Ka Kusaci Allah
Mai Sāka wa Dukan Waɗanda Suke Bauta Masa
“NA GODE.” Waye ba ya farin ciki idan aka yi masa godiya domin aiki mai kyau da ya yi ko kuma domin wata kyauta da ya bayar? Dukanmu muna son a yaba mana, musamman ma idan waɗanda muke ƙauna ne suka yi hakan. Hakika, muna ƙaunar Allahnmu, Jehobah, fiye da kome. Shin Allah yana ɗaukan ƙoƙarin da muke yi don mu bauta masa da muhimmanci kuwa? Bari mu bincika yadda ya bi da Ebed-melech, mutumin da ya sadaukar da ransa don ya ceci wani annabin Allah.—Karanta Irmiya 38:7-13; 39:16-18.
Wane ne Ebed-melech? Ga alama, shi ma’aikaci ne a fadar Zedekiah, Sarkin Yahuda.a Ebed-melech, wanda Allah ya aika ya gargaɗi Yahuda marar aminci game da halaka da za ta faɗo mata ya rayu ne a lokaci ɗaya da Irmiya. Ko da yake yana zama tare da ’ya’yan sarakunan da ba sa tsoron Allah, Ebed-melech yana da tsoron Allah kuma ya daraja Irmiya sosai. An jarraba Ebed-melech, mutumi mai tsoron Allah sa’ad da waɗannan mugayen hakimai suka yi wa Irmiya zargin ƙarya cewa yana ta da zaune tsaye, saboda haka suka jefa shi cikin ramin da ke cike da laka kuma suka ƙi ba shi abinci don ya mutu. (Irmiya 38:4-6) Mene ne Ebed-melech zai yi?
Ebed-melech ya ɗauki matakin da ya nuna ƙarfin hali kuma bai ji tsoron abin da hakiman za su yi masa ba. A fili ya tunkari Zedekiah kuma ya ce masa yadda aka wulaƙanta Irmiya bai dace ba. Wataƙila yana nuna waɗannan mugayen mutanen da yatsa sa’ad da yake gaya wa sarkin cewa: “Waɗannan mutane sun yi mugun aiki . . . [ga] Irmiya.” (Irmiya 38:9) Zedekiah ya saurari Ebed-melech kuma ya gaya masa ya ɗebi mutane 30 su tafi tare su cece Irmiya.
Ebed-melech ya nuna wani hali mai kyau, wato, alheri. Ya saukar da “waɗansu tsummoki da waɗansu yan ruɓaɓun zanuwa, . . . da igiyoyi cikin ramin zuwa wurin Irmiya.” Me ya sa ya saukar masa da tsummoki da kuma zannuwa? Don Irmiya ya kāre hammatarsa da su, kada ya ji rauni sa’ad da ake jawo shi daga rami mai laka.—Irmiya 38:11-13.
Jehobah ya ga abin da Ebed-melech ya yi. Ya yaba masa kuwa? Ta baƙin Irmiya, Allah ya gaya wa Ebed-melech cewa halakar Yahuda ta kusa. Sai Allah ya ba Ebed-melech abin da wani masani ya kira “tabbaci guda biyar da suka nuna cewa zai samu tsira.” Jehobah ya ce: “Zan cece ka . . . Ba kuwa za a bashe ka a cikin hannun mutanen . . . ba. Gama zan cece ka . . . Ba kuwa za ka fāɗi ta kaifin takobi ba . . . Za ka tsira da ranka.” Me ya sa Jehobah ya yi alkawari cewa zai ceci Ebed-melech? Jehobah ya gaya masa: “Tun da ka bada gaskiya gareni.” (Irmiya 39:16-18) Jehobah ya san cewa Ebed-melech ya yi wannan abu ne ba kawai don ya damu da Irmiya ba, amma domin yana da bangaskiya kuma ya dogara da Allah.
Ga darasin: Jehobah yana yaba mana don abubuwan da muke yi yayin da muke bauta masa. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da mu cewa Jehobah yana tunawa da abu mafi ƙanƙanta da muka yi a bautarsa saboda bangaskiya. (Markus 12:41-44) Za ka so ka kusaci wannan Allahn da yake ɗaukan hidimarka da tamani? Idan haka ne, ka tabbata cewa zai kasance abin da Kalmarsa ta kira shi: “Mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.”—Ibraniyawa 11:6.
[Hasiya]
a An kira Ebed-melech “bābā.” (Irmiya 38:7) Ko da yake waɗanda aka dandaƙe ne ake kira da wannan sunan, ana kuma yin amfani da wannan sunan idan za a kira ma’aikaci a fadar sarki.