Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 3/1 p. 7
  • Shi “Allah na . . . Masu Rai” Ne

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shi “Allah na . . . Masu Rai” Ne
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Tashin Matattu —Koyarwa Da Ta Shafe Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Allah Ya Gwada Bangaskiyar Ibrahim
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • An Gwada Bangaskiyarsa
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 3/1 p. 7

KA KUSACI ALLAH

Shi “Allah na . . . Masu Rai” Ne

Shin, mutuwa ta fi ƙarfin Allah ne? A’a! Yaya za a ce mutuwa ko wani “maƙiyi” dabam ya fi ƙarfin “Allah” Maɗaukakin Sarki? (1 Korintiyawa 15:26; Fitowa 6:3) Allah yana da iko ya kawar da mutuwa kuma ya yi alkawari cewa zai yi hakan ta wajen ta da matattu a sabuwar duniya.a Za mu iya dogara ga wannan alkawarin kuwa? Hakika. Ta furucin da ya yi, Ɗan Allah, Yesu, ya tabbatar mana cewa za mu iya dogara ga wannan alkawarin.—Ka karanta Matta 22:31, 32.

Sa’ad da Yesu yake magana da Sadukiyawa, waɗanda ba su gaskata da tashin matattu ba, ya ce: “Amma ga zancen tashin matattu, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya faɗa maku ba, cewa, Ni Allah na Ibrahim ne, Allah na Ishaku, Allah na Yaƙub kuma? Allah ba Allah na matattu ba ne, amma na masu-rai” ne. A nan, Yesu yana magana ne game da tattaunawar da Allah ya yi da Musa a kurmi mai cin wuta a shekara ta 1514 kafin zamanin Kristi. (Fitowa 3:1-6) Yesu ya bayyana cewa waɗannan kalamin da Jehobah ya yi wa Musa cewa: “Ni Allah na Ibrahim ne, Allah na Ishaƙu, Allah na Yaƙub” sun nuna cewa alkawarin da Allah ya yi na ta da matattu zai cika tabbas. Ta yaya?

Ka yi la’akari da yanayin. A lokacin da Jehobah ya yi magana da Musa, su Ibrahim da Ishaku da Yakubu sun mutu da daɗewa. A lokacin, Ibrahim ya yi shekaru 329 da mutuwa, Ishaƙu kuma, shekaru 224, sa’an nan Yakubu ya yi shekara 197 da mutuwa. Duk da haka, Jehobah ya ce, “Ni ne” Allahnsu—bai ce, “a dā ni ne” Allahnsu ba. Jehobah ya yi magana game da waɗannan amintattun bayinsa kamar suna raye ne a lokacin. Me ya sa?

Yesu ya bayyana cewa: Jehobah ba “Allah na matattu ba ne, amma na masu-rai” ne. Ka yi tunani a kan waɗannan kalaman. Da a ce ba za a ta da matattu ba, da Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yakubu ba za su sake rayuwa a nan gaba ba, kuma hakan yana nufin cewa Jehobah Allah ne na matattu. Ƙari ga haka, zai zama cewa mutuwa ta fi ƙarfin Jehobah, wato, kamar ba shi da iko ya ta da amintattun bayinsa daga matattu.

Tun da hakan ba gaskiya ba ne, mene ne za mu ce game da Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu da kuma dukan amintattun bayin Jehobah da suka mutu? Yesu ya yi wannan tabbatacciyar magana: “Duka suna rayuwa gareshi.” (Luka 20:38) Hakika, alkawarin da Jehobah ya yi na ta da amintattun bayinsa zai cika tabbas shi ya sa yana musu ganin rayayyu. (Romawa 4:16, 17) Jehobah ba zai manta da su ba har sai lokaci ya yi da zai ta da su daga matattu.

Jehobah yana da ikon ta da matattu

Shin, kana sha’awar sake ganin ƙaunatattunka da suka mutu? Idan amsarka e ce, ka tuna cewa Jehobah ya fi ƙarfin mutuwa kuma yana da ikon ta da matattu. Ba abin da zai hana shi cika alkawarinsa na ta da waɗanda suka mutu. Babu shakka, za ka so ka ƙara koya game da wannan alkawarin da kuma Allahn da zai cika alkawarin. Yin hakan zai jawo ka kusa da Jehobah, “Allah na . . . masu rai.”

Karatun Littafi Mai Tsarki na Fabrairu-April

Matta 22–Luka 21

a Za ka sami ƙarin bayani game da alkawarin da Allah ya yi na tashin matattu a sabuwar duniya a babi na 7 na wannan littafin, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba