Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/15 pp. 7-11
  • Bari Jehobah Ya Yi Maka Ja-gora Don Ka Samu ’Yanci Na Gaske

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bari Jehobah Ya Yi Maka Ja-gora Don Ka Samu ’Yanci Na Gaske
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SHARI’AR DA KE ’YANTAR DA MU
  • YADDA “CIKAKKIYAR SHARI’A” TAKE ’YANTAR DA MU
  • KA BINCIKA KALMAR ALLAH
  • RUHU MAI TSARKI ZAI IYA ’YANTAR DA KAI
  • IKILISIYAR KIRISTA TANA ’YANTAR DA MU
  • “’YANCIN DARAJAR ’YA’YAN ALLAH”
  • Ku Bauta wa Jehobah, Allah Mai Ba da ’Yanci na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Yadda Za Mu Sami ’Yanci na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • ’Yanci da Masu Bauta wa Jehovah Suke Morewa
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/15 pp. 7-11

Bari Jehobah Ya Yi Maka Ja-gora Don Ka Samu ’Yanci Na Gaske

‘Ka duba cikin cikakkiyar shari’a ta ’yanci.’—JAS. 1:25.

ZA KA IYA BA DA AMSA GA WAƊANNAN TAMBAYOYIN?

Wace shari’a ce take sa a samu ’yanci na gaske, kuma su wane ne suke amfana daga wannan shari’ar?

Mene ne ya kamata mu yi don mu samu ’yanci na gaske?

Wane ’yanci ne waɗanda suka ci gaba da yin biyayya ga Jehobah za su samu?

1, 2. (a) Mene ne yake faruwa da ’yancin ’yan Adam, kuma me ya sa? (b) Wane ’yanci ne bayin Jehobah suke begen samu?

MUNA zama a lokacin da mutane suke yin haɗama da aikata laifi da kuma yin mugunta sosai. (2 Tim. 3:1-5) Saboda haka, gwamnatoci suna kafa sababbin dokoki da inganta yadda ’yan sanda suke tsaro da kuma kafa na’urorin tsaro. A wasu ƙasashe, mutane suna ƙoƙarin ƙara tsare kansu ta wajen saka ƙararrawa a gidajensu da ƙara makullai da kuma katanga mai wutar lantarki da zai iya jan mutum. Mutane da yawa ba sa fita waje daddare ko kuma su bar yaransu su yi wasa su kaɗai. Hakika, mutane ba su da ’yanci kuma wataƙila hakan zai ci gaba.

2 A lambun Adnin, Shaiɗan ya ce mutane za su samu ’yanci na gaske idan suka ƙi yin biyayya ga Jehobah. Abin da ya bi bayan hakan ya nuna cewa ƙarya ce ya tabka! Yayin da mutane suke ci gaba da yin abin da suke so ba abin da Allah ya gaya musu ba, hakan yana ƙara sa ’yan Adam su sha wahala. Bayin Jehobah ma suna shan wahala domin wannan yanayin. Amma, muna da begen cewa wata rana ’yan Adam za su samu ’yanci daga zunubi da ɓacewa kuma za su more abin da Littafi Mai Tsarki ya kira “’yancin darajar ’ya’yan Allah.” (Rom. 8:21) Hakika, Jehobah ya riga ya soma shiri don bayinsa su samu wannan ’yancin. Yaya yake yin hakan?

3. Wace doka ce Jehobah ya ba mabiyan Kristi, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Jehobah ya ba mu abin da wani marubucin Littafi Mai Tsarki mai suna Yaƙub ya kira ‘cikakkiyar shari’a ta ’yanci’ don ya shirya mu mu samun ’yanci a nan gaba. (Karanta Yaƙub 1:25.) Mutane ba sa son bin doka don suna gani tana hana su samun ’yanci. Amma, mece ce ‘cikakkiyar shari’a ta ’yanci’? Kuma ta yaya wannan shari’ar take ’yantar da mu?

SHARI’AR DA KE ’YANTAR DA MU

4. Mece ce ‘cikakkiyar shari’a ta ’yanci,’ kuma su wane ne suke amfana daga wannan shari’ar?

4 ‘Cikakkiyar shari’a ta ’yanci’ ba Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ba ce, domin wannan dokar ta nuna cewa Isra’ilawa masu zunubi ne, kuma Kristi ya cika wannan Dokar. (Mat. 5:17; Gal. 3:19) To, wace shari’a ce, Yaƙub yake maganarta? Yana magana ne game da “shari’ar Kristi” da “shari’ar bangaskiya” da kuma “shari’a ta ’yanci.” (Gal. 6:2; Rom. 3:27; Yaƙ. 2:12) Saboda haka, “cikakkiyar shari’a” ta ƙunshi dukan abubuwan da Jehobah yake bukatar mu yi. Kiristoci shafaffu da kuma “waɗansu tumaki” suna amfana daga wannan shari’ar.—Yoh. 10:16.

