Ka Koya Daga Kalmar Allah
Ta Yaya Ne Za Mu Iya Zaɓan Abokan Kirki?
Wannan talifin ya tattauna tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin tunani a kansu kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali yayin da muke zaɓan abokai?
Mutane da yawa suna son a amince da su. Wannan sha’awar tana sa mu yi koyi da mutanen da suke kusa da mu. Saboda haka, abokai suna da tasiri mai girma a kan irin halayenmu. Abokai da muka zaɓa za su iya shafan irin mutum da za mu zama.—Karanta Misalai 4:23; 13:20.
Hurarren marubucin Littafi Mai Tsarki, Dauda, ya zaɓi abokan kirki. Ya yi tarayya da waɗanda suka taimaka masa ya riƙe amincinsa a matsayin bawan Allah. (Zabura 26:4, 5, 11, 12) Alal misali, Dauda ya ji daɗin abutar Jonathan domin Jonathan ya ƙarfafa shi ya dogara ga Jehobah.—Karanta 1 Sama’ila 23:16-18.
2. Ta yaya za ka iya zama abokin Allah?
Ko da yake Jehobah mai iko duka ne, za mu iya zaman abokansa. Alal misali, Ibrahim ya zama abokin Allah. Ibrahim ya gaskata da Jehobah kuma ya yi masa biyayya, saboda haka Jehobah ya ƙulla abuta da shi. (Farawa 22:2, 9-12; Yaƙub 2:21-23) Idan mun gaskata da Jehobah kuma mun aikata abin da ya ce mu yi, mu ma za mu iya zama abokan Allah.—Karanta Zabura 15:1, 2.
3. Ta yaya za ka amfana daga abokan kirki?
Abokan kirki suna da aminci kuma za su taimake ka ka yi abin da ya dace. (Misalai 17:17; 18:24) Alal misali, ko da yake Jonathan ya girme Dauda da wajen shekaru 30 kuma shi ne ya kamata ya gaji sarautar Isra’ila, cikin aminci ya goyi bayan Dauda a matsayin wanda Allah ya zaɓa ya zama sarki. Abokan kirki suna da gaba gaɗin yi maka gyara idan suka ga cewa kana yin abin da bai dace ba. (Zabura 141:5) Abokai da suke ƙaunar Allah suna taimaka wa mutum ya koyi halaye masu kyau.—Karanta 1 Korintiyawa 15:33.
Za ka iya samun mutanen da kamar kai suna ƙaunar abin da ya dace a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah. A wurin, za ka samu abokai da za su ƙarfafa ka domin ka ci gaba da ƙoƙarin faranta wa Allah rai.—Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.
Duk da haka, abokai da suke ƙaunar Allah ma za su iya ɓata maka rai a wasu lokatai. Kada ka yi hanzarin yin fushi domin kurakurensu. (Mai-Wa’azi 7:9, 20-22) Ka tuna, ba za ka iya samun aboki kamiltacce ba, kuma abokai da suke ƙaunar Allah suna da tamani a gare mu. Kalmar Allah ta aririce mu mu gafarta wa ’yan’uwanmu Kiristoci laifuffukansu.—Karanta Kolosiyawa 3:13.
4. Idan waɗanda suke da’awar cewa su abokanka ne suna hamayya da kai fa?
Mutane da yawa sun gane cewa sa’ad da aka soma taimakon su domin su fahimci Kalmar Allah, wasu cikin abokansu na dā suna hamayya da su. Mai yiwuwa waɗannan abokai ba su fahimci cewa ka samu shawara mai amfani ko kuma tabbataccen bege a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Wataƙila za ka iya taimakon su.—Karanta Kolosiyawa 4:6.
A wasu yanayi, waɗanda suke da’awar cewa su abokanka ne suna iya ba’ar albishirin da ke Kalmar Allah. (2 Bitrus 3:3, 4) Wasu za su yi maka ba’a domin ƙoƙarinka na yin abin da ya dace. (1 Bitrus 4:4) Idan ka samu kanka a cikin wannan yanayin, mai yiwuwa za ka zaɓi ko ka yi abuta da mutane ko kuma da Allah. Idan ka yanke shawarar zama abokin Allah, ka zaɓi aboki na ƙwarai da mutum zai taɓa samu.—Karanta Yaƙub 4:4, 8.
Domin ƙarin bayani, ka duba babi na 12 da kuma 19 na littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.