Kada Ka Sa Rashin Lafiya Ya Hana Ka Yin Farin Ciki
A CE ka tashi da safe kuma kana fata cewa dare ya yi nan da nan. Za ka sake jimre wa azaba na zahiri da na motsin rai wata rana kuma. Kana iya jin kamar Ayuba wanda ya ce: “Gara in mutu da in rayu da wannan wahalata.” (Ayu. 7:15, The New English Bible) Idan yanayin ya ci gaba, har shekaru da yawa kuma fa?
Mephibosheth, ɗan Jonathan, abokin Sarki Dauda ya kasance a cikin irin wannan yanayin. Sa’ad da Mephibosheth yake ɗan shekara biyar, “sai ya fāɗi, ya zama gurgu.” (2 Sam. 4:4) Wahalarsa ta motsin rai ta ƙaru sosai sa’ad da aka yi masa zargin ƙarya cewa ya ci amanar sarkin da ya kai ga yin hasarar dukiyarsa, kuma hakan ya sa ya yi masa wuya ya jimre da naƙasarsa ta zahiri. Duk da haka, ya kasance misali mai kyau na jimrewa da rashin lafiya da tsegumi da kuma takaici, kuma bai sa waɗannan gwaje-gwajen su hana shi farin ciki ba.—2 Sam. 9:6-10; 16:1-4; 19:24-30.
Wani misali kuma shi ne manzo Bulus. Ya taɓa rubuta game da ‘masuki cikin jiki’ da ya jimre da shi. (2 Kor. 12:7) Masukin da ya ambata zai iya zama naƙasa na dogon lokaci ko kuma mutane da suke ƙalubalantar ikonsa na manzo. Ko mene ne dai, matsalar ta jima, kuma ya jimre da azaba ta zahiri ko kuma ta motsin rai da hakan ya jawo masa.—2 Kor. 12:9, 10.
Bayin Allah a yau suna fuskantar rashin lafiya mai tsanani da ke raunana mutum ko kuma matsala na motsin rai. Sa’ad da Magdalena take ’yar shekara 18, likita ya ce tana da wata cuta mai suna systemic lupus erythematosus, wata cuta da ke yaƙar garkuwar jiki. Ta ce: “Hakan ya birkita ni sosai. Kuma da shigewar lokaci, yanayina ya daɗa taɓarɓarewa sosai kuma abin da ke narkar da abinci a ciki na ya samu matsala kuma ina da ciwon gyambo a baki da ciwon maƙogwaro.” Izabela kuma ta jimre da wata matsala da ba gama gari ba ce. Ta bayyana: “Ina da ciwon baƙin ciki tun ina ƙarama. Hakan ya sa ina da ciwon tsoro da numfashi da kuma ciki. Kuma hakan yana gajiyar da ni sosai.”
Amincewa da Kasawarka
Ciwo da kuma naƙasa zai iya hana ka farin ciki a rayuwa. Idan hakan ya faru, zai yi kyau mu zauna kuma mu yi tunani sosai a kan yanayinmu. Amincewa da kasawarka ba zai kasance da sauƙi ba. Magdalena ta ce: “Ciwo na sai daɗa tsanani yake yi. Sau da yawa ina gajiya ainun har ba zan iya tashiwa daga gado ba. Da yake ba zan iya sanin yadda ciwon za ta kasance ba, hakan yana sa ya yi mini wuya na tsara ayyukana. Abin da ya fi sa ni baƙin ciki shi ne ba na iya yin yadda nake yi dā a hidimar Jehobah.”
Zbigniew ya ce: “Da shigewar shekaru, ciwon sanyin ƙashi ya sa ni gajiya kuma yana halaka gaɓa na ɗaya bayan ɗaya. A wani lokaci sa’ad da ciwon ya yi tsanani, ba na iya yin ko aiki mafi sauƙi ma. Hakan ya sa ni sanyin gwiwa.”
A ’yan shekaru da suka shige, an gano cewa Barbara tana da ciwon daji na ƙwaƙwalwa. Ta ce: “Yanayin jiki na ya ci gaba da canjawa. Ina jin ba ni da ƙarfi da kuma ciwon kai a ko da yaushe kuma ina da matsalar rashin mai da hankali. Domin wannan sabon kasawa da nake fuskanta, ina bukata na sake tsara ayyuka na.”
Dukan waɗannan mutane ne da suka keɓe kai ga Jehobah. A gare su, yin nufinsa ya fi muhimmanci. Sun dogara gabaki ɗaya ga Allah kuma sun amfana daga tallafawarsa.—Mis. 3:5, 6.
Ta Yaya Jehobah Yake Taimako?
Bai kamata mu riƙa tunani cewa rashin lafiya yana nuna rashin amincewar Allah ne a gare mu ba. (Mak. 3:33) Ka yi tunanin abin da Ayuba ya fuskanta duk da cewa shi “kamili ne, mutum mai-adalci” ne kuma. (Ayu. 1:8) Allah ba ya gwada mutane da mugunta. (Yaƙ. 1:13) Mun gāji dukan rashin lafiya, haɗe da mai tsanani da na motsin rai daga wurin iyayenmu na farko Adamu da Hauwa’u ne.—Rom. 5:12.
Jehobah da Yesu ba za su ƙyale masu adalci ba tare da taimako ba. (Zab. 34:15) Muna fahimtar cewa Allah shi ne ‘mafakarmu da marayarmu kuma’ musamman a lokatan da muke fuskantar yanayi mai wuya a rayuwa. (Zab. 91:2) Saboda haka, sa’ad da muke jimre wa yanayi mai wuya a rayuwa, mene ne zai taimake mu kasance da farin ciki?
Addu’a: Ta bin misalin bayin Allah masu aminci na zamanin dā, za ka iya zuba dukan nawayarka ga Ubanka na sama cikin addu’a. (Zab. 55:22) Ta yin hakan, za ka iya shaida “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka.” Wannan kwanciyar hankali “za ta tsare zukatanku da tunaninku.” (Filib. 4:6, 7) Ta wurin dogara ga Jehobah cikin addu’a, Magdalena ta iya jure da ciwonta mai raunanawa. Ta ce: “Gaya wa Jehobah damuwa ta ya kawo mini sauƙi kuma dawo mini da farin ciki na. Yanzu na fahimta sosai abin da yake nufi a dogara ga Allah kowacce rana.”—2 Kor. 1:3, 4.
Ta wurin amsa addu’o’inka, Jehobah zai iya ba ka ƙarfi ta wurin ruhunsa mai tsarki da Kalmarsa da kuma ’yan’uwancinmu na Kirista. Ba za ka zaci Jehobah ya cire cutarka ta mu’ujiza ba. Duk da haka, za ka iya dogara a gare shi ya ba ka hikima da kuma ƙarfin da kake bukata don ka jimre da kowacce wahala. (Mis. 2:7) Zai iya ƙarfafa ka, kuma ya ba ka “mafificin girman iko.”—2 Kor. 4:7.
Iyali: Yanayin ƙauna da juyayi a gida zai iya taimaka maka ka jure da ciwo. Ka tuna cewa ’yan’uwanka ƙaunatattu ma suna shan wahala. Za su iya jin ba su da mai taimako kamar kai. Duk da haka, su naka ne ko ma a lokatan wahala. Yin addu’a tare zai taimake ka ka kasance da zuciya mai lumana.—Mis. 14:30.
Barbara ta yi magana game da ’yarta da kuma wasu ’yan’uwa mata biyu matasa da suke cikin ikilisiya: “Suna tallafa mini a hidimar fage. Ƙwazonsu yana ƙarfafa ni kuma na sa ni farin ciki.” Zbigniew yana ɗaukan yadda matarsa take tallafa masa da tamani sosai. “Tana yin yawancin aikace-aikacen gida. Tana kuma taimaka mini na yi shiri kuma sau da yawa tana ɗaukan jakata zuwa tarurrukan Kirista da kuma a hidima.”
’Yan’uwa masu bi: Sa’ad da muke tare da ’yan’uwanmu masu bi, suna ƙarfafa mu da kuma yi mana ta’aziyya. Idan ba za ka iya halartan taro domin rashin lafiya kuma fa? Magdalena ta ce: “Ikilisiyar ta tabbata cewa ina amfana daga tarurruka ta wajen ɗaukan jawaban a tef. Sau da yawa ’yan’uwa masu bi suna kira a waya don su ga yadda za su taimaka mini. Suna kuma rubuta mini wasiƙu masu ban ƙarfafa. Da yake suna tunawa da ni kuma suna damuwa da zaman lafiyata yana taimaka mini na jimre.”
Izabela, wadda take ciwon baƙin ciki, ta ce: “A cikin ikilisiya ina da ‘mahaifi’ da ‘mahaifiya,’ masu yawa waɗanda suke saurara ta da kuma ƙoƙari su fahimce ni. Ikilisiyar ita ce iyalita, a nan ne nake samun salama da farin ciki.”
Yana da kyau waɗanda suke shan wahala dabam-dabam su guji ‘ware kansu.’ Maimakon haka, suna ɗaukan cuɗanyarsu da ikilisiya da tamani. (Mis. 18:1) Ta hakan suna zama tushen ƙarfafa sosai ga mutane. Da farko kana iya yin jinkirin gaya wa ’yan’uwa bukatunka. Amma, ’yan’uwanka masu bi za su yi farin ciki idan ka gaya musu kai tsaye. Zai ba su zarafin nuna “sahihiyar ƙauna ta ’yan’uwa.” (1 Bit. 1:22) Ka gaya musu kana bukata a kai ka taro kuma za ka so ka fita hidimar fage tare da su ko kuma tattaunawa mai ban ƙarfafa. Hakika, bai kamata mu zama masu yawan bukatar taimako ba amma muna nuna godiya don taimakonsu.
Ka kasance da ra’ayi mai kyau: Sau da yawa ya rage naka ne ko za ka ci gaba da farin ciki yayin da kake jimrewa da rashin lafiya mai tsanani. Halin baƙin ciki zai iya kai ga mugun tunani. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ruhun mutum ya kan jimre da cutarsa: Amma ruhun da ya karai wa za ya ɗora shi?”—Mis. 18:14.
Magdalena ta ce: “Ina yin ƙoƙari sosai na guji mai da hankali ga matsaloli na. Ina ƙoƙari na ji daɗin kwanaki da na ɗan samu sauƙi. Ina samun ƙarfafa ta wajen karanta labaran rayuwa na mutane da suka kasance da aminci duk da rashin lafiya mai tsanani.” Izabela tana samun ƙarfafa da ra’ayin cewa Jehobah yana ƙaunarta da kuma ɗaukanta da tamani. Ta ce: “Na ji kamar ana bukata ta, kuma ina da amfani ga wani a rayuwa. Kuma ina da bege mai ban al’ajabi a nan gaba.”
Zbigniew ya ce: “Rashin lafiyana ya koya mini tawali’u da biyayya. Yana koya mini na nuna basira da sanin ya kamata da kuma gafarta wa mutane da dukan zuciyata. Na koya na ji daɗin bauta wa Jehobah ba tare da jin tausayin kaina ba. Hakika, hakan ya motsa ni na ci gaba da samun ci gaba a ruhaniya.”
Ka tuna cewa Jehobah yana lura da jimirinka. Yana jin tausayinka kuma yana kula da kai. Bai zai “manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa” ba. (Ibran. 6:10) Ka tuna da alkawarin da ya yi wa dukan waɗanda suke jin tsoronsa: “Daɗai ba ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba.”—Ibran. 13:5.
Idan a wani lokaci kana sanyin gwiwa, ka mai da hankali ga bege mai ban al’ajabi na zama a sabuwar duniya. Lokaci yana kusatowa sosai sa’ad da idanunka za su ga albarka ta Mulkin Allah a duniya!
[Akwati/Hotona a shafi na 28]
Sun Ci Gaba da Yin Wa’azi Duk da Rashin Lafiya Mai Tsanani
“Ba na iya tafiya da kaina, saboda haka matata ko wasu ’yan’uwa suna bi na a hidima. Nakan haddace gabatarwa da zan yi a hidima da kuma nassosin Littafi Mai Tsarki.”—Jerzy, ba ya gani sosai.
“Ƙari ga yin wa’azi da tarho, ina rubuta wasiƙu a kai a kai ga kalilan waɗanda suke son saƙonmu. Sa’ad da nake asibiti, a ko da yaushe ina ajiye Littafi Mai Tsarki da littattafan Shaidun Jehobah kusa da gadona. Hakan ya taimaka mini na soma tattaunawa da mutane da yawa.”—Magdalena, wadda aka gano cewa tana da wata cuta mai suna systemic lupus erythematosus, wata cuta da ke yaƙar garkuwar jiki.
“Ina son hidima ta ƙofa ƙofa, amma sa’ad da ba na jin daɗi, ina yin wa’azi ta waya.”—Izabela, wadda take ciwon baƙin ciki.
“Ina jin daɗin koma ziyara da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki. A ranakun da na ɗan samu sauƙi, Ina wa’azi gida gida.”—Barbara, wadda take da ciwon daji na ƙwaƙwalwa.
“Ina ɗaukan jakar wa’azi marar nauyi. Ina zuwa wa’azi yawan yadda gaɓoɓina suka ƙyale ni.”—Zbigniew, wanda yake ciwon sanyin ƙashi.
[Hoto a shafi na 30]
Matasa da tsofaffi za su zama tushen ƙarfafa