Jehobah Yana Tattara Iyalinsa
‘Ina roƙonku ku kiyaye ɗayantuwar ruhu cikin ɗaurin salama.’ —AFIS. 4:1, 3.
MECE CE AMSARKA?
Mene ne manufar wakilci na Allah?
Ta yaya za mu “kiyaye ɗayantuwar ruhu”?
Mene ne zai taimaka mana mu ‘kasance da kirki zuwa ga junanmu’?
1, 2. Mene ne nufin Jehobah ga duniya da kuma mutane?
WANE tunani kake yi sa’ad da ka ji kalmar nan, iyali? Kana yin tunanin ƙauna da kuma farin ciki? Kana yin tunanin yin aiki tare don cim ma wata manufa? Ko kuma kana tunanin yin aiki tare da iyalinka don ku cim ma wani maƙasudi? Ko kuwa kana tunanin wuri mai kyau da za ka yi girma, ka koya abubuwa kuma ka tattauna abin da kake tunani? Wataƙila za ka yi wannan tunanin idan iyalinka suna da ƙauna sosai. Jehobah ne ya kafa iyali. (Afis. 3:14, 15) Kuma nufin Allah shi ne dukan halittunsa da ke sama da kuma duniya su samu kāriya, su amince da juna kuma su kasance da haɗin kai.
2 Bayan Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, Allah ya cire mutane daga cikin iyalinsa. Amma wannan zunubin bai canja nufin Allah ba. Zai tabbata cewa ’ya’yan Adamu da Hauwa’u sun kasance a cikin Aljanna a duniya. (Far. 1:28; Isha. 45:18) Ya shirya dukan abubuwan da ake bukata don ya cika wannan alkawarin. An bayyana mafi yawa cikin waɗannan shirye-shiryen a littafin Afisawa. Kuma jigon littafin haɗin kai ne. Bari mu tattauna wasu ayoyi na wannan littafin don mu koya yadda za mu ba da haɗin kai ga nufin Jehobah ga halittunsa.
WAKILCI DA KUMA AIKINSA
3. Mene ne wakilcin da aka ambata a littafin Afisawa 1:10, kuma a wane lokaci ne aka soma shirya sashensa na farko?
3 Dukan abin da Jehobah ya yi sun jitu da nufinsa. Ya soma shirya dukan abin da ke sama da kuma duniya don su kasance da haɗin kai. Ya kira wannan shirin “wakilci.” (Karanta Afisawa 1:8-10.) Wannan wakilci yana da sassa biyu. Na farko, Allah ya shirya shafaffu don su yi rayuwa a cikin sama. Kuma za su yi hidima a ƙarƙashin ikon Yesu Kristi. Wannan ya soma a Fentakos na shekara ta 33 a zamanin Yesu, sa’ad da Jehobah ya soma tattara waɗanda za su yi sarauta tare da shi a sama. (A. M. 2:1-4) Saboda hadayar fansa na Yesu, Allah ya sanar da shafaffu a matsayin masu aminci kuma waɗanda suka cancanci samun rai. Shafaffu sun san cewa an zaɓe su a matsayin “’ya’yan Allah.”—Rom. 3:23, 24; 5:1; 8:15-17.
4, 5. Mene ne sashe na biyu na wakilcin?
4 Na biyu, Allah ya shirya waɗanda za su kasance a cikin Aljanna a duniya. Sun amince da ikon Yesu da kuma shafaffun da ke sama. “Taro mai-girma” ne rukuni na farko da za su kasance a cikin Aljanna. (R. Yoh. 7:9, 13-17; 21:1-5) A lokacin sarauta ta shekara dubu ta Yesu, za a ta da biliyoyin mutane daga matattu. (R. Yoh. 20:12, 13) Ka yi tunanin yadda tashin matattu zai daɗa sa mu kasance da haɗin kai. A ƙarshen shekara dubun, za a gwada “abubuwan da ke bisa duniya.” Waɗanda suka kasance da aminci za su zama “’ya’yan Allah.”—Rom. 8:21; R. Yoh. 20:7, 8.
5 A yau, Jehobah yana shirya shafaffu su kasance a sama da kuma waɗansu tumaki su kasance a Aljanna a duniya. Amma a wacce hanya ce kowannenmu yake goyon bayan wakilcin?