5. Me ya sa ba shi da wuya a kiyaye shari’a ta ’yanci?

5 “Cikakkiyar shari’a” ta yi dabam da dokokin da ƙasashe da yawa suke kafawa. Dokoki da ƙa’idodi ne masu sauƙi da ba su da wuyar fahimta ko kuma kiyayewa. (1 Yoh. 5:3) Yesu ya ce: “Karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.” (Mat. 11:29, 30) Ƙari ga haka, “cikakkiyar shari’a,” ba ta bukatar jerin dokoki, don ƙauna ce tushenta kuma kamar an rubuta ta cikin zuciyar mutane ba a kan allon duwatsu ba.—Karanta Ibraniyawa 8:6, 10.

YADDA “CIKAKKIYAR SHARI’A” TAKE ’YANTAR DA MU

6, 7. Mene ne za mu iya cewa game da mizanin Jehobah, kuma wace dama ce shari’a ta ’yanci take ba mu?

6 Dokokin da Jehobah ya ba mu don amfaninmu ne kuma suna kāre mu. Alal misali, ka yi la’akari da dokokin da ke sarrafa halitta kamar ƙarfin maganaɗisun ƙasa wato, gravity. Mutane ba sa gunaguni cewa bin waɗannan dokokin suna hana su sakewa. Maimakon hakan, suna godiya don sun san cewa waɗannan dokokin suna amfanar su. Haka nan ma, abubuwan da Jehobah yake bukata a gare mu da suke cikin “cikakkiyar shari’a” na Kristi suna amfanar mu.

7 Shari’a ta ’yanci tana kāre mu kuma tana sa mu cim ma muradinmu masu kyau ba tare da mun yi wa kanmu lahani ba ko kuma taka hakkin waɗansu. Saboda haka, idan muna son mu samu ’yanci na gaske wato, mu yi abin da muke so, muna bukatar mu yi abubuwan da Jehobah yake so da kuma abin da yake bukata a gare mu. Wannan yana nufin cewa za mu yi ƙaunar abubuwan da Jehobah yake ƙauna kuma mu tsani abubuwan da ya tsana. Shari’a ta ’yanci tana taimaka mana mu yi hakan.—Amos 5:15.

8, 9. Ta yaya muke amfana daga shari’a ta ’yanci? Ka ba da misali.

8 Saboda mu ajizai ne, yana yi mana wuya mu sha kan sha’awoyin da ba su da kyau. Duk da haka, yayin da muka manne wa shari’a ta ’yanci, muna samun ’yanci ko a yanzu ma. Alal misali, wani mutum mai suna Jay da yake fama da jarabar shan taba ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ya koya cewa shan taba yana ɓata wa Allah rai, ya tsai da shawara. Mece ce shawarar? Shin zai ci gaba shan taba ne ko kuwa zai ba da kansa ga Jehobah? Ya yanke shawara cewa zai bauta wa Allah ko da yake ya yi masa wuya ainun ya daina shan taba. Yaya ya ji bayan ya shawo kan wannan jarabar? Ya ce: “Na samu ’yanci sosai kuma ina farin ciki.”

9 Abin da ya faru da Jay ya sa ya fahimci cewa ’yancin da duniya take bayarwa da ke sa mutane su yi abubuwa marasa kyau, ba ’yanci na gaske ba ne, bauta ce ta zunubi, amma ’yancin da Jehobah yake bayarwa, wanda yake nufin “himmantuwar ruhu,” ’yanci ne na gaske kuma yana kai ga “rai da lafiya.” (Rom. 8:5, 6) Me ya ba Jay ƙarfin shawo kan jarabar shan taba? Jehobah ne ya ba shi ƙarfin. Ya ce: “Ina nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai kuma ina roƙon Allah ya ba ni ruhu mai tsarki kuma na amince da taimakon da ’yan’uwa da ke cikin ikilisiya suka yi mini.” Waɗannan tanadodin za su iya taimaka mana mu samu ’yanci na gaske. Bari mu tattauna wannan.

KA BINCIKA KALMAR ALLAH

10. Mene ne “duba” cikin shari’ar Allah yake nufi?

10 Littafin Yaƙub 1:25 ya ce: ‘Wanda ya duba cikin cikakkiyar shari’a ta ’yanci, ya lizima, zai zama mai-albarka a cikin aikinsa.’ Kalmar Hellenanci na asali da aka fassara “duba” tana nufin yin “bincike sosai” wato, cikin natsuwa. Hakika, idan muna son shari’a ta ’yanci ta shafi tunaninmu da zuciyarmu, wajibi ne mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ƙwazo kuma mu yi bimbini sosai a kan abin da muka nazarta.—1 Tim. 4:15.

11, 12. (a) Ta yaya Yesu ya nuna muhimmancin yin amfani da gaskiya a dukan fannoni na rayuwarmu? (b) Wane haɗari ne musamman ya kamata matasa su guje wa?

11 Bugu da ƙari, wajibi ne mu ‘lizima’ ko kuwa mu daure wajen aikata abin da Kalmar Allah ta ce, ta yin hakan muna sa gaskiyar ta bayyana a dukan fannonin rayuwarmu. Yesu ya yi irin wannan maganar sa’ad da ya ce wa wasu da suka gaskata da shi: ‘Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske; za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da ku.’ (Yoh. 8:31, 32) Za mu iya ce mun san gaskiyar idan muna amfani da abin da muka koya a dukan fannoni na rayuwarmu. Sa’ad da muka yi hakan ne za mu iya ce “maganar Allah” tana “aiki” a cikinmu, tana sa mu yi canje-canje a halayenmu don mu yi koyi sosai da Ubanmu da ke sama.—1 Tas. 2:13.

12 Ka tambayi kanka, ‘Na san gaskiya kuwa? Ina amfani da gaskiya a dukan fannonin rayuwata? Ko kuwa har yanzu ina sha’awar wasu “’yancin” da duniya take bayarwa?’ Wata ’yar’uwa da iyayenta Shaidun Jehobah ne ta ce: “Idan ka yi girma a cikin ƙungiyar Jehobah, za ka san cewa akwai Jehobah. Amma, a nawa yanayin, ba ni da cikakken imani ga Jehobah. Ban tsani abin da Jehobah ya tsana ba. Ban gaskata cewa abubuwa da nake yi suna da muhimmanci a gare shi ba. Sa’ad da nake cikin matsala ba na yin addu’a. Ina dogara ga kaina, kuma yanzu na san cewa yin hakan wauta ce.” Abin farin ciki ne cewa ’yar’uwar ta ankara cewa ra’ayinta ba daidai ba ne, kuma ta yi canje-canje masu muhimmanci. Ta ma soma hidima a matsayin majagaba na kullum.

RUHU MAI TSARKI ZAI IYA ’YANTAR DA KAI

13. Ta yaya ruhu mai tsarki na Allah yake taimaka mana mu samu ’yanci?

13 2 Korintiyawa 3:17, ta ce: “Inda Ruhun Ubangiji yake kuma, a nan ’yanci yake.” Ta yaya ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu samu ’yanci? Yana taimaka mana mu kasance da halayen da ke sa mu samu ’yanci kamar su, ‘ƙauna da farin ciki da salama da tsawon jimrewa da nasiha da nagarta da aminci da tawali’u da kamewa.’ (Gal. 5:22, 23) Mutane ba za su samu ’yanci ba idan babu waɗannan halaye, musamman ma ƙauna, kuma yanayin da muke gani a duniya yau yana nuna hakan. Bayan da manzo Bulus ya ambata ’yar ruhu, ya ci gaba da cewa: “Irin waɗannan babu shari’a a kansu.” Mene ne yake nufi? Babu dokar da za ta taɓa hana mu ci gaba da nuna waɗannan halayen. (Gal. 5:18) Jehobah yana son mu ci gaba da nuna waɗannan halayen a kai a kai babu fashi.

14. Ta yaya ruhun duniya yake sa mutane su zama bayi?

14 Waɗanda suka yarda ruhun duniya ya rinjaye su kuma suna cim ma muradinsu marasa kyau suna ganin cewa suna da ’yanci. (Karanta 2 Bitrus 2:18, 19.) Amma, su bayi ne. Irin waɗannan mutanen ne suke sa gwamnatocin suna kafa dokoki da yawa saboda su hana su yin waɗannan abubuwa marasa kyau. Bulus ya ce: “Ba a kafa shari’a domin mutum mai adalci ba, amma domin marasa-bin shari’a da marasa-jin gari.” (1 Tim. 1:9, 10) Kuma suna bauta wa zunubi don suna ‘bin burin jiki’ kuma wannan jikin yana zaluntarsu. (Afis. 2:1-3) Irin waɗannan mutanen suna kama da ƙwarin da suka je shan ruwan zuma, amma kwaɗayi ya sa suka kasa fitowa.—Yaƙ. 1:14, 15.

IKILISIYAR KIRISTA TANA ’YANTAR DA MU

15, 16. Ta yaya muke amfana tun da muka fara tarayya da ikilisiyar Kirista, kuma wane ’yanci ne muke morewa?

15 Yin tarayya da ikilisiyar Kirista ba kamar yin cuɗanya da wani kulob ba ne. Amma, kana tarayya da ikilisiyar Kirista ne don Jehobah ya jawo ka. (Yoh. 6:44) Me ya sa ya jawo ka? Shin ya ga cewa kai mai adalci ne da kuma mai tsoron Allah? Babu shakka, za ka ce: “A’a!” To me ya sa Jehobah ya jawo ka? Ya ga cewa za ka so ka bi shari’arsa ta ’yanci kuma ka amince da ja-gorarsa. Tun lokacin da ka fara tarayya da ikilisiyar Kirista, Jehobah ya ci gaba da kula da kai ta wajen koya maka kalmarsa, ya ’yantar da kai daga ƙarya da camfi na addini, ya kuma nuna maka yadda za ka koyi halayen Kristi. (Karanta Afisawa 4:22-24.) Saboda haka, ka samu gatan kasancewa cikin mutanen da su kaɗai ne suke da ’yanci na gaske a dukan duniya.—Yaƙ. 2:12.

16 Shin kana jin tsoro sa’ad da kake tare da waɗanda suke ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu? Sa’ad da kake tare da ’yan’uwa a cikin Majami’ar Mulki, kana riƙe jakarka gam-gam don kada wani ya sace ta? A’a! Kana da kwanciyar hankali. Kana jin haka ne sa’ad da kake tare da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah? Da ƙyar! ’Yancin da kake jin daɗinsa yanzu soma taɓi ne na ’yancin da za ka mora a nan gaba.

“’YANCIN DARAJAR ’YA’YAN ALLAH”

17. Ta yaya “bayyanuwar ’ya’yan Allah” za ta taimaka wa ’yan Adam su samu ’yanci?

17 Sa’ad da Bulus yake maganar ’yancin da Jehobah yake shirya wa bayinsa da ke duniya, ya ce: “Gama begen talikai yana sauraron bayyanuwar ’ya’yan Allah. . . . Halitta da kanta kuma za ta tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yancin darajar ’ya’yan Allah.” (Rom. 8:19-21) “Halitta” tana nufin ’yan Adam da suke da begen yin rayuwa har abada a duniya yayin da suke morar albarkar “bayyanuwar ’ya’yan Allah.” Za a soma wannan bayyanuwar ne sa’ad da aka ta da waɗannan “’ya’yan” daga matattu zuwa sama inda za su kawar da dukan mugunta kuma su sa “taro mai-girma” su shiga cikin sabuwar duniya.—R. Yoh. 7:9, 14.

18. Ta yaya ’yan Adam za su ƙara samun ’yanci, kuma wane ’yanci ne za su mora a nan gaba?

18 A lokacin, ’yan Adam za su ji daɗin ’yanci na musamman. Shaiɗan da aljanunsa ba za su iya rinjayar su kuma ba. (R. Yoh. 20:1-3) Wannan shi ne ’yanci na gaske! Daga lokacin, sarakuna da firistoci 144,000 na Kristi za su yi amfani da hadayar fansa a madadin ’yan Adam don su kawar da zunubi da ajizanci gabaki ɗaya. (R. Yoh. 5:9, 10) Bayan an sake gwada ’yan Adam kuma suka kasance da aminci, za su samu cikakken ’yanci da ainihi Jehobah ya nufe su da shi, wato, “’yancin darajar ’ya’yan Allah.” Ka yi tunanin wannan yanayin! Ba za ka sake gwagwarmaya don ka yi abin da Allah yake so ba, domin a lokacin, jikinka da zuciyarka da kuma tunaninka duka za su zama kamiltattu kuma za ka yi koyi da halaye masu kyau na Allah.

19. Mene ne muke bukata mu ci gaba da yi idan muna son mu samu ’yanci na gaske?

19 Kana son ka samu “’yancin darajar ’ya’yan Allah”? Idan amsarka e ce, zai dace ka sa ‘cikakkiyar shari’a ta ’yanci’ ta ci gaba da yi maka ja-gora. Ka duƙufa a yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ka riƙa bin gaskiya kuma kana aikata ta a dukan fannonin rayuwarka. Ka roƙi Allah ya ba ka ruhu mai tsarki. Ka yi amfani da dukan zarafi don ka amfana daga koyarwar da Jehobah yake tanadarwa a cikin ikilisiyar Kirista. Kada ka yarda Shaiɗan ya yaudare ka kuma ya sa ka yi tunani cewa dokokin Allah suna da wuyan kiyayewa kamar yadda ya yaudari Hauwa’u. Ko da yake Shaiɗan yana da wayo sosai. Amma, kamar yadda za mu tattauna a talifi na gaba, ba ma bukatar mu bar “Shaiɗan ya ci ribar kome a bisanmu: gama ba mu cikin rashin sanin makiɗansa ba.”—2 Kor. 2:11.

[Hotona a shafi na 9]

Har yanzu, ina sha’awar “’yancin” da mutanen duniya suke morewa?

[Hotona a shafi na 9]

Ina amfani da gaskiya a dukan fannoni na rayuwata kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba