Ka Yi Farin Ciki Don Begenmu
“[Akwai] bege na rai marar matuƙa, wanda Allah, da ba ya iya yin ƙarya, ya alkawarta tun gaban madawwaman zamanu.”—TIT. 1:2.
BITA
․․․․․
Yaya muka san cewa ana farin ciki a sama sa’ad da shafaffe guda ya kasance da aminci har mutuwa?
․․․․․
Yaya begen waɗansu tumaki yake da nasaba da na shafaffu?
․․․․․
Idan muna son begenmu ya kasance da gaske, waɗanne “tasarrufi mai-tsarki” da ayyukan “ibada” ne ya kamata mu kasance da su?
1. Ta yaya begen da Jehobah ya ba mu zai taimaka mana mu jimre?
MANZO Bulus ya ce, Jehobah, ‘Allah na bege ya cika mu da dukan farin zuciya da salama cikin bada gaskiya, domin mu yalwata cikin bege, cikin ikon Ruhu Mai-tsarki.’ (Rom. 15:13) Idan muna da bege sosai, za mu iya jimrewa da kowane irin yanayin da muke fuskanta, kuma za mu ci gaba da yin farin ciki da salama. Wannan begen zai zama “anka (anchor) na rai, tabbatacen bege mai-tsayawa mai-shiga” ga Kiristoci shafaffu da kuma waɗansu tumaki. (Ibran. 6:18, 19) Sa’ad da muke fuskantar matsaloli a rayuwa, begenmu zai taimaka mana mu yi tsayin daka kuma kada mu yi shakka ko rasa bangaskiyarmu.—Karanta Ibraniyawa 2:1; 6:11.
2. Waɗanne bege biyu ne Kiristoci suke da shi kuma yaya “waɗansu tumaki” za su amfana daga begen da shafaffu suke da shi?
2 Kiristocin da suke rayuwa a wannan kwanaki na ƙarshe suna da ɗaya cikin bege biyu da Kiristoci suke da shi. “Ƙaramin garke” da suka rage a duniya yau suna da begen zuwa sama don yin rayuwa har abada. Kuma za su zama sarakuna da firistoci tare da Kristi a Mulkinsa. (Luk 12:32; R. Yoh. 5:9, 10) “Taro mai girma” da “waɗansu tumaki” suna da begen yin rayuwa a cikin aljanna a duniya har abada, a ƙarƙashin Mulkin Almasihu. (R. Yoh. 7:9, 10; Yoh. 10:16) Ya kamata waɗansu tumaki su tuna cewa za su samu ceto idan sun goyi bayan “’yan’uwan” Yesu shafaffu da suka rage a duniya. (Mat. 25:34-40) Za a ba shafaffu da kuma waɗansu tumaki ladarsu. (Karanta Ibraniyawa 11:39, 40.) Bari mu fara tattauna begen da shafaffu suke da shi.
‘BEGE MAI RAI’ DA KIRISTOCI SHAFAFFU SUKE DA SHI
3, 4. Ta yaya Jehobah ya ba Kiristoci shafaffu ‘maya haihuwarmu bisa bege mai rai,’ kuma mene ne wannan begen?
3 Manzo Bitrus ya rubuta wa Kiristoci shafaffu wasiƙu biyu. Kuma a cikin wannan ya kira su “zaɓaɓu.” (1 Bit. 1:1) Ya bayyana begen da ƙaramin garke suke da shi dalla-dalla. A wasiƙarsa ta farko, Bitrus ya rubuta: “Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, wanda ya maya haihuwarmu bisa ga jinƙansa mai-girma zuwa bege mai-rai ta wurin tashin Yesu Kristi daga matattu, zuwa gādo marar-ruɓewa, marar-ƙazantuwa, wanda ba shi yanƙwanewa, ajiyayye a sama dominku, cikin wannan kuna murna dayawa.”—1 Bit. 1:3-6.
4 An “maya haihuwar” waɗannan Kiristoci da Jehobah ya zaɓa don su yi sarauta tare da Kristi a Mulkin sama a matsayin ’ya’yan Allah shafaffu. An shafa su da ruhu mai tsarki don su zama sarakuna da firistoci tare da Kristi. (R. Yoh. 20:6) Bitrus ya bayyana cewa wannan “maya haihuwar” ya sa su samu “bege mai-rai,” wanda ya kira “marar-ruɓewa, marar-ƙazantuwa, wanda ba shi yanƙwanewa, ajiyayye a sama” dominsu. Shi ya sa shafaffu suke ‘murna’ sosai don begensu. Amma suna bukatar su kasance da aminci, don su samu cikar wannan begen.
5, 6. Me ya sa ya kamata Kiristoci shafaffu su yi iya ƙoƙarinsu don su samu ladarsu na zuwa sama?
5 A wasiƙarsa ta biyu, Bitrus ya gargaɗi shafaffu Kiristoci su ‘daɗa bada anniya garin su tabbatar da kiransu da zaɓensu.’ (2 Bit. 1:10) Wajibi ne su yi ƙoƙari sosai don su samu halaye masu kyau kamar su bangaskiya da ibada da son ’yan’uwa da kuma ƙauna. Bitrus ya ce: “Idan waɗannan abu naku ne, suna kuwa yawaita, su za su hana ku zama raggaye ko kuwa marasa-amfani.”—Karanta 2 Bitrus 1:5-8.
6 Sa’ad da Yesu wanda ya tashi daga matattu ya rubuta wasiƙa a ƙarni na farko zuwa ga dattawan da ke ikilisiyar Filadalfiya, a Asiya Ƙarama, ya ce: “Tun da ka kiyaye maganar haƙurina, ni ma zan kiyaye ka daga sa’ar jaraba, wannan da ke zuwa bisa ga dukan duniya, domin a jarabci mazaunan duniya. Ina zuwa da sauri: ka riƙe abin da ka ke da shi da kyau, domin kada kowa shi amshi rawaninka.” (R. Yoh. 3:10, 11) Idan Kirista shafaffe ya rasa amincinsa, ba zai samu “rawanin daraja” da aka yi alkawarinsa ga zaɓaɓɓun da suka kasance da aminci har mutuwa ba.—1 Bit. 5:4; R. Yoh. 2:10.
SHIGAN MULKIN ALLAH
7. Wane bege ne Yahuda ya bayyana a wasiƙarsa?
7 A misalin shekara ta 65 K.Z., Yahuda ɗan’uwan Yesu ya rubuta wasiƙa ga ’yan’uwansa Kiristoci shafaffu waɗanda ya kira, “kirayayyu.” (Yahu. 1; gwada Ibraniyawa 3:1.) Ya yi niyyar rubuta musu wasiƙa da ta yi magana game da begen samun ceto da Kiristocin da za su je sama suke da shi. (Yahu. 3) Yahuda yana da wasu batutuwa masu muhimmanci sosai da zai yi magana a kansu. Amma a ƙarshen gajeriyar wasiƙar da ya rubuta, ya bayyana abin da ke gaba game da begen da Kiristoci shafaffu suke da shi: “Yanzu ga wanda yana da iko ya tsare ku daga yin tuntuɓe, ya sanya ku marasa-aibi cikin mafificin farinzuciya a gaban bayyanuwar darajarsa, ga Allah Makaɗaici Mai-cetonmu, ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu, daraja, da ɗaukaka, da mulki da iko, tun gaban zamanai duka, da yanzu kuma, har abada abadin.”—Yahu. 24, 25.
8. Yaya littafin Yahuda 24 ya nuna cewa ana matuƙar farin ciki a sama sa’ad da shafaffe guda ya kasance da aminci har mutuwa?
8 Ya kamata Kiristoci shafaffu su yi hankali don kada su rasa amincinsu, kuma a sakamako a halaka su. Suna begen cewa Yesu zai ta da su daga matattu a matsayin ruhu kamiltattu. Sa’ad da shafaffe mai aminci guda ya rasu, yana da begen ‘tashi cikin jiki mai-ruhaniya,’ da “cikin rashin ruɓa” da kuma “cikin iko.” (1 Kor. 15:42-44) Idan ana “murna cikin sama bisa mai-zunubi guda ɗaya wanda ya tuba,” babu shakka za a yi matuƙar farin ciki a cikin sama sa’ad da shafaffe guda ya kasance da aminci har mutuwa. (Luk 15:7) Kamar yadda Yahuda ya faɗa, ana “mafificin farin zuciya” a sama, sa’ad da shafaffe ya samu ladarsa.—Karanta 1 Yohanna 3:2.
9. Ta yaya ake ba shafaffu masu aminci shiga “mai-yalwa” zuwa Mulkin, kuma yaya hakan ya shafe shafaffun da suka rage a duniya?
9 Bitrus ya kuma rubuta cewa idan Kiristoci shafaffu suka kasance da aminci, za su samu shiga “mai-yalwa zuwa cikin madawwamin mulki na Ubangijinmu da Mai-cetonmu Yesu Kristi.” (2 Bit. 1:10, 11) Sa’ad da Bitrus ya faɗa cewa za su samu shiga “mai-yalwa,” yana nufin cewa za su shiga cikin sama da ɗaukaka. Ko kuma yana magana a kan albarka mai yawa da za a ba su a cikin sama. Za su tuna cewa sun kasance da aminci har mutuwa, kuma hakan zai faranta su sosai. Babu shakka, wannan begen yana ƙarfafa shafaffun da suka rage a duniya, kuma yana sa su ‘yi ɗamara, su natsu,’ kuma.—1 Bit. 1:13.
BEGEN DA WAƊANSU TUMAKI SUKE DA SHI
10, 11. (a) Wane bege ne waɗansu tumaki suke da shi? (b) Ta yaya wannan begen ya shafi Kristi da kuma “bayyanuwar ’ya’yan Allah”?
10 Manzo Bulus ya rubuta wa shafaffu “’ya’yan Allah,” game da begen da suke da shi na zaman “masu-tarayyan gādo” da Kristi. Sai kuma ya rubuta game da begen da waɗansu tumaki suke da shi, ya ce: “Gama begen talikai [’yan Adam] yana sauraron bayyanuwar ’ya’yan Allah [shafaffu]. Gama aka ƙasƙantar da talikai zuwa banza, ba da yardar kansu ba, amma sanadin shi wanda ya sanya su, ana bege halitta da kanta kuma za ta tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yancin darajar ’ya’yan Allah.”—Rom. 8:14-21.
11 Jehobah ne ya ba ’yan Adam dalilin “bege,” sa’ad da ya yi musu alkawari cewa zai cece su daga “tsohon macijin,” wato, Shaiɗan Iblis, ta hannun “zuriyar” da aka yi alkawarinsa. (R. Yoh. 12:9; Far. 3:15) Yesu Kristi ne wannan “zuriyar.” (Gal. 3:16) Ta wajen mutuwarsa da kuma tashinsa daga matattu, Yesu ya sa ’yan Adam su kasance da bege cewa za a ’yantar da su daga bautar ɓacewa na zunubi da kuma mutuwa. Za su soma ganin sakamakon wannan begen sa’ad da “’ya’yan Allah” suka bayyana. Shafaffu da aka ɗaukaka ne sashe na biyu na wannan zuriyarar. Hanya ɗaya da waɗannan shafaffu za su ‘bayyana’ ita ce sa’ad da suka goyi bayan Yesu wajen halaka wannan mugun zamani na Shaiɗan. (R. Yoh. 2:26, 27) A sakamako, za a ceci waɗansu tumaki da suka fito daga ƙunci mai girma.—R. Yoh. 7:9, 10, 14.
12. Wane amfani ne ’yan Adam za su samu daga bayyanuwar shafaffu?
12 Shekara dubu da Yesu zai yi sarauta zai sa ’yan Adam su samu ’yanci sosai. A wannan lokacin, “’ya’yan Allah” za su bayyana a wata hanya. Za su yi hidima a matsayin firistoci da Kristi, kuma za su taimaki ’yan Adam su more amfanin fansa ta Yesu. ’Yan Adam masu biyayya za su “tsira daga bautar ɓacewa,” sa’ad da Mulki Allah ta yi sarauta bisa duniya. Za su samu ’yanci daga sakamakon zunubi da kuma mutuwa. Idan sun kasance da aminci a Shekara Dubu ta Sarautar Yesu da kuma gwaji na ƙarshe da za a yi a ƙarshen shekara dubun, za a rubuta sunayensu a cikin “littafin rai” a dindindin. Za su samu “’yancin darajar ’ya’yan Allah.” (R. Yoh. 20:7, 8, 11, 12) Wannan bege ne na musamman.
YADDA ZA MU CI GABA DA KASANCEWA DA BEGE
13. Me ya sa begenmu tabbatacce ne, kuma a wane lokaci ne Yesu zai bayyana?
13 Abubuwan da Bitrus ya rubuta a cikin wasiƙunsa biyu sun taimaka wa shafaffu da waɗansu tumaki su kasance da bege. Ya bayyana cewa begensu ba domin ayyukansu ba ne, amma domin alherin Jehobah ne. Ya rubuta: “Ku sa zuciyarku sosai kan alherin da zai zo muku a bayyanar Yesu Almasihu.” (1 Bit. 1:13, Littafi Mai Tsarki) Yesu zai bayyana, sa’ad da zai bayyana don ya ba mabiyansa masu aminci lada kuma ya zartar da hukuncin Jehobah a kan miyagun mutane.—Karanta 2 Tasalonikawa 1:6-10.
14, 15. (a) Mene ne ya kamata mu yi don mu ci gaba da kasancewa da bege? (b) Wane gargaɗi ne Bitrus ya bayar?
14 Domin mu ci gaba da kasancewa da wannan begen, wajibi ne mu tuna cewa “ranar” Jehobah za ta zo nan ba da daɗewa ba. Kuma ya kamata wannan ra’ayin ya shafe mu. Jehobah zai halaka “sammai,” wato, mulkin ’yan Adam da kuma “duniya,” wato, miyagun mutane da kuma ‘dukkan abin da ke cikinsu.’ Bitrus ya rubuta: “Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama . . . kuna sauraron ranar Allah, kuna kuwa marmarin zuwanta ƙwarai; bisa ga zuwanta kuwa sammai da suke cin wuta za su narke, rundunan kuma za su narke da ƙuna mai-zafi.”—2 Bit. 3:10-12.
15 Za a sauya “sammai,” wato, mulkin ’yan Adam da “sababbin sammai,” wato, Mulkin da Kristi zai yi sarauta. Kuma za a sauya “duniya,” wato, miyagun mutane da “sabuwar duniya,” wato, mutane masu aminci ga Jehobah. (2 Bit. 3:13) Bayan haka, Bitrus ya ba da wani gargaɗi kai tsaye game da “sauraron” ko kuma kasancewa da bege cewa za mu gāji sabuwar duniya. Ya ce: “Domin wannan, ƙaunatattu, tun da kuke sauraron waɗannan al’amura, sai ku ba da anniya a tarar da ku cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi a gabansa.”—2 Bit. 3:14.
YIN RAYUWAR DA TA JITU DA BEGENMU
16, 17. (a) Waɗanne “tasarrufi mai-tsarki” da ayyukan “ibada” ne ya kamata mu kasance da su? (b) Yaya za mu samu sakamakon begenmu?
16 Muna bukatar mu ci gaba da kasancewa da bege da kuma yin rayuwa da ta jitu da begenmu. Ya kamata mu tabbata cewa muna bauta wa Jehobah yadda yake so. “Tasarrufi mai-tsarki” ya haɗa da yin ayyukan da suka ‘dace wurin al’ummai,’ ta wurin kasancewa da hali mai kyau. (2 Bit. 3:11; 1 Bit. 2:12) Dole ne mu nuna ‘ƙauna ga junanmu.’ Yin hakan ya haɗa da yin iya ƙoƙarinmu don mu ci gaba da kasancewa da haɗin kai a ikilisiyoyinmu, da kuma a dukan duniya. (Yoh. 13:35) Ayyukan “ibada” suna nufin abubuwan da muke yi don mu ci gaba da kusantar Jehobah sosai. Hakan ya haɗa da yadda muke addu’a da karanta Littafi Mai Tsarki kullum da yin nazari mu kaɗai da nazarin iyalinmu da kuma yin wa’azin ‘bishara ta mulki’ da ƙwazo.—Mat. 24:14.
17 Ya kamata mu yi ayyuka masu kyau da za su sa ya cece mu sa’ad da zai halaka wannan mugun zamanin. Idan mun yi hakan, begenmu na “rai marar matuƙa, wanda Allah, da ba ya iya yin ƙarya, ya alkawarta tun gaban madawwaman zamanu,” zai kasance gaskiya a gare mu.—Tit. 1:2.
[Hoto a shafi na 22]
Kiristoci shafaffu suna ‘maya haihuwa zuwa bege mai-rai’
[Hoto a shafi na 24]
Ka sa iyalinka ta ci gaba da kasancewa da bege