Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/1 pp. 29-31
  • Ku Gina Ruhaniya a Matsayin Mata da Miji

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Gina Ruhaniya a Matsayin Mata da Miji
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wane Irin Hali Ne Ya Kamata Kiristoci Su Kasance da Shi?
  • Me ya Sa ya Kamata Mata da Miji Su Kasance Masu Ruhaniya?
  • Za Ku Girbe Abin da Kuka Shuka
  • Magance Matsaloli
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ku Sa “Harshen Wuta . . . na Ubangiji” Ya Ci Gaba da Ci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ku Ƙarfafa Aurenku Ta Wajen Tattaunawa Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Ci Gaba da Karfafa Dangantakarka da Jehobah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/1 pp. 29-31

Abubuwan da ke Kawo Farin Ciki a Iyali

Ku Gina Ruhaniya a Matsayin Mata da Miji

Fredericka: “Lokacin da muka yi aure, na nace cewa dole ne ni da matata mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Na ƙudurta cewa sai ta ba da hankalinta ga nazarin. Amma Leanne ta kasa natsuwa. Kuma idan na yi tambayoyi, amsar da take ba da wa ita ce e ko a’a kawai. Ba ta ba da cikakkun amsoshi kamar yadda nake tunanin ya kamata ta yi sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki.”

Leanne: “Ina ’yar shekara 18 sa’ad da na auri Frederick. Muna nazarin Littafi Mai Tsarki tare a kai a kai, amma Frederick yana amfani da lokacin nazarin don ya gaya mini kurakuraina da kuma hanyoyin da nake bukatar yin gyara a matsayin matar aure. Abin ya sa ni sanyin gwiwa da baƙin ciki!”

ME KAKE tunanin cewa ita ce matsalar dangantakar da ke tsakanin Frederick da Leanne? Muradinsu yana da kyau. Suna ƙaunar Allah. Kuma sun ga cewa suna bukatar yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Amma ainihin abin da ya kamata ya haɗa kansu ba ya yin hakan. Gaskiya ne cewa suna yin nazari tare, amma ba sa gina ruhaniya a matsayin ma’aurata.

Mece ce ruhaniya? Me ya sa ya kamata ma’aurata su ƙoƙarta su gina ta? Waɗanne ƙalubale ne za su iya fuskanta, kuma ta yaya za su warware su?b

Wane Irin Hali Ne Ya Kamata Kiristoci Su Kasance da Shi?

Littafi Mai Tsarki ya kwatanta halaye iri-iri da mutane suke da shi, da kuma yadda suke ɗaukan abubuwa a rayuwa. (Yahuda 18, 19) Alal misali, marubucin Littafi Mai Tsarki, Bulus, ya nuna bambancin da ke tsakanin mutumin da ya ɗauki mizanan Allah da tamani da kuma mutumin da ke nuna son kai. Bulus ya nuna cewa waɗanda suke nuna son kai sun fi mai da hankali ga kansu fiye da wasu. Maimakon su yi rayuwar da ta jitu da mizanan Allah, suna yin abin da suka ga dama.—1 Korintiyawa 2:14; Galatiyawa 5:19, 20.

Akasin haka, waɗanda suke da ruhaniya suna ɗaukan mizanan Allah da tamani. Sun ɗauki Jehobah Allah a matsayin Aboki kuma suna ƙoƙartawa wajen yin koyi da halinsa. (Afisawa 5:1) Da haka, suna nuna ƙauna, alheri, da kuma hankali a sha’aninsu da mutane. (Fitowa 34:6) Kuma suna yin biyayya ga Allah ko da yin hakan ba shi da sauƙi. (Zabura 15:1, 4) Darren, wanda ya yi shekara 35 da yin aure kuma yana zaune a ƙasar Kanada ya ce: “A ganina, mutum mai ruhaniya yana tunanin yadda furucinsa da ayyukansa za su shafi dangantakarsa da Allah a kowane lokaci.” Matarsa, Jane, ta ce: “A ganina mace mai ruhaniya ita ce wadda take ƙoƙartawa a kowace rana domin ta nuna ’yar ruhun Allah a halinta.”—Galatiyawa 5:22, 23.

Hakika, mutum ba ya bukatar yin aure kafin ya kasance mai ruhaniya. Littafi Mai Tsarki ya ce kowane mutum yana da hakkin ya koya game da Allah kuma ya yi abin da Allah yake so.—Ayyukan Manzanni 17:26, 27.

Me ya Sa ya Kamata Mata da Miji Su Kasance Masu Ruhaniya?

Me ya sa ya kamata ma’aurata su haɗa kai don su gina ruhaniyarsu tare? Ku yi la’akari da wannan misalin: Mutane biyu suna so su noma kayan lambu a lambun da su biyun suka mallaka. Ɗaya daga cikin su yana son ya shuka iri a daidai wani lokacin shekara, shi kuma ɗayan yana ganin cewa ya kamata a shuka irin ne a wani lokaci dabam. Ɗaya yana son ya yi amfani da wani irin taki, amma ɗayan ya nace cewa shuke-shuken ba sa bukatar taki. Ɗaya yana son ya yi aiki tuƙuru a lambun a kowace rana. Amma ɗayan ya fi son ya zauna har sai amfanin ya girma ba tare da ya yi aikin kome ba. A irin wannan yanayin, ana iya samun ɗan ƙaramin amfanin gona a lambun, amma amfanin ba zai kai wanda za a samu ba da a ce mutanen nan biyu da suke da lambun sun yarda su yi abin da ya kamata kuma sun haɗa kai wajen cim ma hakan.

Mata da miji suna kama ne da waɗannan masu aikin lambun. Idan wani daga cikinsu ya gina ruhaniya, hakan zai iya kyautata dangantakarsu. (1 Bitrus 3:1, 2) Amma dangantakarsu za ta yi inganci sosai idan su biyun suka yarda su yi rayuwar da ta jitu da mizanan Allah kuma suka yi aiki tuƙuru domin su tallafa wa juna yayin da suke bauta wa Allah! Sarki Sulemanu mai hikima ya rubuta cewa: “Biyu sun fi ɗaya.” Me ya sa? “Gama za su fi samun amfanin wahalar aikinsu. Gama idan ɗaya daga cikinsu ya fāɗi, ɗayan zai taimake shi ya tashi.”—Mai-Wa’azi 4:9, 10, Littafi Mai Tsarki.

Mai yiwuwa kana ɗokin gina ruhaniya tare da matarka. Amma kamar aikin lambu, kasancewa da muradi kawai ba zai cim ma kome ba. Ku yi la’akari da ƙalubale guda biyu da za ku iya fuskanta da kuma yadda za ku iya warware su.

ƘALUBALE NA 1: Ba mu da lokaci. Sue wadda ba ta daɗe da yin aure ba ta ce: “Maigidana yana zuwa wurin aikina ya ɗauke ni a mota da ƙarfe 7:00 na yamma. Sa’ad da muka isa gida, dukan aikace-aikacen gida suna nan suna jiran mu. Zuciyarmu da jikinmu suna gwagwarmaya da juna; zuciyarmu tana gaya mana cewa ya kamata mu zauna tare kuma mu yi aiki tuƙuru don mu gina ruhaniyarmu, amma jikinmu yana bukatar hutu.”

Abin da zai iya taimakawa: Ku daidaita yanayinku kuma ku ba juna haɗin kai. Sue ta ce: “Ni da maigidana muka yanke shawara mu riƙa tashi da sassafe mu karanta wani sashen Littafi Mai Tsarki kuma mu tattauna shi tare kafin mu tafi aiki. Yana kuma taimaka mini ya yi wasu aikace-aikacen gida domin in samu lokacin kasancewa tare da shi.” Wane amfani ne aka samu daga wannan ƙoƙartawar? Ed, maigidan Sue, ya ce: “Na gan cewa sa’ad da ni da Sue muka fara tattauna batutuwa na ruhaniya tare a kai a kai, muna warware matsalolin da muke fuskanta cikin sauƙi kuma mun rage yawan alhinin da muke yi.”

Ƙari ga tattaunawa da juna, yana da muhimmanci ku yi amfani da ’yan mintoci a kowace rana ku yi addu’a tare. Ta yaya hakan zai taimaka? “A kwanan baya, ni da matata mun fuskanci matsala mai tsanani a aurenmu. Amma mun keɓe lokaci domin mu yi addu’a tare a kowane dare, muna gaya wa Allah damuwarmu. Ina ganin cewa yin addu’a tare ya taimaka mana mu warware matsalolinmu kuma mu ci gaba da jin daɗin aurenmu,” in ji Ryan.

KU GWADA WANNAN: Ku keɓe ’yan mintoci a ƙarshen kowace rana domin ku tattauna abubuwa masu kyau da kuka shaida a matsayin ma’aurata, abubuwan da za su sa ku yi godiya ga Allah. Ku kuma tattauna ƙalubalen da kuka fuskanta, waɗanda musamman kuna bukatar taimako daga Allah don ku jure su kuma ku warware su, idan hakan zai yiwu. Gargaɗi: Kada ka yi amfani da wannan zarafin don ambata jerin kurakuren matarka. Maimakon haka, sa’ad da kuka yi addu’a tare, ka ambata ƙalubalen da kuke bukatar warwarewa tare kaɗai. Washegari, ku ɗauki matakan da suka jitu da addu’ar da kuka yi.

ƘALUBALE NA 2: Iyawarmu sun bambanta. Zama wuri guda ina karatu da nazari yana yi mini wuya,” in ji Tony. Matarsa, Natalie, ta ce: “Ni mai son karatu ne, kuma ina son yin magana game da abin da na koya. A wasu lokatai ina ganin ina tsoratar da maigidana sa’ad da muke tattauna batutuwan da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki.”

Abin da zai iya taimakawa: Ku kasance da haɗin kai, kada ku yi gāsa ko ku sūki juna. Ka gaya wa matarka cewa kana yaba mata saboda abubuwan da take yi kuma ka ƙarfafa ta ta ƙudurta yin abin da ya dace a hidimar Jehobah. Tony ya ce: “Yadda matata take ɗokin tattauna batutuwan Littafi Mai Tsarki yana rikitar da ni a wasu lokatai, kuma a dā ba na son tattauna batutuwa na ruhaniya da ita. Amma, Natalie tana ba ni haɗin kai sosai. Yanzu, muna tattauna batutuwa na ruhaniya tare a kai a kai, kuma na gano cewa ba na bukatar jin tsoron kome sa’ad da muke tattaunawa tare. Ina jin daɗin tattauna waɗannan batutuwa da ita. Hakan ya taimaka mana mu kasance da kwanciyar hankali kuma mu zauna lafiya a matsayin ma’aurata.”

Ma’aurata da yawa sun gan cewa aurensu ya ƙara inganci yayin da suka keɓe lokaci a kowane mako a kai a kai don su karanta Littafi Mai Tsarki kuma su yi nazarin sa tare. Gargaɗi: Ka faɗi yadda kai da kanka za ka yi amfani da duk wata shawarar da ka karanta daga Nassi, ba yadda matarka za ta yi amfani da ita ba. (Galatiyawa 6:4) Ku tattauna batutuwa da za su iya kawo saɓani a aure a wani lokaci dabam, ba a lokacin da kuke nazari ba. Me ya sa?

Alal misali: Za ka so ka wanke ciwon da ke wari kuma ka ɗaure shi da bandeji a lokacin da kake cin abinci tare da iyalinka? Ba za ka yi hakan ba. Za ka sa abincin ya gunduri kowa. Yesu ya kwatanta koyo game da Allah da kuma yin nufinsa da cin abinci. (Matta 4:4; Yohanna 4:34) Idan ka ta da zancen matsalolin da ke tsakaninku a duk lokacin da kuke nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka iya sa cin abinci na ruhaniya ya gunduri matarka. Babu shakka, kuna bukatar ku tattauna matsaloli tare. Amma ku yi hakan a lokacin da kuka keɓe musamman don hakan.—Misalai 10:19; 15:23.

KU GWADA WANNAN: Ka rubuta halaye guda biyu ko uku na matarka da ka fi so. Sa’ad da kuke tattauna batutuwa na ruhaniya da suka shafi waɗannan halaye, ka gaya wa matarka cewa kana son yadda take nuna waɗannan halayen.

Za Ku Girbe Abin da Kuka Shuka

Idan kuka shuka, ko kuma kuka gina ruhaniya a matsayin mata da miji, a ƙarshe za ku girbe zaman lafiya da kuma gamsuwa a aurenku. Hakika, Kalmar Allah ta ba da tabbaci cewa “iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.”—Galatiyawa 6:7.

Frederick da Leanne, waɗanda aka yi ƙaulinsu a farkon wannan talifin, sun shaida gaskiyar wannan mizani na Littafi Mai Tsarki. Yanzu, sun yi shekara 45 da yin aure kuma sun ga cewa nuna himma yana da amfani sosai. Frederick ya ce: “A dā ina ɗora wa matata laifin rashin tattaunawarmu. Amma da wucewar lokaci, na fahimci cewa ina bukatar ƙoƙartawa.” Leanne ta ce: “Abin da ya taimaka mana a wannan lokaci mai wuya shi ne ƙaunar da muke da ita ga Jehobah Allah. A dukan shekarun nan, muna yin nazari da kuma addu’a tare a kai a kai. Sa’ad da na ga maigidana yana ƙoƙarin ya kyautata yadda yake nuna halayen Kirista, nuna masa ƙauna ba ya yi mini wuya.”

[Hasiya]

a An canja sunaye.

b Wannan talifin ya shafi mata da miji.

KA TAMBAYI KANKA . . .

▪ Yaushe rabonmu da yin addu’a tare a matsayin mata da miji?

▪ Mene ne zan iya yi domin in ƙarfafa matata ta tattauna batutuwa na ruhaniya tare da ni?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba