Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 3/15 pp. 25-29
  • Kada Ka Kalli Abubuwan Da Ke “Baya”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Kalli Abubuwan Da Ke “Baya”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • RA’AYIN CEWA ZAMANIN DĀ YA FI NA YANZU
  • SADAUKARWAR DA MUKA YI A DĀ
  • ABUBUWA MARASA KYAU DA MUKA FUSKANTA A DĀ
  • Ka Mai da Hankali ga Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Mene ne Zama Mabiyin Yesu Ya Kunsa?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Ku Tuna da Matar Lutu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ku Tuna da Matar Lutu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 3/15 pp. 25-29

Kada Ka Kalli Abubuwan Da Ke “Baya”

“Kowane mutum wanda ya sa hannunsa ga keken noma, idan ya duba baya, ba ya cancanci mulkin Allah ba.”—LUK 9:62.

MECE CE AMSARKA?

․․․․․

Me ya sa ya kamata mu “tuna da matar Lutu”?

․․․․․

Waɗanne abubuwa uku ne ya kamata mu guje wa?

․․․․․

Yaya za mu samu ci gaba tare da ƙungiyar Jehobah?

1. Wane gargaɗi ne Yesu ya ba da, kuma wace tambaya ce za a amsa?

“KU TUNA da matar Lutu.” (Luk 17:32) Wannan gargaɗin da Yesu ya ba da fiye da shekara dubu biyu da suka gabata ya fi muhimmanci yanzu. Amma mene ne wannan kashedi na Yesu yake nufi? Yahudawa ne Yesu yake wa wannan maganar. Kuma ba sa bukatar ƙarin bayani domin sun san labarin matar Lutu sosai. Sa’ad da Jehobah ya ce Lutu da iyalinsa su fita daga birnin Saduma, ya ce kada su kalli baya. Amma matar Lutu ta yi rashin biyayya kuma ta zama umudin gishiri.—Karanta Farawa 19:17, 26.

2. Mene ne wataƙila ya sa matar Lutu ta kalli baya, kuma mene ne sakamakon hakan?

2 Amma mene ne ya sa matar Lutu ta kalli baya? Shin ta kalli baya ne don ta san abin da ke faruwa? Ko kuwa rashin bangaskiya ce ta sa ta kalli baya? Ko dai tana sha’awar dukan abubuwan da ta bar a birnin Saduma ne? (Luk 17:31) Ko da mene ne ya sa ta kalli baya, ta mutu a sakamakon rashin biyayyar da ta yi. Ka yi tunani a kan wannan yanayin sosai. Ta mutu a ranar da Jehobah ya halaka miyagun mutanen da ke birnin Saduma da Gumrata. Shi ya sa Yesu ya ce: “Ku tuna da matar Lutu.”

3. Ta yaya Yesu ya nanata cewa kada mu kalli abubuwan da ke baya?

3 Mu ma muna rayuwa a kwanakin da bai kamata mu kalli abubuwan da ke baya ba. Yesu ya nanata wannan sosai sa’ad da yake amsa mutumin da ya ce yana son ya koma wurin iyalinsa domin ya musu ban kwana kafin ya zama almajirin Yesu. Yesu ya ce: “Kowane mutum wanda ya sa hannunsa ga keken noma, idan ya duba baya, ba ya cancanci mulkin Allah ba.” (Luk 9:62) Shin yadda Yesu ya amsa wannan mutumin bai dace ba? Ya dace, gama ya san cewa mutumin yana neman hujja ne kawai, don kada ya zama almajirin Yesu. Yesu ya kwatanta irin wannan hujjar da kallon abubuwan da ke “baya.” Mutumin da ke huɗa a gona zai iya kallon baya na ɗan lokaci ko kuma ya ajiye garmar a ƙasa kuma ya kalli baya. Yin hakan zai janye hankalinsa daga abin da yake yi, kuma ba zai yi aikinsa ba.

4. Ya kamata mu mai da hankalinmu ga mene ne?

4 Ya kamata mu mai da hankali ga nan gaba, ba ga abin da ya faru a dā ba. Ka lura da yadda aka bayyana hakan sarai a littafin Misalai 4:25: “Bari idanunka su duba gaba sosai, Maƙibtanka kuma su tafi rankai.”

5. Me ya sa bai kamata mu kalli abubuwan da ke baya ba?

5 Akwai dalili mai kyau da ya sa bai kamata mu kalli abubuwan da ke baya ba. Hakan yana da muhimmanci domin, muna “cikin kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1) Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai halaka ba kawai birane biyu ba, amma wannan mugun zamanin gabaki ɗaya. Mene ne zai taimaka mana don kada mu zama kamar matar Lutu? Da farko, ya kamata mu san abubuwan da ke bayanmu da bai kamata mu kalla ba. (2 Kor. 2:11) Yanzu, bari mu tattauna waɗannan abubuwan kuma mu san yadda za mu iya guje musu.

RA’AYIN CEWA ZAMANIN DĀ YA FI NA YANZU

6. Me ya sa tunaninmu ba ya yawan yin daidai?

6 Za mu iya yin kuskure cewa rayuwa a dā ta fi na yanzu kyau. Yadda ƙwaƙwalwarmu take sa mu tuna da abubuwan da suka faru a dā, ba ta yawan yin daidai. Muna iya jin cewa matsalolin da muke da su a dā ba su kai na yanzu ba. Kuma muna iya yin tunani cewa rayuwa ta fi daɗi a dā. Wannan tunanin da bai yi daidai ba, zai iya sa mu soma marmarin yanayinmu na dā. Amma Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Kada ka tambaya, don me kwanakin dā sun fi na yanzu kyau? Gama ba da hikima ka ke binciken wannan ba.” (M. Wa. 7:10) Me ya sa irin wannan tunanin yake da haɗari sosai?

7-9. (a) Mene ne ya faru da Isra’ilawa a ƙasar Masar? (b) Mene ne ya sa ya kamata Isra’ilawa su yi farin ciki? (c) Mene ne ya sa Isra’ilawa suka soma gunaguni?

7 Ka yi la’akari da abin da ya faru da Isra’ilawa a zamanin Musa. Sa’ad da Isra’ilawa suka fara zuwa ƙasar Masar, suna ɗaukansu a matsayin baƙi, amma bayan zamanin Yusufu, suka mai da Isra’ilawa “shugabanni na gandu a bisansu fa, waɗanda za su wulakanta su da nawayyansu.” (Fit. 1:11) Daga baya, Fir’auna ya ce a kashe dukan jarirai maza na Isra’ilawa, domin ba ya son su yi yawa. (Fit. 1:15, 16, 22) Shi ya sa Jehobah ya gaya wa Musa: “Hakika na ga ƙuncin mutanena waɗanda ke cikin Masar, na kuwa ji kukarsu saboda shugabanninsu na gandu; gama na san baƙinzuciyarsu.”—Fit. 3:7.

8 Ka yi tunanin irin matuƙar farin cikin da Isra’ilawa suka yi sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar, kuma suka samu ’yanci. Sun shaida sa’ad da Jehobah ya yi amfani da ikonsa wajen buga Fir’auna mai fahariya da kuma mutanensa da annoba. (Karanta Fitowa 6:1, 6, 7.) Daga baya, Masarawa suka ce wa Isra’ilawa su tafi, kuma suka ba su zinariya da azurfa da yawa. Kuma wannan baiwar zai iya sa a ce mutanen Allah sun “washe Masarawa.” (Fit. 12:33-36) Isra’ilawa sun kuma yi farin ciki sosai sa’ad da Jehobah ya halaka Fir’auna da rundunarsa a Jar Teku. (Fit. 14:30, 31) Babu shakka, ya kamata ganin wannan aukuwar ta ƙarfafa bangaskiyarsu sosai.

9 Amma abin mamaki, ba da daɗewa ba, bayan aka cece su, suka soma gunaguni. Gunaguni game da mene ne? Game da abinci. Ba su gamsu da abin da Jehobah ya ba su ba, kuma suka soma gunaguni. Suka ce: “Mun tuna da kifi da muka ci a banza a Masar; da su kurzunu, da kabewa, da albasa ƙanana da manya, da tafarnuwa: amma yanzu ranmu ya bushe sarai, ba mu da wani abu a nan, sai dai mu ga wannan manna kawai.” (Lit. Lis. 11:5, 6) Hakika sun manta da wahalar da suka sha a ƙasar Masar, kuma sun so su koma ƙasar. (Lit. Lis. 14:2-4) Isra’ilawa sun kalli abubuwan da suke baya, kuma sun yi rashin tagomashin Jehobah.—Lit. Lis. 11:10.

10. Wane darasi muka koya daga misalin Isra’ilawa?

10 Wane darasi muka koya daga wannan labarin? Sa’ad da muke fuskantar mawuyacin yanayi da kuma matsaloli, kada mu mai da hankalinmu ga abubuwan da muke ji cewa muna morewa a dā, wataƙila, kafin ma mu soma bauta wa Jehobah. Ko da yake ba laifi ba ne mu yi tunani game da abubuwan da suka faru a dā, da kuma abubuwan da muka mora. Amma ya kamata mu kasance da daidaita, kuma kada mu riƙa tunani cewa muna bala’in jin daɗi a dā. Idan ba haka ba, za mu soma ƙyamar yanayinmu kuma mu koma irin rayuwarmu ta dā.—Karanta 2 Bitrus 2:20-22.

SADAUKARWAR DA MUKA YI A DĀ

11. Yaya wasu suke ji game da sadaukarwar da suka yi a dā?

11 Abin baƙin ciki, wasu suna tunani game da sadaukarwa da suka yi a dā, kuma suna da-na-sani. Wataƙila ka taɓa samun zarafin shigan makarantar jami’a ko zaman shahararre ko kuma mai arziki sosai, amma ka ƙi waɗannan abubuwan. Wasu ’yan’uwa maza da mata a dā suna aikin da ake biyansu albashi mai tsoka sosai. Alal misali, suna yin sana’a ko waƙa ko kuma su farfesa ne a makarantun jami’a ko suna wasanni. Amma sun bar waɗannan ayyukan. An ɗan jima, kuma ƙarshe bai zo ba har yanzu. Shin kana tunanin irin wadatar da za ka samu, da a ce ba ka yi wannan sadaukarwa ba?

12. Yaya Bulus ya ji game da sadaukarwar da ya yi?

12 Manzo Bulus ya yi sadaukarwa sosai don ya zama mabiyin Yesu. (Filib. 3:4-6) Yaya ya ji game da wannan sadaukarwar da ya yi? Ya ce: “Duk da wannan abubuwan da su ke ribobi a gareni, waɗannan na lissafa su hasara sabili da Kristi.” Me ya sa? Ya ce: ‘Ina lissafta dukan abu hasara kuma bisa ga fifikon sanin Kristi Yesu Ubangijina: wanda na sha hasarar dukan abu sabili da shi, kamar kayan banza [shara] kuwa na ke maishe su, domin in ribato Kristi.’a (Filib. 3:7, 8) Mutum da ya zubar da shara a bola ba ya yin da-na-sani. Haka ma Bulus ya yi. Bai yi da-na-sani game da sadaukarwar da ya yi ba. Daga baya bai yi tunanin cewa suna da amfani sosai ba.

13, 14. Ta yaya za mu iya bin misalin Bulus?

13 Mene ne ya kamata mu yi idan muka ci gaba da yin tunani game da sadaukarwar da muka yi a dā? Ya kamata mu bi misalin Bulus. Ta yaya? Ka yi tunani game da abin da kake da shi yanzu. Kana da dangantaka na kud da kud da Jehobah kuma kana bauta masa da dukan zuciyarka. (Ibran. 6:10) Babu abin da duniyar nan za ta iya ba mu da za ta kai abubuwan da muke morewa yanzu, da waɗanda za mu more a nan gaba.—Karanta Markus 10:28-30.

14 Bulus ya kuma ambata wani abu da zai taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da aminci. Ya ce ya ‘manta da abubuwan da ke baya, kuma yana kutsawa zuwa ga waɗanda ke gaba.’ (Filib. 3:13) Ka lura cewa Bulus ya ambata abubuwa biyu da ya kamata mu yi. Na farko, muna bukatar mu manta da abubuwan da ke baya. Bai kamata mu riƙa yin tunani a kai a kai game da su ba. Na biyu, kamar mai tseren da ya kusan game tsere, ya kamata mu kalli abubuwan da ke gaba ba baya ba.

15. Me ya sa yake da kyau mu yi tunani game da misalin amintattun bayin Allah?

15 Ka yi tunanin amintattun bayin Jehobah da suka kasance a zamanin dā da kuma a zamaninmu. Misalansu za su taimaka maka ka ci gaba da kallon abubuwan da ke gaba ba baya ba. Alal misali, da a ce Ibrahim da Saratu sun ci gaba da yin tunani game da birnin Ur, “da sun sami damar komawa.” (Ibran. 11:13-15) Amma ba su koma ba. A lokaci na farko da Musa ya bar ƙasar Masar, ya bar abubuwan da suka fi wanda sauran Isra’ilawa suka bari daga baya. Amma Littafi Mai Tsarki bai faɗa cewa ya sake neman waɗannan abubuwan ba. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce “yana maida zargi domin Kristi wadata ne mafi girma bisa ga dukiyar Masar: gama yana sauraron sakamakon.”—Ibran. 11:26.

ABUBUWA MARASA KYAU DA MUKA FUSKANTA A DĀ

16. Yaya abubuwan da suka faru a dā za su iya shafanmu?

16 Wataƙila wasu abubuwan da muka fuskanta a dā sun yi wuya sosai. Alal misali, wataƙila kuskure ko kuma zunubin da muka yi a dā yana damunmu sosai. (Zab. 51:3) Wataƙila ba mu huce ba tukun don gargaɗin da aka yi mana. (Ibran. 12:11) Mai yiwuwa kuma, ba mu manta ba da rashin adalcin da aka yi mana ba, ko abin da muke tunanin cewa rashin adalci ne. (Zab. 55:2) Mene ne zai taimaka mana don mu manta da waɗannan abubuwan da suka faru? Ka yi la’akari da misalai uku.

17. (a) Me ya sa Bulus ya ce shi mafi ƙanƙanta ne “cikin tsarkaka duka”? (b) Me ya sa Bulus bai ƙyale baƙin ciki don kuskurensa ya hana shi bauta wa Allah?

17 Kuskuren da muka yi a dā. Manzo Bulus ya kwatanta kansa a matsayin mutum mafi ƙanƙanta “cikin tsarkaka duka.” (Afis. 3:8) Me ya sa yake jin hakan? Ya ce: “Da ya ke na tsananta ikilisiya ta Allah.” (1 Kor. 15:9) Ka yi tunanin yadda Bulus ya ji sa’ad da ya haɗu da wasu cikin waɗanda ya tsananta wa. Amma, maimakon ya ƙyale wannan ya dame shi, Bulus ya mai da hankali ga yadda Allah ya yi masa jin ƙai da kuma alheri. (1 Tim. 1:12-16) A sakamako, Bulus ya yi ƙwazo sosai a hidimarsa. Abubuwan da Bulus yake son ya manta da su, sun haɗa da kurakuren da ya yi a dā. Tun da ba za mu iya soke kurakuren da muka yi a dā ba, yin alhini game da su zai zama aikin banza, kamar yin harara a duhu. Maimakon haka, ya kamata mu tuna da jin ƙai da Jehobah ya yi mana kuma mu yi amfani da ƙarfinmu don bauta wa Jehobah yanzu.

18. (a) Me zai iya faruwa idan muka ci gaba da tunani a kan gargaɗin da aka ba mu a dā? (b) Yaya za mu bi shawarar Sulemanu game da karɓan gargaɗi?

18 Gargaɗin da aka taɓa mana da ya ɓata mana rai. Za mu iya ci gaba da tunani game da gargaɗin da aka mana a dā. Hakan zai iya sa mu fushi kuma ya sa mu sanyin gwiwa. (Ibran. 12:5) Ko da mun ƙi gargaɗin nan da nan ko kuma muna amince da shi, amma daga baya muka soma sanyin gwiwa, duk ɗaya ne. Ba mu ƙyale gargaɗin ya taimaka mana ba. Zai fi kyau mu bi gargaɗin Sulemanu: “Ka kama koyarwa da kyau: kada ka sake ta: Ka kiyaye ta: gama ranka ce.” (Mis. 4:13) Kamar direban mota da ke bin alamun da ke kan hanya, zai fi kyau ka karɓi gargaɗin, ka yi amfani da shi, kuma ka ci gaba da bauta wa Jehobah.—Mis. 4:26, 27; karanta Ibraniyawa 12:12, 13.

19. Ta yaya za mu iya yin koyi da Habakkuk da kuma Irmiya?

19 Sa’ad da aka yi mana rashin adalci ko muna jin cewa an yi mana hakan. A wasu lokatai, muna iya ji kamar annabi Habakkuk wanda ya kai kara wurin Jehobah don rashin adalci da ke faruwa a zamaninsa. Bai fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale mutane su riƙa yin irin waɗannan ayyukan ba. (Hab. 1:2, 3) Yana da muhimmanci mu yi koyi da bangaskiyar wannan annabin, wanda ya ce; “Duk da haka zan yi murna cikin Ubangiji; zan yi murna a cikin Allah mai-cetona.” (Hab. 3:18) Idan mun kasance da bege kamar Irmiya na zamanin dā kuma muna da imani ga Jehobah, Allah na adalci, za mu kasance da tabbaci cewa zai daidaita kome a lokacin da ya dace.—Mak. 3:19-24.

20. Yaya za mu nuna cewa mun “tuna da matar Lutu”?

20 Muna rayuwa a lokaci na musamman. Abubuwa masu ban al’ajabi suna faruwa kuma wasu za su faru a nan gaba. Ƙungiyar Jehobah tana samun ci gaba kuma ya kamata mu samu ci gaba tare da ita. Bari mu bi ja-gorar Littafi Mai Tsarki na kallon gaba ba abubuwan da ke baya ba. Idan mun yi hakan, za mu nuna cewa mun “tuna da matar Lutu.”

[Hasiya]

a A yare na asali da aka rubuta wannan furucin “shara,” yana nufin abin da aka “ba kare,” ko “kashin dabbobi” ko kuma “kashin mutum.” Wani masani na Littafi Mai Tsarki ya ce Bulus ya yi amfani da wannan furucin don kwatanta abin da mutum ya riga ya yar baki ɗaya. Mutumin yana ɗaukansa kamar abin banza kuma ba ya son ya sake ganinsa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba