Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 8/15 pp. 8-10
  • ‘Za Ka Sami Ladan Aikinka’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Za Ka Sami Ladan Aikinka’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TARIHIN ASA
  • ASA A BAKIN DĀGA
  • ƘARFAFA DA KUMA GARGAƊI
  • “KA YI AIKIN WAUTA”
  • Ka Yi Amfani da Zarafin da Kake da Shi Yanzu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Yadda Jehobah Yake Kusantar Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Asa Ya Kasance da Ƙarfin Zuciya, Kai fa?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 8/15 pp. 8-10

‘Za Ka Sami Ladan Aikinka’

SARKI ASA ya ja-goranci rundunarsa cikin kwari mai zurfi daga duwatsun Yahudiya zuwa filin da ke gaɓar teku. Sa’ad da suka zo wurin da kwarin yake da faɗi, sai Asa ya tsaya. Ya hangi sansani mai girma na rundunar Habasha a filin kuma abin da ya gani ya ba shi mamaki! Babu shakka, sojojin sun kai miliyan ɗaya. Amma, rundunar Asa kusan 580,000 ne kawai.

Asa yana bukatar yin yaƙi. Amma, a wannan lokacin, mene ne zai soma yi? Zai ba da umurni ne ga rundunarsa? Zai ƙarfafa su ne? Ko kuma zai aika wasiƙu zuwa ga iyalinsa ne? Asa bai yi ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ba. A cikin wannan yanayin mai wuya, Asa ya fara yin addu’a.

Kafin mu yi magana a kan addu’ar da kuma abin da ya biyo bayan haka, bari mu yi magana a kan Asa da kansa. Me ya sa ya ɗauki wannan matakin? Asa yana da dalilai na gaskata cewa Jehobah zai taimake shi ne? Wane darasi za mu koya game da yadda Jehobah yake yi wa bayinsa albarka sa’ad da suka yi abin da ya dace?

TARIHIN ASA

Shekara 20 bayan mulkin ƙasar Isra’ila ya rabu kashi biyu, mutanen Yahuda sun lalace sosai saboda bautar ƙarya. Lokacin da Asa ya zama sarki a shekara ta 977 kafin zamanin Yesu, ma’aikata a fadar ma suna bauta wa allolin ni’ima na ƙasar Kan’ana. Amma, hurarren labarin sarautar Asa ya bayyana mana cewa “Asa fa ya yi aikin nagarta, abin da ke daidai kuma a gaban Ubangiji Allahnsa: gama ya kawas da baƙin bagadai, da masujadai, ya rurrushe umudai, ya sassara Asherim.” (2 Laba. 14:2, 3) Bugu da ƙari, Asa ya kawar da “Ƙadashim [‘maza da ke karuwanci a haikali,’ NW] waɗanda suke luwaɗi da sunan addini. Asa bai tsaya a nan ba. Ya kuma ƙarfafa mutanensa su “biɗi Ubangiji, Allah na ubanninsu, su kiyaye shari’a da umurnin.”—1 Sar. 15:12, 13; 2 Laba. 14:4.

Jehobah ya ji daɗin ƙwazon da Asa ya nuna don bauta ta gaskiya kuma saboda haka, ya albarkace shi da zaman lafiya na shekaru da yawa. Sarkin da kansa ya ce: “Mun biɗi Ubangiji Allahnmu; mun neme shi, ya kuma ba mu hutu a kowane wuri.” Mutanen sun yi amfani da wannan yanayin don su ƙarfafa biranen ƙasar Yahuda. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Suka gina: abin ya yi albarka kuwa.”—2 Laba. 14:1, 6, 7.

ASA A BAKIN DĀGA

Asa ya san cewa Jehobah yana saka wa waɗanda suka nuna bangaskiya ta ayyukansu. Shi ya sa ya yi addu’a ga Jehobah sa’ad da yake fuskantar runduna mafi girma da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. A addu’ar da Asa ya yi, ya roƙi Jehobah ya taimake shi. Asa ya san cewa idan ya dogara ga Jehobah, zai sa ya yi nasara kome ƙarfi ko kuma girman rundunar maƙiyan. Asa ya san cewa sakamakon yaƙi zai shafi sunan Jehobah, saboda wannan dalilin, ya roƙi Allah ya sa ya yi nasara. Ya ce: “Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama muna dogara gareka, a cikin sunanka kuma mun zo yaƙi da wannan babban taro. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu: kada ka bar mutum shi rinjaye ka.” (2 Laba. 14:11) Kamar dai Asa yana cewa: ‘Jehobah, Habashawa sun kai maka hari. Kada ka ƙyale su su ɓata sunanka ta wajen barin ’yan Adam ajizai su yi nasara a kan mutanenka.’ Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ubangiji fa ya buga Kushawa [Habashawa] daga gaban Asa da Yahuda; Kushawa kuwa suka gudu.”—2 Laba. 14:12.

A yau, mutanen Jehobah suna fuskantar maƙiya da yawa masu ƙarfi. Ba za mu yaƙe su da makaman zahiri a filin dāga ba. Duk da haka, za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ba amintattun bayinsa da suke ɗaukaka sunansa nasara. Wataƙila kowannenmu yana fama sosai da banzan tunani na duniya da ajizancinmu ko kuma duk wani abin da zai ɓata dangantakar iyalinmu da Jehobah. Ko mene ne matsalar da muke fama da ita, addu’ar da Asa ya yi zai iya ƙarfafa mu. Jehobah ne ya ba shi nasara. Idan muka dogara ga Jehobah, zai taimaka mana mu ci galabar duk wani abin da ke ci mana tuwo a ƙwarya. Babu wanda ya isa ya daddage masa.

ƘARFAFA DA KUMA GARGAƊI

Sa’ad da Asa yake dawowa daga yaƙin, annabi Azariah ya same shi a hanya. Annabi Azariah ya ƙarfafa shi kuma ya ba shi gargaɗi, ya ce: “Ka ji ni, ya Asa, da kai, da dukan Yahuda da Banyamin: Ubangiji yana tare da ku, muddar kuna tare da shi; idan kun neme shi, yā samu a gareku; amma idan kun yashe shi, shi kuma za ya yashe ku. . . . Ku yi ƙarfi, kada hannunku su sake: gama za ku sami ladan aikinku.”—2 Laba. 15:1, 2, 7.

Waɗannan kalmomin za su iya ƙarfafa bangaskiyarmu. Suna nuna cewa Jehobah yana tare da mu muddin muna bauta masa da aminci. Idan mun nemi taimakonsa, zai ji kukanmu. Azariah ya ce: “Ku yi ƙarfi, kada hannunku su sake.” A yawancin lokaci, muna bukata mu kasance da gaba gaɗi sosai don mu yi abin da ya dace, amma mun san cewa za mu iya yin nasara idan Jehobah ya taimaka mana.

Kakar Asa Maakah ta yi “wata sifa mai-ƙazamta domin Asherah,” amma, Asa ya sauke ta daga zama “sarauniya” kuma ya ƙone sifarta ko da yake wannan abu mai wuya ne a gare shi. (1 Sar. 15:13) Jehobah ya yi wa Asa albarka don tsayin dakan da ya yi da kuma gaba gaɗin da ya nuna. Wajibi ne mu manne wa Jehobah da kuma ƙa’idodinsa na adalci ko da danginmu suna da aminci ga Jehobah ko a’a. Idan muka yi hakan, Jehobah zai albarkace mu don amincinmu.

Wani lada da Asa ya samu shi ne na ganin Isra’ilawa da yawa da ke mulkin arewanci na ƙasar da suka yi ridda suna ƙaura zuwa Yahuda sa’ad da suka ga cewa Jehobah yana tare da shi. Saboda suna son bauta ta gaskiya, waɗannan mutanen sun bar gidajensu don su zauna tsakanin bayin Jehobah. Asa da Yahuda duka suka yi farin ciki kuma suka ‘yi alkawarin biɗan Ubangiji, Allah na ubanninsu, da dukan zuciyarsu da dukan ransu.’ Mene ne sakamakon? Allah “ya kuwa samu garesu: Ubangiji kuwa ya kewaye su da hutu ko’ina.” (2 Laba. 15:9-15) Muna farin ciki sosai sa’ad da masu son adalci suka soma bauta wa Jehobah!

Sa’ad da annabi Azariah yake ƙarfafa Asa, ya yi masa gargaɗi. Ya ce: “Idan kun yashe [Jehobah], shi kuma za ya yashe ku.” Kada mu taɓa yarda hakan ya faru da mu, domin yana iya kasancewa da mummunar sakamako! (2 Bit. 2:20-22) Littafi Mai Tsarki bai bayyana dalilin da ya sa Jehobah ya ba wa Asa wannan gargaɗin ba, amma mun san cewa Asa bai saurari wannan gargaɗin ba.

“KA YI AIKIN WAUTA”

A shekara ta 36 ta sarautar Asa, Sarki Baasha na Isra’ila ya kai wa Yahuda hari. Sarki Baasha ya ƙarfafa garun birnin Ramah, wanda yake iyaka da ke tsakanin Isra’ila da Yahuda kuma yana da nisan mil 5 daga Urushalima. Maimakon Asa ya biɗi taimakon Jehobah yadda ya yi sa’ad da Habashawa suka kai musu hari, Asa ya nemi taimakon ɗan Adam. Ya aika wa Sarkin Suriya kyauta don ya kai wa Mulkin Arewanci na Isra’ila hari. Bayan rundunar Suriya suka kai wa Isra’ila hari, sai Baasha ya janye daga Ramah.—2 Laba. 16:1-5.

Jehobah bai ji daɗin matakin da Asa ya ɗauka ba, saboda haka, ya aiki annabi Hanani ya yi masa magana. Ya kamata Asa ya koyi darasi daga abin da Allah ya yi wa rundunar Habasha cewa “idanun [Jehobah] suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” Wataƙila an ba wa Asa mugun shawara ko kuma ya yi tunanin cewa rundunar Baasha ba ta kai wadda zai nemi taimakon Jehobah ba kuma ya san abin da zai yi don ya yi nasara a kansu. Ko mene ne dalilin, ya bi ra’ayin ɗan Adam kuma ya ƙi ya dogara ga Jehobah. Annabi Hanani ya ce masa: “A nan ka yi aikin wauta; gama daga nan gaba za ka sha yaƙi.”—2 Laba. 16:7-9.

Abin da annabi Hanani ya ce ya ɓata wa Asa rai sosai har ya jefa shi cikin kurkuku. (2 Laba. 16:10) Wataƙila Asa ya yi tunanin cewa ya fi ƙarfin horo saboda ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah da aminci. Ko kuma tsufa ce ta shafi tunaninsa. Ko ma mene ne dalilin, Littafi Mai Tsarki bai bayyana ba.

A shekara ta 39 ta sarautar Asa, ya kamu da wata muguwar cuta a ƙafafunsa. “Duk da haka cikin ciwutassa ba ya biɗi Ubangiji ba, amma ya biɗi masu-magani,” in ji labarin. A lokacin, kamar dai dangantakarsa da Jehobah ba ta da ƙarfi kamar dā. Kuma mai yiwuwa yanayinsa bai canja ba har mutuwarsa a shekara 41 ta sarautarsa.—2 Laba. 16:12-14.

Duk da haka, Jehobah bai manta da Asa ba saboda halayensa masu kyau da ƙwazonsa don bauta ta gaskiya. Asa bai daina bauta wa Jehobah ba. (1 Sar. 15:14) Wane darasi ne za mu iya koya daga tarihin Asa? Idan muka ci gaba da tunawa da yadda Jehobah ya taimaka mana a dā, za mu nemi taimakonsa ta wajen yin addu’a sa’ad da muke fuskantar sababbin matsaloli. Duk da haka, kada mu yi tunani cewa don mun yi shekaru muna bauta wa Jehobah da aminci, ba ma bukatar shawararsa. Jehobah zai yi mana horo idan muka yi kuskure. Sa’ad da ya yi hakan, muna bukatar mu amince da gyarar cikin tawali’u don ya amfane mu. Darasi mafi muhimmanci da muka koya shi ne Ubanmu na sama zai kasance tare da mu idan muka ci gaba da kasancewa tare da shi. Jehobah yana bincika ko’ina a dukan duniya don ya taimaka wa waɗanda suke da aminci a gare shi. Yana yi musu albarka ta wajen yin amfani da ikonsa a madadinsu. Jehobah ya taimaka wa Asa kuma zai taimaka mana.

[Bayanin da ke shafi na 9]

Jehobah yana yi wa amintattu albarka

[Bayanin da ke shafi na 10]

Muna bukatar gaba gaɗi don yin abin da ya dace

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba