Ka Ci Gaba Da Fakewa A Cikin Kwarin Jehobah
“Ubangiji za ya . . . yi yaƙi da waɗannan al’ummai, kamar yadda ya yi a dā cikin ranar yaƙi.”—ZAK. 14:3.
1, 2. Wane yaƙi ne za a yi nan ba da daɗewa ba, kuma me za a bukaci bayin Allah su yi a wannan yaƙin?
A SHEKARA TA 1938, mutane da yawa a Amirka sun saurari wani shirye-shiryen rediyo. Sa’ad da ake shirye-shiryen, masu ba da labarin suka sanar cewa wasu halittu daga wata duniya a sararin sama da ake kira Mars za su shigo duniya, su kuma halaka ta. Mutane da yawa ba su san cewa wannan shirye-shiryen rediyo ne kawai ba. Sun yi zato cewa an soma yaƙi da gaske, kuma suka ji tsoro sosai. Wasu kuma sun ɗauki matakai don su kāre kansu daga wannan halakar.
2 Nan ba da daɗewa ba, za a yi yaƙi na gaske. Amma, mutane da yawa sun yi kunne uwar shegu ga wannan gargaɗin. Wannan ba tatsuniya ba ce. Yaƙin Armageddon ne, wato, yaƙin da Allah zai halaka miyagu da shi. Mun san cewa za a yi wannan yaƙin, domin Allah ya sanar mana da hakan a cikin Littafi Mai Tsarki. (R. Yoh. 16:14-16) Ba za mu bukaci saka hannu a wannan yaƙin ba. Amma, Jehobah zai yi amfani da ikonsa don ya cece mu a hanya mai ban al’ajabi.
3. Wane annabci ne za mu nazarta, kuma me ya sa yake da muhimmanci?
3 Akwai wani annabci a littafin Zakariya sura 14 da ya bayyana wannan yaƙin Armageddon dalla-dalla. Ko da yake an yi wannan annabcin shekara 2,500 da ta shige, amma ya shafe mu sosai a yau. (Rom. 15:4) Wannan annabcin ya ambata abubuwan da suka faru da bayin Jehobah tun daga lokacin da Yesu ya soma sarauta a sama a shekara ta 1914. Ya kuma bayyana abubuwan da za su faru nan ba da daɗewa ba. Wannan annabcin ya ambata wani “kwari mai girma” da kuma “ruwa mai-rai.” (Zak. 14:4, 8) A wannan talifin, za mu tattauna ma’anar wannan kwarin da kuma yadda zai iya kāre bayin Jehobah. Za mu kuma koya ma’anar ruwa mai-rai da yadda zai amfane mu. Hakan zai nuna mana muhimmancin shan wannan ruwan, kuma za mu so shan sa. Za mu soma tattauna wannan annabcin yanzu.—2 Bit. 1:19, 20.
‘RANAR JEHOBAH’ TA SOMA
4. (a) Yaushe ne “ranar Ubangiji” ta soma? (b) Shafaffu sun yi wa’azi game da me kafin shekara ta 1914, kuma mene ne ’yan siyasa da limamai suka yi?
4 Kalmomin farko na littafin Zakariya sura 14 sun ce: “Ranar Ubangiji tana zuwa.” (Karanta Zakariya 14:1, 2.) Mece ce wannan ranar? Ɗaya take da “ranar Ubangiji” wadda ta soma a shekara ta 1914, sa’ad da Yesu ya zama Sarkin Mulkin Allah a sama. (R. Yoh. 1:10; 11:15) Tun da daɗewa sosai, shafaffun Kiristoci sun yi wa’azi cewa ƙarshen “zamanan Al’ummai” zai zo a shekara ta 1914. Sun kuma sanar cewa daga lokacin, za a soma irin matsalolin da ba a taɓa yi ba a duniya. (Luk 21:24) Waɗanne matakai ne al’ummai suka ɗauka? Ba su ko kula ba. Maimakon haka, ’yan siyasa da limamai suka yi wa waɗannan Kiristocin ba’a kuma suka tsananta musu. Ta hakan, suna wa Allah Maɗaukaki ba’a, domin Kiristoci shafaffu suna wakiltar Mulkin Allah.—Ibran. 12:22, 28.
5, 6. (a) Mene ne maƙiyan bayin Allah suka yi? (b) Su waye ne sauran ‘mutane da ba za a raba su da birnin ba’?
5 Zakariya ya faɗi abin da al’ummai za su yi. Ya ce: ‘Za a ci birnin.’ “Birnin” Urushalima ne, kuma yana wakiltar Mulkin Allah. Shafaffun Kiristoci da ke duniya har yanzu, suna cikin sashen wannan Mulkin. (Filib. 3:20) An “ci birnin” a lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, sa’ad da aka jefa ’yan’uwan da ke da gata a ƙungiyar Jehobah cikin kurkuku a birnin Atlanta, Georgia, a Amirka. Maƙiya sun ci zalin Kiristoci shafaffu, sun hana su buga littattafai, kuma sun nemi su hana su yin wa’azi. Hakan ya yi kamar maƙiya sun “washe” gidajen da ke birnin.
6 Ko da yake maƙiya sun tsananta wa bayin Allah kuma sun tabka ƙarya game da su, amma ba su iya halaka bauta ta gaskiya ba. Akwai Kiristoci shafaffu da suka kasance da aminci. Kamar yadda Zakariya ya ce, su ne sauran ‘mutane da ba za a raba su da birnin ba.’
7. Wane misali ne Kiristoci shafaffu suka kafa mana a yau?
7 Shin wannan annabcin ya cika bayan Yaƙin Duniya na ɗaya ne? A’a. Domin sun ci gaba da zaluntar waɗannan Kiristoci shafaffu da kuma abokansu masu aminci da suke da begen zama a duniya. (R. Yoh. 12:17) Alal misali, an tsananta wa ’yan’uwa sosai a lokacin Yaƙin Duniya na biyu. Yadda ’yan’uwa shafaffu suka kasance da aminci, ya ƙarfafa bayin Allah a yau su jimre da duk gwajin da suke fuskanta daga danginsu da ba Shaidu ba ko abokan aiki ko kuma abokan makaranta da suke musu ba’a don imaninsu. (1 Bit. 1:6, 7) A duk inda suke zama, bayin Jehobah sun ƙudura niyya su ɗage “cikin ruhu ɗaya,” kuma ba za su ‘firgita ba ko kaɗan saboda magabtansu.’ (Filib. 1:27, 28) To, a ina ne mutanen Jehobah za su samu mafaka a cikin duniya da ta tsane su?—Yoh. 15:17-19.
JEHOBAH YA KAFA “KWARI MAI GIRMA” SOSAI
8. (a) A cikin Littafi Mai Tsarki, mene ne duwatsu suke wakilta a wasu lokatai? (b) Mene ne “dutsen zaitun” yake wakilta?
8 Mun koya a cikin wannan annabcin cewa, “birni” ko kuma Urushalima yana wakiltar Mulkin Allah. To, mene ne “dutsen zaitun” yake wakilta? Ta yaya zai “rabu a tsaka” kuma ya zama tuddai biyu? Me ya sa Jehobah ya kira su “duwatsuna”? (Karanta Zakariya 14:3-5.) A cikin Littafi Mai Tsarki, duwatsu suna wakiltar mulkoki ko gwamnatoci a wasu lokatai. Sau da yawa, Littafi Mai Tsarki yakan ce ana samun albarka da kāriya daga dutsen Allah. (Zab. 72:3; Isha. 25:6, 7) Saboda haka, dutsen zaitun yana wakiltar yadda Jehobah yake sarautar halittunsa.
9. Mene ne yake nufi cewa “dutsen zaitun” ya rabu a tsakiya?
9 Mene ne yake nufi cewa dutsen zaitun ya rabu a tsakiya? Yana nufin cewa Jehobah ya kafa wata sarauta don wata manufa ta musamman. Wannan gwamnati ta Allah ce, amma Yesu Kristi ne Sarkin. Tun da yake gwamnatin na Jehobah ne, ya kira duwatsu biyun “duwatsuna.”—Zech. 14:4.
10. Mene ne “kwari mai girma” da ke tsakanin duwatsun yake nufi?
10 Annabcin ya ce sa’ad da dutsen ya rabu, gefe ɗaya ya yi ta arewa, gefe ɗaya kuma ya yi ta yamma. Kuma, sawayen Jehobah sun tsaya a kan kowanne. Wannan rabuwar ta sa aka samu “kwari mai girma” a ƙarƙashin sawayen Jehobah. Wannan kwarin alama ce na kāriya daga Jehobah. Kamar yadda mutane sukan sami kāriya sa’ad da suka shiga kwari, haka nan ma bayin Jehobah suke samun kāriya a ƙarƙashin mulkinsa da na ɗansa. Jehobah ba zai taɓa ƙyale a kawar da bauta ta gaskiya ba. Yaushe ne aka raɓa dutsen zaitun? Hakan ya faru ne sa’ad da Yesu ya soma sarauta a sama, a shekara ta 1914. Annabcin ya kuma ce mutanen Jehobah za su gudu su shiga cikin “kwari mai girma.” A wane lokaci ne suka soma yin hakan?
AN SOMA GUDU ZUWA KWARIN
11, 12. (a) A wane lokaci ne mutanen Allah suka soma shiga kwarin? (b) Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana kāre mutanensa?
11 Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi: “Za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana.” (Mat. 24:9) Al’ummai sun tsane su sosai, tun daga somawar kwanaki na ƙarshe a shekara ta 1914. A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, magabta sun tsananta wa Kiristoci shafaffu masu aminci sosai, amma ba su iya kawar da bauta ta gaskiya ba. A shekara ta 1919, mutanen Allah sun sami ’yanci daga addinin ƙarya, wato, Babila Babba. (R. Yoh. 11:11, 12)a A wannan shekarar ce mutanen Allah suka soma gudu zuwa kwarin.
12 Tun daga shekara ta 1919, Jehobah ya ci gaba da kāre masu bauta masa a faɗin duniya. A cikin shekaru da yawa yanzu, gwamnatoci masu yawa sun ƙoƙarta su sa Shaidun Jehobah su daina yin wa’azi ko kuma hana su rarraba littattafansu. Har ila, hakan yana faruwa a wasu ƙasashe. Amma, Jehobah bai ƙyale su su kawar da bauta ta gaskiya ba. Ko da mene ne gwamnatoci za su yi don su hana aikin, Jehobah zai ci gaba da yin amfani da ikonsa don ya kāre mutanensa.—K. Sha 11:2.
13. Ta yaya za mu fake a cikin kwarin Jehobah, kuma me ya sa ya fi muhimmanci mu yi hakan yanzu?
13 Jehobah zai ci gaba da kāre mu idan muka kasance da aminci a gare shi. Shi da Ɗansa ba za su ƙyale kowa ko kuma wani abu ya fitar da mu daga kwarinsa ba. (Yoh. 10:28, 29) Jehobah yana taimaka mana mu miƙa kai ga sarautarsa da kuma na Ɗansa. Za mu bukaci taimakonsa sosai a lokacin ƙunci mai girma da ke nan tafe. Saboda haka, ya fi muhimmanci yanzu mu ci gaba da fakewa a cikin kwarin Jehobah.
“RANAR YAƘI” TA KAI
14, 15. Mene ne zai faru da waɗanda ba su fake a cikin kwarin Jehobah ba, a ranar da zai halaka magabtansa?
14 Yayin da ƙarshen wannan zamanin yake kusatowa, Shaiɗan zai daɗa tsananta wa mutanen Allah. Amma nan ba da daɗewa ba, Shaiɗan zai kai harinsa na ƙarshe. A ranar, Allah zai yaƙi dukan magabtan bayinsa, kuma ya halaka su. Wannan yaƙin zai nuna cewa Jehobah ne Mayaƙi da ya fi iko.—Zak. 14:3.
15 Mene ne zai faru da waɗanda ba su fake a cikin kwarin Jehobah ba a ranar da zai halaka dukan magabtansa? Annabcin ya ce ba za su samu “haske” na Allah ba. Hakan yana nufin cewa ba za su samu tagomashin Allah ba. Annabcin ya ci gaba da cewa “doki, da alfadari, da raƙumi, da jaki, da dukan dabbobin” za su ƙandare. Hakan yana nufin cewa makaman da za a yi amfani da su a yaƙi za su daskare, wato, ba za su kasance da amfani ba. Jehobah zai kuma yi amfani da cuta da “annoba.” Idanunsu da kuma harshensu za su “ruɓe.” Ba mu san ko hakan zai faru a zahiri ba. Amma, mun san cewa ba za su iya kawo mana hari ba ko kuma su yi maganar banza game da Allah. (Zak. 14:6, 7, 12, 15) Dukan sarakuna na duniya da sojojinsu za su goyi bayan Shaiɗan, amma za a halaka dukansu, a duk inda suke a duniya. (R. Yoh. 19:19-21) “A ran nan fa za a ga kisassun Ubangiji tun daga wannan iyakar duniya zuwa wannan iyaka.”—Irm. 25:32, 33.
16. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu, kuma mene ne ya kamata mu yi a lokacin ƙunci mai girma?
16 Mutane suna shan wahala sosai a lokacin yaƙi, har da waɗanda suka ci yaƙin ma. Mu ma muna iya shan wahala a lokacin ƙunci mai girma. Muna iya rashin abinci, ko kuma mu yi hasarar dukiyarmu. Ba za mu iya samun ’yancin da muke da shi yanzu ba. Mene ne za mu yi idan muka fuskanci waɗannan matsalolin? Za mu yi ta rawar jiki ne? Shin za mu yi sanyin gwiwa kuma mu fid da rai ne? Za mu daina bauta wa Jehobah ne? Wajibi ne mu fake a cikin kwarin Jehobah a lokacin ƙunci mai girma, ta wajen kasancewa da aminci a gareshi da kuma sa rai cewa zai kāre mu.—Karanta Habakkuk 3:17, 18.
“RUWA MAI-RAI ZA YA FITO”
17, 18. (a) Mene ne “ruwa mai-rai”? (b) Mene ne “tekun gabas” da “tekun yamma” suke wakilta? (c) Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?
17 Bayan yaƙin Armageddon, “ruwa mai-rai” zai ɓulɓulo a yalwace daga kursiyin Mulkin Almasihu. Wannan ruwa mai rai yana nufin dukan abubuwan da Allah ya ba ’yan Adam don su rayu har abada. “Teku na gabas” yana nufin tekun gishiri kuma yana wakiltar mutanen da suke cikin kabari, kuma za a ta da su daga matattu. “Teku na yamma” yana nufin Bahar Maliya da ke cike da abubuwa masu rai, kuma hakan yana wakiltar “taro mai-girma” da suka tsira daga yaƙin Armageddon. (Karanta Zakariya 14:8, 9; R. Yoh. 7:9-15) Dukansu za su sha “ruwa mai-rai” da ya ɓulɓulo daga “kogin ruwa na rai.” Hakan zai sa su zama kamiltattu kuma su rayu har abada.—R. Yoh. 22:1, 2.
18 Sa’ad da Jehobah ya halaka wannan zamanin, zai kāre mu kuma ya sa mu shiga cikin sabuwar duniyarsa ta adalci. Ko da yake dukan al’ummai na wannan duniyar sun tsane mu, amma mu ƙudura niyya cewa za mu kasance da aminci ga Mulkin Allah, kuma mu fake a cikin kwari na Jehobah.
a Ka duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax at Hand! shafuffuka na 169-170.