‘KA KIYAYE ƊAYANTUWAR RUHU’
6. Ta yaya nassosi suka nuna cewa wajibi ne Kiristoci su yi taro?
6 Littafi Mai Tsarki ya ce wajibi ne Kiristoci su yi taro. (1 Kor. 14:23; Ibran. 10:24, 25) Amma idan muna son mu kasance da haɗin kai, ba ma bukata mu taru a wuri ɗaya kawai kamar yadda mutane suke yi a kasuwa ko kuma a filin kwallo. Muna kasance da haɗin kai idan mun yi abin da Jehobah yake koya mana kuma mun ƙyale ruhu mai tsarki na Allah ya taimaka mana mu zama mutane masu kirki.
7. Mene ne “kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama” take nufi?
7 Jehobah yana ɗaukanmu a matsayin amintattu, domin mun yi imani ga hadayar fansa na Yesu. Idan mu shafaffu ne, yana ɗaukanmu a matsayin ’ya’ya, idan kuma mu waɗansu tumaki ne yana ɗaukanmu a matsayin abokai. Amma tun da yake muna zama a wannan zamanin, dole ne mu riƙa samun matsala da mutane a wasu lokatai. (Rom. 5:9; Yaƙ. 2:23) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa haƙuri da juna. Amma, mene ne ya wajaba mu yi don mu kasance da haɗin kai da ’yan’uwa maza da mata? Muna bukatar mu zama masu “tawali’u da ladabi” sosai. Ƙari ga hakan, Bulus ya aririce mu mu yi ƙoƙari don mu “kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.” (Karanta Afisawa 4:1-3.) Hanya ɗaya da za mu yi amfani da wannan shawarar ita ce ta wajen ƙyale ruhun Allah ya canja yadda muke aikatawa kuma mu nuna ’ya’yan ruhu. Kuma za mu ƙi abubuwan da Allah ba ya so. Waɗannan halayen za su taimaka mana mu sasanta matsalar da ta taso tsakaninmu da wasu. Tana sa mu kasance da haɗin kai. Amma, ayyukan jiki suna jawo tsatsaguwa.
8. Ta yaya ne ayyukan jiki suke jawo tsatsaguwa?
8 Ta yaya “ayyukan jiki” suke jawo tsatsaguwa? (Karanta Galatiyawa 5:19-21.) Fasikanci yana raba mutum daga Jehobah da kuma ikilisiya. Kuma zina tana iya raba yara daga iyayensu da kuma ma’aurata. Ƙazamta tana hana mutum samun haɗin kai da Allah da kuma bayinsa. Ƙazamin rashin kunya yana nuna ƙin daraja ƙa’idoji masu girma na Allah. Kowanne cikin waɗannan ayyukan jiki yana raba mutum da Allah da kuma ’yan Adam. Jehobah ya tsane irin wannan halin.
9. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu don mu san ko muna ƙoƙari don kasance da salama da kuma haɗin kai?
9 Saboda haka, kowannenmu yana bukatar ya tambayi kansa: ‘Ina yin ƙoƙari sosai don na zauna cikin salama da haɗin kai da ’yan’uwana maza da mata? Mene ne nake yi idan na samu matsala da mutane? Shin ina gaya wa abokaina don su goyi baya na? Ina sa rai cewa dattawa za su sa baki a batun maimakon na yi ƙoƙari don kasance da salama da ’yan’uwana? Idan akwai matsala tsakani na da wani, ina kaucewa duk sa’ad da na gan shi don kada mu tattauna matsalar? Idan muna yin hakan, shin muna nuna cewa muna goyon bayan nufin Jehobah na sa dukan mutane su kasance da haɗin kai a ƙarƙashin sarautar Yesu?
10, 11. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da salama da ’yan’uwanmu? (b) Mene ne za mu iya yi don mu kasance da salama kuma mu samu albarkar Jehobah?
10 Yesu ya ce: “Idan fa kana cikin miƙa baikonka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baikonka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baikonka. Ka shirya da abokin husumanka da sauri.” (Mat. 5:23-25) Yaƙub ya ce “ana shuka ɗiyan adalcin cikin salama domin masu-yin salama.” (Yaƙ. 3:17, 18) Saboda haka, idan ba ma cikin salama, ba za mu iya yin abin da ya dace ba.
11 Alal misali, a wasu ƙasashe da ake yawan yaƙe-yaƙe, mutane ba sa iya nome babban sashe na filayen domin an binne bama-bamai a ƙasa. Idan bam da aka binne a ƙasa ya tashi, mutane suna gudu su bar wurin. Kuma hakan ya sa yana wa mutane wuya su samu aiki da kuma abinci. Hakazalika, zai kasance da wuya sosai mu nuna halayen Kirista idan halayenmu suna hana mu zama cikin salama da ’yan’uwanmu. Hakan zai zama kamar bam da aka binne a ƙasa. Idan haka halinmu yake, muna bukatar mu yi gyara. Idan muna yafe wa mutane da sauri kuma muna yi musu alheri, za mu samu salama da kuma albarkar Jehobah.
12. Ta yaya dattawa za su taimaka mana mu kasance da haɗin kai?
12 Ƙari ga hakan, “kyautai ga mutane” za su iya sa mu kasance da haɗin kai. (Afis. 4:8, 13) Idan dattawa suna aiki tare da mu a tsarkakkiyar hidima kuma suka yi amfani da Kalmar Allah don yi mana gyara, hakan zai taimaka mana mu canja halayenmu. (Afis. 4:22-24) Idan dattijo ya ba ka shawara, ka tuna cewa Jehobah yana yin amfani da shi don shirya ka ka kasance a sabuwar duniya. Ku kuma dattawa, ku tabbata cewa kuna wa mutane gargaɗi a hanyar da za su ga cewa kuna son ku taimaka musu.—Gal. 6:1.
“KU KASANCE DA NASIHA ZUWA GA JUNANKU”
13. Mene ne zai faru idan ba mu bi shawarar da ke littafin Afisawa 4:25-32 ba?
13 Littafin Afisawa 4:25-29 ya ambata abubuwan da bai kamata mu yi ba. Bai kamata mu riƙa yin ƙarya ba da yin fushi sosai da zama ragwaye da kuma yin ɗanyen magana ba. Maimakon haka, ya kamata mu yi magana game da abubuwa da suke da kyau da kuma ƙarfafawa. Duk wanda ya ƙi bin wannan shawarar yana jawo tsatsaguwa. Zai riƙa “ɓata zuciyar Ruhu Mai-tsarki na Allah,” kuma wannan ruhun ne yake sa mutane su kasance da haɗin kai. (Afis. 4:30) Muna kuma bukatar mu bi shawarar da ke gaba wadda Bulus ya ba da idan muna son mu kasance da salama da kuma haɗin kai: “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gare ku, tare da dukan ƙeta: ku kasance da [kirki] zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku gafara, kamar yadda Allah kuma cikin Kristi ya gafarta maku.”—Afis. 4:31, 32.
14. (a) Mene ne ma’anar kalmomin nan ‘ku kasance da kirki’? (b) Mene ne zai taimaka mana mu nuna kirki?
14 Kalmomin nan ‘ku kasance da kirki’ suna nufin cewa wataƙila ba ma yawan nuna kirki kuma muna bukatar mu koyi daɗa yin hakan. Muna bukatar mu yi tunani cewa ra’ayin mutane ya fi namu. (Filib. 2:4) A wasu lokatai, za mu so mu faɗi wani abu da zai sa mutane dariya ko kuma da zai sa a ɗauke mu kamar masu basira sosai. Amma, bai kamata mu furta wannan abun ba idan ba zai nuna kirki ba. Idan mun yi tunani kafin mu yi magana, zai taimaka mana mu kasance da kirki ga mutane.
KOYON NUNA ƘAUNA DA DARAJA A CIKIN IYALI
15. Ta yaya littafin Afisawa 5:28 ya taimaki mazaje su san yadda za su yi koyi da Kristi?
15 Littafi Mai Tsarki ya kamanta dangantakar Kristi da ikilisiya da dangantakar ma’aurata. Misalin Yesu yana taimaka wa mai-gida ya fahimci cewa yana bukatar ya kāre da kuma yi ƙaunar matarsa kuma ya kula da ita, kuma mata tana bukata ta yi biyayya ga mijinta. (Afis. 5:22-33) Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce, ‘Haka nan ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu’? (Afis. 5:28) Abin da ya ce game da Yesu da kuma ikilisiya ya taimaka mana mu amsa tambayar. Ya ce Kristi ya yi ƙaunar ikilisiyar kuma ya ba da kansa domin ta kuma ya tsarkake ta da “ruwa ta wurin Kalma.” Saboda haka, miji yana da hakkin taimaka wa kowanne mutum a cikin iyalinsa ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Idan ya yi hakan, yana goyon bayan nufin Jehobah na sa dukan waɗanda suke ƙarƙashin sarautar Yesu su kasance da haɗin kai.
16. Wane sakamako ne za a samu idan iyaye suka kula da yaransu sosai?
16 Ya kamata iyaye su tuna cewa Jehobah ne ya ba su hakkin kula da yaransu. Amma abin baƙin ciki ne cewa mutane da yawa a yau ba su da “ƙauna irin na tabi’a.” (2 Tim. 3:1, 3) Maza da yawa ba sa ɗaukan hakkinsu da muhimmanci kuma hakan yana samun sakamako marar kyau ga yaransu kuma yana sa su baƙin ciki. Amma, Bulus ya ba da gargaɗi ga Kiristoci waɗanda ubanni ne: “Kada ku yi wa ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin foron Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) A cikin iyali ne yara suke soma koyan nuna ƙauna da kuma biyayya ga hukuma. Idan iyaye suka koya wa yaransu waɗannan abubuwan, hakan zai nuna cewa suna goyon bayan Jehobah don ya sa kowa ya kasance da haɗin kai. Ya kamata iyaye su sa yaransu su san cewa ana ƙaunarsu a cikin iyali. Hakan yana nufin cewa ya kamata su riƙe fushinsu. Kuma bai kamata su riƙa yi wa yaransu ihu ko kuma baƙar magana ba. Idan sun yi haka, za su nuna wa yaransu yin ƙauna da kuma daraja hukuma. Hakan zai shirya yaran don su yi rayuwa a sabuwar duniya da Allah ya shirya.
17. Mene ne muke bukata mu yi don mu yi tsayayya da Iblis?
17 Ya kamata mu tuna cewa Shaiɗan yana neman ya hana mutane bauta wa Jehobah. Kuma zai yi iya ƙoƙarinsa don ya cim ma wannan manufar. Mutane da yawa a duniya suna yin abin da Iblis yake son su yi sa’ad da suka kashe aurensu ko kuma suka zauna ba tare da yin aure ba ko kuma amince da aure tsakanin ’yan daudu. Amma ba ma yin koyi da halaye da suka zama gama-gari a duniya na yau. Muna yin koyi da Kristi. (Afis. 4:17-21) Don mu yi tsayayya da Iblis da kuma aljannunsa, muna bukata mu “yafa dukan makamai na Allah.”—Karanta Afisawa 6:10-13.
“KU YI TAFIYA CIKIN ƘAUNA”
18. Mene ne za mu yi don mu kasance da haɗin kai?
18 Muna bukata mu nuna ƙauna idan muna son mu kasance da haɗin kai. Muna ƙaunar ‘Ubangijinmu ɗaya’ sosai da “Allah ɗaya” da kuma juna daga zuciyarmu. Shi ya sa muka ƙuduri aniya mu “kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.” (Afis. 4:3-6) Yesu ya yi addu’a mu nuna irin wannan ƙaunar sa’ad da ya ce: “Kuma ba domin waɗannan kaɗai ni ke yin addu’a ba, amma domin waɗancan kuma da ke bada gaskiya gareni ta wurin maganarsu: domin su duka su zama ɗaya; kamar yadda kai, Uba, kana cikina, ni kuma a cikinka, domin su kuma su zama cikinmu. . . . Na kuma sanar masu da sunanka, zan kuma sanarda shi; domin wannan ƙauna wadda ka ƙaunace ni da ita ta zauna cikinsu, ni kuma a cikinsu.”—Yoh. 17:20, 21, 26.
19. Mene ne ka ƙuduri aniya za ka yi?
19 Idan muna fama da wani hali marar kyau don ajizancinmu, ƙauna za ta sa mu yi addu’a yadda wani marubucin zabura ya yi: “Ka daidaita zuciyata ta ji tsoron sunanka.” (Zab. 86:11) Bari mu ƙuduri aniyar yin tsayayya da Iblis da dabarunsa na raba mu da Ubanmu mai ƙauna da kuma ’yan’uwanmu. Ya kamata mu yi aiki tuƙuru don mu ‘zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu; mu yi tafiya cikin ƙauna’ a cikin iyali, sa’ad da muke wa’azi da kuma a cikin ikilisiya.—Afis. 5:1, 2.
[Hoto a shafi na 29]
Ya bar baikonsa a kan bagadi, ya je don ya sulhunta da ɗan’uwansa
[Hoto a shafi na 31]
Iyaye, ku koya wa yaranku yin ladabi