Hassada—Hali Ne da Zai Iya Ɓata Zuciyarmu
Napoleon Bonaparte ya yi hassada. Julius Ceasar ya yi hassada. Iskandari Mai Girma ya yi hassada. Duk da cewa suna da iko kuma sanannu ne, waɗannan mutane suna da abu a zuciyarsu da yake kamar guba da za ta iya ɓata zuciyar mutum. Su uku sun yi hassadar wani.
Bertrand Russell, ɗan falsafa na Turanci ya rubuta, “Napoleon ya yi hassadar Caesar, Caesar ya yi hassadar Iskandari Mai Girma kuma Iskandari ya yi hassadar Hercules, wanda bai taɓa wanzuwa ba.” Kowane mutum yana iya yin hassada, har ma mawadaci da mai iyawa da kuma mai nasara a rayuwa.
Mene ne hassada take nufi? Tana nufin ƙin wasu saboda dukiyarsu da kuɗi da albarka da kuma wasu abubuwan da suke da shi. Wani aikin bincike na Littafi Mai Tsarki da aka yi ya ce: “Kishi son samun abin da wani yake da shi ne, amma hassada son ƙwace abin da wani yake da shi ne.” Mutum mai hassada yana kishin abin da wasu mutane suke da shi kuma yana son ya ƙwace shi daga wajensu.
Yana da kyau mu yi tunani a kan yadda za mu iya zama masu hassada da kuma sakamakon yin hakan. Muna bukatar musamman mu san abin da za mu yi don kada hassada ta sarrafa rayuwarmu.
HALIN DA ZAI IYA SA HASSADA TA ƘARU
Ko da yake ’yan Adam ajizai suna da halin “hassada,” abubuwa dabam dabam suna iya sa a kasance da wannan halin. (Yaƙ. 4:5, NW) Manzo Bulus ya gaya mana game da ɗaya cikin su sa’ad da ya rubuta: “Kada ku zama masu girman kai da masu neman suna kuna cakunan juna, kuna [hassadar] juna kuma.” (Gal. 5:26) Halin son mu nuna cewa mun fi wasu zai iya sa halinmu marar kyau na yin hassada ya ƙaru sosai. Kiristoci biyu masu suna Cristina da Joséa sun koya cewa hakan gaskiya ne.
Wata majagaba na kullum mai suna Cristina, ta ce: “Sau da yawa nakan tsinci kaina ina hassadar wasu mutane. Nakan gwada abin da suke da shi da abin da ba ni da shi.” Akwai wata rana da Cristina take cin abinci tare da wasu ma’aurata da suke hidimar masu kula masu ziyara. Da yake ta san cewa ita da mijinta, Eric da mai kula mai ziyara da matarsa tsara ne kuma a dā suna da gata iri ɗaya, sai Cristina ta ce: “Mijina ma dattijo ne! Ta yaya kuke aikin ziyara kuma mu ba kome ba ne?” Halin son ta fi wasu ya sa ta yin hassada kuma ta manta da aiki mai kyau da ita da mijinta suke yi kuma hakan ya sa ba ta farin ciki a rayuwa.
José yana son ya zama bawa mai hidima a cikin ikilisiyarsu. Sa’ad da aka naɗa wasu amma ba a naɗa shi ba, sai ya soma hassadarsu da kuma fushi da mai tsara ayyukan rukunin dattawansu. “Hassada ta sa na tsane wannan dattijon da kuma tunani cewa wannan ɗan’uwan ba ya son na samu gata a cikin ikilisiyar,” in ji José. Idan hassada ta soma ja-gorar rayuwarka, za ka zama mai son kai kuma ba za ka yi tunani da kyau ba.”
ABIN DA MISALAN NASSI SUKA KOYA MANA
Da akwai misalai na gargaɗi da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki. (1 Kor. 10:11) Wasu cikin waɗannan sun nuna yadda ake soma hassada da kuma yadda za ta zama kamar guba a rayuwar waɗanda suka ƙyale ta ta sha kansu.
Alal misali, Kayinu ɗan fari na Adamu da Hauwa’u ya yi fushi domin Jehobah ya amince da hadayar Habila amma ya ƙi da nasa. Da Kayinu ya zaɓa ya yi abin da ya dace, amma hassada ta sha kansa har ya kashe ƙanensa. (Far. 4:4-8) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Kayinu “wanda yake na Mugun” Shaiɗan ne!—1 Yoh. 3:12.
’Yan’uwan Yusufu goma sun yi hassadar dangantaka na musamman da yake da shi da babansu. Sun ƙara tsane Yusufu sa’ad da ya gaya musu game da mafarkin annabci da ya yi. Sun ma so su kashe shi. A ƙarshe, suka sayar da shi a matsayin bawa kuma suka yi wa babansu ƙarya cewa Yusufu ya mutu. (Far. 37:4-11, 23-28, 31-33) Bayan shekaru da yawa, sun amince cewa sun yi zunubi kuma suka gaya wa juna: “Hakika mu masu-laifi ne wajen ɗan’uwanmu, da shi ke mun ga azabar ransa, sa’anda ya roƙe mu, mu kuwa muka ƙi ji.”—Far. 42:21; 50:15-19.
Kora da Datan da Abiram sun yi hassada sa’ad da suka gwada gatansu da na Musa da kuma na Haruna. Sun zargi Musa cewa yana ƙoƙarin ‘mai da kansa sarki’ da kuma ɗaga kansa fiye da wasu. (Lit. Lis. 16:13) Hakan ba gaskiya ba ne. (Lit. Lis. 11:14, 15) Jehobah ne da kansa ya naɗa Musa. Amma waɗannan ’yan tawaye sun yi hassadar matsayin Musa. A ƙarshe Jehobah ya halaka su domin hassadarsu.—Zab. 106:16, 17.
Sarki Sulemanu ya ga miyagun ayyuka da hassada za ta sa mutane su yi. Wata mata da jaririnta ya rasu ta yi ƙoƙari ta sa wata mata ta gaskata cewa jaririn matar ne ya rasu. Sa’ad da ake ƙoƙari a warware batun, maƙaryaciyar ta yarda a kashe jaririn. Amma Sulemanu ya tabbata cewa an ba da jaririn ga ainihin mahaifiyarsa.—1 Sar. 3:16-27.
Hassada tana da mugun sakamako. Misalan Littafi Mai Tsarki da aka ambata sun nuna cewa tana iya jawo ƙiyayya da rashin adalci da kuma kisan kai. Bugu da ƙari, a kowanne cikin wannan labarin da muka tattauna, wanda ake yin hassadarsa bai yi laifi ba. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu tabbata cewa hassada ba ta mamaye rayuwarmu ba?
HANYOYI MASU KYAU NA MAGANCE HASSADA!
Ka ƙaunaci ’yan’uwanka. Manzo Bitrus ya gargaɗi Kiristoci: “Da ya ke kun tsarkake rayukanku cikin biyayyarku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar ƙauna ta ’yan’uwa, sai ku yi ƙaunar junanku daga zuciya mai-gaskiya.” (1 Bit. 1:22) Mene ne ƙauna? Manzo Bulus ya rubuta: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi; ƙauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta.” (1 Kor. 13:4, 5) Idan muna nuna irin wannan ƙaunar ga mutane, zai hana mu kasancewa da halin yin hassada. (1 Bit. 2:1) Maimakon Jonathan ya yi hassadar Dauda, “ya ƙaunace shi kamar ransa.”—1 Sam. 18:1.
Ka yi cuɗanya da masu bauta wa Allah. Marubucin Zabura ta 73 ya yi hassadar miyagu waɗanda suke jin daɗin rayuwarsu kuma suke kamar ba su da matsaloli. Amma, ya daina wannan hassadar ta wajen shiga “wuri mai-tsarki na Allah.” (Zab. 73:3-5, 17) Yin cuɗanya da ’yan’uwa masu bauta wa Allah ya taimaka wa marubucin wannan zabura ya fahimci albarka da ya samu ta wurin ‘kusantar Allah.’ (Zab. 73:28) Mu ma za mu iya amfana ta wurin yin tarayya a kai a kai da ’yan’uwanmu a tarurrukanmu na Kirista.
Ka nemi hanyoyin yin nagargarun ayyuka. Sa’ad da Allah ya lura da hassada da kishi da Kayinu ya yi, ya gaya masa ya koma ga yin nagarta. (Far. 4:7) Mene ne yin nagarta yake nufi ga Kiristoci? Yesu ya ce dole mu ‘yi ƙaunar Ubangiji Allahnmu da dukan zuciyarmu da dukan ranmu da dukan azancinmu, kuma mu yi ƙaunar maƙwabcinmu kamar ranmu.’ (Mat. 22:37-39) Sa’ad da bauta wa Jehobah da kuma taimaka wa mutane ne ya fi muhimmanci a rayuwarmu hakan zai taimaka mana mu kawar da hassada. Yin wa’azi na Mulkin da almajirtarwa sosai hanya ce mai kyau na bauta wa Allah da kuma taimaka wa maƙwabtanmu, kuma hakan zai sa mu sami “albarkar Ubangiji.”—Mis. 10:22.
“Ku yi farin zuciya tare da waɗanda ke farin zuciya.” (Rom. 12:15) Yesu ya yi farin ciki sa’ad da almajiransa suka sami sakamako mai kyau a hidimarsu, kuma ya ce za su yi fiye da abin da ya cim ma a aikin wa’azi. (Luk 10:17, 21; Yoh. 14:12) Mutanen Jehobah suna da haɗin kai, kuma idan an cim ma abu mai kyau muna farin ciki tare. (1 Kor. 12:25, 26) Ya kamata hakan ya sa mu yi farin ciki maimakon yin kishi sa’ad da wasu suka samu ƙarin gata.
BA SHI DA SAUƘI A KAWAR DA HASSADA!
Za mu ci gaba da yin ƙoƙari don mu kawar da hassada. Cristina ta ce: “Har ila ina da halin yin hassada sosai. Ko da yake ba na son halin, na ci gaba da kame kaina.” Hakan ma ya faru da José. Ya ce: “Jehobah ya taimaka mini na lura da halaye masu kyau na mai tsara ayyukan rukunin dattawanmu. Dangantaka mai kyau da Allah ne ya taimaka mini.”
Yin hassada ɗaya ne cikin “ayyukan jiki” da ya kamata Kiristoci su guji. (Gal. 5:19-21) Idan mun ƙi yin hassada, za mu yi farin ciki kuma hakan zai faranta wa Ubanmu na sama, wato, Jehobah rai.
[Hasiya]
a An canja sunayen.
[Bayanin da ke shafi na 17]
“Ku yi farin zuciya tare da waɗanda ke farin zuciya.”