Shi Misali Mai Kyau Ne A Gare Ka Ko Kuma Kashedi?
“Allah na Yaƙub . . . za ya koya mana tafarkunsa, mu kuma mu kama tafiya cikin hanyoyinsa.”—ISHA. 2:3.
1, 2. A waɗanne hanyoyi biyu ne za ka iya amfana daga misalan da ke cikin Littafi Mai Tsarki?
SHIN ka amince cewa za ka iya amfana daga abin da aka rubuta cikin Littafi Mai Tsarki? Za ka iya samun labaran maza da mata masu aminci da za ka iya so yin koyi da tafarkin rayuwarsu da kuma halayensu. (Ibran. 11:32-34) Amma dai, wataƙila ka ga misalan maza da mata da ya kamata ka ƙi tafarkunsu.
2 Hakika, wasu mutane da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki misali mai kyau ne da ya kamata mu bi da kuma waɗanda ya kamata mu ƙi. Ka yi la’akari da Dauda, makiyayi mai tawali’u da kuma sarki mai iko. Shi mutum ne da ke ƙaunar gaskiya kuma yana dogara ga Jehobah. Duk da haka, Dauda ya yi zunubi mai tsanani, kamar wanda ya faru tsakaninsa da Bath-sheba da Uriah da kuma kiɗayar da ya yi da bai dace ba. Amma bari mu mai da hankali ga ɗansa Sulemanu sarki da kuma marubucin Littafi Mai Tsarki. Za mu fara tattauna hanyoyi biyu da shi misali mai kyau ne.
‘Hikimar Sulemanu’
3. Me ya sa za mu iya ce Sulemanu ya kafa mana misali mai kyau?
3 Sulemanu mafi girma, wato, Yesu Kristi, ya yi kalami mai kyau game da Sarki Sulemanu, wanda misali ne mai kyau a gare mu. Yesu ya gaya wa wasu Yahudawa da suke shakka: ‘Sarauniyar kudu za ta tashi tsaye a ranar shari’a tare da wannan tsara, za ta kuwa kashe ta: gama daga nisan duniya ta zo garin ta ji hikimar Sulemanu: ga kuwa wanda ya fi Sulemanu girma a nan.’ (Mat. 12:42) Hakika, Sulemanu sanannen mai hikima ne, kuma ya shawarce mu mu zama masu hikima.
4, 5. Ta yaya Sulemanu ya samu hikima, amma yaya hakan ya bambanta da mu a yau?
4 Sa’ad da Sulemanu ya soma sarautarsa, Allah ya bayyana masa a mafarki kuma ya gaya masa ya faɗi abin da yake so. Da yake ya san cewa bai ƙware ba sosai, sai ya roƙi hikima. (Karanta 1 Sarakuna 3:5-9.) Da yake Allah ya yi farin ciki cewa sarkin ya roƙi a ba shi hikima maimakon wadata da iko, sai ya ba Sulemanu “zuciya mai-hikima, mai-ganewa” da kuma wadata. (1 Sar. 3:10-14) Kamar yadda Yesu ya ambata, Sulemanu yana da hikima sosai har sarauniyar Sheba ta ji labari game da wannan kuma ta yi tafiya mai nisa sosai don ta shaida hakan da kanta.—1 Sar. 10:1, 4-9.
5 Ba ma sa rai cewa za mu samu hikima ta mu’ujiza. Sulemanu ya ce “Ubangiji yana bada hikima,” amma ya rubuta cewa ya kamata mu sa ƙwazo don mu samu wannan hali mai kyau: “Ka karkata kunnenka ga hikima, ka maida zuciyarka ga fahimi.” Sulemanu ya kuma ce mu ‘tada muryarmu garin nema,’ mu “neme ta” kuma mu “biɗe ta,” wato, hikima. (Mis. 2:1-6) Hakika, hakan yana nuna cewa za mu iya samun hikima.
6. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa muna amfana daga misali mai kyau na Sulemanu game da hikima?
6 Zai dace mu tambayi kanmu, ‘Shin ina bimbini a kan misalin Sulemanu na daraja hikimar da Allah yake bayarwa?’ Taɓarɓarewar tattalin arziki ya sa mutane da yawa su fi mai da hankali ga aikinsu da dukiyarsu ko kuma ya shafi shawarar da suke tsai da na irin ilimin da ya kamata su biɗi. Kai da iyalinka kuma fa? Shin zaɓinka yana nuna cewa kana daraja da kuma neman hikima da Allah yake bayarwa? Shin yin gyara ga maƙasudinka zai sa ka samu ƙarin hikima? Hakika, samu da kuma yin amfani da hikima don amfaninka ne. Sulemanu ya rubuta: “Sa’annan za ka fahimci adalci da shari’a, da daidaita, i, kowace hanya mai-kyau.”—Mis. 2:9.
Ɗaukaka Bauta ta Gaskiya Tana Kawo Salama
7. Ta yaya aka gina wa Allah babban haikali?
7 A farkon sarautarsa, Sulemanu ya ɗauki matakai don ya gina wani haikali da zai musanya mazaunin da ake amfani da shi tun zamanin Musa. (1 Sar. 6:1) Muna iya kiransa haikalin Sulemanu, amma bai gina shi don ya yi suna ba. Kuma ba shi ba ne ya fara ce a gina haikalin ba. Hakika, Dauda ne ya fara cewa yana son ya gina haikali, sai Allah ya bayyana masa dalla-dalla yadda zai gina haikalin da kuma kayan cikin. Kuma Dauda ya ba da kuɗi da kayayyaki da yawa don wannan aikin. (2 Sam. 7:2, 12, 13; 1 Laba. 22:14-16) Duk da hakan, Sulemanu ne ya gina haikalin cikin shekara bakwai da rabi.—1 Sar. 6:37, 38; 7:51.
8, 9. (a) Wane misali na nacewa wajen yin ayyuka masu kyau ne Sulemanu ya kafa? (b) Mene ne sakamakon ɗaukaka bauta ta gaskiya da Sulemanu ya yi?
8 Da hakan, Sulemanu ya kafa mana misali mai kyau na yin naciya a aiki mai kyau kuma ya kasance da ra’ayi mai kyau. Sa’ad da aka kammala ginin kuma aka saka sunduƙin alkawari a ciki, sai Sulemanu ya yi addu’a. Ya yi addu’a ga Jehobah ya ce: “[Bari] idanunka su kasance a buɗe a wajen wannan gida dare da rana, wurin da ka ambata ke nan ka ce, sunana za ya kasance a wurin; domin ka saurari addu’a wadda bawanka za ya yi zuwa wurin nan.” (1 Sar. 8:6, 29) Isra’ilawa da baƙi za su iya yin addu’a game da wannan haikalin wanda aka gina don a ɗaukaka sunan Allah.—1 Sar. 8:30, 41-43, 60.
9 Mene ne sakamakon ɗaukaka bauta ta gaskiya da Sulemanu ya yi? Bayan an yi bikin keɓe haikalin, mutanen suka yi “murna da farinciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya nuna ma bawansa Dauda da Isra’ila jama’atasa.” (1 Sar. 8:65, 66) Hakika, an yi salama da kuma lumana sosai a sarautar da Sulemanu ya yi na shekara 40. (Karanta 1 Sarakuna 4:20, 21, 25.) Zabura ta 72 ta nuna hakan kuma ta sa mu fahimci albarkar da za mu more ƙarƙashin sarautar Sulemanu mai girma, wato Yesu Kristi.—Zab. 72, 6-8, 16.
Misalin Sulemanu Gargaɗi ne a Gare Mu
10. Wane kuskuren da Sulemanu ya yi ne za mu iya tunawa da sauri?
10 Me ya sa za mu iya cewa rayuwar Sulemanu kashedi ne a gare mu? Abu na farko da za ka iya yin tunani a kai shi ne matansa da baƙi ne da kuma ƙwarƙwaransa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama ya zama, lokacin da [Sulemanu] ya tsufa, matansa suka juyar da zuciyatasa zuwa bin waɗansu alloli; zuciyatasa ba ta kamilta zuwa ga Ubangiji Allahnsa” ba. (1 Sar. 11:1-6) Babu shakka, ka ƙuduri aniya ba za ka taɓa bin mummunar misalinsa ba. Amma shi ke nan kashedin da muka koya daga rayuwar Sulemanu? Ka yi la’akari da wasu abubuwa game da rayuwarsa da za a iya mantawa da sauƙi, kuma mu ga gargaɗin da ke ciki.
11. Mene ne za mu iya kammalawa game da mata ta farko da Sulemanu ya aura?
11 Sulemanu ya yi sarauta na shekara 40. (2 Laba. 9:30) Saboda haka, me za ka iya kammalawa daga 1 Sarakuna 14:21? (Karanta.) Kamar yadda ayar ta nuna, bayan Sulemanu ya rasu, ɗansa Yerobowam ya zama sarki sa’ad da yake ɗan shekara 41, kuma sunan mahaifiyarsa ‘Naamah ce, Ba-ammoniya.’ Hakan yana nufin cewa kafin Sulemanu ya zama sarki, ya auri baƙuwa daga ƙasar da ke bautar gumaka da ta tsane mutanen Allah. (Alƙa. 10:6; 2 Sam. 10:6) Shin ta bauta musu? Ko da ta bauta wa gumaka a dā, wataƙila ta rabu da bauta musu kuma ta soma bauta wa Allah na gaskiya, kamar yadda Rahab da kuma Ruth suka yi. (Ruth 1:16; 4:13-17; Mat. 1:5, 6) Duk da haka, Sulemanu ya samu surukai da dangi na Ammonawa da ba sa bauta wa Jehobah.
12, 13. Wace shawara marar kyau ce Sulemanu ya tsai da a farkon sarautarsa kuma wataƙila mene ne ya yi zato?
12 Kuma babu shakka, abubuwa sun daɗa muni sosai bayan ya zama sarki. Sulemanu ya yi “amana da Fir’auna sarkin Masar, ya ɗauko ɗiyar Fir’auna, ya kawo ta cikin birnin Dauda.” (1 Sar. 3:1) Shin wannan matar ta yi koyi da Ruth wadda ta rungumi bauta ta gaskiya? Babu alama cewa ta yi hakan. Maimakon haka, da shigewar lokaci Sulemanu ya gina mata gida (da wataƙila bayinta ’yan ƙasar Masar) a waje da Birnin Dauda. Me ya sa? Nassosi sun ce ya yi hakan domin bai dace mai bauta wa gumaka ya zauna kusa da sunduƙin alkawari ba.—2 Laba. 8:11.
13 Wataƙila Sulemanu ya yi zato cewa aurar gimbiya yana da kyau domin hakan zai ƙarfafa dangantaka tsakanin Isra’ilawa da Masarawa. Amma hakan ba hujja ba ce. Da daɗewa, Allah ya riga ya hana su aurar Kan’aniyawa masu bautar gumaka har ma ya lissafa sunayensu. (Fit. 34:11-16) Shin Sulemanu ya yi tunani cewa Masarawa ba sa cikin wannan jerin ƙasashen? Ko da ya yi tunani haka, shin hakan hujja ce? Sulemanu bai yi biyayya ga umurnin da Jehobah ya bayar ba cewa ba shi da kyau a auri mace daga wata ƙasa. Wadda ba ta bauta wa Jehobah za ta iya rinjayi Ba’isra’ile ya soma bautar gumaka.—Karanta Kubawar Shari’a 7:1-4.
14. Ta yaya misalin Sulemanu zai iya amfanar mu?
14 Shin za mu bar misalin Sulemanu ya zama gargaɗi ne a gare mu? ’Yar’uwa tana iya neman hujja don karya dokar Allah da ta ce a yi aure “cikin Ubangiji” kaɗai. (1 Kor. 7:39) Mutum yana iya yin hujja kuma ya saka hannu a wasanni ko ƙungiyoyi a makaranta ko da yin hakan ba dole ba ne. Ko kuma mutum yana iya neman hujja don kada ya biya haraji ko kuma zai iya yin ƙarya sa’ad da aka tambaye shi abin da ya yi. Abin da ya kamata mu tuna shi ne, za mu iya neman hujja don karya dokokin Allah, kamar yadda babu shakka Sulemanu ya yi.
15. Ta yaya Jehobah ya bi da Sulemanu da jin ƙai, amma mene ne ya kamata mu tuna game da hakan?
15 Yana da kyau mu san cewa ko da yake Sulemanu ya riga ya auri mata daga wasu ƙasashe, amma duk da haka Allah ya ba shi hikima da ya roƙa da kuma wadata. (1 Sar. 3:10-13) Sulemanu ya ƙi bin umurnin da Allah ya ba shi, amma duk da haka babu inda aka faɗa cewa Allah ya ƙi shi nan da nan a matsayin sarki ko kuma ya yi masa horo sosai. Wannan ya nuna cewa Allah ya san cewa mu ajizai ne kuma an halicce mu da turɓaya. (Zab. 103:10, 13, 14) Amma ya kamata mu tuna cewa, ayyukanmu za su iya shafanmu yanzu ko kuma a nan gaba.
Mata da Yawa!
16. Wane umurni ne Sulemanu ya ƙi bi sa’ad da ya auri mata da yawa?
16 A cikin littafin Waƙar Waƙoƙi, Sulemanu ya ce wata budurwa ta fi sarauniya 60 da ƙwaraƙwarai 80 kyau. (W. Waƙ. 6:1, 8-10) Wataƙila yawan mata da ƙwaraƙwaran da yake da su ke nan a lokacin. Ko da yawanci ko kuma dukansu suna bauta wa Jehobah, amma Allah ya umurci Musa cewa kada sarki a Isra’ila ya “auri mata da yawa don kada zuciyarsa ta karkace.” (K. Sha 17:17, Littafi Mai Tsarki) Amma kuma Allah bai yasar da Sulemanu ba. Hakika, duk da haka Allah ya albarkace Sulemanu kuma ya yi amfani da shi wajen rubuta littafin Waƙar Waƙoƙi.
17. Wacce gaskiya ce bai kamata mu manta ba?
17 Shin hakan ya nuna cewa Sulemanu bai shaida sakamakon karya dokokin Allah ba ko kuma mu ma za mu iya yin hakan? A’a. Maimako, hakan ya nuna cewa Allah zai iya yin haƙuri na dogon lokaci. Kuma mutum zai iya karya dokar Allah amma ba zai fuskanci sakamakon nan da nan ba. Amma hakan ba ya nufin cewa ba za a fuskanci sakamakon a nan gaba ba. Ka tuna da abin da Sulemanu ya rubuta: “Saboda ba a aika shari’a da aka hukunta a bisa mugunta da sauri ba, shi ya sa zuciyar ’yan adam ta kan ji ƙarfin aika mugunta.” Amma ya daɗa: “Na sani lallai, waɗanda ke tsoron Allah za su zama lafiya, masu-ibada ke nan.”—M. Wa. 8:11, 12.
18. Ta yaya labarin Sulemanu ya tabbatar da gaskiyar da ke cikin Galatiyawa 6:7?
18 Abin baƙin ciki, Sulemanu bai yi biyayya ga wannan gaskiyar ba! Ya yi abubuwa masu kyau kuma ya samu albarka da yawa daga wurin Jehobah. Amma da shigewar lokaci, ya yi kuskure ɗaya bayan ɗaya. Kuma karya dokokin Jehobah ya zama jininsa. Hakan ya yi daidai da abin da manzo Bulus ya rubuta daga baya: “Kada ku ɓata; ba a yi ma Allah ba’a ba: gama iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe”! (Gal. 6:7) Daga baya, Sulemanu ya girbe sakamako marar kyau don ƙin bin dokokin Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sarki [Sulemanu] yana ƙaunar mata baƙi da yawa, banda ɗiyar Fir’auna, su matan Moab kuma, da Ammonawa, da Edomawa da Zidoniyawa, da Hittiyawa.” (1 Sar. 11:1) Wataƙila da yawa cikin waɗannan matan ba su daina bauta wa allolin ƙarya ba kuma hakan ya rinjayi Sulemanu. Ya bijire kuma ya daina more tagomashin Allahnmu mai haƙuri.—Karanta 1 Sarakuna 11:4-8.
Ka Koyi Darasi Daga Misalinsa Mai Kyau da Marar Kyau
19. Me ya sa za ka iya ce Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalai da yawa masu kyau?
19 Jehobah ya hure Bulus ya rubuta: “Gama iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyar littattafai mu zama da bege.” (Rom. 15:4) Waɗannan abubuwan da aka rubuta sun haɗa da misalai da yawa na maza da mata masu bangaskiya sosai. Kuma Bulus ya ce: “Me zan daɗa cewa fa? gama zarafi zai yi mani kaɗan in ba da labarin su Jid’auna, da Baraƙa, da Shamshuna, da Yaftaha; da Dauda da Sama’ila da annabawa: waɗanda suka ƙasar da mulkoki ta wurin bangaskiya, suka aika adalci, suka amshi alkawarai . . . daga cikin rashin ƙarfi aka ƙarfafa su.” (Ibran. 11:32-34) Za mu iya kuma ya kamata mu koyi darasi daga misalai masu kyau da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki.
20, 21. Me ya sa kake son ka ci gaba da koyon darasi daga misalan da suke cikin Littafi Mai Tsarki?
20 Amma wasu labarai na Littafi Mai Tsarki gargaɗi ne. Wasu cikinsu maza da mata ne da Jehobah yake amincewa da su a dā. Sa’ad da muke karanta Littafi Mai Tsarki, za mu iya lura da inda suka yi kuskure, kuma mu guji bin misalinsu. Za mu iya koya cewa wasu cikinsu sun koya halaye marasa kyau da sannu-sannu, kuma daga baya suka yi zunubi mai tsanani. Ta yaya za mu iya koyi darasi daga irin waɗannan labarai? Za mu iya yi wa kanmu tambayoyi kamar su: ‘Ta yaya hakan ya soma? Shin hakan zai iya faru da ni? Mene ne zan iya yi don na guji yin hakan kuma na amfana daga wannan kashedin?’
21 Yana da kyau mu yi la’akari da waɗannan misalai sosai, domin an hure Bulus ya rubuta: “Waɗannan al’amura dai suka same su watau misali ne; kuma aka rubuta su domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.”—1 Kor. 10:11.
Mene ne Ka Koya?
• Me ya sa za ka iya samun misali mai kyau da kuma marar kyau a cikin Littafi Mai Tsarki?
• Me ya sa Sulemanu ya yi kuskure ɗaya bayan ɗaya?
• Yaya za ka iya amfana daga kuskuren da Sulemanu ya yi?
[Hoto a shafi na 9]
Sulemanu ya yi amfani da hikimar da Allah ya ba shi
[Hotona a shafi na 12]
Kana amfana daga kuskuren da Sulemanu ya yi?