Ka Koya Daga Kalmar Allah
Ta Yaya Za Ka Kusaci Allah?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Allah yana jin dukan addu’o’i ne?
Jehobah yana gayyatar mutane daga dukan al’ummai su kusace shi ta hanyar addu’a. (Zabura 65:2) Amma ba dukan addu’o’i ba ce yake ji ba. Alal misali, sa’ad da Isra’ilawa suka nace wajen aikata mugunta, Allah ya ƙi jin addu’o’insu. (Ishaya 1:15) Kuma ba zai ji addu’o’in wanda yake wulaƙanta matarsa ba. (1 Bitrus 3:7) Amma, Allah zai ji addu’ar masu zunubi idan suka tuba.—Karanta 2 Labarbaru 33:9-13.
2. Ta yaya za mu yi addu’a?
Addu’a gata ce kuma sashe ce ta bautarmu, saboda haka, za mu yi addu’a ne kaɗai ga Jehobah. (Matta 4:10; 6:9) Tun da yake mu ajizai ne, za mu yi addu’a ne a cikin sunan Yesu domin shi ne aka naɗa a matsayin “hanya.” (Yohanna 14:6) Jehobah ba ya so mu maimaita addu’o’in da aka haddace ko waɗanda aka rubuta, amma yana so mu yi addu’a ne daga zuciyarmu.—Karanta Matta 6:7; Filibiyawa 4:6, 7.
Mahaliccinmu yana jin addu’o’in da aka yi a zuciya. (1 Sama’ila 1:12, 13) Ya gaya mana mu yi addu’a a kowane lokaci, alal misali, a somawa da kuma ƙarshen rana da lokacin cin abinci da kuma sa’ad da muke fuskantar matsaloli.—Karanta Zabura 55:22; Matta 15:36.
3. Me ya sa Kiristoci suke taro?
Kasancewa kusa da Allah ba shi da sauƙi domin muna zaune ne a tsakanin mutanen da ba su yi imani da Allah ba kuma suna ba’a ga alkawarinsa na kawo salama a duniya. (2 Timotawus 3:1, 4; 2 Bitrus 3:3, 13) Saboda haka, muna bukatar mu riƙa yin tarayya mai ƙarfafawa tare da ’yan’uwa masu bi.—Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.
Za ka iya kusantar Allah idan ka yi abota da mutanen da ke ƙaunar Allah. Taron da Shaidun Jehobah suke yi za su ba ka zarafin amfana daga bangaskiyar wasu.—Karanta Romawa 1:11, 12.
4. Ta yaya za ka kusaci Allah?
Za ka iya kusantar Jehobah ta wajen yin bimbini a kan abin da ka koya daga Kalmarsa. Ka yi tunani a kan ayyukansa da ja-gorancinsa da kuma alkawuransa. Yin bimbini tare da addu’a za su sa zuciyarka ta cika da godiya saboda ƙauna da kuma hikima da Allah ya nuna.—Karanta Joshua 1:8; Zabura 1:1-3.
Za ka iya kusantar Allah idan ka dogara da shi kaɗai, wato, idan ka gaskata da shi. Amma bangaskiya tana kama da abu mai rai da ke bukatar a riƙa kula da shi kullum. Dole ne ka riƙa ƙarfafa bangaskiyarka a kai a kai ta wajen yin bimbini a kan abubuwan da ka gaskata.—Karanta 1 Tasalonikawa 5:21; Ibraniyawa 11:1, 6.
5. Ta yaya kasancewa kusa da Allah zai amfane ka?
Jehobah yana kula da waɗanda suke ƙaunar sa. Yana kāre su daga dukan wani abin da zai jefa bangaskiyarsu da kuma begensu na rai madawwami cikin haɗari. (Zabura 91:1, 2, 7-10) Ya gargaɗe mu game da hanyoyin rayuwa da za su iya yi wa lafiyar jikinmu da kuma farin cikinmu barazana. Jehobah yana koya mana hanya mafi kyau na yin rayuwa.—Karanta Zabura 73:27, 28; Yaƙub 4:4, 8.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 17 na wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.