Ku Biɗi Salama
“Mu bi waɗannan abu fa da ke nufa wajen salama.”—ROM. 14:19.
1, 2. Me ya sa akwai salama tsakanin Shaidun Jehobah?
A YAU babu salama ta gaske tsakanin mutanen duniya. Mutane daga ƙasa da kuma suke yare iri ɗaya ba sa yawan kasancewa da haɗin kai. Addini da siyasa da kuɗi da ilimi sun raba su. Akasin mutanen duniya, Shaidun Jehobah suna kasancewa tare cikin haɗin kai, ko da yake sun fito ne daga “cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna.”—R. Yoh. 7:9.
2 Da akwai dalilai masu kyau da ya sa muke kasancewa cikin salama da juna. Ainihin dalilin shi ne domin muna “kasance da salama wurin Allah.” Muna kasancewa da wannan salama don mun ba da gaskiya ga Ɗansa, wanda ya ba da ransa a gare mu. (Rom. 5:1; Afis. 1:7) Jehobah yana kuma ba bayinsa masu aminci ruhu mai tsarki kuma ’yar ruhun ta ƙunshi salama. (Gal. 5:22) Dalili na biyu da ya sa muke kasancewa da salama da kuma haɗin kai shi ne don mu “ba na duniya ba ne.” (Yoh. 15:19) Hakan yana nufin cewa ba ma saka hannu a siyasa da kuma yaƙi. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa, mutanen Jehobah sun “bubbuge takubansu su zama garmuna.”—Isha. 2:4.
3. Wane zarafi ne salamar da muke da ita take kawowa, kuma mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 Ko da yake dukan mu a cikin ikilisiya mun fito daga wurare da kuma al’adu dabam-dabam kuma yadda muke tunani ba iri ɗaya ba ne, amma muna “ƙaunar juna.” (Yoh. 15:17) Salamarmu ta sa muna ‘aika nagarta zuwa ga dukan mutane, musamman ga waɗanda su ke cikin iyalin imani.’ (Gal. 6:10) Wannan salamar tsakanin Jehobah da ’yan’uwanmu tana da tamani sosai. Muna bukatar mu kāre ta. Bari mu tattauna yadda za mu iya kasancewa da salama a cikin ikilisiya.
Sa’ad da Muka Yi “Tuntuɓe”
4. Mene ne za mu yi don mu biɗi salama sa’ad da muka wa wani laifi?
4 Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Dukanmu mu kan yi tuntuɓe. Idan wani ba ya yi tuntuɓe ga wajen magana ba, wannan cikakken mutum ne.” (Yaƙ. 3:2) Wannan ya nuna cewa akwai lokacin da mutane biyu a cikin ikilisiya za su samu saɓani ko kuma za su samu wasu matsaloli. (Filib. 4:2, 3) Amma idan sun samu matsala, ya kamata su daidaita matsalar don salama ta kasance cikin ikilisiya. Alal misali, karanta abin da Yesu ya ce mu yi idan muna ji cewa mun yi wa wani laifi.—Karanta Matta 5:23, 24.
5. Mene ne za mu yi don mu biɗi salama sa’ad da wani ya yi mana laifi?
5 Idan wani ya yi mana laifi kuma fa? Shin ya dace mu sa rai cewa ya kamata wanda ya yi mana laifi ya zo ya ba mu haƙuri? 1 Korintiyawa 13:5 ya ce: “[Ƙauna] ba ta yin nukura.” Sa’ad da wani ya yi mana laifi, muna nuna cewa muna son salama ta kasance ta wajen gafarta wa mutumin kuma mu manta da abin da ya faru. (Karanta Kolosiyawa 3:13.) Wannan shi ne abu mafi kyau da ya kamata mu yi sa’ad da akwai ɗan matsala. Hakan yana taimaka mana mu kasance da haɗin kai da ’yan’uwanmu. Kuma muna farin ciki domin mun yi abin da ya dace. Wani karin magana mai ɗauke da hikima ya ce: “Daraja ne kuwa a . . . ƙyale laifi.”—Mis. 19:11.
6. Me ya kamata mu yi sa’ad da wani ya yi mana laifin da ya yi mana wuyar gafartawa?
6 Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da muka ga cewa laifin da aka yi mana yana da wuyar gafartawa? Ba abin hikima ba ne mu faɗa wa wani. Irin wannan gulman yana jawo matsala cikin ikilisiya. Mene ne za mu iya yi don yin maganin matsalar? Matta 18:15 ya ce: “Idan ɗan’uwanka ya yi maka zunubi, ka tafi, ka nuna masa laifinsa tsakaninka da shi kaɗai: idan ya ji ka, ka ribato ɗan’uwanka.” Ko da yake littafin Matta 18:15-17 yana magana ne game da laifi mai tsanani, amma za mu iya yin amfani da ƙa’idar da ke aya ta 15 a wasu yanayi. Saboda haka, sa’ad da muke da matsala da wani, yana da kyau mu faɗa masa laifinsa shi kaɗai. Ya kamata mu yi magana da ɗan’uwanmu cikin fara’a kuma mu yi ƙoƙarin sa salama ta kasance tsakaninmu kuma.a
7. Me ya sa ya kamata mu yi hanzarin shirya matsaloli?
7 Manzo Bulus ya rubuta: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.” (Afis. 4:26, 27) Kuma Yesu ya ce: “Ka shirya da abokin husumanka da sauri.” (Mat. 5:25) Saboda haka, muna bukatar mu shirya matsalolin da suka taso da wani da sauri don salama ta kasance. Idan ba mu yi hakan ba, matsalar za ta daɗa ƙaruwa da kuma tsanani, kamar yadda ƙaramin rauni zai iya daɗa girma idan ba mu sa magani ba. Kada mu ƙyale fahariya da kishi ko son kuɗi su hana mu daidaita matsalar da ta taso tsakaninmu da ’yan’uwanmu.—Yaƙ. 4:1-6.
Sa’ad da Matsala ta Shafi Mutane da Yawa
8, 9. (a) Wane irin musu ne ya taso a ikilisiyar Roma? (b) Kuma yaya Bulus ya daidaita Kiristocin da ke Roma?
8 Wasu matsaloli suna iya shafar mutane da yawa a cikin ikilisiya. Hakan ya faru wa wasu Kiristoci a ƙasar Roma. Akwai musun da ya taso tsakanin Kiristoci Yahudawa da na ’Yan Al’umma. Wasu suna da raunannen lamiri. Ko da yake Nassi bai haramta abubuwa da yawa ba, amma lamirinsu bai ƙyale su su yi waɗannan abubuwan ba. Amma wasu a cikin ikilisiyar ba su da raunannen lamiri. Sun yi zato cewa sun fi waɗanda suke da raunannen lamiri. Sai waɗanda suke da raunannen lamiri suka soma kushe waɗanda lamirinsu bai raunana ba. Amma dukan waɗannan musu a kan batun da zaɓin kai ne. Mene ne Bulus ya gaya wa ikilisiyar?—Rom. 14:1-6.
9 Bulus ya yi wa waɗannan Kiristocin gyara. Ya gaya wa waɗanda lamirinsu bai raunana ba cewa kada su yi tunani cewa sun fi waɗanda lamirinsu ya raunana daraja. (Rom. 14:2, 10) Irin wannan tunanin zai iya sa masu bi da lamirinsu ya raunana sanyin gwiwa kuma su daina abuta da Jehobah. Bulus ya daɗa cewa: “Sabili da nama kada a rushe aikin Allah.” Ya kuma ce: “Ya yi kyau kada a ci nama, kada a kuwa sha ruwan anab, kada a yi kome wanda ɗan’uwanka za ya yi tuntuɓe da shi.” (Rom. 14:14, 15, 20, 21) Bulus ya gaya wa waɗanda lamirinsu ya raunana cewa kada su kushe waɗanda ba su da irin ra’ayinsu. (Rom. 14:13) Ya gaya musu: Ina “fāɗa wa kowane mutum wanda ke cikinku, kada shi aza kansa gaba da inda ya kamata.” (Rom. 12:3) Bayan ya yi wa waɗannan Kiristocin gyara sai ya ce: “Mu bi waɗannan abu fa da ke nufa wajen salama, da abubuwa waɗanda za mu gina junanmu da su.”—Rom. 14:19.
10. Kamar yadda ya faru da Kiristoci a Roma, me ya kamata waɗanda suke gardama su yi?
10 Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa ikilisiyar Roma ta amince da abin da Bulus ya gaya musu kuma sun yi gyare-gyaren da suke bukata. A yau za mu iya daidaita matsalar da ta taso tsakaninmu da ’yan’uwanmu a cikin ƙauna idan mun yi abin da Littafi Mai Tsarki ya gaya mana. Kamar yadda ya faru a ikilisiyar Roma, idan matsala ta taso a ikilisiya a yau, dukan waɗanda batun ya shafa suna bukatar su yi gyare-gyare don su “zauna lafiya kuma da junan[su].”—Mar. 9:50.
Yadda Dattawa Za Su Taimaka
11. Mene ne ya kamata dattijo ya lura da shi idan wani Kirista yana son ya yi masa magana game da matsalar da ya samu da wani ɗan’uwa?
11 Idan Kirista yana son ya tattauna da dattijo game da matsalar da taso tsakanin shi da wani cikin iyalinsa ko kuma wani mai shela kuma fa? Misalai 21:13 ya ce: “Wanda ya toshe kunnuwansa ga jin kukan talaka, shi kuma za ya yi kuka, ba kuwa za a ji shi ba.” Dattijo ba zai “toshe kunnuwansa” ba. Amma wani misali ya ce: “Wanda ya fara kawo da’awatasa shi a ke gani da gaskiya: Amma maƙwabcinsa ya kan zo ya tone shi.” (Mis. 18:17) Dattijon ya saurara sosai, amma ya mai da hankali don kada ya goyi bayan wanda ya kawo ƙarar. Bayan ya saurari batun, zai tambayi wanda ya kawo ƙarar ko ya yi wa wanda ya yi masa laifi magana. Dattijon zai kuma iya tattauna matakan da Nassosi sun bayar a kan abin da wanda aka wa laifi zai iya yi don salama ta kasance.
12. Ka ambata misalan da suka nuna haɗarin yin hanzarin yin hukunci bayan an kai ƙarar wani?
12 Misalai uku na Littafi Mai Tsarki da za mu tattauna sun nuna haɗarin ɗaukan mataki nan da nan bayan mutum ɗaya kawai ya kawo ƙara. Fotifar ya amince da sharrin da matarsa ta yi wa Yusufu cewa yana son ya yi mata fyaɗe. Fotifar ya yi fushi ba gaira ba dalili, kuma ya sa aka jefa Yusufu cikin kurkuku. (Far. 39:19, 20) Sarki Dauda ya amince da abin da Ziba ya faɗa cewa maigidansa, Mephibosheth ya goyi bayan maƙiyan Dauda. Dauda ya hanzarta ya yanki hukunci yana cewa: “Ga shi, dukan abin da ke hannun Mephibosheth naka ne.” (2 Sam. 16:4; 19:25-27) An gaya wa Sarki Artaxerxes cewa Yahudawa suna sake gina ganuwar Urushalima kuma suna son su yi tawaye da Daular Fasiya. Sarkin ya yarda da ƙaryar kuma ya ce a daina ginin a Urushalima. A sakamako, Yahudawa suka dakatar da aiki a Haikalin Allah. (Ezra 4:11-13, 23, 24) Abin hikima ne dattawa su bi umurnin Bulus ga Timotawus kuma kada su yi hukunci ba tare da sun san gaskiyar batun ba.—Karanta 1 Timotawus 5:21.
13, 14. (a) Mene ne ya kamata ’yan’uwa biyu su tuna sa’ad da suke gardama? (b) Mene ne zai taimaka wa dattawa su yanka hukunci mai kyau?
13 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan kowane mutum yana tsammani ya san kome, bai sani ba tukuna yadda ya kamata ya sani.” (1 Kor. 8:2) Za mu iya tsammani cewa mun san abin da ya faru sa’ad da mutane biyu suka yi gardama. Amma ya kamata mu tuna cewa ba mu san dukan abu ba. Kuma wataƙila ba mu san kome game da mutane biyu da suka samu saɓanin ba. Wajibi ne dattawa su mai da hankali sa’ad da suke yin shari’a a kan batun kuma kada su ƙyale a yi musu ƙarya ko kuma a yi musu jita-jita game da abin da ya faru. Kuma, bai kamata su gaskata da wani don kawai shi mai kuɗi ne. Alƙalin da Allah ya zaɓa, Yesu, ba ya yin “shari’a bisa ga abinda ya bayyana ga idanunsa ba, ba kuwa za shi yanka magana bisa ga abin da kunnensa ke ji ba.” (Isha. 11:3, 4) Ruhun Allah ne yake ja-gorar Yesu. Dole ne ruhun Allah ya ja-goranci dattawa Kiristoci.
14 Kafin dattawa su yi shari’a a kan wata matsala da ta taso, suna bukatar yin addu’a don samun ruhun Jehobah kuma su yi amfani da Kalmar Allah da kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai tsarki na bawan nan mai-aminci, mai-hikima.—Mat. 24:45.
Wajibi ne Mu Kasance da Salama da Allah
15. A wane lokaci ne ya kamata mu kai ƙarar zunubi mai tsanani da wani ya yi?
15 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana mu yi zaman lafiya da mutane. Kuma ya ce: ‘Hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce dafari, bayan wannan mai-salama ce.’ (Yaƙ. 3:17) Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata mu fara kasancewa da tsarki. Kasancewa da tsarki yana nufin barin Allah ya gaya mana abin da yake da kyau da wanda ba shi da kyau da kuma yin rayuwa da ke faranta masa rai. Idan Kirista ya san wani ɗan’uwa da ya yi zunubi mai tsanani, ya kamata ya ƙarfafa shi ya gaya wa dattawa game da zunubinsa. (1 Kor. 6:9, 10; Yaƙ. 5:14-16) Idan wanda ya yi zunubin bai yi hakan ba, Kiristan da ya san game da zunubin sai ya gaya wa dattawa. Ƙin yin hakan don a kasance da salama da mai zunubin zai sa mutum ya goyi bayan zunubi.—Lev. 5:1; karanta Misalai 29:24.
16. Mene ne za mu iya koya daga abin da ya faru tsakanin Jehu da Sarki Jehoram?
16 Akwai wani abu da Jehu ya yi da ya nuna cewa yin abin da ya dace ya fi kasancewa da salama da wanda ya yi zunubi. Allah ya aiki Jehu ya hukunta iyalin Sarkin Ahab. Mugun Sarki Jehoram ne ɗan Ahab da kuma Jezebel. Ya shiga karusarsa zuwa wurin Jehu kuma ya yi tambaya: “Lafiya, Jehu?” Sai Jehu ya amsa ya ce: “Ina fa lafiya, muddar karuwancin uwarka Jezebel da maitatta suna da yawa haka?” (2 Sar. 9:22) Da hakan, sai Jehu ya zaro bakar sa kuma ya harɓe Jehoram a zuciya. Ya kamata dattawa su yi koyi da yadda Jehu ya aikata kuma kada su amince da waɗanda suke zunubi da gangan kuma ba su tuba ba da sunan suna son salama ta kasance. Suna yi wa masu zunubi da ba su tuba ba yankan zumunci don ikilisiyar ta ci gaba da more salama da Allah.—1 Kor. 5:1, 2, 11-13.
17. Mene ne dukan Kiristoci suke bukata su yi don salama ta kasance?
17 Ba a bukatar yin shari’a a yawancin matsaloli da ba masu tsanani ba ne da suke tasowa tsakanin ’yan’uwa. Abu mai kyau ne mu yafe kurakuren ’yan’uwanmu cikin ƙauna. Kalmar Allah ta ce: “Wanda ya rufe laifi, ƙauna ya ke biɗa: amma wanda ya yi gori yana raba abokan gaske.” (Mis. 17:9) Bin waɗannan kalaman za su taimaka mana mu sa salama ta kasance a cikin ikilisiya kuma mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah.—Mat. 6:14, 15.
Ana Samun Albarka don Kasancewa da Salama
18, 19. Waɗanne albarka ne ake samu don biɗan salama?
18 Jehobah yana mana albarka sa’ad da muka yi ƙoƙari don salama ta kasance. Muna da dangantaka mai ƙarfi da Jehobah kuma muna da hakki na sa haɗin kai ya kasance a cikin ikilisiya. Sa’ad da muke kasancewa da salama cikin ikilisiya, muna kuma koya yadda ya kamata mu kasance da salama da waɗanda muke wa wa’azin “bishara ta salama.” (Afis. 6:15) Muna a shirye mu “yi nasiha ga duka” kuma mu zama masu “hanƙuri.”—2 Tim. 2:24.
19 Ka kuma tuna cewa za a yi “tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (A. M. 24:15) Hakan yana nufin cewa Jehobah zai ta da miliyoyin mutane iri-iri daga matattu. Za su tashi daga wurare dabam-dabam na duniya da kuma a lokaci dabam-dabam, har waɗanda suka mutu tun farkon wanzuwar ’yan Adam a duniya! (Luk 11:50, 51) Zai kasance mana babban gata mu koyar da waɗanda suka tashi daga matattu su yi ƙaunar salama. Abin da muka koya yanzu zai taimaka mana sosai a lokacin!
[Hasiya]
a Don samun ja-gorar Littafi Mai Tsarki game da yadda za a bi da zunubai masu tsanani kamar tsegumi da zamba, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1999, shafuffuka na 15-20.
Mene ne Ka Koya?
• Ta yaya za mu biɗi salama idan mun yi wa wani laifi?
• Me ya kamata mu yi don mu biɗi salama sa’ad da aka yi mana laifi?
• Mene ne ya kamata mu tuna, idan mutane biyu suka yi gardama?
• Me ya sa ya fi muhimmanci mu yi abin da ya dace fiye da kasancewa da salama da wanda yake yin zunubi?
[Hotona a shafi na 29]
Jehobah yana ƙaunar waɗanda suke gafarta wa mutane a sake