Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/1 pp. 4-8
  • Shin Allah Ya Damu da Mata Kuwa da Gaske?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin Allah Ya Damu da Mata Kuwa da Gaske?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Dokoki da Suka Bayyana Ra’ayin Allah Game da Mata
  • An Ɓata Dokar Allah Game da Mata
  • Mene ne Matsayin Mata a Tsarin Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Mata Suna da Mutunci A Gaban Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/1 pp. 4-8

Shin Allah Ya Damu da Mata Kuwa da Gaske?

WANI LITTAFI MAI SUNA SIRAK, NA ƘARNI NA BIYU KAFIN ZAMANIN YESU YA CE: “A gun mace ne saɓo ya samo tushensa, saboda ita ne ma dukanmu muke mutuwa.”

WANI MARUBUCI A ƘARNI NA BIYU A ZAMANIN YESU MAI SUNA TERTULLIAN YA YI WANNAN FURUCIN GAME DA MATA: “Ku ne kofar iblis: ku ne kuka ci haramtaccen itacen: ku ne kuka fara karya dokar Allah . . . Ku ne kuka ɓata mutum, wanda Allah ya halitta cikin kamanninsa.”

BA DAGA cikin Littafi Mai Tsarki ba ne aka ɗauko waɗannan ayoyin. An daɗe ana amfani da waɗannan ayoyin wajen ba da hujjar wariyar da ake nuna wa mata. Har wa yau, wasu masu tsattsauran ra’ayi suna amfani da abubuwan da aka rubuta a cikin littattafan addinai don su ba da hujjar danniyar da suke yi wa mata kuma suna da’awar cewa mata ne suka jefa ’yan Adam cikin halin da suka samu kan su a yau. Shin nufin Allah ne maza su riƙa wulaƙanta mata? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da hakan? Bari mu gani.

◼ Allah ya la’anta mata ne?

A’a. Wannan ‘tsohon macijin wanda ake kira Iblis da Shaiɗan’ ne Allah ya ‘la’anta.’ (Ru’ya ta Yohanna 12:9; Farawa 3:14) Sa’ad da Allah ya ce Adamu zai ‘mallaki’ matarsa, ba ya nufin cewa maza su riƙa bi da mata yadda suka ga dama. (Farawa 3:16, Littafi Mai Tsarki) Abin da yake nufi shi ne, Adamu da Hawa’u za su fuskanci mugun sakamako saboda zunubin da suka yi.

Saboda da haka, ba nufin Allah ba ne cewa a nuna wa mata wariya, a maimakon hakan wariyar da ake nuna wa mata a yau sakamakon zunubin da Adamu da Hawa’u suka yi ne. Wannan ra’ayin cewa zunubin da Adamu da Hawa’u suka yi ne ya sa maza suke nuna wa mata wariya ba daga Littafi Mai Tsarki ba ne.—Romawa 5:12.

◼ Allah ya halicci ta mace ƙasa da namiji ne?

A’a. Littafin Farawa 1:27 ya ce: “Allah fa ya halicce mutum cikin kamaninsa, cikin kamanin Allah ya halicce shi; na miji da ta mace ya halicce su.” Saboda haka, tun daga farkon halitta, Allah ya halicci namiji da ta mace a hanyar da dukan su za su iya yin koyi da shi. Ko da yake Adamu da Hawa’u sun bambanta a yadda Allah ya halicce su da kuma a halayensu, Allah ya ba su aiki iri ɗaya kuma ba wanda ya fi wani a gabansa.—Farawa 1:28-31.

Kafin Allah ya halicci Hawa’u, ya ce: ‘Zan yi masa [Adamu] mataimaki mai-dacewa da shi.’ (Farawa 2:18) Shin wannan kalmar “mataimaki” yana nufin cewa mace tana ƙasa na namiji ne? A’a. Ka yi la’akari da yadda likita mai yin fiɗa da likita mai ba da allurar kashe raɗaɗi suke aiki tare a lokacin tiyata. Shin, likita mai fiɗar zai iya yin aikinsa ne ba tare da taimakon mai ba da allurar kashe raɗaɗi ba? Ko da yake shi ne ainihin mai yin fiɗar, hakika, bai fi likita mai ba da allurar muhimmanci ba. Hakazalika, Allah ya halicci mace da namiji don su riƙa aiki tare, ba don su riƙa gāsa da juna ba.—Farawa 2:24.

◼ Me ya nuna cewa Allah yana kula da mata?

Bayan Allah ya hangi abin da maza ajizai za su yi, sai ya shirya yadda zai kāre mata. Wata mawallafiya mai suna Laure Aynard ta rubuta cewa: “A wurare da yawa da aka ambaci mata a cikin dokokin da Allah ya ba Musa a shekara ta 1513 kafin zamanin Kristi, an yi hakan ne domin a kāre mutuncinsu.”

Alal misali, a cikin dokokin, an umurci Isra’ilawa su girmama mahaifinsu da mahaifiyarsu. (Fitowa 20:12; 21:15, 17) An ƙara ba da umurni a cikin dokokin cewa su riƙa mutunta mata masu juna biyu. (Fitowa 21:22) A ƙasashe da yawa a duniya, an tsara dokoki don kāre mutuncin mata ko da yake ba a cika aiwatar da waɗannan dokokin ba. Amma, dokokin da Allah ya ba wa Isra’ilawa sun fi waɗannan amfani sosai. Ban da wannan ma, akwai wasu abubuwa da suka nuna cewa Allah yana kula da mata.

Dokoki da Suka Bayyana Ra’ayin Allah Game da Mata

Dokokin Allah sun amfane Isra’ilawa maza da mata a dukan fannoni na rayuwa. Dokokin sun inganta rayuwarsu kuma sun sa Isra’ilawa sun kasance da ɗabi’a mai kyau da kuma dangantaka mai kyau da Jehobah. Idan sun kiyaye dokokin, sai Allah ya ‘ɗaukaka su bisa dukan al’umman duniya.’ (Kubawar Shari’a 28:1, 2) Mene ne dokokin suka ce game da mata? Ka yi la’akari da bayanin da ke gaba.

1. ’Yancin kai. Matan Isra’ilawa sun samu ’yanci sosai fiye da mata da suke wasu al’ummai a zamaninsu. Ko da yake maza ne aka ba wa hakkin kula da iyali, matan za su iya ‘lura da gona da kyau, sa’an nan su saya kuma su dasa gonar anab’ da yardar maigidan. Idan matar aure ta iya kaɗi da saka, tana iya yin kasuwanci. (Misalai 31:11, 16-19) A cikin dokokin da aka ba wa Isra’ilawa, an ba wa mata ’yancin yin wasu abubuwa.

Mata suna da ’yancin ƙulla dangantaka da Allah. Littafi Mai Tsarki ya ba da misalin Hannatu wadda ta yi addu’a kuma ta yi wa Allah alkawari. (1 Samuila 1:11, 24-28) Wata mace a birnin Shunem takan je wurin annabi Elisha a ranar Assabaci don neman shawara. (2 Sarakuna 4:22-25) Allah ya sa mata kamar su Deborah da Huldah su yi hidima a matsayin wakilansa. Har sanannun maza da firistoci ma sukan je wurin su don neman shawara.—Alƙalawa 4:4-8; 2 Sarakuna 22:14-16, 20.

2. Neman ilimi. Tun da yake dokokin da Allah ya ba wa Isra’ila sun shafe mata, a kan gayyaci mata su yi sauraro sa’ad da ake karanta dokokin don su ma su ƙara iliminsu. (Kubawar Shari’a 31:12; Nehemiya 8:2, 8) Ana kuma koyar da mata don yin wasu abubuwa a wuraren ibada. Alal misali, wataƙila wasu mata sun yi “hidima” a mazauni, wasu kuma sun yi waƙoƙi.—Fitowa 38:8; 1 Labarbaru 25:5, 6.

Mata da yawa sun ƙware wajen kasuwanci. (Misalai 31:24) Akasin mutanen wasu ƙasashe a dā da mahaifi ne kaɗai yake tarbiyyar da ’ya’ya maza, mahaifiya a ƙasar Isra’ila za ta iya tarbiyyar da ɗanta. (Misalai 31:1) Hakika, ana koyar da mata a ƙasar Isra’ila.

3. An ba su girma da kuma daraja. A cikin Dokoki Goma, Allah ya bayyana dalla-dalla cewa: “Ka bada girma ga ubanka da uwarka.” (Fitowa 20:12) Haka ma Sarki Sulemanu mai hikima ya ce: “Ɗana, ka ji koyarwar ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yarda ita.”—Misalai 1:8.

Dokokin sun nuna yadda ya dace maza marasa aure su bi da mata marasa aure don su daraja su. (Levitikus 18:6, 9; Kubawar Shari’a 22:25, 26) Maigidan kirki ya kamata ya san kasawar matarsa don yadda aka halicce ta.—Levitikus 18:19.

4. Ana kāre hakkinsu. A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya kwatanta kansa a matsayin ‘uban marayu kuma mai yin shari’a domin gwamraye.’ Ma’ana, yana kula da waɗanda ba su da mahaifi da kuma mata da ba su da maza da za su kāre hakkinsu. (Zabura 68:5; Kubawar Shari’a 10:17, 18) Shi ya sa sa’ad da mutumin da yake bin matar wani annabin da ya mutu bashi ya wulakanta ta, Jehobah ya sa annabinsa ya yi mu’ujiza don ta biya bashin kuma ta kāre mutuncinta.—2 Sarakuna 4:1-7.

Sa’ad da Isra’ilawa suna jeji, wato, kafin su shiga Ƙasar Alkawari, wani Ba’isra’ile mai suna Zelophehad ya mutu bai haifi ɗa namiji da zai gaje shi ba. Duk da haka, ’ya’yan Zelophehad waɗanda mata ne zalla, sun roƙi Musa ya ba su “gādo” a Ƙasar Alkawari. Allah ya sa an ba su abin da ya fi wanda suka roƙa. Ya gaya wa Musa cewa: “Ka ba su rabo na gādo cikin ‘yan’uwan ubansu; ka sa gādon ubansu kuma ya zama nasu.” Daga wannan lokacin, ’ya’ya mata a ƙasar Isra’ila suka fara cin gādo har su bar wa yaransu gādon.—Littafin Lissafi 27:1-8.

An Ɓata Dokar Allah Game da Mata

A cikin dokokin da Allah ya ba da ta hannun Musa, an ɗauki mata da mutunci kuma an ba su hakkinsu. Amma daga ƙarni na huɗu kafin zamanin Kristi, sai mabiya addinin Yahudawa suka soma amincewa da al’adun Helenawa da ke sa a wulaƙanta mata.—Ka duba akwatin nan “Yadda Littattafai na Dā Suka Sa Mutane Nuna wa Mata Wariya.”

Alal misali, wani mawaƙi Baheleni mai suna Hesiod, wanda ya yi rayuwa fiye da shekaru 2000 da suka shige, ya ce mata ne suka jawo dukan matsalolin da mutane suke fuskanta. A wannan lokacin ne koyarwar ta shiga addinin Yahudawa. Wani littafin al’adar Yahudawa mai suna Talmud da aka wallafa sama da shekaru 1800 da suka shige ya gargaɗi maza cewa: “Kada su cika yin taɗi da mata don hakan zai kai su ga yin lalata.”

Tun daga lokacin nan ne Yahudawa suka soma bin wannan ra’ayin. Kafin zamanin Yesu, an keɓe wani ɓangare a cikin haikali, kuma nan ne kawai ake barin mata su shiga don su yi bauta. Maza ne kawai suke samun ilimin addini, kuma yana yiwuwa cewa ana saka mata a wuri dabam da maza a cikin majami’a. Littafin ya yi ƙaulin wani malamin Yahudawa yana cewa: “Duk wanda ya koya wa ’yarsa abin da ke cikin Attaura, wato, dokokin da Allah ya ba da ta hannun Musa, lalaci yake koya mata.” Ta wajen murɗe ra’ayin Allah, shugabannin addinin Yahudawa sun sa maza da yawa su rena wa mata.

A lokacin da Yesu yake duniya, ya lura da yadda al’ada ta sa ake nuna wa mata wariya. (Matta 15:6, 9; 26:7-11) Waɗannan koyarwar sun sa Yesu ya rena wa mata ne? Mene ne za mu iya koya daga yadda ya bi da mata? Koyarwar Kiristanci na gaskiya ya kawo wa mata kwanciyar hankali ne? Talifin da ke gaba zai ba da amsoshin waɗannan tambayoyin.

[Akwati a shafi na 7]

Yadda Littattafai na Dā Suka Sa Mutane Nuna wa Mata Wariya

Tun shekaru sama da 1900 da suka shige, marubuta kamar su Philo ɗan ƙasar Alexandria ya soma bayyana labarin Adamu da Hawa’u bisa ga ra’ayin falsafar Helenawa. A rubutunsa, ya ce jima’i ne zunubin da Hawa’u ta yi shi ya sa ta “rasa ’yancinta kuma maigidanta ya mallake ta.” Hakan ya sa ’yan addinin Yahudawa suka ƙara nuna wa mata wariya kuma limaman cocin lokacin suka yaɗa wannan mummunar ra’ayi game da mata a littattafansu.

Wani malamin Yahudawa ya bayyana a cikin wani rubutu da ake kira Midrash Rabba cewa mata su riƙa yafa gyale don mace tamkar mai laifi ce, saboda haka, ya kamata ta riƙa kunyar jama’a. Wani ɗan tauhidi, marubuci wanda littattafansa suka yi farin jini shekaru sama da 1800 da suka shige ya ce mata su riƙa “baƙin ciki da nadama kamar Hawa’u.” Irin waɗannan ra’ayoyin sun daɗa sa mutane nuna wa mata wariya kuma an ɗauka cewa Littafi Mai Tsarki ne tushensu. Amma a gaskiya, ba Littafi Mai Tsarki ba ne tushen waɗannan ra’ayoyin.

[Hoto a shafi na 5]

Allah ya halicci Hawa’u don ta zama mataimakiyar Adamu

[Hoto a shafi na 6]

Mata a zamanin Isra’ilawa na dā sun yi harkar kasuwanci

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba