son ka nuna tausayi ne, ba warware matsalar nan take ba. Saboda haka, ka kasa kunne sosai. Ka bari abin da ka ji ya motsa ka. Bayan haka ne za ka ɗauki mataki don ka biya bukatun matarka. Idan ka yi haka, za ka nuna cewa kana daraja abokiyar aurenka.

KA GWADA WANNAN: Nan gaba, idan matarka ta soma yi maka magana, ka guji ba da amsa nan take. Ka jira har sai matarka ta gama magana kuma ka fahimci abin da ta ce. Bayan haka, ka je wajen matarka ka tambaye ta, “Mene ne kike ganin zan yi don in inganta yadda nake saurarar ki sosai?”

Sa’ad da Kake da Abin da Za Ka Faɗa

Ƙalubale: “Wasu irin wasannin ban dariya da ake nunawa a talabijin suna nuna cewa daidai ne mutum ya faɗi munanan abubuwa game da matarsa ko kuma ya zage ta ko ya yi mata gatse,” in ji Linda, wadda aka yi ƙaulinta ɗazu. Wasu sun girma ne a iyalin da aka saba yin baƙar magana. Idan irin waɗannan mutanen suka yi aure, yana yi musu wuya su guje wa nuna irin wannan halin a tasu iyalin. Ivy wadda take zaune a Kanada, ta ce: “Na girma ne a wurin da aka saba yin ashar, daka wa mutane tsawa da kuma kiran mutane da sunayen banza.”

Yadda Za a Warware Matsalar: Sa’ad da kake tattaunawa da mutane game da matarka, ka furta “irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda ake bukata, domin shi ba da alheri ga waɗanda suke ji.” (Afisawa 4:29) Ka girmama matarka sa’ad da kake magana game da ita.

Ko a lokacin da kai da matarka kaɗai kuke tare, ka guji yin baƙar magana da kuma kiran ta sunayen banza. A Isra’ila ta dā, Michal ta yi fushi da maigidanta, Sarki Dauda. Ta yi masa gatse kuma ta ce ya mai da kansa ‘kamar asharari.’ Kalmominta sun ɓata wa Dauda rai, kuma Jehobah ma bai ji daɗinsu ba. (2 Sama’ila 6:20-23) Mene ne darasin? Sa’ad da kake magana da matarka, ka mai da hankali sosai ga maganar da za ta fito daga bakinka. (Kolosiyawa 4:6) Phil, wanda ya yi shekara takwas da yin aure ya ce shi da matarsa suna samun rashin jituwa. Kuma ya lura cewa a wasu lokatai abin da ya ce yana daɗa ɓata al’amarin. “Na fahimci cewa yin jayayya don na ‘samu nasara’ a gardamar da muke yi yana ƙara ɓata al’amarin ne. Na fahimci cewa gina dangantakarmu ita ce mafi gamsarwa da amfani.”

Wata tsohuwar gwauruwa a zamanin dā ta ƙarfafa surukanta su ‘sami hutawa, kowace ɗayansu a cikin gidan mijinta.’ (Ruth 1:9) Sa’ad da mata da miji suka daraja juna, za su mai da gidansu‘wurin hutawa.’

KA GWADA WANNAN: Da kai da matarka, ku keɓe lokaci don ku tattauna shawarwarin da ke ƙarƙashin wannan ƙaramin jigon. Ka tambayi matarka: “Sa’ad da nake magana game da ke a cikin jama’a, kina ganin ina daraja ki ne ko kuma ina zubar da mutuncinki? Waɗanne gyare-gyare ne kike ganin nake bukatar in yi?” Ku saurari juna sosai sa’ad da kowannenku yake bayyana yadda yake ji. Ku yi amfani da shawarwarin da kuka ji.

Ka Amince da Bambancin da Ke Tsakaninka da Matarka

Ƙalubale: Wasu sababbin ma’aurata suna kammalawa cikin rashin sani cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya kira zama “nama ɗaya” yana nufin cewa dole ne ma’aurata su kasance da ra’ayi ko hali iri ɗaya. (Matta 19:5) Amma, nan da nan sai su fahimci cewa irin wannan tunanin wasiƙar jaki ce. Da zarar sun yi aure, bambancin da suke da shi yana jawo jayayya. Linda ta ce “Wani babban bambancin da ke tsakani na da Phil shi ne, ba ya yawan damuwa kamar ni. A wasu lokatai, yana iya kwantar da hankalinsa sa’ad da nake damuwa, kuma hakan yana ɓata mini rai domin ina ganin bai damu da abin da ke damuna ba.”

Yadda Za a Warware Matsalar: Ku amince da bambancin da ke tsakaninku kuma ka daraja matarka. Alal misali: Aikin da idanunka suke yi ya bambanta da na kunnuwanka; duk da haka, suna aiki ne tare domin ka ƙetare hanya lami-lafiya. Adrienne, wadda ta yi shekaru kusan talatin da yin aure, ta ce: “Muddin ra’ayinmu bai saɓa wa Kalmar Allah ba, ni da maigidana muna ba juna zarafin kasancewa da ra’ayin da ya bambanta. Balle ma, mun auri juna ne, ba wai mun fito daga ciki a haɗe ba.”

Idan matarka tana da ra’ayin da ya bambanta da naka, kada ka mai da hankali ga naka ra’ayin kawai. Ka yi la’akari da yadda matarka take ji. (Filibiyawa 2:4) Kyle, maigidan Adrienne, ya ce: “Ba a kowane lokaci ba ne nake fahimtar ko kuma amincewa da ra’ayin matata. Amma ina tuna wa kaina cewa ina ƙaunar ta fiye da ra’ayina. Idan tana farin ciki, ni ma zan yi farin ciki.”

KA GWADA WANNAN: Ka lissafa hanyoyin da ra’ayin matarka ko kuma yadda take bi da al’amura suka fi naka. (Filibiyawa 2:3)

Ban girma tana ɗaya daga cikin abubuwan da suke sa aure ya kasance da farin ciki kuma ya dawwama. “Ban girma tana kawo wadar zuci da kuma kwanciyar rai a aure,” in ji Linda, wadda aka yi ƙaulinta ɗazu. “Hakika, yana da kyau a koyi wannan halin.”

[Hasiya]

a An canja sunaye.

b Wannan talifin ya shafi mata da miji.

KA TAMBAYI KANKA . . .

▪ A wace hanya ce bambancin hali na matata ya inganta iyalinmu?

▪ Me ya sa yake da kyau in bi ra’ayin matata idan hakan ba zai saɓa wa mizanan Littafi Mai Tsarki ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba