Yesu Ya Kafa Misali Na Tawali’u
“Na yi muku kwatanci, domin ku kuma ku yi kamar yadda na yi muku.”—YOH. 13:15.
MECE CE AMSARKA?
Ta yaya ne Yesu ya nuna tawali’u tun yana sama?
Ta yaya Yesu ya nuna tawali’u sa’ad da yake duniya?
Waɗanne albarka ne aka samu domin Yesu ya kasance da tawali’u?
1, 2. Wane darasi ne Yesu ya koya wa manzanninsa a daren da aka kashe shi?
A DAREN da aka kashe Yesu, ya kasance tare da manzaninsa a wani gidan bene a Urushalima. Sa’ad da suke cin abinci, sai Yesu ya tashi ya tuɓe mayafinsa, ya ɗauko ɗan zane ya yi ɗamara da shi. Ya sa ruwa a cikin tasa ya soma wanke sawayen almajiransa kuma ya share su da zanen. Bayan haka, sai ya yafa mayafinsa. Me ya sa Yesu ya yi wannan aikin?—Yoh. 13:3-5.
2 Yesu da kansa ya bayyana: “Kun san abin da na yi muku? . . . Idan fa ni, Ubangiji da Malami, na wanki sawayenku, ya kamata ku kuma ku wanki na juna. Gama na yi muku kwatanci, domin ku kuma ku yi kamar yadda na yi muku.” (Yoh. 13:12-15) Ta wajen kasancewa a shirye ya yi wannan aikin, Yesu ya koya wa manzanninsa darasi da za su riƙa tunawa kuma hakan zai ƙarfafa su su zama masu tawali’u.
3. (a) Ta yaya Yesu ya nanata muhimmancin tawali’u? (b) Mene ne za a tattauna a wannan talifin?
3 Wannan daren ba lokaci na farko ba ne, da Yesu ya koya musu amfanin zama masu tawali’u. Akwai wani lokacin da manzanninsa suka yi musu game da wanda ya fi girma. Sai Yesu ya jawo ƙaramin yaro kusa da shi, kuma ya gaya musu: “Dukan wanda ya karɓi ɗan ƙaramin yaron nan a cikin sunana, ni ya ke karɓa: kuma dukan wanda ya karɓe ni, yana karɓan wanda ya aiko ni: gama wanda shi ke ƙanƙani a cikinku duka, shi ne babba.” (Luk 9:46-48) Tun da yake Yesu ya san cewa Farisawa suna son girma, sai ya ce musu: “Dukan wanda ya ɗaukaka kansa za a ƙasƙantadda shi; wanda ya ƙasƙantadda kansa kuwa za a ɗaukaka shi.” (Luk 14:11) Yesu ba ya son mabiyansa su zama masu fahariya da girman kai. Za mu bincika misalin da Yesu ya kafa mana a batun tawali’u domin mu yi koyi da shi. Za mu kuma ga yadda wannan halin zai taimaka mana da kuma wasu.
“BAN KUWA BADA BAYA BA”
4. Ta yaya Yesu ya kasance da tawali’u kafin ya zo duniya?
4 Yesu mai tawali’u ne tun kafin ya zo duniya. Ya kasance tare da Ubansa a sama shekaru da yawa. Littafin Ishaya ya kwatanta dangantaka na kud da kud da ke tsakanin Ɗan da Ubansa cewa: “Ubangiji Yahweh ya ba ni harshe na koyayyun mutane, domin in san yadda zan tokare da magana wanda ya gaji: safiya kan safiya ya kan tashe ni, ya kan farkarda kunnena domin in ji kamar koyayyun mutane. Ubangiji Yahweh ya buɗe kunnena, ban yi tayarwa ba, ban kuwa bada baya ba.” (Isha. 50:4, 5) Ɗan Allah ya kasance da tawali’u kuma ya mai da hankali ga abin da Jehobah ya koya masa. Yana ɗokin koyan abubuwa daga Allah na gaskiya. Babu shakka, ya lura da yadda Jehobah ya yi wa ’yan Adam masu zunubi jin ƙai.
5. Ta yaya Yesu ya nuna tawali’u da filako sa’ad da ya yi jayayya da Iblis?
5 Ba dukan mala’iku ne suka kasance da tawali’u kamar Yesu ba. Maimakon Shaiɗan Iblis ya yi koyi da Jehobah, ya zama mai fahariya da girman kai kuma ya yi tawaye da Jehobah. Yesu ya gamsu da matsayinsa a sama kuma ya yi amfani da ikonsa yadda ya dace. Yesu ne shugaban mala’iku, duk da haka, bai wuce gona da irin ba sa’ad da ‘ya yi gardama da Shaiɗan a kan jikin Musa’ ba. Maimakon hakan, ya kasance da tawali’u da kuma filako. Jehobah ne Alƙali mafi girma, kuma Yesu ya yi farin cikin barin ya warware al’amura a lokacin da ya dace.—Karanta Yahuda 9.
6. Ta yaya Yesu ya nuna tawali’u ta wajen yarda ya zama Almasihu?
6 Sa’ad da Yesu yake sama, ya san dukan abin da aka annabta za su same shi a matsayin Almasihu. Saboda haka, wataƙila ya san cewa zai sha azaba sosai. Duk da haka, Yesu ya yarda ya zo duniya kuma ya mutu a matsayin Almasihu da aka yi alkawarinsa. Me ya sa? Manzo Bulus ya nuna cewa Yesu mai tawali’u ne, sa’ad da ya ce: “Da ya ke cikin surar Allah, ba ya maida kasancewarsa daidai da Allah abin raini ba, amma ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa, yana kasancewa da sifar mutane.”—Filib. 2:6, 7.
“YA ƘASƘANTAR DA KANSA” SA’AD DA YAKE DUNIYA
7, 8. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya kasance da tawali’u sa’ad da yake yaro da kuma hidima a duniya?
7 Manzo Bulus ya ce: “Da aka iske shi [Yesu] cikin kamanin mutum, ya ƙasƙantar da kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa, i, har mutuwa ta giciye.” (Filib. 2:8) Yesu ya kasance da tawali’u tuna yana yaro. Ko da yake Yusufu da Maryamu ajizai ne, Yesu ya ci gaba da yi musu “biyayya.” (Luk 2:51) Yesu ya kafa wa matasa misali mai kyau, kuma Allah zai albarkace su idan sun yi wa iyayensu biyayya.
8 Sa’ad da Yesu ya yi girma, ya kasance da tawali’u ta wajen sa nufin Jehobah ya fi muhimmanci a gare shi. (Yoh. 4:34) Sa’ad da yake hidima a duniya, ya yi amfani da sunan Allah kuma ya taimaka wa mutane su koya game da halayen Jehobah da kuma nufe-nufensa ga ’yan Adam. Yesu ya yi rayuwa da ta jitu da abin da ya koya wa mutane game da Jehobah. Alal misali, sa’ad da ya koya wa mutane yin addu’a, abu na farko da ya ce shi ne: ‘Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.’ (Mat. 6:9) Ta yin haka, ya koya wa mabiyansa cewa tsarkake sunan Jehobah ne ya fi muhimmanci. Shi da kansa ya yi hakan. Sa’ad da Yesu ya kusan barin duniya, ya yi addu’a ga Jehobah. Ya ce: “Na kuma sanar masu [manzannin] da sunanka, zan kuma sanarda shi.” (Yoh. 17:26) Bugu da ƙari, a lokacin da yake hidima a duniya, ya yaba wa Jehobah don abubuwan da ya cim ma a duniya.—Yoh. 5:19.
9. Wane annabci ne Zakariya ya yi game da Almasihu, kuma yaya Yesu ya cika wannan annabcin?
9 Zakariya ya annabta game da Almasihu cewa: “Ki yi murna sarai, ya ɗiyar Sihiyona; ki yi sowa, ya ɗiyar Urushalima; ga sarkinki, yana zuwa wurinki; mai-adilci ne shi, mai-nasara ne kuwa; mai-tawali’u, haye a kan jaki, a kan aholakin jaki.” (Zech. 9:9) Wannan annabcin ya cika sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima kafin Idin Ketarewa na shekara ta 33. Taron jama’a suka shimfiɗa mayafansu a ƙasa kuma suka saka ganyayen dabino a kan hanya. Mutanen sun yi farin ciki sa’ad da yake shigan birnin. Yesu ya kasance da tawali’u sa’ad da mutanen suke yabonsa a matsayin Sarki.—Mat. 21:4-11.
10. Mene ne Yesu ya nuna da yake ya kasance da aminci har mutuwa?
10 Yesu Kristi ya kasance da tawali’u kuma ya yi biyayya har mutuwarsa a kan gungumen azaba. Ta hakan, ya nuna cewa ’yan Adam za su iya kasancewa da aminci ga Jehobah ko idan sun fuskanci gwaji mai tsanani. Yesu ya kuma ƙaryata Shaiɗan wanda ya ce ’yan Adam suna bauta wa Jehobah don abubuwa da ya ba su. (Ayu. 1:9-11; 2:4) Yadda Kristi ya kasance da aminci sosai ya nuna cewa yana goyon baya Jehobah a matsayin Maɗaukakin Sarki. Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya ga cewa Ɗansa mai tawali’u ya kasance da aminci.—Karanta Misalai 27:11.
11. Wace dama ce mutuwar Yesu ta ba mutane masu aminci?
11 Yesu ya mutu a kan gungumen azaba, kuma ta hakan, ya fanshi ’yan Adam. (Mat. 20:28) Wannan ya ba ’yan Adam ajizai damar yin rayuwa har abada kuma ya sa su zama masu adalci. Bulus ya ce: ‘Ta wurin aiki guda ɗaya mai-adalci, kyautar ta zo ga dukan mutane zuwa kuɓutar rai.’ (Rom. 5:18) Mutuwar Yesu ta ba Kiristoci shafaffu zarafin yin rayuwa a sama, “waɗansu tumaki” kuma za su rayu har abada a duniya.—Yoh. 10:16; Rom. 8:16, 17.
NI “MAI-ƘASƘANTAR ZUCIYA” NE
12. Yaya Yesu ya nuna sauƙin kai da kuma tawali’u a sha’aninsa da mutane?
12 Yesu ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.” (Mat. 11:28, 29) Yesu mai tawali’u ne da kuma ƙasƙantar zuciya, shi ya sa ya bi da mutane ajizai cikin jin ƙai kuma bai nuna wariya ba. Bai bukaci almajiransa su yi abin da ya fi ƙarfinsu ba. Yesu ya ƙarfafa su. Bai rena su ba, kuma bai bi da su kamar bayi ba. Maimakon haka, Yesu ya nuna musu cewa za su sami hutawa idan suka kusace shi kuma suka yi biyayya da shi, domin karkiyarsa mai sauƙi ce kuma kayansa ba nauyi. Dukan mutane sun saki jiki sa’ad da suke tare da shi.—Mat. 11:30.
13. Ta yaya Yesu ya nuna juyayi ga talakawa?
13 Yesu ya nuna juyayi ga talakawan da ke Isra’ila kuma ya taimaka musu. Akwai wani lokacin da yake kusa da Yariko, sai ya haɗu da wani makaho maroƙi mai suna Bartimawas da abokinsa. Sun yi ta roƙon Yesu ya taimaka musu, amma mutane suka ce su yi tsit. Shin Yesu ya yi wa waɗannan maroƙan kunnen uwar shegu? A’a. Yesu ya ce a kawo su, kuma cike da juyayi ya buɗe idanunsu. Hakika, Yesu ya yi koyi da Ubansa Jehobah ta wajen nuna tawali’u da kuma jin ƙai ga masu zunubi.—Mat. 20:29-34; Mar. 10:46-52.
ZA A ƊAUKAKA “DUKAN WANDA YA ƘASƘANTAR DA KANSA”
14. Waɗanne amfani ne aka samu domin Yesu ya kasance da tawali’u?
14 Tawali’u da Yesu ya nuna ya kawo farin ciki da kuma albarka ga mutane da yawa. Jehobah ya yi farin ciki domin Ɗansa ya kasance da aminci. Manzanni da kuma almajiransa sun samu wartsakewa domin Yesu mai tawali’u ne. Misalin da Yesu ya kafa da koyarwarsa da kuma yadda ya ƙarfafa su ya taimake su su kyautata dangantakarsu da Jehobah. Yesu ya koyar da mutane da yawa, ya ƙarfafa su kuma ya biya bukatunsu. Tabbas, za a albarkaci dukan masu imani ga hadayar fansa na Yesu.
15. Ta yaya Yesu ya amfana domin shi mai tawali’u ne?
15 Shin, Yesu ma ya amfana daga tawali’unsa kuwa? Ƙwarai kuwa. Shi ya sa ya ce wa almajiransa: “Dukan wanda ya ƙasƙantar da kansa kuwa za ya ɗaukaka.” (Mat. 23:12) Bulus ya gaya mana cewa abin da ya faru da Yesu ke nan. Ya ce: “Allah kuma ya ba shi [Yesu] mafificiyar ɗaukaka, ya ba shi suna wanda ke bisa kowane suna; domin cikin sunan Yesu kowace gwiwa ta rusuna, ta cikin sama da ta kan duniya da ta ƙarƙashin duniya, kowane harshe kuma shi shaida Yesu Kristi Ubangiji ne, zuwa darajar Allah Uba.” Domin Yesu ya kasance da tawali’u da kuma aminci, Jehobah ya ɗaukaka shi ta wajen naɗa shi bisa dukan halittun da ke cikin sama da kuma duniya.—Filib. 2:9-11.
YESU ZAI “TSARE GASKIYA DA ADALCI”
16. Mene ne ya nuna cewa Yesu ba zai daina kasancewa da tawali’u ba?
16 Yesu zai ci gaba da kasancewa da tawali’u. Wani marubucin zabura ya bayyana yadda Yesu zai halaka maƙiyan Allah sa’ad da yake sarauta a sama. Ya ce: “A cikin ɗaukakarka kuma ka hau ka yi tafiya da albarka, domin gudunmuwar gaskiya da tawali’u da adalci.” (Zab. 45:4) A yaƙin Armageddon, Yesu zai kāre masu tawali’u da adalci da kuma masu son gaskiya. Kuma mene ne zai faru a ƙarshen Sarautar Yesu na Shekara Dubu, “sa’anda ya rigaya ya kawarda dukan hukunci, da dukan sarauta, da dukan iko”? Yesu zai nuna tawali’u ta wajen “bada mulki ga Allah, Uba.”—Karanta 1 Korintiyawa 15:24-28.
17, 18. (a) Me ya sa yake da muhimmanci bayin Jehobah su zama masu tawali’u kamar Yesu? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
17 Mu kuma fa? Shin za mu zama masu tawali’u kamar Yesu? Masu tawali’u da adalci ne kaɗai Yesu zai ceta a yaƙin Armageddon. Saboda haka, dole ne mu kasance da tawali’u. Tawali’u da Yesu ya nuna ya amfane shi da kuma wasu. Hakazalika, za mu amfani kanmu da kuma wasu idan muka kasance da tawali’u.
18 Mene ne zai taimaka mana mu zama masu tawali’u kamar Yesu? Mene ne zai taimaka mana mu nuna tawali’u duk da ƙalubalen da za mu fuskanta? Za a amsa waɗannan tambayoyi a talifi na gaba.
[Hotona a shafi na 12]
Ta yaya za mu amfana daga tawali’un da Yesu ya nuna?
[Hoto a shafi na 13]
Ya kamata mu yi koyi da jin ƙan da Yesu ya nuna