Ka Koya Daga Kalmar Allah
Ta Yaya Ne Dokokin Allah Suke Amfanar Mu?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Me ya sa ya kamata mu yi biyayya ga Allah?
Ya kamata mu yi biyayya ga Allah, shi ne ya halicce mu. Yesu ma ya yi biyayya ga Allah a kowane lokaci. (Yohanna 6:38; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Dokokin Allah suna ba mu damar nuna cewa muna ƙaunar sa.—Karanta 1 Yohanna 5:3.
Dukan dokokin Jehobah Allah suna da amfani a gare mu. Sun nuna mana hanyar yin rayuwa mafi kyau a yau da kuma yadda za mu iya more albarka na har abada a nan gaba.—Karanta Zabura 19:7, 11; Ishaya 48:17, 18.
2. Ta yaya ne dokokin Allah suke kyautata lafiyarmu?
Dokar Allah game da yin maye tana kāre mu daga muguwar cuta da kuma haɗarurruka. Yawan shan giya jaraba ce kuma tana kai ga wauta. (Misalai 23:20, 29, 30) Jehobah ya yarda mu sha giya, amma daidai kima.—Karanta Zabura 104:15; 1 Korintiyawa 6:10.
Jehobah ya kuma yi mana gargaɗi a kan nuna kishi, hasala da sauran munanan halaye. Idan muka bi wannan shawarar, za mu kyautata lafiyar jikinmu.—Karanta Misalai 14:30; 22:24, 25.
3. Ta yaya dokar Allah za ta iya kāre mu?
Dokar Allah ta hana mutum ya kwana da wadda bai aura ba. (Ibraniyawa 13:4) Ma’auratan da suka bi wannan dokar suna samun kwanciyar rai a aurensu kuma suna sa gidansu ya kasance wurin zama mai kyau ga ’ya’yansu. Akasin haka, yin jima’i da wadda mutum bai aura ba, sau da yawa yana jawo cuta da kashe aure da rikici da baƙin ciki da kuma cikin shege.—Karanta Misalai 5:1-9.
Idan muka guje ma yanayin da zai kai mu mu kwana da wadda ba mu aura ba, za mu kāre abutarmu da Allah. Za mu kuma guje wa jawo lahani ga wasu.—Karanta 1 Tasalonikawa 4:3-6.
4. Ta yaya ne daraja rai yake amfanar mu?
Waɗanda suke daraja ran da Allah ya ba da kyauta suna more lafiyar jiki sa’ad da suka daina halayen nan kamar su shan taba da kuma abubuwa masu haɗari. (2 Korintiyawa 7:1) Allah yana daraja ɗan tayin da ke cikin ciki. (Fitowa 21:22, 23) Saboda haka, kada mu kashe jaririn da ke cikin ciki da gangan. Haka kuma, waɗanda suke daraja rai kamar Allah suna ɗaukan matakai don su kāre kansu daga samun haɗari a wurin aikinsu, a gida da kuma motarsu. (Kubawar Shari’a 22:8) Ƙari ga haka, ba sa yin wasanni masu haɗari, domin rai kyauta ce daga Allah.—Karanta Zabura 36:9.
5. Ta yaya darajar da jini yake da shi take amfanar mu?
Jini yana da tsarki domin Allah ya ce jini yana wakiltar ran halitta. (Farawa 9:3, 4) Dokar Allah, ta kamanta darajar jini da na rai. Domin wannan dokar, Allah ya sa ya yiwu mu samu gafarar zunubanmu.—Karanta Levitikus 17:11-13; Ibraniyawa 9:22.
Ta yaya ya yi hakan? Ya aiko Ɗansa zuwa duniya don ya fanshe mu da jininsa. Jinin Yesu yana da daraja sosai domin shi kamili ne. Yesu ya miƙa wa Allah abin da ke wakiltar ransa, wato, jininsa. (Ibraniyawa 9:12) Jininsa da ya zubar ya ba mu damar samun rai na har abada.—Karanta Matta 26:28; Yohanna 3:16.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 12 da 13 na wannan littafin, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.