Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 11/15 pp. 6-10
  • “Kada Ka Jingina Ga Naka Fahimi”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kada Ka Jingina Ga Naka Fahimi”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sa’ad da Muke Fuskantar Matsaloli
  • Sa’ad da Muke Tsai da Shawara
  • Sa’ad da Muke Ƙoƙari Mu Tsayayya wa Jarrabobi
  • Yadda Za Mu Inganta Adduꞌoꞌinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Me Ya Sa Za Mu Yi Addu’a Ba Fasawa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Yadda Za Ka Inganta Adduꞌarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • “Kada Ku Faɗa Ga Gwaji”
    Ka Zauna A Faɗake!
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 11/15 pp. 6-10

“Kada Ka Jingina Ga Naka Fahimi”

“Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi.”—MIS. 3:5.

1, 2. (a) Waɗanne yanayi ne za mu iya fuskanta? (b) Wane ne ya kamata mu dogara gare shi sa’ad da muke fama da wahala da tsai da shawara ko kuma tsayayya wa gwaji kuma me ya sa?

SHUGABAN aikin Cynthiaa ya rufe wasu sashen kamfaninsa kuma ya sallame ma’aikata da yawa. Cynthia tana ji ita ma za a sallame. Mene ne za ta yi idan an sallame ta? A ina za ta samu kuɗin da za ta yi sayayya da shi? Wata ’yar’uwa Kirista mai suna Pamela tana son ta ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai, amma tana tunani ko ta ƙaura ko a’a. Wani matashi mai suna Samuel yana da wata matsala dabam. Ya soma kallon hotunan batsa tun yana ƙarami. Amma yanzu da ya wuce shekara ashirin, Samuel yana fuskantar gwajin koma ga mummunar halinsa na dā. Ta yaya zai iya yin tsayayya da wannan gwajin?

2 Wane ne kake dogara ga sa’ad da kake fuskantar mawuyacin yanayi da sa’ad da kake tsai da shawara mai muhimmanci da kuma sa’ad da kake tsayayya wa gwaje-gwaje? Kana dogara ga kanka ne, ko kuwa kana “zuba nawayarka bisa Ubangiji”? (Zab. 55:22) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙarassu.” (Zab. 34:15) Yana da muhimmanci sosai mu dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu kuma bai kamata mu dogara ga fahiminmu ba!—Mis. 3:5.

3. (a) Dogara ga Jehobah ya ƙunshi mene ne? (b) Me ya sa wasu suke dogara ga nasu fahimi?

3 Dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu tana nufin yin abubuwa yadda yake so, bisa nufinsa. Wajibi ne mu ci gaba da yin addu’a ga Jehobah muna roƙonsa ya yi mana ja-gora. Amma dai, yana yi wa mutane da yawa wuya su dogara gabaki ɗaya ga Jehobah. Alal misali, wata ’yar’uwa Kirista mai suna Lynn ta ce: “Ba ya kasance mini da sauƙi na dogara ga Jehobah ba.” Me ya sa? Ta ce: “Ba ni da dangantaka da mahaifina, kuma mahaifiyata ba ta kula da ni a zahiri da kuma motsin rai ba. Saboda haka, na soma kula da kaina tun ina ƙarama.” Yadda aka rene Lynn ya sa ya kasance mata da wuya ta dogara ga kowa gabaki ɗaya. Ingancin kai da kuma yin nasara zai iya sa mutum ya dogara ga kansa. Dattijo zai iya dogara ga hikimarsa, kuma ya soma kula da batutuwa da suka shafi ikilisiyar ba tare da yin addu’a ga Allah ba.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Jehobah yana son mu yi iya ƙoƙarinmu don mu aikata daidai da addu’o’inmu da kuma nufinsa. Ta yaya za mu iya daidaita tsakanin zuba nawayarmu ga Allah da kuma yin ƙoƙari don yin maganin mawuyacin matsalolin da suka taso? Ya kamata mu yi hattara da mene ne, idan ya zo ga batun tsai da shawara? Me ya sa addu’a take da muhimmanci sa’ad da muke neman mu tsayayya wa gwaje-gwaje? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin ta yin la’akari da misalan Nassosi.

Sa’ad da Muke Fuskantar Matsaloli

5, 6. Mene ne Hezekiya ya yi sa’ad da sarkin Assuriya ya yi masa barazana?

5 Littafi Mai Tsarki ya ce game da Sarki Hezekiya: “Ya manne ma Ubangiji, ba ya rabu da binsa ba, amma ya kiyaye umurnansa waɗanda Ubangiji ya umurta ma Musa.” Hakika, “ya dogara ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.” (2 Sar. 18:5, 6) Mene ne Hezekiya ya yi sa’ad da Sarki Sennakerib na Assuriya ya aika wakilansa, haɗe da Rabshakeh zuwa Urushalima tare da rundunar sojoji masu yawa? Runduna masu ƙarfi na ƙasar Assuriya sun riga sun ƙwace birane masu yawa na Yahuda, kuma yanzu Sennakerib ya mai da hankalinsa ga Urushalima. Hezekiya ya je haikalin Jehobah kuma ya soma addu’a: “Ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu, ina roƙonka, daga cikin hannunsa, domin dukan mulkokin duniya su sani, kai Ubangiji, Allah ne, kai kaɗai.”—2 Sar. 19:14-19.

6 Hezekiya ya aikata daidai da addu’arsa. Kafin ya je haikalin don yin addu’a, ya umurce mutanen su yi banza da tuhumar Rabshakeh. Hezekiya ya kuma aika mutane zuwa wurin annabi Ishaya don neman shawara. (2 Sar. 18:36; 19:1, 2) Hezekiya ya ɗauki matakan da suka dace. A wannan lokacin, bai yi ƙoƙarin neman mafita da ba ta jitu da nufin Jehobah ba ta neman taimako daga ƙasar Masar ko kuma al’ummai da suke kewaye da su ba. Maimakon Hezekiya ya dogara ga nasa fahimi, ya dogara ga Jehobah. Bayan da mala’ikan Jehobah ya kashe rundunar Sennakerib 185,000, sai Sennakerib ya “tashi” ya koma Nineba da zama.—2 Sar. 19:35, 36.

7. Ta yaya addu’o’in Hannatu da Yunana za su iya ƙarfafa mu?

7 Hannatu, matar Elkanah Balawi ma ta dogara ga Jehobah sa’ad da take baƙin ciki don ba ta iya haifan ɗa ba. (1 Sam. 1:9-11, 18) An ceci annabi Yunana daga cikin babban kifi bayan ya yi addu’a: “Saboda ƙuncina na kira ga Ubangiji. Ya kuwa amsa mini; daga can cikin Sheol na yi kira, ka kuwa ji muryata.” (Yun. 2:1, 2, 10) Abin ƙarfafa ne sanin cewa ko yaya tsananin wahalar da muke ciki, za mu iya yin kira ga Jehobah don ya taimaka mana.—Karanta Zabura 55:1, 16.

8, 9. Hezekiya da Hannatu da kuma Yunana sun yi addu’a game da wanne damuwa kuma mene ne za mu iya koya daga wannan?

8 Misalan Hezekiya da Hannatu da kuma Yunana sun koya mana wani darasi mai muhimmanci game da abin da ya kamata mu tuna sa’ad da muke addu’a yayin da muke fuskantar barazana. Sa’ad da su uku suke fuskantar matsaloli, sun yi baƙin ciki. Duk da haka, addu’o’insu sun nuna cewa ba su damu da kansu kaɗai ba don su samu sauƙi daga matsalolinsu. Amma sun fi damuwa da sunan Allah da bautarsa da kuma yin nufinsa. Hezekiya ya damu domin ana ɓata sunan Jehobah. Hannatu ta yi alkawari cewa za ta sa yaron da ta ce Jehobah ya ba ta ya riƙa hidima a mazaunin da ke Shiloh. Kuma Yunana ya ce: “Zan biya abin da na yi wa’adinsa.”—Yun. 2:9.

9 Ya kamata mu bincika muradinmu sa’ad da muka yi addu’a don Allah ya cece mu daga mawuyacin yanayi. Shin muna damuwa ainun ga samun sauƙi daga matsalar, ko kuwa muna mai da hankali ga ƙudurin Jehobah? Wahalar da muke sha za ta iya nauyaya mu har mu manta da abubuwa na ruhaniya. Ya kamata mu mai da hankali ga Jehobah da tsarkake sunansa da kuma kunita ikon mallakarsa sa’ad da muke addu’a ga Allah don ya taimaka mana. Yin hakan zai taimaka mana mu kasance da daidaitaccen ra’ayi ko da al’amura ba su kasance yadda muke sa rai ba. A wasu lokatai, Jehobah yana amsa addu’o’inmu ta wajen ba mu ƙarfin da muke bukata don jimre da yanayin.—Karanta Ishaya 40:29; Ishaya 12:2.

Sa’ad da Muke Tsai da Shawara

10, 11. Mene ne Jehoshaphat ya yi sa’ad da ya fuskanci yanayin da ya fi ƙarfinsa?

10 Ta yaya za ka iya tsai da shawarwari masu muhimmanci a rayuwa? Shin kana fara tsai da shawara ne kafin ka yi addu’a ga Jehobah? Ka yi la’akari da abin da Jehoshaphat sarkin Yahuda ya yi sa’ad da rundunar Mowabawa da Ammonawa suka tasam masa. Sun fi Yahuda ƙarfi sosai. Wane mataki ne Jehoshaphat zai ɗauka?

11 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Jehoshaphat ya ji tsoro, ya sa zuciyatasa ga neman Ubangiji.” Ya umurce mutanen Yahuda su yi azumi kuma ya tattara mutanen don su “biɗi taimako daga wurin Ubangiji.” Sai ya tashi tsaye cikin jama’ar Yahuda da Urushalima ya yi addu’a. Ya ce: “Ya Allahnmu, ba za ka shar’anta masu ba? gama mu ba mu da wani ƙarfi wurin wannan babban taron da ke zuwa yaƙi da mu; mun kuwa rasa yadda za mu yi: amma idanunmu suna gareka.” Allah na gaskiya ya saurari addu’ar da Jehoshaphat ya yi kuma ya cece shi ta mu’ujiza. (2 Laba. 20:3-12, 17) Zai dace mu dogara ga Jehobah ba ga fahiminmu ba sa’ad da muke tsai da shawarwari, musamman waɗanda suka shafi ruhaniyarmu.

12, 13. Wane misali ne Sarki Dauda ya kafa game da tsai da shawara?

12 Me ya kamata mu yi sa’ad da muke fuskantar yanayin da muke ganin ba shi da wuya sosai, wataƙila domin mun yi maganin abin da gaggawa a dā sa’ad da muka fuskanci yanayin? Labarin Sarki Dauda ya nuna abin da ya kamata mu yi. Sa’ad da Amalekawa suka kai wa birnin Ziklag hari, sun ɗauki matan Dauda da yaransa da kuma na bayinsa. Dauda ya biɗi Jehobah, ya ce: “Idan na bi sawun waɗannan mahara zan ci masu?” Jehobah ya amsa: “Bi sawunsu: gama hakika za ka ci masu; ba makawa kuma za ka sāke karɓo su duka.” Dauda ya bi shawarar, kuma ya “sāke amshe dukan abin da Amalekawa suka ƙwace.”—1 Sam. 30:7-9, 18-20.

13 Bayan da Amalekawa suka kai wa birnin Ziklag hari, Filistiyawa ma suka tasam ma Isra’ila. Dauda ya sake tambayar Jehobah kuma ya ba shi amsa dalla-dalla. Allah ya ce: “Ka hau: gama hakika sai in bada Filistiyawa cikin hannunka.” (2 Sam. 5:18, 19) Ba da daɗewa ba, Filistiyawa suka sake kai wa Dauda hari. Mene ne Dauda zai yi wannan lokacin? Da wataƙila ya yi tunani: ‘Na taɓa fuskantar irin wannan yanayin sau biyu. Bari na kai wa maƙiyan Allah hari yadda na yi a dā.’ Ko kuwa Dauda zai nemi ja-gora daga wurin Jehobah? Dauda bai dogara ga abin da ya faru a dā ba. Ya sake addu’a ga Jehobah. Babu shakka ya yi farin ciki sosai don ya yi hakan! Domin umurnin da aka ba shi a wannan lokacin ya bambanta. (2 Sam. 5:22, 23) Sa’ad da muke fuskantar irin wannan yanayin ko matsala, wajibi ne mu mai da hankali don kada mu dogara gabaki ɗaya ga abin da ya taɓa faruwa.—Karanta Irmiya 10:23.

14. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Joshua da dattawan Isra’ila suka bi da Gibeyonawa?

14 Da yake mu ajizai ne, ya kamata dukan mu haɗe da dattawa da suka manyanta mu mai da hankali don kada mu fasa neman ja-gorar daga wurin Jehobah sa’ad da muke son mu tsai da shawarwari. Ka yi la’akari da yadda magajin Musa, Joshua da kuma dattawan Isra’ila suka aikata sa’ad da Gibeyonawa masu basira da suka canja kamaninsu kuma suka yi kamar sun taho ne daga ƙasa mai nisa. Ba tare da tambayar Jehobah ba, Joshua da sauran mutanen suka yi wa’adin salama da Gibeyonawa, har da yi musu alkawari. Ko da Jehobah ya goyi bayan shawarar da suka tsai da, ya tabbata cewa an rubuta wannan kuskuren da aka yi na fasa neman ja-gorarsa a cikin Nassosi don amfaninmu.—Josh. 9:3-6, 14, 15.

Sa’ad da Muke Ƙoƙari Mu Tsayayya wa Jarrabobi

15. Ka bayyana dalilin da ya sa addu’a take da muhimmanci don tsayayya wa jarraba?

15 Da yake muna da “shari’ar zunubi” a cikinmu, muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu yaƙi wannan halin. (Rom. 7:21-25) Za mu iya yin nasara. Ta yaya? Yesu ya gaya wa mabiyinsa cewa addu’a tana da muhimmanci don tsayayya wa jarraba. (Karanta Luka 22:40.) Ko da sha’awa ko tunani marar kyau ta ci gaba bayan mun yi addu’a, muna bukatar mu ci gaba da yin “roƙo ga Allah” don mu samu hikimar da za ta taimaka mana mu tsayayya wa jarrabar. Muna da tabbaci cewa yana “bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma.” (Yaƙ. 1:5) Yaƙub ya kuma rubuta: “Akwai mai-ciwo [na ruhaniya] a cikinku? sai shi kira dattiɓan ikilisiya su yi addu’a a bisansa, suna shafe shi da mai cikin sunan Ubangiji: addu’ar bangaskiya kuwa za ta ceci mai-ciwo.”—Yaƙ. 5:14, 15.

16, 17. Sa’ad da muke neman taimako don tsayayya wa jarraba, wane lokaci ne ya fi dacewa mu yi addu’a?

16 Addu’a tana da muhimmanci don tsayayya wa jarraba, amma ya kamata mu san cewa ya kamata mu yi addu’a a lokacin da ya dace. Ka yi la’akari da misalin wani saurayi da aka ambata a littafin Misalai 7:6-23. Yana yin tafiya da duku-duku a inda wata karuwa take zama. Sa’ad da ta lallashe shi kuma ta yi masa maganganu masu daɗi, sai ta rinjaye shi, kuma ya soma bin ta kamar sa mai-tafiya wurin fawa. Me ya sa wannan saurayi ya je wurin? Tun da yake shi “marar-fahimi” ne, wataƙila yana fama ne da muguwar sha’awa. (Mis. 7:7) Da a wane lokaci ne addu’a za ta amfane shi sosai? Hakika, da zai fi kyau ya yi addu’a don tsayayya wa gwaji a lokacin da matar take masa magana. Amma da lokaci mafi kyau da zai yi addu’a shi ne sa’ad da ya fara yin sha’awar takawa zuwa kusa da gidanta.

17 A yau mutum zai iya yin fama ya daina kallon hotunan batsa. Amma a ce ya shiga dandalin Intane inda ya san cewa akwai hotuna da bidiyon batsa. Shin hakan ba zai kasance daidai da misalin wannan saurayi da aka kwatanta a littafin Misalai sura 7 ba? Wannan hanya marar kyau ce da bai kamata a bi ba! Don tsayayya wa jarrabar kallon batsa, mutum yana bukata ya nemi taimakon Jehobah a addu’a kafin ya soma neman abu a cikin Intane.

18, 19. (a) Me ya sa tsayayya wa jarraba yake da wuya, amma yaya za mu iya shawo kan matsalar? (b) Mene ne ka ƙuduri aniya za ka yi?

18 Ba shi da sauƙi mu tsayayya wa jarraba ko kuma shawo kan hali marar kyau. Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka.” Saboda haka, “ba [ma] iya yin abin da [muke] so.” (Gal. 5:17, Littafi Mai Tsarki) Muna bukatar yin addu’a sosai sa’ad da muka fara tunani a kan sha’awa marar kyau ko muke fuskantar jarraba kuma muna bukata mu aikata bisa abin da muka roƙa. “Babu wata jaraba ta same ku sai irin da mutum ya iya jimrewa,” kuma da taimakon Jehobah, za mu iya kasancewa da aminci.—1 Kor. 10:13.

19 Ko muna fama da yanayi mai wuya ko tsai da shawara mai muhimmanci ko kuma yin ƙoƙarin tsayayya wa jarraba, Jehobah ya riga ya ba mu baiwa mai kyau, wato, baiwa mai tamani na yin addu’a. Ta wannan hanyar, mun nuna muna dogara ga Allah. Ya kamata mu ci gaba da roƙon Allah don ya ba mu ruhu mai tsarki, da zai ja-goranci da kuma ƙarfafa mu. (Luk 11:9-13) Kuma ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don dogara ga Jehobah kuma kada mu dogara ga namu fahimi.

[Hasiya]

a An canja sunayen.

Ka Tuna?

• Mene ne ka koya daga Hezekiya da Hannatu da kuma Yunana game da dogara ga Jehobah?

• Ta yaya misalin Dauda da Joshua suka nanata amfanin yin hattara sa’ad da muke tsai da shawara?

• Sa’ad da muke fuskantar jarraba, a wane lokaci ne ya dace mu yi addu’a?

[Hoto a shafi na 9]

Wane lokaci ne yake da kyau mu yi addu’a don tsayayya wa jarraba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba