Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 4/1 pp. 4-7
  • Amsoshin Tambayoyinmu Game da Yesu Kristi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyinmu Game da Yesu Kristi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Wane ne Yesu Kristi?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Wane ne Yesu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Kansa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 4/1 pp. 4-7

Amsoshin Tambayoyinmu Game da Yesu Kristi

“Taron suna ce da ni wanene?”—LUKA 9:18.

YESU ya yi wa almajiransa wannan tambayar ne domin ya san cewa mutane suna da ra’ayoyi dabam-dabam game da shi. Duk da haka, babu wani ƙwaƙƙwaran dalilin da zai hana mutane sanin ko wane ne shi. Yesu ba mai gudun jama’a ba ne kuma ba ya yin abubuwa a ɓoye. Yana yin sha’ani da mutane a fili. Ya yi wa’azi kuma ya koyar da mutane a fili domin yana son su san gaskiya game da shi.—Luka 8:1.

Za mu iya sanin gaskiya game da Yesu daga furucinsa da kuma ayyukansa da aka rubuta a cikin Linjilar Matta da Markus da Luka da Yohanna. A cikin waɗannan hurarrun rubutu ne za mu samu amsoshin tambayoyinmu game da Yesu.—Yohanna 17:17.

TAMBAYA: Yesu ya taɓa wanzuwa kuwa da gaske?

AMSA: E. ’Yan tarihi, har da Josephus da Tacitus a ƙarni na farko, sun ce tarihi ya nuna cewa Yesu mutumi ne mai muhimmanci. Mafi muhimmanci, labaran Linjila sun tabbatar mana da cewa Yesu ya taɓa rayuwa a duniya. An ambata lokaci da kuma ainihin wurin da waɗannan abubuwan suka faru a cikin Linjila. Alal misali, don ya tabbatar da shekarar da Yesu ya soma hidima, marubucin Linjila Luka ya ambata sunayen masu sarauta guda bakwai waɗanda ’yan tarihi ma suka yi maganar su.—Luka 3:1, 2, 23.

Akwai ƙwaƙƙwarar shaidar da ta tabbatar da cewa Yesu ya taɓa wanzuwa. “Yawancin masana za su yarda cewa wani mutumi mai suna Yesu Ba-nazarat ya rayu a ƙarni na farko,” in ji littafin nan Evidence for the Historical Jesus.

TAMBAYA: Da gaske ne cewa Yesu Allah ne?

AMSA: A’a. Yesu bai taɓa ɗaukan kansa a matsayi ɗaya da Allah ba. Akasin haka, Yesu ya nuna a kai a kai cewa yana ƙasa da Jehobah.a Alal misali, Yesu ya kira Jehobah “Allahna” da kuma ‘Allah makaɗaici mai-gaskiya.’ (Matta 27:46; Yohanna 17:3) Wanda yake ƙasa da wani ne kawai zai iya yin amfani da waɗannan furucin sa’ad da yake magana game da magabacinsa. Ma’aikacin da ya kira wanda ya ɗauke shi aiki “shugabana” yana nuna cewa yana ƙasa da shugaban.

Yesu ya kuma nuna cewa shi da Allah ba ɗaya ba ne. Yesu ya taɓa gaya wa ’yan hamayya da suka ƙalubalanci ikonsa cewa: “Cikin Attaurarku kuma an rubuta, Shaidar mutum biyu gaskiya ce. Ni ne wanda na ke shaidar kaina, Uba kuma wanda ya aiko ni yana shaidata.” (Yohanna 8:17, 18) Hakika, Yesu da Jehobah ba ɗaya ba ne. In da ba haka ba ne, me zai sa a ɗauke su a matsayin shaidu biyu?

TAMBAYA: Yesu mutumin kirki ne kawai?

AMSA: A’a, Yesu ya wuce hakan sosai. Yesu ya san cewa ya taka rawa na musamman da dama wajen yin nufin Allah. Ga kaɗan daga cikin su:

● ‘Ɗan Allah Makaɗaici.’ (Yohanna 3:18, Littafi Mai Tsarki) Yesu ya san asalinsa. Ya rayu ne tun kafin a haife shi a duniya. “Na sauko daga sama,” in ji shi. (Yohanna 6:38) Yesu ne halittar farko na Allah kuma Allah ya yi amfani da shi wajen halittar sauran abubuwa. A matsayin wanda Allah ya halitta da kansa, Yesu ya kira kansa ‘Ɗan Allah makaɗaici.’—Yohanna 1:3, 14, LMT; Kolosiyawa 1:15, 16.

● “Ɗan mutum.” (Matta 8:20) Sau da yawa, Yesu ya kira kansa “Ɗan mutum,” kuma wannan furucin ya bayyana wajen sau 80 a cikin Linjila. Wannan furucin ya nuna cewa shi mutum ne ba Allah ba da ya zo duniya a siffar mutum. Ta yaya aka haifi Ɗa makaɗaici na Allah a duniya a matsayin ɗan Adam? Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki kuma ya saka ran Ɗansa cikin mahaifar Maryamu wadda budurwa ce Ba-yahudiya, hakan ya sa ta yi juna biyu. A sakamakon hakan, an haifi Yesu a matsayin kamiltacce, marar zunubi.—Matta 1:18; Luka 1:35; Yohanna 8:46.

● “Malam.” (Yohanna 13:13) Yesu ya bayyana dalla-dalla cewa aikin da Allah ya ba shi shi ne ‘koyarwa . . . da yin wa’azin bishara’ game da Mulkin Allah. (Matta 4:23; Luka 4:43) Yesu ya yi bayani dalla-dalla a kan ko mene ne Mulkin Allah da kuma abin da mulkin zai yi wajen cika nufin Jehobah.—Matta 6:9, 10.

● “Kalma.” (Yohanna 1:1) Yesu ya yi hidima a matsayin Kakakin Allah, wato, ya idar da saƙo da kuma umurni daga Allah. Jehobah ya yi amfani da Yesu wajen idar da saƙo ga ’yan Adam.—Yohanna 7:16, 17.

TAMBAYA: Shin, Yesu ne Almasihun da aka yi alkawarinsa?

AMSA: E. Annabcin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Almasihu ko kuma Kristi, wanda yake nufin “Shafaffe” zai zo. Wannan Wanda aka yi alkawarin zuwansa zai taka rawa na musamman wajen cika nufin Jehobah. Akwai lokacin da wata Ba-samariya ta gaya wa Yesu cewa: “Na sani Almasihu yana zuwa wanda ake ce da shi Kristi.” Yesu ya fito fili ya gaya mata cewa: “Ni wanda na ke zance da ke, ni ne shi.”—Yohanna 4:25, 26.

Shin, akwai wata shaidar da ta tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu? Kamar yadda ake amfani da zanen yatsa don a gano mutum, akwai ƙwaƙƙwarar shaida guda uku waɗanda suka tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu.

● Asalinsa. Littafi Mai Tsarki ya yi annabci cewa Almasihu zai fito ne daga zuriyar Ibrahim, a cikin iyalin Dauda. (Zabura 132:11, 12; Ishaya 11:1, 10) Yesu ya fito ne daga zuriyar mutanen nan biyu.—Matta 1:1-16; Luka 3:23-38.

● Annabcin da suka cika. Nassin Ibrananci yana ɗauke da annabci masu yawa na rayuwar Almasihu a duniya, har da bayanai game da haihuwarsa da kuma mutuwarsa. Duka waɗannan annabcin sun cika a kan Yesu. Wasu daga cikinsu su ne: An haife shi a Bai’talahmi (Mikah 5:2; Luka 2:4-11), an kirawo shi daga cikin Masar (Hosea 11:1; Matta 2:15), an kashe shi ba tare da an ƙarya ƙasusuwansa ba (Zabura 34:20; Yohanna 19:33, 36). Babu yadda za a yi Yesu ya juya rayuwarsa don ta cika dukan waɗannan annabcin da aka yi game da Almasihu.b

● Shaidar da Allah da kansa ya bayar. A lokacin da aka haifi Yesu, Allah ya aiko da mala’iku su sanar da maƙiyaya cewa an haifi Almasihu. (Luka 2:10-14) Sa’ad da Yesu yake hidima a duniya, Allah ya yi magana daga sama sau da yawa don ya nuna cewa ya amince da Yesu. (Matta 3:16, 17; 17:1-5) Jehobah ya ba Yesu ikon yin mu’ujizoji, kuma hakan ya ƙara tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu.—Ayyukan Manzanni 10:38.

TAMBAYA: Me ya sa Yesu ya sha wahala kuma ya mutu?

AMSA: A matsayin mutumi marar zunubi, bai cancanta Yesu ya sha wahala ba. Hakazalika, bai cancanta a kafa shi a kan gungumen azaba don ya yi mutuwar wulakanci kamar mai laifi ba. Duk da haka, Yesu ya san cewa za a zalunce shi kuma ya miƙa wuya ga hakan.—Matta 20:17-19; 1 Bitrus 2:21-23.

Annabcin da aka yi game da Almasihu ya ce Yesu zai sha wahala kuma zai mutu don a gafarta zunuban mutane. (Ishaya 53:5; Daniyel 9:24, 26) Yesu da kansa ya ce ya zo ne ya ‘ba da ransa domin fansar mutane da yawa.’ (Matta 20:28) Waɗanda suke ba da gaskiya da fansar da mutuwarsa ta kawo suna da begen samun ceto daga zunubi da mutuwa kuma za su rayu har abada a cikin Aljanna a duniya.c—Yohanna 3:16; 1 Yohanna 4:9, 10.

TAMBAYA: Da gaske ne cewa an ta da Yesu daga matattu?

AMSA: Hakika. Yesu ya san cewa za a ta da shi daga matattu. (Matta 16:21) Amma, yana da muhimmanci mu san cewa, Yesu ko kuma Littafi Mai Tsarki bai ambata cewa zai tashi daga matattu ba tare da mu’ujiza ba. Wannan ra’ayin ba zai taɓa kasancewa gaskiya ba. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Allah kuwa ya ta da shi, bayan da ya kwance azabar mutuwa.’ (Ayyukan Manzanni 2:24) Idan mun yi imani da cewa akwai Allah kuma shi ne Mahaliccin dukan abubuwa, muna da dalilin gaskata cewa zai iya ta da Ɗansa daga matattu.—Ibraniyawa 3:4.

Akwai tabbatacciyar shaidar da ta nuna cewa an ta da Yesu daga matattu? Ka lura da waɗannan shaidar da ke gaba.

● Shaidun gani da ido. A misalin shekaru 22 bayan Yesu ya mutu, manzo Bulus ya rubuta cewa mutane sama da ɗari biyar ne suka ga Yesu bayan ya tashi daga matattu, kuma a lokacin da ya yi wannan rubutun, yawancinsu suna da rai. (1 Korintiyawa 15:6, LMT) Ana iya yin watsi da shaidar mutum ɗaya ko biyu, amma wane ne zai iya ƙaryata shaidar mutane fiye da 500?

● Amintattun shaidu. Almajiran Yesu na farko, waɗanda suka san ainihin abin da ya faru, sun faɗa da gaba gaɗi cewa an ta da Yesu daga matattu. (Ayyukan Manzanni 2:29-32; 3:13-15) Hakika, sun gaskata cewa wajibi ne Kirista na gaskiya ya gaskata da tashin Yesu daga matattu. (1 Korintiyawa 15:12-19) Waɗannan almajiran sun gwammace su mutu maimakon su musanta bangaskiyar da suke da ita ga Yesu. (Ayyukan Manzanni 7:51-60; 12:1, 2) Babu wanda zai yarda ya mutu domin abin da ya san cewa ƙarya ne, ko ba haka ba?

Mun tattauna amsoshin muhimman tambayoyi guda shida game da Yesu daga Littafi Mai Tsarki. Waɗannan amsoshin sun bayyana mana ko wane ne Yesu. Amma sanin waɗannan amsoshin yana da wani muhimmanci ne? Wato, kana iya kasancewa da duk ra’ayin da ka ga dama game da Yesu?

[Hasiya]

a A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah shi ne sunan Allah.

b Ka karanta shafi na 200 a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? don ka ga jerin annabcin da suka cika a kan Yesu.

c Ka karanta babi na 5 a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? don ka samu ƙarin bayani game da fansar da mutuwar Yesu ta kawo.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba