Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 10/15 pp. 18-22
  • Bauta Wa Jehobah Ne Yake Sa Ni Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bauta Wa Jehobah Ne Yake Sa Ni Farin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ziyarar da Ta Canja Rayuwata
  • Yadda Gwaggo Mary Ta Taimake Ni
  • Manyanta na Ruhaniya da Baftisma da kuma Hidimar Bethel
  • Wasu Tarurrukan Gunduma da Aikin Gine-Gine da Ba Zan Taɓa Mantawa Ba
  • Canji a Rayuwa
  • Ƙalubalen Tsufa
  • Abin da Misalin Maryamu Ya Koya Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ban Taba Daina Koyan Abubuwa Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 10/15 pp. 18-22

Bauta Wa Jehobah Ne Yake Sa Ni Farin Ciki

Fred Rusk ne ya ba da labarin

Sa’ad da nake ƙarami, na shaida kalaman Dauda da ke Zabura 27:10: “Gama ubana da uwata sun yashe ni. Amma Ubangiji za ya ɗauke ni.” Bari na bayyana yadda hakan ya faru.

N A YI girma a gonar audugar kakana a birnin Georgia, a Amirka, a lokacin da tattalin arziki ta taɓarɓare a shekara ta 1930 zuwa 1939. Rasuwar mahaifiya ta da ƙane na ya firgita mahaifi na sosai, har ya bar ni wajen kakana kuma ya ƙaura zuwa wani birni mai nisa inda ya samu aiki. Daga baya, ya yi ƙoƙari na zo na zauna tare da shi a wurin, amma bai yiwu ba.

’Ya’yan kakana mata ne suke kula da iyalin. Ko da yake ba shi da wani addini, amma ’ya’yansa suna son addini sosai. Tsoron dūka ne yake sa na je coci duk ranar Lahadi. Saboda haka, ba na son addini tun ina ƙarami. Amma, ina jin daɗin makaranta da kuma wasanni.

Ziyarar da Ta Canja Rayuwata

Wata rana a shekara ta 1941, sa’ad da nake ɗan shekara 15, wani mutum dattijo da matarsa sun zo gidanmu. Ya ce shi kawuna ne mai suna Talmadge Rusk. Ban taɓa samun labari game da shi ba amma na ji cewa shi da matarsa Shaidun Jehobah ne. Abin da ya bayyana cewa nufin Allah ne ’yan Adam su yi rayuwa a duniya har abada ya bambanta da abin da aka koya mana a coci. Yawancin dangi na sun yi ƙyamar abin da suka ce. Ba su sake ƙyale su su shigo cikin gidanmu ba. Amma dai, gwaggo ta mai suna Mary, wadda ta girme ni da shekara uku, ta karɓi Littafi Mai Tsarki da littattafai da ke bayyana shi.

Ba da daɗewa ba, Mary ta amince cewa ta samu gaskiyar Littafi Mai Tsarki kuma ta yi baftisma a shekara ta 1942 a matsayin Mashaidiyar Jehobah. Ta kuma fuskanci abin da Yesu ya annabta, wato: “Maƙiyan mutum za su kasance daga iyalin gidansa.” (Mat. 10:34-36) Iyali na sun tsananta mini sosai. Wata yar gwaggo Mary da take da mukami sosai a siyasa a yankin ta haɗa baki da hakimin kuma ya sa aka kama kawuna Talmadge. Sun ce yana talla ba tare da samun izini ba. Aka saka shi a kurkuku.

An rubuta a jaridar cewa hakimin, wanda shi ne kuma alƙali a shari’ar ya ce wa ma’aikatan kotun: “Littattafan da wannan mutum yake rarrabawa yana da lahani kamar guba.” Kawuna ya yi afil kuma ya yi nasara, amma ya yi kwanaki goma a cikin kurkuku.

Yadda Gwaggo Mary Ta Taimake Ni

Ƙari ga yi mini magana game da sabon imaninta, Mary ta soma wa maƙwabta wa’azi. Na raka ta zuwa wurin wani mutum da ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi da littafin nan The New World.a Matarsa ta ce mijinta bai yi barci daddare ba domin yana karanta littafin. Ko da yake ba na so na soma sha’anin addini nan da nan, amma ina sha’awar abin da nake koya sosai. Amma dai, ba koyarwar Littafi Mai Tsarki kaɗai ba ne ya sa na amince cewa Shaidu bayin Allah ne, amma yadda ake bi da su ne.

Alal misali, wata rana da muke dawowa gida daga gonar tumatiri, ni da Mary mun ga alama cewa ’yan’uwanta uku mata sun ƙona takardunta da garmahonta da ke ɗauke da saƙon Littafi Mai Tsarki. Na yi fushi sosai saboda kalaman da suka yi cewa, “Za ki yi mana godiya a nan gaba saboda abin da muka yi.”

An tilasta wa Mary ta bar gida a shekara ta 1943 domin ta ƙi ta yi watsi da sabon addinin da take bi kuma ta daina yi wa maƙwabta wa’azi. Amma a lokacin na yi farin cikin sanin cewa sunan Allah, Jehobah ne, kuma yana da ƙauna da tausayi kuma ba ya ƙona mutane a cikin wuta. Na kuma koyi cewa Jehobah yana da ƙungiya mai ƙauna, ko da yake ban halarci taro ba tukun.

Daga baya, sa’ad da nake yankan ciyayi, wata mota ta shigo wurin a hankali, kuma mazaje biyu da suke ciki suka tambaye ni ko ni ne Fred. Sa’ad da na san cewa su Shaidu ne, sai na ce, “Bari na shigo, domin mu je wani gefe mu yi magana.” Mary ta shirya su ziyarce ni. Ɗaya cikinsu Shield Toutjian, mai kula mai ziyara ne kuma ya ƙarfafa ni a daidai lokacin da nake bukatar hakan. Iyali na suka haura kaina domin na yi ƙoƙari na kāre imanin Shaidun Jehobah.

Mary ta rubuto mini wasiƙa daga Virginia, inda ta koma, kuma ta ce idan na ƙudurta na bauta wa Jehobah, zan iya zuwa na zauna tare da ita. Nan da nan, na tsai da shawarar yin hakan. A wata ranar Jumma’a da yamma a shekara ta 1943, na saka abubuwan da nake bukatar cikin akwati kuma na ɗaura shi a kan itacen da ke da ɗan nisa daga gidanmu. A ranar Asabar, na ɗauko akwatin kuma na biyo bayan gidan maƙwabta kuma daga nan na hau mota zuwa cikin gari. Sa’ad da na isa birnin Roanoke, na tarar da Mary a gidan Edna Fowlkes.

Manyanta na Ruhaniya da Baftisma da kuma Hidimar Bethel

Edna Mashaidiya ce shafaffiya mai tausayi sosai, kuma ita Lidiya ce ta zamani, wadda ta karɓi hayar babban gida inda gwaggo Mary da matar ɗan’uwan Edna da kuma ’ya’yanta biyu suke. Waɗannan ’yan matan, Gladys da Grace Gregory, sun zama masu wa’azi a ƙasashen waje daga baya. Gladys, wadda yanzu ta fi shekara 90, tana bauta wa Jehobah da aminci a reshen ƙasar Japan.

Sa’ad da nake zama a gidan Edna, ina halartar tarurruka a kai a kai kuma an koya mini yadda ake wa’azi. Samun ’yancin yin nazarin Kalmar Allah da kuma halartar tarurrukan Kirista ya sa na manyanta sosai. Na yi baftisma a ranar 14 ga Yuni, a shekara ta 1944. Mary da Gladys da Grace Gregory sun soma hidimar majagaba kuma sun soma hidima a arewancin Virginia. Sun taimaka wajen kafa sabuwar ikilisiya a Leesburg. A farkon shekara ta 1946, na soma hidimar majagaba a garin da ke kusa da nasu. A wannan shekarar, mun yi tafiya tare zuwa taron ƙasashe da ba zan taɓa mantawa ba, da aka yi a birnin Cleveland, Ohio, a ranar 4 zuwa 11 ga Agusta.

A taron ne Ɗan’uwa Nathan Knorr wanda ke ja-gora a ƙungiyar a lokacin ya bayyana cewa ana shiri a faɗaɗa Bethel da ke Brooklyn. Za a gina sabon masauki da kuma maɗaba’a. Ana bukatar ’yan’uwa maza matasa da yawa. Na tsai da shawara cewa nan ne zan so na bauta wa Jehobah. Sai na saka takarda, kuma ’yan watanni bayan hakan, a ranar 1 ga Disamba, a shekara ta 1946, na koma zama a Bethel.

Kusan shekara guda bayan hakan, mai kula da maɗaba’an, Ɗan’uwa Max Larson, ya zo wuri na a Sashen Aika Saƙonni. Ya gaya mini cewa an tura ni zuwa Sashen Kula da Hidima. A wannan sashen, na koya yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma yadda aka tsara ƙungiyar Allah, musamman sa’ad da nake aiki tare da Ɗan’uwa T. J. (Bud) Sullivan, wanda ke kula da sashen.

Mahaifi na ya kawo mini ziyara sau da yawa a Bethel. Daga baya ya soma son addini. A ziyararsa ta ƙarshe a shekara ta 1965, ya ce, “Za ka iya zuwa ka ziyarce ni, amma ba zan taɓa zuwa nan kuma ba.” Na ziyarce shi a kai a kai kafin ya rasu. Ya tabbata cewa zai je sama. Ina bege cewa Jehobah yana tunawa da shi, kuma idan haka ne, a lokacin tashin matattu zai kasance a nan duniya ba a wurin da yake zato ba kuma zai kasance cikin Aljanna har abada.

Wasu Tarurrukan Gunduma da Aikin Gine-Gine da Ba Zan Taɓa Mantawa Ba

Taron gunduma suna sa mutum ya kyautata ruhaniyarsa. Haka ma yake da taron ƙasashe da aka yi a Filin Wasan Yankee da ke Amirka a shekara ta 1950. Mutane 253,922 daga ƙasashe 123 ne suka halarci taron da aka yi a Filin Wasan Yankee da Polo a shekara ta 1958. Akwai wani abin da ya faru a taron da ba zan taɓa mantawa ba. Sa’ad da nake aiki a wani ofishi a wurin taron, Ɗan’uwa Knorr ya zo wuri na da gaggawa. Ya ce: “Fred, na manta ban zaɓa ɗan’uwan da zai ba da jawabi ga majagaban da suka hallara a majami’ar da ke kusa da wurin nan ba. Don Allah za ka iya zuwa wurin da gaggawa ka ba su jawabi mai kyau a kan wani jigo da ka yi tunaninsa a kan hanya?” Na yi addu’a sosai kafin na isa wurin.

Yayin da adadin ikilisiyoyi ya ƙaru sosai a Birnin New York a tsakanin shekara ta 1950 zuwa 1969, bai dace kuma ba a yi hayar wurare don Majami’ar Mulki ba. Saboda haka, daga shekara ta 1970 zuwa 1990, mun saya gidaje uku a birnin Manhattan da za mu riƙa taro a wurin kuma mun gyara su. Ni ne mai kula da kwamitin gini na wannan aikin kuma na samu labarai da yawa na yadda Jehobah ya albarkaci ikilisiyoyin da suka saka hannu a aikin kuma suka ba da gudummawa don kammala wannan aikin da aka ci gaba da amfani da shi don bauta ta gaskiya.

Canji a Rayuwa

Wata rana a shekara ta 1957, sa’ad da nake tafiya daga masauki na a Bethel zuwa maɗaba’a, sai aka soma ruwa. Na hangi wata kyakkyawar budurwa wadda sabuwa ce a Bethel a gaba na. Ba ta da laima, sai muka yi amfani da nawa. Ta haka ne na haɗu da Marjorie, kuma tun aurenmu a shekara ta 1960, muna yin aiki tare a hidimar Jehobah da farin ciki, a lokaci mai wuya da a lokaci mai kyau. Mun yi bikin cika shekara 50 a aurenmu a watan Satumba 2010.

Ba da daɗewa ba bayan bikin aurenmu, Ɗan’uwa Knorr ya gaya mini cewa an naɗa ni na riƙa koyarwa a Makarantar Gileyad. Wannan babban gata ne sosai! Daga shekara ta 1961 zuwa 1965, an gudanar da azuzuwa biyar da suka fi daɗewa waɗanda aka yi koyarwa ta musamman ga wasu ’yan’uwa da suke hidima a ofishin reshe a kan yadda ake gudanar da reshe. A lokacin ɗari na shekara ta 1965, aka mai da ajin wata biyar, kuma muka mai da hankali ga koyar da masu wa’azi a ƙasashen waje.

A shekara ta 1972, an tura ni daga Makarantar Gileyad zuwa Sashen Amsa Tambayoyin Masu Karatu, inda na yi aiki a matsayin mai kula. Yin bincike don amsa tambayoyi dabam dabam da kuma magance matsaloli ya taimaka mini na fahimci koyarwar Kalmar Allah sosai da kuma yin amfani da ƙa’idodin Allahnmu don taimaka wa mutane.

A shekara ta 1987, aka mai da ni wani sabon sashe wato, Sashen Masu Ba da Bayani Game da Asibitoci. Mun shirya taron ƙara wa juna sani don a koyar da dattawa da suke Kwamitin Hulɗa da Asibitoci a kan yadda za a tattauna da likitoci da alƙalai da kuma masu kula da jama’a game da imaninmu na Nassi a kan jini. Babban matsalar ita ce likitoci suna ba yaranmu ƙarin jini da izinin kotu ba na iyayen ba.

Idan aka tattauna da su game da wasu hanyoyin magani da ba su ƙunshi ƙarin jini ba, sukan amsa cewa ba su da shi ko kuma suna da tsada sosai. Abin da nake yawan amsa wa likitan da ya ce hakan shi ne, “Dakata don Allah.” Idan ya dakata, sai na ce, “Kana da magani mafi kyau da za ka yi amfani da shi ba tare da ƙarin jini ba.” Wannan yabon ya tuna masa abin da ya sani sosai, wato, yin amfani da aska sosai yana rage yawan jini da ke zuba.

Cikin shekara ashirin da ta shige, Jehobah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcen nan na koyar da waɗannan likitoci da alƙalai. Ra’ayinsu ya canja sa’ad da suka fahimci matsayinmu sosai. Sun koyi cewa bincike ya nuna cewa jinya ba tare da ƙarin jini ba ya fi kyau kuma akwai likitoci da asibitocin da za a iya kai majiyyata.

Tun shekara ta 1996, Ni da matata muna hidima a Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, New York, wanda ke da nisa mil 70 daga arewancin Brooklyn. A nan na yi hidima ta ɗan lokaci a Sashen Kula da Hidima kuma na saka hannu wajen koyar da masu hidima a ofishin reshe da kuma masu kula masu ziyara. A cikin shekara 12 da ta shige, na sake hidima a matsayin mai kula a Sashen Amsa Tambayoyin Masu Karatu, wanda aka ƙaura da shi daga Brooklyn zuwa Patterson.

Ƙalubalen Tsufa

Kula da hakki na a Bethel ya daɗa wuya sosai da yake na kusan shekara casa’in. Ina fama da ciwon daji fiye da shekara goma. Ina ji kamar Hezekiya wanda Jehobah ya daɗa masa kwanaki a rayuwarsa. (Isha. 38:5) Matata ma tana rashin lafiya, kuma muna ƙoƙari tare don jimrewa da Alzheimer, wato, ciwon mantuwa. Matata mai ƙwazo ce a hidimar Jehobah, mai ba matasa shawara kuma ta kasance mini mataimakiya da abokiya mai aminci. Ita ɗaliba da malama ce mai kyau na Littafi Mai Tsarki, kuma yaranmu na ruhaniya da yawa suna ziyarar mu a kai a kai.

Gwaggo na Mary ta rasu a watan Maris na shekara ta 2010 tana ’yar shekara 87. Ta yi nasara a matsayin mai koyar da Kalmar Allah kuma ta taimaka wa mutane su soma bauta ta gaskiya. Ta yi hidima ta cikkaken lokaci shekaru da yawa. Ina mata godiya don yadda ta taimaka mini na koyi gaskiya ta Kalmar Allah kuma na zama bawan Allah, Jehobah mai ƙauna kamar ita. An binne Mary kusa da mijinta, wanda ya taɓa hidimar mai wa’azi a ƙasashen waje a ƙasar Isra’ila. Ina da tabbaci cewa Jehobah yana tunawa da su kuma zai ta da su daga matattu.

Yayin da na yi tunani game da shekara 67 da na yi ina bauta wa Jehobah, ina godiya don albarkarsa a gare ni. Ina farin cikin yin nufin Jehobah! Da yake na dogara ga alherinsa, ina ɗokin samun rabo cikin alkawarin da Ɗansa ya yi: ‘Kowanene ya bar gidaje, ko ’yan’uwa maza, ko ’yan’uwa mata, ko uba, ko uwa, ko ’ya’ya, ko ƙasashe, sabili da sunana, za ya sami riɓi ɗari; za ya kuma gāji rai na har abada.’—Mat. 19:29.

[Hasiya]

a An wallafa a shekara ta 1942 amma an daina bugawa.

[Hoto a shafi na 19]

A gonar audugar kakana a jihar Georgia, Amirka a shekara ta 1928

[Hoto a shafi na 19]

Gwaggona Mary da Kawuna Talmadge

[Hoto a shafi na 20]

Mary da Gladys da Grace

[Hoto a shafi na 20]

Ranar da na yi baftisma a ranar 14 ga Yuni, 1944

[Hoto a shafi na 20]

A Sashen Kula da Hidima a Bethel

[Hoto a shafi na 21]

Tare da Mary a taron ƙasashe a Filin Wasan Yankee a shekara ta 1958

[Hoto a shafi na 21]

Tare da matata a ranar bikin aurenmu

[Hoto a shafi na 21]

Tare da matata a shekara ta 2008

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba